Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shin Kana Kin Mutane Don Yadda Suke?

Shin Kana Kin Mutane Don Yadda Suke?

WANI Mashaidi mai suna Don da yake zama a ƙasar Kanada ya yi ƙoƙari ya riƙa yi wa mutanen da suke zama a kan titi wa’azi. Ɗan’uwan ya ba da labarin wani, ya ce: “Akwai wani mutumin da yake zama a kan titi mai suna Peter kuma shi ne ya fi ƙazanta a kan titin. Ban da haka ma, akwai shi da masifa kuma ba ya son mutane su riƙa zuwa wurinsa. Ƙari ga haka, ba ya son mutane su taimaka masa.” Duk da haka, ɗan’uwa Don ya yi fiye da shekaru 14 yana ƙoƙari ya yi wa wannan mutumin alheri.

Wata rana Peter ya tambayi Don: “Kowa ya fita sha’anina, kai me ya sa kake damuwa da ni?” Ɗan’uwa Don ya yi amfani da nassosi guda uku don ya ratsa zuciyar Peter. Da farko ya tambayi Peter ko ya san cewa Allah yana da suna, bayan haka sai ya ce masa ya karanta littafin Zabura 83:18 don ya gani da kansa. Ban da haka ma, don ya nuna masa cewa ya damu da shi, ɗan’uwan ya karanta masa littafin Romawa 10:​13, 14 da suka ce “dukan wanda za ya kira bisa sunan Ubangiji za ya tsira.” A ƙarshe, ɗan’uwa Don ya karanta masa littafin Matta 9:36 kuma ya sake cewa Peter ya karanta da kansa, wannan ayar ta ce: “Amma sa’anda [Yesu] ya ga taron, ya yi juyayi a kansu, domin suna wahala, suna watse kuma, kamar tumakin da ba su da makiyayi.” Bayan haka, Peter ya ce da hawaye a idanunsa: “Ni ma ina cikin waɗannan tumakin?”

Sai Peter ya soma canja salon rayuwarsa, ya yi wanka kuma ya aske gemunsa. Ban da haka ma, ya saka kaya mai kyau da ɗan’uwa Don ya ba shi, kuma Peter ya ci gaba da kasancewa da tsabta.

Peter yana da wani littafin da ya raba sashe dabam-dabam inda ya rubuta abubuwan da suka faru a rayuwarsa. Abubuwan da ya rubuta da farko a cikin littafin na baƙin ciki ne, amma abubuwan da ya rubuta a ƙarshe ya yi dabam. A wani sashe ya rubuta: “Yau na koyi sunan Allah, yanzu zan iya yin addu’a ga Jehobah. Kuma ina farin cikin sanin sunansa. Mutumin nan Don ya faɗa mini cewa zan iya  zama aminin Jehobah, kuma zai saurare ni a duk inda nake ko kuma ko da mene ne nake gaya masa.”

Peter ya rubuta wasiƙar nan ga ’yan’uwansa cewa:

“Ba na jin daɗi yau, don na tsufa, amma ko da yau ne ranata ta ƙarshe, na san cewa zan sake ganin abokina [Don] a Aljanna. Idan kuna karanta wannan saƙo ku san cewa ba ni da rai. Amma a wurin jana’izata idan kuka ga wani mutumin da bai kamata ya zo wurin ba, ku yi masa magana kuma don Allah ku karanta masa littafin nan mai ruwan shuɗi. * Littafin ya bayyana min cewa zan sake ganin abokina a Aljanna, kuma na gaskata hakan da dukan zuciyata. Ɗan’uwanku Peter.

Bayan jana’izar, ’yar’uwar Peter mai suna Ummi ta ce: “Kusan shekara biyu da ta shige ya zo ya ziyarce ni, kuma yana farin ciki, na daɗe ban gan shi yana farin ciki kamar haka ba, har ma ya yi mini murmushi.” Ta gaya wa Don cewa: “Zan karanta littafi saboda abin da zai iya ratsa zuciyar ɗan’uwana, yana da muhimmanci sosai.” Ummi ta yarda cewa za ta yi nazarin littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? da wata Mashaidiyar Jehobah.

Mu ma bai kamata mu riƙa ƙin mutane saboda yadda suke ba, amma muna bukatar mu nuna musu ƙauna kuma mu yi haƙuri da su. (1 Tim. 2:​3, 4) Idan muna yin hakan, za mu iya sa mutane kamar Peter waɗanda mutane suke ƙyamarsu su canja salon rayuwarsu kuma su zama mutanen kirki. Ƙari ga haka, muna bukatar mu kasance da tabbaci cewa Allah da yake “duban zuciya” zai taimaka ma waɗanda suke so su koya game da shi su san shi.​—1 Sam. 16:7; Yoh. 6:44.

^ sakin layi na 7 Wato littafin nan “Gaskiya Mai Bishe Zuwa Rai Madauwami” da yake bayyana Littafi Mai Tsarki da aka ba shi shekaru da yawa da suke shige. Shaidun Jehobah ne suka wallafa, amma an daina bugawa.