Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Kwallafa Ranka ga Al’amuran Ibada

Ka Kwallafa Ranka ga Al’amuran Ibada

“Wurin da ajiyarku take, nan kuma zuciyarku za ta zauna.”​—LUK. 12:34.

WAƘOƘI: 153, 104

1, 2. (a) Waɗanne abubuwa masu tamani guda uku ne Jehobah ya ba mu? (b) Me za mu bincika a wannan talifin?

JEHOBAH ya fi kowa arziki a sama da kuma duniya. (1 Laba. 29:​11, 12) Da yake shi mai karimci ne, yana koya wa duk waɗanda suke mutunta shi da Kalmarsa. Muna godiya sosai don ya nuna mana al’amura na ibada da suka ƙunshi (1) Mulkin Allah, da (2) wa’azin ceto da muke yi da kuma (3) Kalmarsa Littafi Mai Tsarki. Amma idan ba mu mai da hankali ba, za mu daina nuna godiya kuma mu yi banza da waɗannan abubuwa masu tamani. Idan ba ma son mu yi hakan, zai dace mu ci gaba da tunawa da muhimmancinsu kuma mu riƙa ƙaunarsu. Yesu ya ce: “Wurin da ajiyarku take, nan kuma zuciyarku za ta zauna.”​—Luk. 12:34.

2 Bari mu bincika yadda za mu ci gaba da ƙauna da kuma daraja Mulkin Allah da wa’azin da muke yi da kuma Kalmar Allah. Sa’ad da muke binciken, zai dace mu yi tunani a kan darussan da za mu koya da za su taimaka mana mu ci gaba da ɗaukan waɗannan abubuwan da muhimmanci.

 MULKIN ALLAH ABU NE MAI TAMANI

3. Mene ne mai fataucin nan yake so ya yi don ya iya sayan wannan lu’ulu’u mai tamani? (Ka duba hoton da ke shafi na 9.)

3 Karanta Matta 13:​45, 46. Yesu ya yi kwatanci da wani mai fatauci da ya yi tafiya don ya je neman lu’ulu’u. Mutumin nan ya yi shekaru yana fataucin lu’ulu’u sosai. A ƙarshe, ya ga wani lu’ulu’u mai daraja ko tamani sosai da mutane suke nema. Amma kafin ya iya saya, sai da ya sayar da duk abin da yake da shi. Babu shakka, wannan lu’ulu’un yana da daraja sosai a gare shi, ko ba haka ba?

4. Me za mu yi idan muna ƙaunar Mulkin Allah kamar yadda mai fataucin nan ya ƙaunaci lu’ulu’un?

4 Wane darasi muka koya daga wannan labarin? Abubuwan da muke koya a Littafi Mai Tsarki game da Mulkin Allah yana kama da lu’ulu’u mai tamani. Idan muka ƙaunace su kamar yadda mai fataucin nan ya so lu’ulu’u, za mu iya barin kome kuma mu ƙwallafa ranmu ga al’amuran Mulkin. (Karanta Markus 10:​28-30.) Bari mu bincika labarin mutane biyu da suka yi hakan.

5. Ta yaya Zakka ya nuna cewa yana son ya ƙwallafa ransa ga Mulkin Allah?

5 Wani shugaban masu karɓan haraji mai suna Zakka, ya yi arziki sosai don ya saba cucin mutane. (Luk. 19:​1-9) Amma da ya ji cewa Yesu yana wa’azi game da Mulkin Allah, ya daraja koyarwar kuma ya ɗauki mataki nan da nan. Ta yaya? Ya ce: Zan bayar da ‘rabin dukiyata ga matalauta; idan kuwa na ƙwace kome a wurin wani, in mayar masa riɓi huɗu.’ Da zuciya ɗaya ya daina aikin da yake yi da kuma cucin mutane.

