Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Kada Ka Bar Kurakuran Wasu Su Hana Ka Bauta wa Jehobah

Kada Ka Bar Kurakuran Wasu Su Hana Ka Bauta wa Jehobah

“Kuna gafarta ma juna.”—KOL. 3:13.

WAƘOƘI: 121, 75

1, 2. Ta yaya Littafi Mai Tsarki ya annabta cewa bayin Jehobah za su ƙaru?

AMINTATTUN bayin Allah, wato Shaidun Jehobah da ke cikin ƙungiyarsa sun fita dabam da sauran mutane. Waɗanda suke cikin ƙungiyar Jehobah ajizai ne kuma suna da kasawarsu. Duk da haka, da taimakon ruhu mai tsarki, suna ƙaruwa kuma suna samun ci gaba. Ka yi la’akari da wasu abubuwan da Jehobah yake cim mawa ta wajen mutanensa da suke bauta masa da son rai duk da cewa su ajizai ne.

2 Sa’ad da aka soma kwanaki na ƙarshe a shekara ta 1914, bayin Allah ba su da yawa a lokacin. Amma da shigewar lokaci, Jehobah ya albarkaci wa’azin bishara da suke yi don miliyoyin mutane sun koyi gaskiyar Littafi Mai Tsarki kuma sun zama Shaidun Jehobah. Jehobah ya annabta cewa hakan zai faru sa’ad da ya ce: “Ƙaramin za ya zama dubu, ƙanƙanin kuma za ya zama al’umma mai-ƙarfi: ni, Ubangiji, zan hanzarta wannan a lotonsa.” (Isha. 60:22) Hakika, wannan annabcin ya cika a wannan kwanaki na ƙarshe. Shi ya sa yanzu adadin bayin Allah a duniya ya wuce yawan jama’a da ke al’ummai da yawa.

3. Ta yaya bayin Allah suka nuna cewa suna ƙaunar mutane?

3 Ƙari ga haka, Jehobah ya taimaka wa mutanensa su daɗa ƙaunar juna domin ƙauna ce halinsa na musamman. (1 Yoh. 4:8) Yesu ya bi misalin Allah kuma ya gaya wa mabiyansa cewa: “Sabuwar doka na ke ba ku, ku yi ƙaunar juna . . . Bisa ga wannan mutane duka za su fahimta ku ne almajiraina, idan kuna da ƙauna ga junanku.” (Yoh. 13:34, 35) Kasancewa da ƙauna ya taimaka wa bayin Jehobah sosai musamman a lokacin da al’ummai suke yaƙi da juna. Alal misali, wajen mutane miliyan 55 ne aka kashe a Yaƙin Duniya na Biyu. Amma Shaidun Jehobah ba su saka hannu a wannan Yaƙin Duniya ba. (Karanta Mikah 4:1, 3.) Hakan ya sa sun “kuɓuta . . . daga jinin dukan mutane.”—A. M. 20:26.

4. Me ya sa yadda mutanen Allah suke ƙaruwa yake da ban mamaki?

4 Abin mamaki shi ne, mutanen Allah sun ci gaba da ƙaruwa duk da cewa suna da maƙiyi da yake da ƙarfi sosai, wato Shaiɗan kuma Littafi Mai Tsarki ya ce shi ne “allah na wannan zamani.” (2 Kor. 4:4) Shaiɗan ne yake ja-gorar siyasa da kuma kafofin yaɗa labarai na wannan duniyar. Amma ba zai iya dakatar da wa’azin bishara ba. Tun da yake ya san cewa lokacinsa yana kurewa, yana amfani da hanyoyi dabam-dabam don ya hana mutane bauta wa Jehobah.—R. Yoh. 12:12.

SHIN ZA KA KASANCE DA AMINCI SA’AD DA WASU SUKA YI KUSKURE?

5. Me ya sa wasu za su iya ɓata mana rai a wani lokaci? (Ka duba hoton da ke shafi na 23.)

5 A matsayinmu na bayin Jehobah, ana ƙarfafa mu mu ƙaunaci Allah da kuma mutane a taronmu. Yesu ya nuna cewa hakan yana da muhimmanci sa’ad da ya ce: “Ka yi ƙaunar Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan azancinka. Wannan ce babbar doka, ita ce kuwa ta fari. Wata kuma ta biyu mai kamaninta ita ce, Ka yi ƙaunar maƙwabcinka kamar ranka.” (Mat. 22:35-39) Duk da haka, Littafi Mai Tsarki ya ce dukanmu ajizai ne saboda zunubin Adamu. (Karanta Romawa 5:12, 19.) Saboda haka, a wani lokaci, wasu a cikin ikilisiya za su iya faɗin wani abu ko kuma su yi abin da zai ɓata mana rai. Idan hakan ya faru, za mu ci gaba da ƙaunar Allah da kuma mutanensa? Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa wasu bayin Allah a dā sun taɓa ɓata wa ’yan’uwansu rai. Bari mu koyi darasi daga abin da Littafi Mai Tsarki ya bayyana game da hakan.

