Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 TALIFIN NAZARI NA 30

Yadda Za Mu Yi Wa’azi ga Mutanen da Ba Sa Bin Addini

Yadda Za Mu Yi Wa’azi ga Mutanen da Ba Sa Bin Addini

“Na zama kowane irin abu ga ko waɗanne irin mutane domin ko ta yaya in cece waɗansu.”​—1 KOR. 9:22.

WAƘA TA 82 ‘Mu Bari Haskenmu Ya Haskaka’

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Waɗanne canja-canje ne muke gani a wasu ƙasashe a kwana-kwanan nan?

YAWANCIN ʼyan Adam sun kwashi shekaru da yawa suna bin addinai dabam-dabam. Amma a kwana-kwanan nan, wannan yanayin ya canja sosai. Mutane da yawa sun daina bin addini. A wasu ƙasashe ma, yawancin mutane sun ce ba su da addini. *​—Mat. 24:12.

2. Me ya sa mutane da yawa ba sa bin addini?

2 Me ya sa mutane da yawa suka daina bin addini? Wasu sun fi mai da hankali a kan jin daɗin rayuwa ko kuma sun ƙyale matsaloli su shawo kansu. (Luk. 8:14) Wasu kuma sun daina amincewa da wanzuwar Allah. Wasu sun amince da wanzuwar Allah, amma sun ce addini tsohon yayi ne kuma bai jitu da kimiyya ba. Wataƙila suna yawan ji abokansu da malamai da kuma taurari a kafofin yaɗa labarai suna cewa abubuwa sun soma wanzuwa ne ta juyin halitta, amma ba su taɓa jin dalilan da za su iya sa su yarda da wanzuwar Allah ba. Wasu kuma suna fushi domin malaman addinai suna neman kuɗi da kuma iko ruwa-a-jallo. A wasu ƙasashe, an kafa dokokin da suka hana mutane bin addini.

3. Mene ne manufar wannan talifin?

3 Yesu yana so mu sa mutanen dukan duniya su ‘zama almajiransa.’ (Mat. 28:19) Ta yaya za mu iya taimaka wa mutanen da ba su da addini su soma ƙaunar Allah kuma su zama almajiran Yesu? Wajibi ne mu san cewa yadda  mutane suke ɗaukan saƙonmu ya dangana ga yadda aka rene su. Alal misali, yadda Turawa za su ɗauki saƙonmu zai bambanta da ʼyan Asiya. Me ya sa? A Turai, mutane da yawa sun san Littafi Mai Tsarki kuma sun san cewa Allah ne ya halicci kome. Amma a Asiya, yawancin mutane ba su san Littafi Mai Tsarki ba kuma wataƙila ba su yarda da wanzuwar Mahalicci ba. Manufar wannan talifin shi ne ya taimaka mana mu iya ratsa zukatan dukan mutanen da muka haɗu da su a wa’azi.

KA KASANCE DA RA’AYIN DA YA DACE

4. Me ya sa muke bukatar mu nuna ra’ayin da ya dace?

4 Ka Nuna Ra’ayin da Ya Dace. A kowace shekara, da akwai wasu da babu ruwansu da addini a dā da suke zama Shaidun Jehobah. Da yawa cikinsu suna da ɗabi’a mai kyau kuma sun ƙi jinin munafuncin da addinai da yawa suke yi. Wasu ba su da ɗabi’a mai kyau kuma suna da halayen banza da suka bukaci su canja. Da taimakon Jehobah, za mu iya taimaka wa mutane da “suke da zuciya ta samun rai na har abada.”​—A. M. 13:​48, NW; 1 Tim. 2:​3, 4.

Ka yi amfani da dabaru dabam-dabam don ka tattauna da mutanen da ba su yarda da Littafi Mai Tsarki ba (Ka duba sakin layi na 5-6) *

5. Mene ne yake yawan sa mutane su saurari saƙonmu?

5 Ka Yi Fara’a da Kuma Basira. Mutane suna yawan saurarar mu don yadda muka yi musu magana ba don abin da muka ce musu ba. Suna farin ciki idan muka nuna mun damu da su, mun mutunta su kuma muka bi da su cikin basira. Ba ma tilasta musu su bi ra’ayinmu. Maimakon haka, muna ƙoƙari mu fahimci dalilin da ya sa ba sa bin kowane addini. Alal misali, wasu mutane ba sa son tattauna batun addini da baƙo. Wasu kuma suna gani bai dace a tambayi mutum ra’ayinsa game da Allah ba. Ƙari ga haka, wasu ba sa so a gan su suna nazarin Littafi Mai Tsarki, musamman tare da Shaidun Jehobah. Ko da mene ne yanayinsu, muna ƙoƙari mu fahimci yadda suke ji.​—2 Tim. 2:24.

