Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shin Sasanta Rigima Zai Sa Ku Yi Zaman Lafiya?

Shin Sasanta Rigima Zai Sa Ku Yi Zaman Lafiya?

JEHOBAH ALLAH yana son Kiristoci su riƙa zaman lafiya da mutane. Zaman lafiya zai sa masu bauta masa su kasance da salama. Kuma hakan zai sa mutane da yawa da ba sa son rigima su soma bauta wa Jehobah.

Alal misali, wani sanannen boka a ƙasar Madagascar ya lura cewa Shaidun Jehobah suna da haɗin kai, sai ya ce, ‘Idan har zan soma bin wani addini, wannan ne zan bi.’ Da shigewar lokaci, ya daina bokanci, kuma ya yi aure bisa doka, sai ya soma bauta wa Jehobah, Allah na salama.

Kamar wannan mutum, mutane da yawa a kowace shekara suna zama Shaidun Jehobah don zaman lafiya da ake yi a cikin ikilisiya. Amma Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa tsananin “kishi” da son kai a cikin ikilisiya suna ɓata abokantaka kuma su jawo matsala. (Yaƙ. 3:​14-16) Duk da haka, a cikin Littafi Mai Tsarki za mu sami shawara mai kyau a kan yadda za mu guji waɗannan matsaloli kuma mu yi zaman lafiya da ’yan’uwanmu. Bari mu bincika yadda wasu suka amfana sa’ad da suka bi wannan shawara.

WASU RIKICE-RIKICE DA YADDA AKA SASANTA SU

CHRIS ya ce: “Ina aiki da wani ɗan’uwa da ba ma shiri. Akwai wani lokaci da muka yi rikici sosai, har mutane biyu suka shigo suka gan mu.”

JANET ta ce: “Wata ’yar’uwa da nakan fita wa’azi da ita ta daina yin hakan da ni. Ban da haka ma, ta daina ma yi min magana. Ban san abin da na yi mata ba.”

MICHAEL ya ce: “Mu uku muna magana ta waya. Sai ɗaya a cikinmu ya ce mana sai an jima, ban san cewa bai kashe wayarsa ba. Sai na yi gulmarsa, ban san yana jin mu ba.”

GARY ya ce: “A ikilisiyarmu akwai majagaba biyu da suka yi faɗa. Sai wata rana ɗayan ta soma zagin ɗayan. Hakan ya sa wasu a cikin ikilisiyar sanyin gwiwa.”

Za ka iya ganin cewa abubuwan da suka jawo rikici a waɗannan misalan ba su taka ƙara sun karya ba. Duk da haka, suna iya sa mutanen baƙin ciki sosai kuma ya hana ’yan’uwa kasancewa da haɗin kai a cikin ikilisiya. Amma, abin farin ciki shi ne cewa waɗannan ’yan’uwan sun bi ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki kuma suka sasanta  rigimar. Waɗanne ƙa’idodi ne suka bi da suka taimaka musu?

Yusufu ya ba ’yan’uwansa da suke komawa wurin mahaifinsu wannan shawara: “Ku yi hankali kada ku yi faɗa a kan hanya.” (Far. 45:24) Kuma wannan shawarar ta dace sosai don idan mutum bai kame kansa ba, yakan yi saurin fushi kuma ya sa wasu fushi. Chris ya lura cewa shi mai fahariya ne kuma ba ya karɓan shawara. Da yake yana son ya canja halinsa, sai ya ba ɗan’uwan da suke rikicin haƙuri kuma ya yi ƙoƙari ya riƙa kame kansa. Sa’ad da abokin aikinsa ya lura cewa yana ƙoƙarin canja halinsa, sai shi ma ya yi hakan. Yanzu suna zaman lafiya kuma suna jin daɗin bauta wa Jehobah tare.

“Wurin da babu shawara, nufe-nufe sukan warware.” (Mis. 15:22) Janet ta tsai da shawara ya kamata ta bi gargaɗin da ke cikin wannan ayar kuma ta je don su sasanta da ƙawarta. Janet ta tambaye ta ko ta ɓata mata rai ne. Da farko ba su ji daɗin tattaunawa ba amma bayan sun ci gaba da yin hakan, sai suka natsu. Sai ’yar’uwar ta fahimci cewa Janet ba ta yi mata laifin kome ba, ita ce ba ta gane abin da ya faru ba. Sai ta roƙi Janet ta gafarce ta kuma su biyun suka soma abokantakarsu kuma suka ci gaba da bauta wa Jehobah tare.