Idan ka yi rayuwa a Isra’ila a zamanin Eli da ’ya’yansa, mene ne za ka yi? (Ka duba sakin layi na 6)

6. Ta yaya Eli ya ƙi ya horar da ’ya’yansa?

6 Alal misali, Eli Babban Firist yana da ’ya’ya biyu kuma ba sa bin dokokin Jehobah. Littafi Mai Tsarki ya ce: “’Ya’yan Eli ’yan Belial ne: ba su san Ubangiji ba.” (1 Sam. 2:12) Ko da yake mahaifinsu ya ɗaukaka bauta ta gaskiya, ’ya’yansa biyu sun yi zunubi masu tsanani. Eli ya san da haka amma bai yi musu horo ba. Saboda haka, Allah ya hukunta shi da ’ya’yansa. (1 Sam. 3:10-14) Da shigewar lokaci, Jehobah ya hana zuriyar Eli su ci gaba da yin hidima a matsayin manyan firistoci. Da a ce kana nan a zamanin Eli kuma ka ga yadda ya ƙi horar da ’ya’yansa saboda zunubin da suka yi, mene ne za ka yi? Shin za ka bar al’amarin ya shafe ka har ya sa ka daina bauta wa Jehobah?

7. Ta yaya Dauda ya yi zunubi mai tsanani, kuma wane mataki ne Allah ya ɗauka game da hakan?

7 Littafi Mai Tsarki ya ce Dauda mutum ne wanda Allah ‘yake ƙauna ƙwarai.’ (1 Sam. 13:13, 14; A. M. 13:22, Littafi Mai Tsarki) Amma daga baya, Dauda ya yi zina da Bath-sheba kuma ta yi ciki. Hakan ya faru ne sa’ad da mijinta yake bakin dāga. Sa’ad da mijin ya dawo gida na ɗan lokaci, Dauda ya yi ƙoƙari ya sa shi ya kwana da matarsa Bath-sheba don ya zama kamar mijinta ne ya yi mata cikin. Amma Uriah ya ƙi ya bi shawararsa saboda haka, Dauda ya ba da umurni cewa a kashe Uriah a yaƙi. Dauda da iyalinsa sun sha wahala sosai saboda wannan abin da ya yi. (2 Sam. 12:9-12) Duk da haka, Allah ya gafarce shi don ya bauta wa Jehobah da ‘sahihiyar zuciya.’ (1 Sar. 9:4) Da a ce kana rayuwa tare da mutanen Allah a lokacin, yaya za ka ji? Shin abin da Dauda ya yi zai sa ka sanyin gwiwa ko hana ka bauta wa Jehobah ne?

8. (a) Ta yaya manzo Bitrus ya kasa cika alkawarin da ya yi? (b) Me ya sa Jehobah ya ci gaba da amfani da Bitrus bayan kuskuren da ya yi?

8 Wani misali da Littafi Mai Tsarki ya bayar kuma shi ne na manzo Bitrus. Yesu ya zaɓe shi ya zama manzonsa; duk da haka, Bitrus ya faɗi ko kuma yi wasu abubuwa da ba su dace ba a wasu lokatai. Alal misali, a lokacin da aka kama Yesu, manzanninsa sun gudu sun bar shi. Kafin wannan lokacin, Bitrus ya yi da’awa cewa ko da sauran manzannin za su gudu su bar Yesu, shi ba zai gudu ba. (Mar. 14:27-31, 50) Amma, sa’ad da aka kama Yesu, dukan manzannin sun gudu sun bar shi, har da Bitrus. Ƙari ga haka, Bitrus ya musunci sanin Yesu. (Mar. 14:53, 54, 66-72) Daga baya, Bitrus ya tuba, kuma Jehobah ya ci gaba da yin amfani da shi. Da a ce kai almajirin Yesu ne a lokacin, za ka bar abin Bitrus ya yi ya sa ka sanyin gwiwa a bautar ka ga Jehobah?