6. Ta yaya manzo Bulus ya bi da mutane dabam-dabam, kuma yaya za mu iya yin koyi da shi?

6 Me za mu iya yi idan wani ba ya so mu ambata kalmar nan: “Littafi Mai Tsarki” ko “halitta” ko “Allah” ko kuma “addini?” Za mu iya yin koyi da misalin manzo Bulus kuma mu yi wa’azi dangane da yanayinsu. Bulus ya yi amfani da Nassosi sa’ad da yake tattaunawa da Yahudawa. Amma a lokacin da ya tattauna da Helenawa a Atina waɗanda ʼyan falsafa ne, bai ambata Littafi Mai Tsarki ba. (A. M. 17:​2, 3, 22-31) Ta yaya za mu iya bin misalinsa? Idan mun haɗu da wani da bai amince da Littafi Mai Tsarki ba, ba zai dace mu ambata Littafi Mai Tsarki kai tsaye ba. Idan ka lura cewa wani ba zai so mutane su ga ana karanta masa Littafi Mai Tsarki ba, kana iya karanta masa a ɓoye ko a na’urarka.

7. Me muke bukatar mu yi don mu yi koyi da misalin manzo Bulus da aka ambata a 1 Korintiyawa 9:​20-23?

7 Ka Nuna Sanin Yakamata Kuma Ka Saurara. Wajibi ne mu fahimci dalilan da suka sa mutanen da muka haɗu da su suke da wani ra’ayi. (K. Mag. 20:5) Ku yi la’akari da misalin Bulus. Ya yi girma da Yahudawa. Amma ya bukaci ya nemi dabarun yi wa mutanen da ba Yahudawa ba wa’azi domin ba su san Nassosi da kuma Jehobah ba sosai ba. Hakazalika, zai dace mu ɗan yi bincike ko kuma mu tattauna da ʼyan’uwan da suka manyanta a cikin ikilisiya domin su bayyana mana ra’ayin mutane a yankinmu.​—Karanta 1 Korintiyawa 9:​20-23.

8. A wace hanya ce za mu iya soma tattaunawa da mutane game da Littafi Mai Tsarki?

8 Maƙasudinmu na yin wa’azi shi ne mu  nemi “mutumin kirki.” (Mat. 10:11) Idan muna so mu yi nasara, dole ne mu sa mutane su furta ra’ayinsu kuma mu saurare su sosai. Wani ɗan’uwa a Ingila yana yawan tambayar mutane ra’ayinsu game da yadda iyalai za su iya yin farin ciki da yadda za a iya renon yara ko kuma yadda za a iya jimre da rashin adalci. Bayan ya saurare su, sai ya ce, “Duba shawarar nan da aka rubuta kusan shekara 2,000 da suka shige.” Sai ya nuna musu wani nassi a wayarsa ba tare da ya ambata sunan nan Littafi Mai Tsarki ba.

