Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Mai da Hankali ga Batun da Ya Fi Muhimmanci

Ka Mai da Hankali ga Batun da Ya Fi Muhimmanci

‘Domin su sani kai, wanda sunanka Jehobah ne, kai kaɗai ne Maɗaukaki bisa dukan duniya.’​—ZAB. 83:18.

WAƘOƘI: 46, 136

1, 2. (a) Wane batu mai muhimmanci ne ya kamata mu mai da masa hankali? (b) Me ya sa wannan batun ya kamata ya zama mana da muhimmanci sosai?

MUTANE da yawa a yau sun sa neman kuɗi a gaba. Suna mai da hankali ga neman kayan duniya ko kāre arzikinsu. Wasu kuma abin da suke ganin ya fi muhimmanci shi ne iyali da lafiyarsu ko kuma wasu abubuwa dabam da suke so su cim ma.

2 Amma abin da ya kamata ya fi muhimmanci ga dukan mutane shi ne goyon bayan sarautar Jehobah. Bai kamata mu riƙa manta da wannan batu mai muhimmanci ba. Me zai iya sa mu manta da wannan batun? Idan muka saka neman kayan duniya a kan gaba, ba za mu iya sanin muhimmancin goyon bayan sarautar Allah ba. Ko kuma idan muka mai da hankali sosai ga matsalolinmu, za mu iya manta da batun nan mai muhimmanci. Amma idan muka mai da hankali sosai ga goyon bayan sarautar Jehobah, hakan zai taimaka mana mu jimre da matsalolin da muke fuskanta. Kuma yin hakan zai sa mu kusaci Jehobah sosai.

 ME YA SA WANNAN BATUN YAKE DA MUHIMMANCI SOSAI?

3. Wace ƙarya ce Shaiɗan ya yi game da sarautar Jehobah?

3 Abin da Shaiɗan ya yi ya sa mutane suna shakka ko Jehobah ne ya cancanci yin sarauta. Ya yi ƙarya cewa sarautar Allah ba ta da kyau kuma ba ya son halittunsa su ji daɗin rayuwa. Shaiɗan ya ce mutane za su ji daɗin rayuwa idan su ne ke sarautar kansu. (Far. 3:​1-5) Shaiɗan ya sake yin da’awa cewa mutane ba za su iya kasancewa da aminci ga Allah ko su goyi bayan sarautarsa ba, idan suka sha wahala. (Ayu. 2:​4, 5) Don haka, Jehobah ya bar mutane su yi sarautar kansu na ɗan lokaci don su gane cewa ba za su iya yi wa kansu sarauta ba.

4. Me ya sa ya kamata a sa mutane su fahimta cewa Jehobah ne ya cancanci yin sarauta?

4 Babu shakka, Jehobah ya san cewa abin da Shaiɗan ya faɗa ƙarya ce. Amma me ya sa ya ƙyale Shaiɗan ya tabbatar da abin da ya faɗa? Amsar wannan tambayar ta shafi dukan ’yan Adam da kuma mala’iku. (Karanta Zabura 83:18.) Iyayenmu na farko sun ƙi sarautar Jehobah kuma mutane da yawa ma sun goyi bayansu. Hakan zai iya sa wasu mutane su ga cewa wataƙila abin da Shaiɗan ya faɗa gaskiya ce. Da yake har ila wasu mala’iku da mutane suna shakkar ko Jehobah ne ya cancanci yin sarauta, ba za a sami jituwa ko salama tsakanin mutane a duniya ba. Amma idan aka samu tabbaci cewa Jehobah ne ya cancanci yin sarauta, kowa zai goyi bayan sarautarsa. Kuma za a sami salama a sama da kuma duniya.​—Afis. 1:​9, 10.

5. Me za mu yi don mu nuna cewa muna goyon bayan sarautar Jehobah?

5 Babu shakka, za a kawar da sarautar Shaiɗan da na mutane kuma kowa zai fahimci cewa Jehobah ne ya cancanci yin sarauta. Yesu ne zai zama sarkin Mulkin Allah kuma zai yi nasara. Ban da haka ma, masu aminci za su tabbatar wa kowa cewa mutane za su iya goyon bayan sarautar Allah. (Isha. 45:​23, 24) Shin kana cikin waɗanda suke goyon bayan sarautar Jehobah? Babu shakka, kana cikinsu. Idan muna son mu zama masu aminci, muna bukatar mu mai da hankali ga babban batun nan kuma mu san muhimmancinsa.

