Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Jehobah “Allahnmu Ubangiji Daya Ne”

Jehobah “Allahnmu Ubangiji Daya Ne”

‘Ku ji fa, ya Isra’ila: Ubangiji Allahnmu Ubangiji ɗaya ne.’—K. SHA. 6:4.

WAƘOƘI: 138, 112

1, 2. (a) Me ya sa mabiyan addinin Yahudawa suka san kalaman da ke Kubawar Shari’a 6:4 sosai? (b) Me ya sa Musa ya ambaci waɗannan kalaman?

MABIYAN addinin Yahudawa sun yi shekaru da yawa suna ƙaulin kalmomin da ke Kubawar Shari’a 6:4 sa’ad da suke wani addu’a ta musamman da suke kira Shema. Suna yin addu’ar kowane safe da yamma. Ta yin hakan, suna bayyana cewa suna bauta wa Allah shi kaɗai.

2 Musa ya ambaci waɗannan kalmomin sa’ad da yake ban kwana da al’ummar Isra’ila a dutsen Moab, a shekara ta 1473 kafin haihuwar Yesu. A lokacin, al’ummar tana so ta ƙetare kogin Urdun kuma ta shiga Ƙasar Alkawari. (K. Sha. 6:1) Musa ya yi shekaru 40 yana ja-gorarsu. Amma a wannan lokacin, yana so su kasance da gaba gaɗi saboda ƙalubalan da za su fuskanta a gaba. Suna bukata su dogara ga Jehobah kuma su kasance da aminci a gare shi. Furucin Musa na ƙarshe ya ƙarfafa su ba kaɗan ba. Bayan haka, sai ya ambaci dokoki goma da kuma wasu umurnai da Jehobah ya ba wa al’ummar. Ƙari ga haka, ya tuna musu da waɗannan kalamai masu muhimmanci da aka rubuta a Kubawar Shari’a 6:4, 5. (Karanta.)

3. Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna a wannan talifin?

 3 Shin Isra’ilawa da suka taru a wannan wurin tare da Musa ba su san cewa Jehobah Allahnsu “Ubangiji ɗaya” ba ne? Hakika, sun sani. Domin amintattun Isra’ilawa sun bauta wa Allah ɗaya kaɗai, Allahn ubanninsu, wato Ibrahim da Ishaku da kuma Yakubu. Tun da haka ne, me ya sa Musa ya sake tuna musu cewa Jehobah Allahnsu “Ubangiji ɗaya ne”? Shin hakan yana da alaƙa da ƙaunar Jehobah da dukan zuciyarsu da dukan ransu da kuma dukan ƙarfinsu kamar yadda aka ambata a aya ta 5 ne? Ta yaya waɗannan kalaman da ke Kubawar Shari’a 6:4, 5 za su amfane mu a yau?

JEHOBAH ALLAHNMU ƊAYA NE

4, 5. (a) Mene ne ma’anar wannan furucin “Ubangiji ɗaya”? (b) Ta yaya Jehobah ya bambanta da sauran alloli?

4 Babu Wani Kamar Sa. Furucin nan “Ubangiji ɗaya” yana nufin cewa babu wani kamar Jehobah. Musa bai yi amfani da wannan kalaman don ya nuna cewa koyarwar Allah-uku-cikin-ɗaya ƙarya ce ba. Jehobah ne ya halicci sama da ƙasa, shi ne mai mulkin duniya da sararin sama. Babu wani Allah na gaskiya sai shi kuma babu wani Allah kamar sa. (2 Sam. 7:22) Saboda haka, Musa yana tuna wa Isra’ilawa cewa wajibi ne su bauta wa Jehobah da dukan zuciyarsu da ransu da kuma ƙarfinsu. Kada su bi halin al’ummai da ke kusa da su da suke bauta wa alloli dabam-dabam. Ana ganin cewa wasu cikin allolin suna iko bisa halittu.

5 Alal misali, Masarawa suna bauta wa allan rana da ake kira Ra, da kuma allahiyar sama da ake kira Nut, da allan duniya mai suna Geb, da allan kogin Nilu da ake kira Hapi da kuma dabbobi da dama. Jehobah ya nuna cewa ya fi waɗannan allolin ikon sa’ad da ya addabe Masarawa da Annoba Goma. Mutanen Kan’ana sun yi imani da Ba’al, wannan shi ne ainihin allansu. Sun gaskata cewa shi ne ya samar da rai kuma shi ne allan sama da ruwan sama da kuma guguwa. A wurare da yawa, mutane sun ɗauki Ba’al a matsayin alla da ke tsare su. (Lit. Lis. 25:3) Isra’ilawa suna bukata su tuna cewa Allahnsu, wato Jehobah, “Ubangiji ɗaya ne.”—K. Sha. 4:35, 39.