9. Me ya sa ka tabbata cewa Allah yana yin abin da ya dace a kowane lokaci?

9 Ban da waɗannan, da akwai wasu misalai da yawa game da bayin Jehobah da suka yi abubuwan da ya ɓata wa wasu rai. Idan hakan ya faru da kai, wane mataki ne za ka ɗauka? Shin za ka bar kurakuran da suka yi ya sa ka daina bauta wa Jehobah tare da mutanensa ne, har da waɗanda suke cikin ikilisiyarku? Ko kuma za ka fahimci cewa Jehobah yana ba wa wanda ya yi kuskuren dama don ya tuba, kuma a ƙarshe Jehobah zai daidaita al’amarin a lokacin da ya dace? A wani yanayi kuma, idan waɗanda suka yi zunubi suka ƙi tuba, shin za ka kasance da tabbaci cewa Jehobah zai hukunta masu zunubi kuma ya fid da su daga cikin ikilisiya idan yin hakan ya dace?

KA CI GABA DA KASANCEWA DA AMINCI

10. Mene ne Yesu ya fahimta game da kurakuran Yahuda Iskariyoti da kuma Bitrus?

10 Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da labaran bayin Jehobah da yawa da suka kasance da aminci ga Jehobah da kuma mutanensa duk da kurakuran da wasu suka yi. Alal misali, Bayan Yesu ya yi dare yana addu’a, sai ya zaɓi manzanni 12. Yahuda Iskariyoti yana cikin waɗannan manzannin. Daga baya Yahuda ya ci amanarsa, amma Yesu bai bar wannan zunubin ko kuma abin da Bitrus ya yi ya ɓata dangantakarsa da Ubansa Jehobah ba. (Luk. 6:12-16; 22:2-6, 31, 32) Yesu ya san cewa ba Jehobah ko mutanensa ne suka sa waɗannan abubuwan suka faru ba. Yesu ya ci gaba da yin hidimarsa duk da kurakuran da wasu daga cikin mabiyansa suka yi. Jehobah ya albarkace shi ta wajen tayar da shi daga mutuwa kuma ya naɗa shi Sarkin Mulkin sama.—Mat. 28:7, 18-20.

11. Mene ne Littafi Mai Tsarki ya annabta game da bayin Jehobah a kwanaki na ƙarshe?

11 Yesu bai daina kasancewa da aminci ga Jehobah da kuma mutanensa ba. Hakika, idan muka yi la’akari da abin da Jehobah yake cim ma wa ta wurin bayinsa a wannan kwanaki na ƙarshe, hakan abin ban al’ajabi ne. Babu wata ƙungiyar da ke yin wa’azin bishara a faɗin duniya a yau. Shaidun Jehobah ne kaɗai suke yin hakan don Jehobah ne yake ja-gorar su. Littafin Ishaya 65:14 ya kwatanta farin ciki da kuma haɗin kai da mutanen Allah suke jin daɗin sa a yau sa’ad da ya ce: “Ga shi kuma, bayina za su yi rairawa domin murna a zuci.”

12. Yaya ya kamata mu ɗauki kurakuran wasu?

12 Bayin Jehobah suna farin ciki game da abubuwa masu kyau da suke yi domin Jehobah ne yake musu ja-gora. Amma, mutanen duniya ba su da bege kuma abubuwa sai daɗa muni suke yi don Shaiɗan ne yake mulkin wannan duniya. Ba zai dace mu daina bauta wa Jehobah tare da mutanensa saboda kuskuren da wasu bayinsa suka yi ba. Muna bukatar mu kasance da aminci ga Jehobah da kuma yadda yake tsara abubuwa. Ƙari ga haka, ya kamata mu koyi yadda za mu ɗauki ko kuma bi da yanayin sa’ad wani ya ɓata mana rai.

ME YA KAMATA KA YI SA’AD DA WANI YA ƁATA MAKA RAI?

13, 14. (a) Me ya sa ya dace mu riƙa haƙuri da juna? (b) Wane alkawari ne ya kamata mu riƙa tunawa?

13 Mene ne ya kamata mu yi idan wani ɗan’uwa ya faɗi ko kuma ya yi wani abin da ya ɓata mana rai? Wata shawarar da ke cikin Littafi Mai Tsarki da za mu iya bi ita ce: “Kada ka yi garaje a ranka garin yin fushi; gama wawa ke riƙe da fushi cikin zuciyarsa.” (M. Wa. 7:9) Dukan mu ajizai ne kuma mukan yi kuskure. Saboda haka, ba zai dace mu riƙa tsammani cewa ’yan’uwa za su yi abubuwan da ya dace a kowane lokaci ba. Kuma kada mu bar kurakuransu su hana mu farin ciki a matsayin mutanen Allah a wannan kwanaki na ƙarshe. Mafi muhimmanci, kada mu bar kurakuran wasu su sa mu daina bauta wa Jehobah. Idan muka bar hakan ya faru, za mu rasa gatan yin nufin Allah, ƙari ga haka, ba za mu kasance da begen yin rayuwa a sabuwar duniya ba.