MU RATSA ZUCIYAR MUTANE

9. Ta yaya za mu iya taimaka wa mutanen da ba sa so su tattauna game da Allah?

9 Za mu iya ratsa zukatan mutanen da ba sa yawan so su yi magana game da Allah idan muka tattauna batun da ya shafe su. Alal misali, mutane da yawa suna son halitta. Saboda haka, za mu iya cewa: “Idan ka lura, za ka ga cewa ʼyan kimiyya sun kwaikwayi halitta sosai. Alal misali, mutanen da suka ƙera makarho sun kwaikwayi kunne, kyamara kuma ido. Wane ne kake gani ya yi waɗannan halittun? Kana ganin wani ne mai iko ko kuma wani abu ne dabam?” Bayan ka saurare shi sosai, za ka iya ce: “Daga wajen wane ne kake ganin injiniyoyin nan suke koyon abubuwan nan? Abin da wani mawaƙi a zamanin dā ya rubuta ya sa ni mamaki. Ya ce: ‘Shi da ya yi kunne, ba ya ji ne? Shi da ya yi ido, ba ya gani ne? . . . Shi ne yake koya wa mutum!’ Wasu ʼyan kimiyya ma sun amince da hakan.” (Zab. 94:​9, 10) Bayan haka, za mu iya nuna wani bidiyo a dandalin jw.org® a sashen “Ganawa da Labarai” a jerin bidiyoyin nan “Ra’ayin Mutane Game da Halitta.” (Ka duba ƙarƙashin LITTATTAFAI > BIDIYO.) Ko kuma za ku iya ba su ƙasidar nan Was Life Created? ko The Origin of Life​—Five Questions Worth Asking.

10. Ta yaya za mu iya soma tattaunawa da mutumin da ba ya so ya yi magana game da Allah?

10 Yawancin mutane suna ɗokin jin daɗin rayuwa a nan gaba. Amma mutane da yawa suna tsoro cewa za a halaka duniya. Wani mai kula mai ziyara da ke ƙasar Norway ya ce mutane da ba sa so su yi magana game da Allah suna yarda su tattauna game da yanayin duniya. Bayan ya gaishe su, yana yawan cewa: “Wane ne zai sa mu ji daɗin rayuwa a nan gaba? Kana ganin ʼyan siyasa ne ko ʼyan kimiyya ko kuma wani dabam?” Bayan ya saurari maigidan sosai, sai ya karanta nassin da ya nuna yadda  yanayinmu zai canja a nan gaba ko kuma ya ambata abin da nassin ya ce. Wasu mutane suna mamaki sosai idan sun ji cewa duniya za ta dawwama kuma mutane za su yi rayuwa a cikinta har abada.​—Zab. 37:29; M. Wa. 1:4.

11. Me ya sa ya dace mu yi amfani da gabatarwa dabam-dabam, kuma ta yaya za mu iya yin koyi da misalin Bulus da ke Romawa 1:​14-16?

11 Zai dace mu yi amfani da gabatarwa dabam-dabam. Me ya sa? Domin mutane sun bambanta. Abincin wani, gubar wani. Wasu suna son tattaunawa game da Allah ko Littafi Mai Tsarki, wasu kuma sun gwammace tattaunawa game da wani abu dabam. Ko da mene ne yanayinsu, zai dace mu nemi zarafin tattaunawa da dukan mutane. (Karanta Romawa 1:​14-16.) Babu shakka, Jehobah ne yake sa gaskiya ta yi jijiya a zuciyar mutanen da suke son gaskiya.​—1 Kor. 3:​6, 7.

YADDA ZA MU YI WA MUTANEN ASIYA WA’AZI

Masu shela da yawa suna nuna sun damu da mutanen da babu ruwansu da addini kuma suna nuna musu shawarwarin da ke cikin Littafi Mai Tsarki (Ka duba sakin layi na 12-13)

12. Me za mu iya yi don mu taimaka wa mutanen da ke ƙasashen Asiya da ba su san cewa akwai Mahalicci ba?

12 ʼYan’uwa a faɗin duniya suna yawan haɗuwa da mutane daga ƙasashen Asiya, har da ƙasashen da gwamnati ta haramta addini. A ƙasashen Asiya da yawa, mutane da yawa ba su taɓa yin la’akari cewa akwai Mahalicci ba. Wasu cikinsu suna amincewa a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da su, wasu kuma suna ɗan jan jiki. Me za mu iya yi don mu taimaka musu? Wasu masu shela da suka ƙware sun yi nasara wajen tattauna batutuwan da ba su shafi addini ba da mutane, su nuna musu sun damu da su, idan sun ga ya dace, sai su gaya musu yadda suka amfana don sun bi wata ƙa’idar Littafi Mai Tsarki.