GOYON BAYAN SARAUTAR ALLAH YA FI CETO MUHIMMANCI

6. Ta yaya goyon bayan sarautar Jehobah yake da muhimmancin sosai?

6 Kamar yadda muka bincika, goyon bayan sarautar Jehobah batu ne mai muhimmanci da ya shafi dukan mutane. Ta yaya? Domin wannan batun ya fi dukan abubuwan da muke so muhimmanci. Shin hakan ya nuna cewa samun ceto ba shi da wani muhimmanci ne ko kuma ya nuna cewa Jehobah bai damu da mu ba? A’a. Me ya sa?

7, 8. Me ya sa goyon bayan sarautar Allah yake da alaƙa da cika alkawarinsa?

7 Jehobah yana ƙaunar mutane sosai, shi ya sa ya fanshe mu da jinin Ɗansa don mu sami rai na har abada. (Yoh. 3:16; 1 Yoh. 4:⁠9) Idan Jehobah ya kasa cika alkawarinsa, Shaiɗan zai sami hujjar kiran Allah maƙaryaci wanda ba ya sarauta yadda ya dace kuma yana hana halittunsa jin daɗi. Ban da haka ma, wasu masu ba’a suna cewa: “Ina alkawarin tafowarsa? gama, tun daga ran da ubanni suka kwanta barci, dukan al’amura suna nan kamar yadda suke tun farkon halitta.” (2 Bit. 3:​3, 4) Don haka, Jehobah zai cika alkawarinsa. Kuma zai tabbata cewa idan ya soma sarauta, za a ceci mutane masu aminci. (Karanta Ishaya 55:​10, 11.) Ƙari  ga haka, Jehobah zai yi sarautarsa da ƙauna. Saboda haka, muna da tabbaci cewa zai ci gaba da ƙauna da mutunta bayinsa masu aminci.​—Fit. 34:6.

8 Idan muka mai da hankali ga goyon bayan sarautar Jehobah, hakan ba ya nufin cewa cetonmu bai da wani muhimmanci a gare shi. Me ya sa? Domin Jehobah yana kula da mu sosai. Don haka, muna bukatar mu riƙa goyon bayan sarautar Jehobah domin abin da ya fi muhimmanci ke nan.

YADDA AYUBA YA CANJA RA’AYINSA

9. Wace ƙarya ce Shaiɗan ya yi game da Ayuba? (Ka duba hoton da ke shafi na 22.)

9 Abin farin ciki ne cewa muna da ra’ayin da ya dace game da muhimmancin goyon bayan sarautar Jehobah. Za mu fahimci hakan idan muka karanta littafin Ayuba wanda yake cikin littattafai na farko na Littafi Mai Tsarki da aka rubuta. Shaiɗan ya yi ƙarya cewa Allah ne ya jawo matsalar Ayuba. Amma ba Jehobah ba ne ya jawo matsalar Ayuba, duk da haka, ya bar Shaiɗan ya gwada bangaskiyar Ayuba, ya ce: “Ga shi dukan abin da yake da shi a hannunka suke.” (Karanta Ayuba 1:​7-12.) Bayan wani lokaci kaɗan, sai bayin Ayuba da yaransa goma suka rasu kuma ya yi asarar dukiyarsa gabaki ɗaya. Kuma Shaiɗan ya yi hakan a hanyar da zai nuna cewa Allah ne da kansa yake jawo wa Ayuba matsalolin. (Ayu. 1:​13-19) Bayan haka, sai Shaiɗan ya addabi Ayuba da wani ciwo mai tsanani. (Ayu. 2:7) Abin da ya fi damun Ayuba shi ne abin da matarsa da kuma abokansa uku suka faɗa da ya sa shi sanyin gwiwa.​—Ayu. 2:9; 3:11; 16:2.

10. (a) Mene ne Ayuba ya yi da ya nuna cewa ya kasance da aminci sosai ga Allah? (b) Kuma me ya sa Ayuba ya manta da batun da ya fi muhimmanci?

