Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Wane ne ko Kuma Mene ne Iblis?

Wane ne ko Kuma Mene ne Iblis?

Wane ne ko kuma mene ne Iblis?

SHIN ZA KA CE Iblis . . .

  • Halitta ne na ruhu?

  • Muguntar da ke cikin zuciyar mutane?

  • Abin da mutane suke da’awa kawai?

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE

Iblis ya tattauna da Yesu kuma ya ‘jarabce’ shi. (Matta 4:​1-4) Saboda haka, Iblis ba muguntar da ke cikin zuciyar mutane ba ne ko kuma abin da mutane suke da’awa ba. Shi mugun halittar ruhu ne.

ME KUMA ZA MU IYA KOYA DAGA LITTAFI MAI TSARKI?

  • A dā, Iblis mala’ika ne mai aminci, amma bai “tsaya a kan gaskiya ba.” (Yohanna 8:44) Ya zama maƙaryaci kuma ya yi wa Allah tawaye.

  • Wasu mala’iku sun goyi bayan Shaiɗan.​—⁠Ru’ya ta Yohanna 12:9.

  • Iblis yana makantar da mutane da yawa don kada su san cewa ya wanzu da gaske.—2 Korinthians 4:4.

Iblis zai iya rinjayar mutane kuwa?

WASU SUN CE yana wa mutane rufa ido, wasu kuma suna tsoron faɗawa cikin hannun miyagun ruhohi. Mene ne ra’ayinka?

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE

‘Duniya duka tana hannun Mugun.’ (1 Yohanna 5: 19, Littafi Mai Tsarki) Iblis yana rinjayar mutane, amma hakan ba ya nufin cewa yana da iko a kan kowane ɗan Adam.

ME KUMA ZA MU IYA KOYA DAGA LITTAFI MAI TSARKI?

  • Iblis yana yaudarar mutane su yi nufinsa.—2 Korintiyawa 11:14.

  • A wasu lokuta, miyagun ruhohi suna iya shigan mutum kuma su sa su su yi nufinsu.—Matta 12:22.

  • Da taimakon Allah, za ka iya yin nasara wajen yin “tsayayya da Shaiɗan.”—Yaƙub 4:7.