HASUMIYAR TSARO—NA NAZARI Yuni 2019

Wannan fitowar tana dauke da talifofin nazari da za a yi daga ranar 5 ga Agusta–1 ga Satumba, 2019

‘Ku Lura Don Kada Wani Ya Kama Hankalinku’!

Shaidan ya kware sosai a yaudarar mutane. Ta yaya yake kokarin yaudarar mu kuma ya sa mu daina bauta wa Jehobah?

Mu Kawar da Kowane Ra’ayin da Ya Saba wa Na Allah!

Yadda aka rene mu da al’adarmu da kuma iliminmu suna shafan yadda muke tunani. Ta yaya za mu kawar da halayen da muke da su da ke da wuyan bari?

Ka Dogara ga Jehobah Sa’ad da Kake Cikin Damuwa

Yawan damuwa yana iya yi mana lahani sosai. Muna iya magance wannan matsalar da wajen yin la’akari da yadda Jehobah ya taimaka wa bayinsa su daina alhini a zamanin dā.

Ka Taimaka wa Mutane Su Jimre da Matsaloli

Lutu da Ayuba da kuma Naomi sun bauta wa Jehobah da aminci, amma sun fuskanci matsaloli a rayuwarsu. Me za mu iya koya daga labarinsu?

Yadda Za Mu Kāre Kanmu Daga Daya Cikin Dabarun Shaidan

Kallon batsa matsala ce babba da bayin Allah da yawa suke fuskanta. Ta yaya za mu guji wannan hali da bai dace ba?.

An “Warware” Wani Tsohon Littafi

A shekara ta 1970, masu tone-tonen kasa sun hako wani nadadden littafi da wuta ta kona a Isra’ila. Fasahar 3-D ta sa ya yiwu a warware littafin kuma a ga rubutun da ke cikinsa. Me aka gano a cikin littafin?