6, 7. Mene ne furucin nan “ɗaya” yake nufi, kuma ta yaya Jehobah ya nuna cewa shi Allah “ɗaya” ne?

6 Ba Ya Canjawa Kuma Shi Mai Aminci Ne. Wannan furucin “ɗaya” yana kuma nufin cewa za a iya dogara da nufinsa da ayyukansa. Jehobah ba Allahn da ba za a iya sanin ayyukansa ba ne. Maimakon haka, shi mai aminci ne, ba ya canjawa kuma shi mai gaskiya ne. Ya yi wa Ibrahim alkawari cewa zuriyarsa za su gāji Ƙasar Alkawari kuma Jehobah ya yi abubuwan ban al’ajabi don ya cika wannan alkawarin. Bayan shekara 430, Jehobah bai fasa cika alkawarin da ya yi ba.—Far. 12:1, 2, 7; Fit. 12:40, 41.

7 Shekaru da yawa bayan haka, sa’ad da Jehobah yake so ya kira Isra’ilawa a matsayin shaidunsa, ya ce: “Ni ne shi; gabana ba a kamanta wani Allah ba, bayana kuma ba za a yi ba.” Don ya nuna cewa ba ya canja nufinsa, Jehobah ya ƙara cewa: “Haka kuwa nake tutur.” (Isha. 43:10, 13, Littafi Mai Tsarki; 44:6; 48:12) Babban gata ne ga Isra’ilawa su zama bayin Jehobah kuma haka ma yake da mu a yau don Jehobah ba ya canjawa kuma za a iya dogara ga dukan ayyukansa!—Mal. 3:6; Yaƙ. 1:17.

8, 9. (a) Mene ne Jehobah yake bukata daga masu bauta masa? (b) Ta yaya Yesu ya nuna cewa kalaman da Musa ya yi suna da muhimmanci sosai?

8 Hakika, Musa ya tuna wa mutanen  cewa Jehobah ba zai daina ƙaunar su ba kuma zai ci gaba da kula da su. Tun da haka ne, ya dace su bauta masa shi kaɗai kuma su ƙaunace shi da dukan zuciyarsu da dukan ransu da kuma dukan ƙarfinsu. An bukaci yara ma su yi hakan don an umurci iyayensu su koyar da su a kowane lokaci.—K. Sha. 6:6-9.

9 Jehobah ba ya canjawa kuma yana cika nufinsa a kowane lokaci. Saboda haka, ya dace a ce dokokinsa da kuma ƙa’idodinsa ba za su canja ba. Idan muna so Jehobah ya amince da ibadarmu, wajibi ne mu bauta masa shi kaɗai kuma mu ƙaunace shi da dukan zuciyarmu da dukan ranmu da kuma dukan ƙarfinmu. Abin da Yesu Kristi ya gaya wa wani mutum ke nan. (Karanta Markus 12:28-31.) Bari mu koyi yadda za mu nuna ta ayyukanmu cewa mun fahimci cewa Jehobah “Allahnmu Ubangiji ɗaya ne.”

KA BAUTA WA JEHOBAH SHI KAƊAI

10, 11. (a) Ta yaya za mu bauta wa Jehobah shi kaɗai? (b) Ta yaya wasu matasa Ibraniyawa suka suna cewa Jehobah Allahn da ya cancanci a bauta masa shi kaɗai ne?

10 Idan muna son Jehobah ya zama Allahnmu shi kaɗai, ya kamata mu bauta masa da dukan zuciyarmu. Ba za mu iya bauta wa Jehobah da wasu alloli a lokaci ɗaya ba, ko kuma mu bi ra’ayoyi da kuma ayyukan bauta ta ƙarya yayin da muke bauta wa Jehobah ba. Ya kamata mu sani cewa Shi ba kawai Allahn da ya fi dukan alloli ko kuma ya fi su iko ba ne amma shi kaɗai ne ya cancanci mu bauta wa.—Karanta Ru’ya ta Yohanna 4:11.

11 A cikin littafin Daniyel, mun karanta game da wasu matasa Ibraniyawa masu suna Daniyel da Hananiah da Mishael, da kuma Azariah. Sun nuna cewa Jehobah ne kaɗai za su bauta wa ta wajen guje wa abincin da Allah ya haramta da kuma sa’ad da suka ƙi bauta wa gunki na zinariya da Nebuchadnezzar ya yi. A gare su, Jehobah ne kaɗai Allahn da ya cancanci a bauta masa. Kuma sun kasance da aminci a gare shi.—Dan. 1:1–3:30.