10 Shin abin da Shaiɗan ya faɗa gaskiya ne? A’a. Duk da cewa Ayuba ya sha wahala sosai, ya riƙe amincinsa ga Jehobah. (Ayu. 27:⁠5) Amma wahalar da Ayuba ya sha ta sa ya manta da batun da ya fi muhimmanci. Ya yi ta faɗin cewa shi bai yi laifin kome ba. Kuma ya nemi sanin dalilin da ya sa yake shan wahala. (Ayu. 7:20; 13:24) Mun san cewa wataƙila irin wahalar da ya sha ne ta sa shi yin maganganun nan. Duk da haka, Allah ya ga muhimmancin daidaita ra’ayin Ayuba. Me Jehobah ya gaya masa?

11, 12. Mene ne Jehobah ya taimaka wa Ayuba ya yi, kuma me Ayuba ya yi?

11 Za mu iya karanta abin da Allah ya gaya ma Ayuba a littafin Ayuba surori 38 zuwa 41. Amma babu wurin da Allah ya gaya wa Ayuba dalilin da ya sa yake shan wahala. Dalilin da ya sa Allah ya yi magana da Ayuba, ba wai yana son ya gaya  masa dalilin da ya sa yake shan wahala ba ne ko kuma don ya kāre kansa ba. Amma Jehobah yana son Ayuba ya san cewa ya fi shi iko sosai. Ban da haka ma, ya so ya taimaka wa Ayuba ya san batu mai muhimmanci da ya kamata ya fi mai da wa hankali. (Karanta Ayuba 38:​18-21.) Hakan ya taimaka wa Ayuba ya daidaita ra’ayinsa.

12 Shin Jehobah yana tsauta wa Ayuba ne bayan Ayuba ya jimre wahalar da ya sha? A’a, kuma Ayuba ma bai ɗauka haka ba. Ayuba ya amince da gyarar da Jehobah ya yi masa har ma daga baya ya ce: “Domin wannan ina jin ƙyamar kaina, na tuba cikin ƙura da toka.” (Ayu. 42:​1-6) Kafin wannan lokacin, matashin nan Elihu ma ya gargaɗi Ayuba. (Ayu. 32:​5-10) Ayuba ya amince da gyarar da Allah ya yi masa kuma ya daidaita ra’ayinsa. Ƙari ga haka, Jehobah ya sa mutane su fahimta cewa ya yi farin ciki da amincin Ayuba.​—Ayu. 42:​7, 8.

13. Ta yaya shawarar da Jehobah ya ba wa Ayuba ta taimaka masa bayan ya daina shan wahala?

13 Shawarar da Jehobah ya ba wa Ayuba za ta taimaka masa har bayan ya daina shan wahala. Ta yaya? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ubangiji ya albarkaci ƙarshen Ayuba.” Daga baya, ya sami “’ya’ya maza bakwai, da ’ya’ya mata uku.” (Ayu. 42:​12-14) Babu shakka, Ayuba ya yi kewar ’ya’yansa da Shaiɗan ya kashe. Wataƙila bayan wani lokaci yakan yi tunanin irin wahalar da ya sha. Ko da yake daga baya ya fahimci dalilin da ya sa ya sha wahala, wataƙila a wasu lokuta yakan tuna dalilin da ya sa Allah ya ƙyale shi ya sha irin wahalar nan. Ko da yake a wasu lokuta ya yi irin wannan tunanin, bai manta da shawarar da Jehobah ya ba shi ba. Hakan ya taimaka masa ya kasance da ra’ayin da ya dace kuma ya riƙa ƙarfafa shi.​—Zab. 94:19.

Zai dace mu mai da hankali ga goyon bayan sarautar Jehobah ba matsalolinmu ba (Ka duba sakin layi na 14)

14. Wane darasi za mu iya koya daga labarin Ayuba?

14 Mu ma za mu iya samun ƙarfafa idan muka karanta littafin Ayuba. Shi ya sa Jehobah ya sa ‘aka rubuta shi domin koyarwarmu, domin ta wurin haƙuri da ta’aziyar littattafai mu zama da bege.’ (Rom. 15:4) Wane darasi muka koya daga wannan labarin? Bai kamata mu bar matsaloli su hana mu mai da hankali ga batun da ya fi muhimmanci ba, wato goyon bayan sarautar Jehobah. Ko da muna shan wahala kamar yadda Ayuba ya sha, ya kamata mu goyi bayan sarautar Jehobah ta wajen kasancewa da aminci.