“Idan fa kana cikin miƙa baikonka a wurin bagadi, can ka tuna ɗan’uwanka yana da wani abu game da kai, sai ka bar baikonka can a gaban bagadi, ka yi tafiyarka, a sulhuntu da ɗan’uwanka tukuna.” (Mat. 5:​23, 24) Yesu ya ba da wannan shawara sa’ad da yake yin Huɗuba a kan Dutse. Michael ya yi baƙin ciki sosai don baƙar magana da ya yi game da wannan ɗan’uwan. Sai ya tsai da shawara ya yi iya ƙoƙarinsa don su sasanta batun. Ya roƙi ɗan’uwan ya gafarta masa. Mene ne sakamakon? Michael ya ce: “Ɗan’uwana ya gafarta min da dukan zuciyarsa.” Sai suka sake zama abokai.

“Kuna haƙuri da juna, kuna gafarta ma juna, idan kowane mutum yana da maganar ƙara game da wani.” (Kol. 3:​12-14) Ka tuna da majagaba biyu da suka samu saɓani? Wani dattijo ya taimaka musu su ga cewa matsalarsu tana sa wasu sanyin gwiwa a cikin ikilisiya. Sai ya tuna musu cewa ya kamata su riƙa haƙuri da juna kuma su sa a kasance da salama a cikin ikilisiya. Sai suka bi wannan shawarar da dattijon ya ba  su. Yanzu suna shiri da juna kuma suna fita wa’azi tare.

Bin abin da littafin Kolosiyawa 3:​12-14 ya ce zai taimaka maka idan wani ya yi abin da ya ɓata maka rai. Mutane da yawa sun fahimci cewa zama masu tawali’u zai taimaka musu su gafarta wa wanda ya ɓata musu rai kuma su mance da batun. Idan kana ƙoƙari ka gafarta wa mutumin amma ka kasa kuma fa? Abin da ke cikin littafin Matta 18:15 zai taimaka maka. A ayar, Yesu yana magana ne game da matakin da mutum zai ɗauka idan wani ya yi masa laifi mai tsanani. Amma muna iya bin wannan shawarar idan wani ya ɓata mana rai. Muna bukatar mu je mu samu ɗan’uwan ko ’yar’uwar da ladabi don mu tattauna batun kuma mu sasanta.

Littafi Mai Tsarki ya ba mu shawarwari masu kyau, kuma dukan su sun ƙunshi neman taimakon ruhu mai tsarki don mu iya nuna halaye kamar su ‘ƙauna, farin ciki, salama, tsawon jimrewa, nasiha, nagarta, aminci, tawali’u, da kamewa.’ (Gal. 5:​22, 23) Irin waɗannan halayen za su taimaka mana mu riƙa sasanta rikici kamar yadda māi yake sa inji ya yi aiki da kyau.

HALAYE DABAM-DABAM SUNA KYAUTATA HAƊIN KAN IKILISIYA

Dukanmu mun bambanta da juna, kuma hakan yana kyautata abokantakarmu da wasu. Duk da haka, yana iya jawo matsala. Wani dattijo ya ce: “Zai yi wa shuru-shuru wuya ya yi tarayya da wanda ya iya surutu. Muna iya ganin cewa wannan bambancin ba wani abu ba ne, amma zai iya jawo matsala.” Shin hakan yana nufin cewa mutanen da halinsu ya bambanta za su riƙa samun saɓani ne? Bari mu yi la’akari da misalin manzanni guda biyu. Muna iya yin tunanin cewa Bitrus mutumi ne da yake faɗan dukan abin da yake zuciyarsa. Yohanna kuma mutumi ne mai hankali da yake yin tunani sosai kafin  ya yi magana. Halin Bitrus da Yohanna ya bambanta, duk da haka, sun yi wa Jehobah hidima tare. (A. M. 8:14; Gal. 2:⁠9) A yau, duk da cewa halinmu ya bambanta, za mu iya yin aiki tare.