6. Wane mataki ne wata mata ta ɗauka don ta iya ƙwallafa ranta ga Mulkin Allah, kuma me ya sa ta yi hakan?

6 A shekarun baya, wata mata ta ji wa’azi game da Mulkin Allah ko da yake ita ’yar maɗigo ce. Ban da haka ma, ita ce shugaba a ƙungiyar masu nema wa ’yan maɗigo da ’yan daudu ’yanci. Bayan da ta yi nazarin Littafi Mai Tsarki ne ta gane cewa koyarwa game da Mulkin Allah yana da tamani sosai. Amma ta san cewa ya kamata ta daina halin rashin da’a da take yi. (1 Kor. 6:​9, 10) Da zuciya ɗaya ta yi murabus daga ƙungiyar kuma ta daina halin da take yi. Matar ta yi baftisma a shekara ta 2009 kuma a shekara ta 2010, sai ta soma hidimar majagaba na kullum. Me ya taimaka mata ta ɗauki wannan matakin? Ta ƙaunaci Jehobah da kuma Mulkinsa fiye da sha’awar banza da take da shi.​—Mar. 12:​29, 30.

7. Ta yaya za mu ci gaba da ƙaunar al’amuran Mulkin Allah?

7 Babu shakka, da yawa daga cikinmu mun daina wasu halaye marasa kyau don mu iya ƙwallafa ranmu ga al’amuran Mulkin Allah. (Rom. 12:⁠2) Har ila tsuguni ba ta ƙare ba. Wajibi ne mu mai da hankali ga abubuwan da za su iya raba hankalinmu kamar neman abin duniya da kuma sha’awar yin lalata. (Mis. 4:23; Mat. 5:​27-29) Don Jehobah ya taimaka mana mu ci gaba da ƙaunar Mulkin Allah, ya ba mu wani abu kuma mai muhimmanci ko tamani.

WA’AZIN CETO

8. (a) Me ya sa manzo Bulus ya kwatanta wa’azin da yake yi da “kaya mai-daraja cikin tukwane na ƙasa”? (b) Ta yaya Bulus ya nuna cewa ya ɗauki wa’azin da yake yi da muhimmanci?

8 Mun sani cewa Yesu ya umurce mu mu yi wa’azi kuma mu koyar da mutane game da Mulkin Allah. (Mat. 28:​19, 20) Manzo Bulus ma ya san muhimmancin yin wa’azi. Ya kwatanta sabon alkawari da “kaya mai-daraja cikin tukwane na ƙasa.” (2 Kor. 4:7; 1 Tim. 1:12) Ko da yake mu ajizai ne,  amma wa’azin da muke yi zai iya taimaka mana mu sami ceto da kuma waɗanda suka saurare mu. Wannan dalilin ne ya sa Bulus ya yi amfani da hanyoyi da yawa don ya yi wa’azi kuma ya ce: “Ina kuwa yin abu duka sabili da bishara, domin in yi tarayya cikin samunta.” (1 Kor. 9:23) Babu shakka, Bulus ya so wa’azin da yake yi sosai shi ya sa ya saka ƙwazo wajen neman almajirai. (Karanta Romawa 1:​14, 15; 2 Timotawus 4:2.) Ƙari ga haka, wannan ƙaunar ta taimaka masa ya jimre sa’ad da ake tsananta masa. (1 Tas. 2:2) Ta yaya mu ma za mu so wa’azin da muke yi kamar yadda Bulus ya yi?

9. A waɗanne hanyoyi ne za mu nuna cewa muna ɗaukan wa’azin da muke yi da muhimmanci?

9 Hanya ɗaya da Bulus ya nuna cewa ya ɗauki wa’azin da yake yi da muhimmanci ita ce yin amfani da hanyoyi dabam-dabam don ya yi wa mutane wa’azi. Kamar yadda manzanni da kuma Kiristoci na farko suka yi, mu ma muna wa’azi a wuraren da jama’a suke da kuma gida-gida. (A. M. 5:42; 20:20) Za mu iya ƙara ƙwazo a wa’azi ta wurin yin hidimar majagaba na ɗan lokaci ko kuma yin hidimar majagaba na kullum. Ban da haka ma, za mu iya koyan wani yare ko kuma mu je hidima a wuraren da ake bukatar masu shela a ƙasarmu ko kuma wata ƙasa.​—A. M. 16:​9, 10.

