Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 

Zama Mai Gaskiya Tsohon Yayi Ne?

Zama Mai Gaskiya Tsohon Yayi Ne?

Wani mai suna Hitoshi mai lissafin kuɗi ne a wani kamfani a ƙasar Jafan. A lokacin da suke lissafi da shugabansa, sai aka gaya masa ya yi wani maguɗi. Hitoshi ya ce ba zai iya yin hakan ba. A sakamakon haka, an kore shi daga aiki.

Hitoshi ya yi sanyin gwiwa sa’ad da ya yi watanni yana neman wani aiki. Alal misali, a wani wuri da ya je neman aiki, Hitoshi ya ambata cewa ba ya so ya yi aikin da ya ƙunshi yin maguɗi. Sai mutumin ya ce: “Wai kai daga ina ka fito ne?” Iyalin Hitoshi sun ƙarfafa shi ya yi tsayin daka a yin gaskiya, duk da haka, ya soma yin shakka. Har ma akwai lokacin da ya ce, “Anya, zama mai gaskiya yana da amfani kuwa?”

Labarin Hitoshi abin ban taƙaici ne domin ya nuna cewa mutane da yawa ba sa son gaskiya. Hakika, wasu za su iya gani cewa hakan cin baya ne musamman a inda ake kasuwanci. Wata mata da take aiki a Afirka ta Kudu ta ce: “Mutanen da muke aiki tare ba sa yin gaskiya, kuma a wasu lokuta suna iya matsa maka ka bi halinsu.”

Yin ƙarya wani fanni ne na rashin gaskiya da ya zama ruwan dare gama gari a duniya. A shekarun da suka shige, wani masani mai suna Robert S. Feldman da ke aiki a wata jami’a a jihar Massachusetts Amherst, ya yi binciken da ya nuna cewa mutane kashi sittin cikin ɗari suna yin ƙarya aƙalla sau ɗaya idan sun yi hirar da ta kai tsawon minti goma. Feldman ya ce: “Wannan adadin abin mamaki ne sosai. Ba mu zata yin ƙarya za ta ci kasuwa a duniya haka ba.” Shin ba abin mamaki ba ne cewa mutane ba sa so a yi musu ƙarya, duk da haka, su da kansu suna yin ƙarya?

Me ya sa yin ƙarya da sata da wasu halayen rashin gaskiya suka cika ko’ina a duniya? Ta yaya rashin gaskiya yake shafan mutane gabaki ɗaya? Mafi muhimmanci ma, ta yaya za mu guji zama masu rashin gaskiya?