Amma mene ne za ka yi idan akwai wani ɗan’uwa ko ’yar’uwa a ikilisiyarku da take yin abin da yake ɓata maka rai? Zai dace ka tuna cewa Kristi ya ba da ransa domin kowanenmu, kuma ya umurce mu mu riƙa nuna ƙauna. (Yoh. 13:​34, 35; Rom. 5:​6-8) Don haka, maimakon mu daina yin abota da ɗan’uwan, muna bukatar mu tambayi kanmu: ‘Shin ɗan’uwana yana yin abin da Littafi Mai Tsarki ya hana ne? Shin yana so ne kawai ya riƙa ɓata min rai? Ko kawai dai don halinmu ya bambanta da juna ne?’ Ban da haka ma: ‘Akwai halinsa mai kyau da zan so in yi koyi da shi ne?’

Alal misali, idan mutum yana son yin surutu, kai kuma shuru-shuru ne, za ka iya fita wa’azi da shi don ka koyi wasu abubuwa. Kuma idan yana yawan taimaka wa mutane amma kai ba ka yin hakan, kana iya yin koyi da yadda yake taimaka wa tsofaffi da masu rashin lafiya da kuma mabukata. Darasin shi ne, ko da halinku ya bambanta da juna, kai da ɗan’uwanka ko ’yar’uwarki za ku iya zama abokai idan kuka mai da hankali ga halayenku masu kyau. Wataƙila yin hakan ba zai sa ku zama aminai ba, amma zai taimaka muku ku kusaci juna kuma ku sa ’yan’uwa a ikilisiya su kasance da salama.

Wataƙila halin Afodiya da Sintiki ya bambanta da juna. Duk da haka, manzo Bulus ya ƙarfafa su “su zama da hankali ɗaya a cikin Ubangiji.” (Filib. 4:⁠2) Shin kai ma za ka iya yin hakan, kuma ka sa ikilisiya ta kasance da salama?

KU SASANTA NAN DA NAN

Me ya sa muke bukatar mu sasanta matsaloli nan da nan? Don kamar yadda zawa take girma a cikin gonar fure, idan ba mu  tuge su ba, za su rufe gonar kuma mu kasa ganin furen da muka shuka. Hakazalika, idan muka ci gaba da yin gāba da ’yan’uwa, hakan zai shafi dukan ikilisiya. Idan muna ƙaunar Jehobah da ’yan’uwanmu, za mu yi iya ƙoƙarin mu mu sa ’yan’uwa a ikilisiya su yi zaman lafiya.

Za ka sami sakamako mai kyau, idan ka kasance mai tawali’u kuma ka yi iya ƙoƙarin ka don ka sasanta da ’yan’uwanka

Za mu samu sakamako mai kyau idan muka yi iya ƙoƙarin mu don mu sasanta da ’yan’uwanmu. Bari mu yi la’akari da misalin wata Mashaidiya da ta ce: “Na ji kamar wata ’yar’uwa tana bi da ni kamar yarinya ƙarama, kuma hakan ya ɓata min rai sosai. Kuma da ta ci gaba da hakan, sai ni ma na soma rena ta, ina ganin cewa ‘Tun da ba ta daraja ni, ni ma ba zan daraja ta ba.’”

Wannan Mashaidiyar ta yi tunani sosai a kan abin da take yi, kuma ta ce: “Sai na soma ganin cewa ni ma ina da matsala, kuma hakan ya sa ni baƙin ciki. Sai na ɗauki matakin canja halina, kuma na yi addu’a ga Jehobah game da batun. Sai na saya wa ’yar’uwar kyauta kuma na rubuta mata wasiƙar neman gafara don wulakanci da na yi mata. Mun sasanta kuma muka rungumi juna.”

Mutane suna bukatar kwanciyar hankali sosai. Amma idan suka ji kamar ana so a ƙwace matsayinsu ko kuma idan aka yi musu abin da bai dace ba, hakan yakan tayar musu da hankali. Abin da mutanen da ba sa bauta wa Jehobah suke yi ke nan, amma bayinsa suna iya ƙoƙarinsu don su kasance da salama. Jehobah ya sa Bulus ya rubuta cewa: “Ina roƙonku ku yi tafiya irin da ta cancanci kira da aka kiraye ku da ita, da dukan tawali’u da ladabi, da jimrewa, kuna haƙuri da junanku cikin ƙauna; kuna ƙwazo ku kiyaye ɗayantuwar Ruhu cikin ɗaurin salama.” (Afis. 4:​1-3) Wannan “ɗaurin salama” tana da muhimmanci sosai. Saboda haka, bari mu yi iya ƙoƙarinmu don mu sasanta dukan saɓani da muka samu da ’yan’uwanmu.