10. Ta yaya Jehobah ya albarkaci Irene don ƙwazon da ta yi a wa’azi?

10 Bari mu bincika labarin Irene, wata ’yar’uwa marar aure da ke ƙasar Amirka. Ta so ta yi wa mutanen Rasha da ke Amirka wa’azi a yarensu. A lokacin da ta soma yi musu wa’azi a shekara ta 1993, akwai masu shela wajen 20 kawai da suke yaren a New York da ke Amirka. Kuma Irene ta yi shekaru 20 tana ma mutanen da suke yaren Rasha wa’azi. Ta ce: “Har yanzu ban iya yaren mutanen Rasha da kyau ba.” Duk da haka, Jehobah ya albarkace ta da kuma wasu don ƙwazon da suke yi a yin hakan. Yanzu ana da ikilisiyoyi shida da suke yaren mutanen Rasha a New York da ke Amirka. Wasu cikin ɗaliban Irene su sha biyar sun yi baftisma. Kuma wasu cikinsu na hidima a Bethel, wasu kuma majagaba ne da kuma dattawa. Irene ta ce: “Da ace na zaɓi wani maƙasudi dabam, da ban yi farin ciki yadda nake yi yanzu ba.” Babu shakka, ta ɗauki hidimar da take yi da muhimmanci!

Shin kana ɗaukan hidimarka a matsayin dukiya mai tamani kuma kana nuna hakan a yadda kake tsara ayyukanka na kowane mako? (Ka duba sakin layi na 11, 12)

11. Wace nasara ake samu idan ’yan’uwa suka ci gaba da yin wa’azi duk da cewa ana tsananta musu?

11 Idan muka ɗauki wa’azin da muke yi da muhimmanci, za mu zama kamar manzo Bulus wanda ya ci gaba da wa’azi duk da tsanantawa da aka yi masa. (A. M. 14:​19-22) A tsakanin shekara ta 1930 da 1940 da wani abu, an tsananta wa ’yan’uwanmu  da ke Amirka sosai. Duk da haka, sun bi misalin Bulus kuma suka ci gaba da wa’azi. An yi ta shari’a a kotu don ’yan’uwa su sami ’yancin yin wa’azi. A shekara ta 1943, sa’ad da Ɗan’uwa Nathan H. Knorr yake magana game da wata nasarar da muka samu a Babban Kotun Amirka, ya ce: “Mun samu wannan nasarar ne saboda gwagwarmayar da kuke yi. Inda a ce ’yan’uwa ba sa fita wa’azi, da babu wanda zai kai ƙararmu Babban Kotu; amma domin ku da dukan ’yan’uwanmu a faɗin duniya kuna fita wa’azi kuma ba ku tsoron tsanantawar da za ku fuskanta, shi ya sa muka sami wannan nasarar.” Irin wannan ƙarfin halin da ’yan’uwanmu suke nuna wa a wasu ƙasashe ne ya sa muke samun nasara sosai. Babu shakka, idan muna son yin wa’azi, za mu sami albarka sosai.

12. Me ka ƙudiri aniyar yi game da wa’azi?

12 Idan muka ɗauki wa’azin da muke yi da tamani, ba za mu riƙa damuwa da awoyi kawai da muke yi a wa’azi ba. A maimakon haka, za mu sa ƙwazo don mu “shaida bishara ta alherin Allah.” (A. M. 20:24; 2 Tim. 4:⁠5) Amma me za mu riƙa koya wa mutane? Bari mu bincika wani abu kuma mai tamani da Jehobah ya ba mu.