15. Mene ne za mu cim ma idan muka jimre sa’ad da muke shan wahala?

15 Labarin Ayuba ya nuna mana cewa idan muna shan wahala ba wai Jehobah  yana fushi da mu ba ne. Amma wahalar da muke sha tana ba mu zarafin goyon bayan sarautar Jehobah. (Mis. 27:11) Idan muka jimre, za mu zama da “ingataccen hali” kuma hakan zai sa mu kasance da bege. (Karanta Romawa 5:​3-5.) Ƙari ga haka, labarin Ayuba ya nuna cewa ‘Ubangiji yana cike da tausayi, mai-jinƙai ne kuma.’ (Yaƙ. 5:11) Don haka, muna da tabbaci cewa zai albarkace mu da dukan waɗanda suke goyon bayansa. Hakan zai taimaka mana mu zama da “haƙuri da jimrewa tare da farin ciki.”​—Kol. 1:11.

KA CI GABA DA GOYON BAYAN SARAUTAR ALLAH

16. Me ya sa ya zama wajibi mu riƙa tuna muhimmancin goyon bayan sarautar Jehobah?

16 Gaskiya ne cewa zai iya mana wuya mu tuna da muhimmancin goyon bayan sarautar Jehobah idan muna shan wahala. Wasu matsalolin da ba su taka kara sun karya ba ma za su iya damunmu sosai idan muka ci gaba da yin tunaninsu. Don haka, bai kamata mu manta da muhimmancin goyon bayan sarautar Allah ba idan muna fuskantar matsaloli.

17. Ta yaya sa ƙwazo a hidimar Jehobah zai taimaka mana mu mai da hankali ga batun nan mai muhimmanci?

17 Idan muka sa ƙwazo a yin hidimar Jehobah, za mu riƙa mai da hankali ga batun nan mai muhimmanci. Alal misali, wata ’yar’uwa mai suna Renee ta sha wahala sosai saboda ciwon shanyewar jiki da kansa. Sa’ad da take jinya a asibiti, ta yi amfani da wannan zarafin don ta yi wa ma’aikatan asibiti da marasa lafiya da kuma waɗanda suka zo ganinsu wa’azi. Akwai wani lokacin da ta yi sati biyu da rabi a wani asibiti tana jinya, kuma ta yi wa’azi na awoyi 80 a wurin. Ko da yake Renee ta san cewa za ta rasu, ba ta manta da batun goyon bayan sarautar Jehobah ba. Kuma hakan ya taimaka mata ta rage damuwan da take yi.

18. Ta yaya labarin wata ’yar’uwa ya nuna muhimmancin goyon bayan sarautar Jehobah?

18 Hakika, za mu iya mai da hankali ga batu mai muhimmanci idan muna cikin wani hali a harkokinmu na yau da kullum. Alal misali, wata ’yar’uwa mai suna Jennifer ta yi kwana uku a tashar jirgin sama tana jira ta sami wanda za ta shiga don ya kai ta gida. Amma ana ta tura tafiyarsu gaba gaba kuma hakan ya sa Jennifer baƙin ciki sosai. Amma da yake ba ta manta da batu mai muhimmanci ba, ta yi addu’a don Jehobah ya taimaka mata ta yi wa mutanen da suke cikin irin yanayinta wa’azi. Ta yi nasara kuwa? Hakika, ta yi wa mutane da yawa wa’azi kuma ta ba su littattafai da yawa. Ta ce: “Na gane cewa Jehobah ya taimaka mini duk da yanayin da nake ciki kuma ya ƙarfafa ni don in yi amfani da sunansa a hanyar da ta dace.” Babu shakka, wannan ’yar’uwar ba ta manta da batun goyon bayan sarautar Jehobah ba.

19. Mene ne ra’ayin Shaidun Jehobah game da goyon bayan sarautar Jehobah?

19 Goyon bayan da muke yi wa sarautar Allah da zuciya ɗaya yana bambanta mu da addinan ƙarya. Bayin Allah tun dā suna goyon bayan sarautar Allah. Wajibi ne kowannenmu ya ci gaba da yin hakan.

20. Yaya Jehobah yake ji game da ƙwazon da muke sakawa don mu goyi bayan sarautarsa?

20 Jehobah yana jin daɗin ƙwazon da muke saka wa don mu goyi bayan sarautarsa idan mun kasance da aminci sa’ad da muke shan wahala. (Zab. 18:25) A talifi na gaba, za mu bincika wasu dalilan da suka sa ya kamata mu goyi bayan sarautar Jehobah da kuma yadda za mu iya yin hakan.