12. Mene ne ya kamata mu guje wa idan muna so mu bauta wa Jehobah shi kaɗai?

12 Idan muna so mu bauta wa Jehobah shi kaɗai, wajibi ne mu yi hankali don kada wasu abubuwa su hana mu bauta masa da dukan zuciyarmu. Waɗanne irin abubuwa ke nan? A dokoki goma da aka ba wa Isra’ila, Jehobah ya bayyana dalla-dalla cewa kada bayinsa su bauta wa wasu alloli ban da shi kuma kada su bauta wa gumaka. (K. Sha. 5:6-10) A yau, bautar gumaka ya ƙunshi abubuwa da yawa, wasu ma suna da wuyan ganewa. Amma ƙa’idodin Jehobah ba su canja ba. Har ila shi “Ubangiji ɗaya ne.” Ta yaya za mu guji bautar gumaka a yau?

13. Waɗanne abubuwa ne za su iya mamaye hankalinmu har ya shafi ƙaunar mu ga Jehobah?

13 A littafin Kolosiyawa 3:5 (karanta), an ba wa Kiristoci gargaɗi game da abubuwan da za su iya hana su bauta wa Jehobah shi kaɗai. A wannan ayar, an nuna cewa kwaɗayi yana da alaƙa da bautar gumaka. Domin duk wani abin da mutum yake sha’awa zai iya mamaye hankalinsa gaba ɗaya har ya zama kamar alla a gare shi. Ƙari ga haka, idan muka yi la’akari da abin da aka ambata a ayar, za mu ga cewa waɗannan abubuwan suna da alaƙa da kwaɗayi da kuma bautar gumaka. Idan mutum yana sha’awar waɗannan abubuwa fiye da kima, hakan zai iya shafan ƙaunarsa ga Allah. Saboda haka, bai kamata mu bar sha’awar waɗannan abubuwan ta mamaye hankalinmu har Jehobah ya daina kasancewa “Ubangiji ɗaya” a gare mu ba.

14. Wane gargaɗi ne manzo Bulus ya bayar?

 14 Manzo Yohanna ya ba da irin wannan gargaɗin sa’ad da ya ce duk wanda yake ƙaunar abubuwan duniya, wato “kwaɗayin jiki, da sha’awar idanu, da darajar rai ta wofi,” hakan ya nuna cewa “ƙaunar Uba ba ta cikinsa ba.” (1 Yoh. 2:15, 16) Saboda haka, ya kamata mu riƙa bincika kanmu a kai a kai don mu ga ko nishaɗi da abota da saka tufafi da mutanen duniya suke yi ya soma shafanmu. A wani fanni kuma, sha’awar abubuwan duniya ta ƙunshi biɗan “manyan” abubuwa kamar zuwa makarantar jami’a da makamantansu. (Irm. 45:4, 5) Muna gab da shiga sabuwar duniya. Saboda haka, mu yi tunani sosai a kan kalaman da Musa ya yi. Idan muka fahimci cewa Jehobah “Allahnmu Ubangiji ɗaya ne,” kuma muka gaskata da hakan, za mu yi iya ƙoƙarinmu mu bauta masa shi kaɗai kuma a hanyar da yake so.—Ibran. 12:28, 29.

KU KASANCE DA HAƊIN KAI

15. Me ya sa Bulus ya tuna wa Kiristoci cewa Jehobah “Ubangiji ɗaya” ne?

15 Da yake Jehobah “Ubangiji ɗaya” ne, hakan ya nuna cewa yana son bayinsa su kasance da muradi ɗaya da kuma haɗin kai yayin da suke bauta masa. A ƙarni na farko, Yahudawa da Helenawa da Romawa da kuma mutane daga wasu ƙasashe ne suke cikin ikilisiyar Kirista. Sun fito ne daga addinai da kuma al’adu dabam-dabam kuma ra’ayoyinsu ya bambanta. Saboda haka, barin waɗannan abubuwan kafin su zama Kiristoci bai kasance wa wasu daga cikinsu da sauƙi ba. Shi ya sa manzo Bulus ya tuna musu cewa Kiristoci suna bauta wa Allah ɗaya, wato Jehobah.—Karanta 1 Korintiyawa 8:5, 6.

16, 17. (a) Wane annabci ne yake cika a zamaninmu, kuma mene ne sakamakon? (b) Waɗanne abubuwa ne za su iya ɓata haɗin kai da muke mora?