ABUBUWAN DA MUKA KOYA DAGA LITTAFI MAI TSARKI

13, 14. Wace ‘dukiya’ ce Yesu ya yi maganarsa a littafin Matta 13:​52, kuma ta yaya za mu same ta?

13 Wani abu mai tamani da muka samu daga Allah shi ne abubuwan da muka koya daga Kalmarsa. Jehobah yana faɗin gaskiya a kowane lokaci. (2 Sam. 7:28; Zab. 31:5) Da yake shi mai karimci ne, yana koya wa mutanen da suke tsoronsa Kalmarsa. Mun ci gaba da koyon gaskiya game da Jehobah daga Littafi Mai Tsarki, tun daga lokacin da muka fara sanin wani abu game da shi. Ban da haka ma, muna koyan abubuwa da yawa daga littattafanmu da manyan taro da kuma taron ikilisiya. Bayan wani lokaci, sai muka sami abin da Yesu ya kwatanta da ‘dukiya’ sababbi da tsofaffi. (Karanta Matta 13:52.) Jehobah zai taimaka mana mu riƙa tunawa da kuma ajiye ilimi game da shi idan muka koyi Kalmarsa da kuzari kamar yadda ake neman dukiya. (Karanta Misalai 2:​4-7.) Ta yaya za mu yi hakan?

14 Zai dace mu riƙa nazari sosai da kuma bincika Kalmar Allah da kuma littattafanmu. Hakan zai taimaka mana mu gane wasu ‘sababbin’ koyarwar Littafi Mai Tsarki da ba mu sani ba. (Josh. 1:​8, 9; Zab. 1:​2, 3) Hasumiyar Tsaro ta farko da aka wallafa a watan Yuli na shekara ta 1879, ya kwatanta gaskiyar da muke koya da furen da ciyawa ya rufe shi. Idan muna son mu ga wannan furen, sai mun neme shi a hankali. Kuma idan mutum ya gan shi, zai so ya ƙara neman wasu kuma ba zai daina nema ba. Hakazalika, idan muka fahimci wata koyarwar Littafi Mai Tsarki, bai kamata mu daina koyon ba. Babu shakka, zai dace mu yi marmarin cika zuciyarmu da koyarwar Littafi Mai Tsarki.

15. Me ya sa muka ce wasu koyarwa ‘tsofaffi’ ne, kuma waɗanne ne ka ɗauka da tamani?

15 Mun koyi wasu abubuwa masu tamani sa’ad da muka soma tarayya da mutanen Allah. An kwatanta abubuwan nan da dukiya ‘tsofaffi’ don su ne abubuwan da muka soma koya sa’ad da muka zama Shaidu. Mene ne waɗannan koyarwar suka ƙunsa? Mun koya cewa Jehobah shi ne Mahaliccinmu. Ban da haka ma, yana da wata manufa shi ya sa ya halicci mutane. Ƙari ga haka, mun koya cewa Allah ya ba da Ɗansa fansa don a ceto mu daga zunubi da kuma mutuwa. Mun sake koya cewa Mulkinsa ne zai kawo ƙarshen  wahala kuma mu sami zarafin yin rayuwa a duniya har abada babu tashin hankali.​—Yoh. 3:16; R. Yoh. 4:11; 21:​3, 4.

16. Mene ne muke bukatar mu yi sa’ad da aka ba da ƙarin haske game da wani koyarwa?

16 A wasu lokatai, ana iya ba da ƙarin haske a kan yadda muka fahimci wani annabcin Littafi Mai Tsarki ko kuma wasu ayoyi. Idan aka yi irin wannan bayanin, ya kamata mu keɓe lokaci don mu yi nazarinsu sosai kuma mu yi bimbini a kansu. (A. M. 17:11; 1 Tim. 4:15) Ƙari ga haka, ya kamata mu fahimci gyarar da aka yi da ya bambanta sabon da na dā. Idan muka yi hakan, za mu riƙa tuna da abin da muka koya. Me ya sa yin waɗannan abubuwan suka dace?