14 Idan muna so mu ci gaba da kasancewa da farin ciki da kuma bege, ya kamata mu riƙa tuna da wannan alkawari mai ban ƙarfafa da Jehobah ya yi: “Ga shi, sabobin sammai da sabuwar duniya na ke halitta: ba za a tuna da al’amura na dā ba, ba kuwa za su shiga zuciya ba.” (Isha. 65:17; 2 Bit. 3:13) Kada ka yarda kurakuran da wasu suka yi su hana ka jin daɗin waɗannan abubuwan da Allah ya yi alkawarin su.

15. Mene ne Yesu ya ce ya kamata mu yi sa’ad da wasu suka yi kuskure?

15 Amma, tun da yake ba ma cikin sabuwar duniya a yanzu, ya kamata mu yi la’akari da ra’ayin Allah a kan yadda za mu bi da al’amura sa’ad da wasu suka faɗa ko kuma suka yi abubuwan da suka ɓata mana rai. Alal misali, ya kamata mu riƙa tuna da wata ƙa’idar da Yesu ya ce: “Idan kuna gafarta wa mutane laifofinsu, Ubanku na sama shi ma za ya gafarta muku. Amma idan ba ku gafarta wa mutane laifofinsu, Ubanku kuma ba za shi gafarta naku laifofin ba.” Ka tuna cewa sa’ad da Bitrus ya yi tambaya ko ya kamata mu gafarta “har so bakwai,” Yesu ya amsa: “Ban ce maka, har so bakwai ba; amma, har bakwai bakwai so saba’in.” Hakika, Yesu yana nufin cewa ya kamata mu riƙa gafartawa a kowane lokaci. Ƙari ga haka, ya dace hakan ya zama mataki na farko da za mu ɗauka.—Mat. 6:14, 15; 18:21, 22.

16. Wane misali mai kyau ne Yusufu ya kafa?

16 Yusufu, ɗan fari cikin ya’ya biyu da Rahila ta haifa wa Yakubu ya kafa misali mai kyau a kan yadda ya kamata a sasanta matsaloli. ’Yan’uwan Yusufu goma suna kishinsa domin mahaifinsu yana son sa sosai. Sai suka sayar da Yusufu zuwa bauta. Bayan shekaru da yawa, nagarin aiki da Yusufu ya yi a ƙasar Masar ya sa ya zama mutum mafi iko na biyu a ƙasar. Sa’ad da aka soma ƙarancin abinci a Kan’ana, ’yan’uwan Yusufu suka zo sayan abinci a ƙasar Masar amma ba su gane shi ba. Shin Yusufu ya yi amfani da ikonsa don ya rama abin da ’yan’uwansa suka yi masa ne? A’a. Maimakon haka, ya gwada ’yan’uwansa don ya ga ko sun canja halinsu. Sa’ad da Yusufu ya ga cewa ’yan’uwansa sun canja da gaske, sai ya bayyana musu kansa. Daga baya, ya ce: “Kada ku ji tsoro: ni zan agaje ku, da ’ya’yanku ƙanana.” Littafi Mai Tsarki ya daɗa cewa: “Ya yi masu ta’aziya ya yi masu magana mai-alheri.”—Far. 50:21.

17. Mene ne za ka yi sa’ad da wasu suka yi abin da bai dace ba?

17 Yana da kyau mu tuna cewa tun da yake dukanmu mukan yi kuskure, wataƙila mu ma muna ɓata wa wasu rai. Idan muka lura cewa mun ɓata wa wani rai, Littafi Mai Tsarki ya gargaɗe mu mu je mu sami mutumin don mu sasanta batun. (Karanta Matta 5:23, 24.) Muna farin ciki idan wasu ba su riƙe mu a zuciya ba, saboda haka, ya kamata mu ma kada mu riƙe su a zuciya. Kolosiyawa 3:13 ta ce: “Kuna haƙuri da juna, kuna gafarta ma juna, idan kowane mutum yana da maganar ƙara game da wani; kamar yadda Ubangiji ya gafarta maku, hakanan kuma sai ku yi.” Littafin 1 Korintiyawa 13:5 ta ce ƙauna “ba ta yin nukura.” Idan muna gafarta wa mutane laifofinsu, Jehobah zai gafarta mana. Hakika, idan ya zo ga batun bi da laifofin da mutane suka yi mana, ya kamata mu yi koyi da yadda Ubanmu yake sha’ani da mu sa’ad da muka yi kuskure.—Karanta Zabura 103:12-14.