16 Shin yaya yanayin yake a cikin  ikilisiyar Kirista a yau? Annabi Ishaya ya ambata cewa “a cikin kwanaki na ƙarshe,” mutane daga dukan al’ummai za su soma bauta ta gaskiya. Za su ce Jehobah zai “koya mana tafarkunsa, mu kuma mu kama tafiya cikin hanyoyinsa.” (Isha. 2:2, 3) Abin farin ciki ne cewa wannan annabcin yana cika a yau kuma muna shaida hakan! Hakan ya sa ikilisiyoyi da yawa sun kasance da ’yan’uwa daga ƙasashe da al’adu da harsuna dabam-dabam kuma suna bauta wa Jehobah tare. Amma wannan bambanci zai iya haifar da wani ƙalubale.

Kana kyautata haɗin kai da muke mora a cikin ikilisiyar Kirista kuwa? (Ka duba sakin layi na 16-19)

17 Alal misali, yaya kake ji game da Kiristoci da al’adarsu ta bambanta da naka? Wataƙila ba ka saba da yarensu da irin tufafin da suke sakawa da ɗabi’arsu da kuma abincinsu ba. Shin kana guje masu kuma ka yi tarayya kawai da ’yan’uwan da al’adarku ɗaya ce? Idan ka girmi wasu dattawa da ke ikilisiyarku ko da’irarku ko yankin ofishin Shaidun Jehobah da ke ƙasarku, ko kuma idan al’adarku ko launin fatarku ya bambanta da nasu fa? Shin kana barin waɗannan abubuwan su shafi yadda kake sha’ani da su? Idan ba mu yi hankali ba, za mu iya barin irin waɗannan bambance-bambance su ɓata haɗin kai da muke mora a ƙungiyar Jehobah.

18, 19. (a) Wace shawara ce aka ambata a Afisa 4:1-3? (b) Mene ne za mu iya yi don mu sa ikilisiya ta kasance da haɗin kai?

18 Mene ne zai taimaka mana mu guje wa irin waɗannan haɗarurrukan? Da yake Afisa birni ne mai arziki kuma mutanen sun fito daga wurare dabam-dabam, manzo Bulus ya ba wa Kiristoci da ke wurin wata shawara da za ta iya taimaka mana a yau. (Karanta Afisawa 4:1-3.) Ka lura cewa Bulus ya ambaci wasu halaye kamar tawali’u da ladabi da haƙuri da kuma ƙauna. Waɗannan halayen suna kamar ginshiƙai da suke riƙe gida. Hakika, irin wannan gida zai tsaya daram. Amma, wajibi ne a riƙa kula da gidan a kai a kai don ta ci gaba da kasancewa da kyan gani. Haɗin kai da suke mora yana kama da wannan gidan. Manzo Bulus ya gaya wa Kiristoci da ke Afisa su “kiyaye ɗayantuwar Ruhu,” wato su ci gaba da kula ko kuma kyautata haɗin kai da ke tsakaninsu.

19 Ya kamata kowannenmu ya ci gaba da yin iya ƙoƙarinsa don ya sa ikilisiya ta ci gaba da kasancewa da haɗin kai. Mene ne za mu iya yi? Da farko, wajibi ne mu koyi kuma mu nuna waɗannan halayen da Bulus ya ambata, wato tawali’u da ladabi da haƙuri da kuma ƙauna. Bayan haka, mu yi aiki tuƙuru don mu kasance da salama da kuma haɗin kai. Ƙari ga haka, muna bukatar mu yi iya ƙoƙarinmu wajen sulhunta duk wata matsala tsakaninmu da ’yan’uwanmu don mu yi zaman lafiya kuma mu kasance da haɗin kai.

20. Ta yaya za mu nuna cewa mun fahimci cewa Jehobah “Allahnmu Ubangiji ɗaya ne”?

20 Jehobah “Allahnmu Ubangiji ɗaya ne.” Wannan furucin yana da muhimmanci sosai! Musa ya tuna wa Isra’ilawa wannan gaskiyar kuma hakan ya sa sun kasance da gaba gaɗi yayin da suke shiga Ƙasar Alkawari. Idan muka nazarci wannan furucin sosai, hakan zai taimaka mana mu fuskanci ƙunci mai girma da ƙarfin zuciya kuma mu inganta haɗin kai da salama a sabuwar duniya. Bari mu ci gaba da bauta wa Jehobah shi kaɗai ta wajen ƙaunar sa da kuma yi masa ibada da dukan zuciyarmu. Mu riƙa yin iya ƙoƙarinmu don mu kyautata haɗin kai da muke mora a ƙungiyar Jehobah. Idan muka ci gaba da yin hakan, za mu iya kasancewa da bege cewa za mu ga cikar annabcin da Yesu ya yi game da mabiyansa da ya kwatanta da tumaki cewa: “Ku zo, ku masu-albarka na Ubana, ku gaji mulkin da an shirya dominku tun kafawar duniya.”—Mat. 25:34.