17, 18. Ta yaya ruhu mai tsarki zai iya taimaka mana?

17 Yesu ya koya mana cewa ruhun Allah yana iya tuna mana abubuwan da muka koya a dā. (Yoh. 14:​25, 26) Ta yaya hakan zai taimaka mana da yake mu masu shela ne? Bari mu yi la’akari da labarin wani ɗan’uwa mai suna Peter. A shekara ta 1970 da yake ɗan shekara 19, sai ya soma hidima a Bethel da ke ƙasar Birtaniya. Wata rana da ya fita wa’azi, sai ya haɗu da wani mutum mai dogon gemu da shekarunsa ya kai kusan 50. Peter ya tambayi mutumin ko zai so ya fahimci Littafi Mai Tsarki da kyau. Abin ya ba mutumin mamaki, sai ya ce wannan gidan Yahudawa ne. Don ya gwada Peter, sai ya yi masa wata tambaya cewa, “Ɗana, da wane yare ne aka rubuta littafin Daniyel?” Sai Peter ya ce, “An rubuta wasu sashe a yaren Aramaic.” Peter ya ce, “Malamin ya yi mamaki cewa na san amsar. Ni ma na yi mamaki sosai yadda na san amsar. Sa’ad da na koma gida, sai na duba mujallun Hasumiyar Tsaro da Awake! da aka wallafa watanni da suka shige, sai na ga talifin da ya bayyana cewa an rubuta littafin Daniel a yaren Aramaic.” (Dan. 2:4) Hakika, ruhu mai tsarki zai iya sa mu tuna da abubuwan da muka karanta a dā.​—Luk. 12:​11, 12; 21:​13-15.

18 Idan muka ɗauki koyarwar Jehobah da tamani, hakan zai sa mu riƙa tuna da abubuwan da muka koya a dā da waɗanda muke koya a yanzu. Ƙari ga haka, za mu riƙa so da kuma nuna godiya don koyarwar Jehobah, kuma za mu zama malaman da aka koyar da su sosai.

KA KIYAYE ABUBUWAN DA KA KOYA GAME DA JEHOBAH

19. Me ya sa za mu ci gaba da son abubuwan da suka shafi ibadarmu?

19 Shaiɗan da wannan duniya suna neman hanyoyin da za su hana mu son koyarwar Allah da muka bincika a wannan talifin. Dukan waɗannan abubuwan suna shafan mu. Abubuwa kamar su aiki ko sana’a da ake samun kuɗi sosai da abubuwan da ake yayinsu ko kuma son nuna cewa muna da arziki zai iya raba hankalinmu. Manzo Yohanna ya tuna mana cewa wannan duniya da dukan sha’awoyinta suna wucewa. (1 Yoh. 2:​15-17) Saboda haka, wajibi ne mu yi iya ƙoƙarinmu don mu yi hattara da irin abubuwan da muke so kuma mu ci gaba da son abubuwan da suka shafi ibadarmu.

20. Mene ne ka ƙudiri aniyar yi don ka kāre abubuwan da ka koya game da Jehobah?

20 Ya kamata ka daina duk wani abu da zai iya hana ka son Mulkin Allah da dukan zuciyarka. Ka ci gaba da yin wa’azi da ƙwazo da kuma son fita wa’azi don hakan yana ceton rayukan mutane. Ƙari ga haka, ka ci gaba da biɗan koyarwar Allah. Yayin da kake waɗannan abubuwan za ka tara dukiyarka a “sama da ba shi sarewa, inda ɓarawo ba shi kusatowa, asu kuma ba shi ɓātawa. Gama wurin da ajiyarku take, nan kuma zuciyarku za ta zauna.”​—Luk. 12:​33, 34.