13. Me zai iya sa mutane su so Littafi Mai Tsarki? (Ka duba hoton da ke bangon gaba.)

13 Shawarwari masu kyau da ke cikin Littafi Mai Tsarki suna sa mutane da yawa su so Kalmar Allah. (M. Wa. 7:12) Wata ’yar’uwa a Amirka da ta ziyarci ʼyan Caina da ke yaren Mandarin, ta ce: “Ina ƙoƙari in nuna cewa na damu da mutane kuma ina saurarar su. Idan na ga cewa ba su daɗe da shigowa ƙasar ba, ina tambayar su cewa: ‘Yaya harkoki? Kun sami aiki kuwa? Ina fata mutane suna mutunta ku?’ ” A wasu lokuta, hakan yana ba ni zarafin soma tattauna Littafi Mai Tsarki da su. Idan lokaci ne da ya dace, ’yar’uwar tana cewa: “Kana ganin mene ne zai iya sa mutane su zauna lafiya? Za ka so in nuna maka wani karin magana a Littafi Mai Tsarki? Ta ce: ‘Mafarin rikici kamar ɓarkewar ruwa ne, sai ka daina mūsu kafin ya kai ga faɗa.’ Kana ganin wannan shawarar za ta iya taimaka mana mu zauna lafiya da mutane?” (K. Mag. 17:14) Irin wannan tattaunawar za ta iya taimaka mana mu san mutanen da za su so mu sake ziyartar su.

14. Ta yaya wani ɗan’uwa a Asiya yake taimaka wa mutanen da ba su yarda da wanzuwar Allah ba?

14 Me za mu iya gaya wa mutanen da suka ce ba su yarda da wanzuwar Allah ba? Wani ɗan’uwa da ya daɗe yana wa’azi ga mutanen da ke da ra’ayin nan a Asiya, ya ce: “A yawancin lokuta, idan mutane a wannan birnin suka ce ba su ‘yarda da Allah ba,’ abin da suke nufi shi ne cewa ba su yarda da allolin da mutanen birnin suke bauta wa ba. Saboda haka, ina yarda cewa mutane ne suka ƙera yawancin allolin da ake bauta wa. Sai in karanta musu littafin Irmiya 16:20. Ayar ta ce: ‘Ɗan Adam zai iya yi wa kansa alloli ne? Ai, waɗannan ba alloli ba ne!’ Sa’an nan, ina cewa: ‘Ta yaya  za ka iya sanin bambanci tsakanin Allah na gaskiya da na ƙarya?’ Ina saurarar amsar da za su bayar, sai in karanta Ishaya 41:23 da ta ce: ‘Ku faɗa mana abin da zai faru nan gaba, domin mu san cewa ku alloli ne!’ Sai in nuna musu yadda Jehobah ya cika annabcin da ya yi game da nan gaba.”

15. Me za ka iya koya daga wani ɗan’uwa a Gabashin Asiya?

15 Wani ɗan’uwa a Gabashin Asiya yana yin amfani da wannan dabarar sa’ad da yake komawa ziyara. Ya ce: “Ina nuna musu hikimar da ke Littafi Mai Tsarki da annabcin da suka cika da kuma abubuwan da ya ce game da sararin sama da duniya. Sa’an nan, sai in bayyana yadda haka ya nuna cewa akwai Mahalicci mai hikima sosai. Idan mutumin ya soma ganin cewa zai yiwu Allah yana wanzuwa da gaske, sai in nuna masa abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da Jehobah.”

16. Kamar yadda Ibraniyawa 11:6 ta nuna, me ya sa muke bukatar mu taimaka wa ɗalibanmu su yi imani da Allah da Kalmarsa, kuma ta yaya za mu sa su yi hakan?

16 Idan muna nazari da mutanen da ba su yarda da wanzuwar Allah ba, wajibi ne mu ci gaba da taimaka musu su yi imani cewa Allah yana wanzuwa da gaske. (Karanta Ibraniyawa 11:6.) Kuma muna bukatar mu sa su amince da Littafi Mai Tsarki. Don mu cim ma hakan, muna iya bukatar mu maimaita wasu batutuwa sau da yawa. A duk lokacin da muka yi nazari da su, muna iya bayyana abubuwan da suka tabbatar da cewa Littafi Mai Tsarki Kalmar Allah ne. Muna iya tattauna annabcin Littafi Mai Tsarki da suka cika da yadda ya jitu da kimiyya da tarihi da kuma yadda yake taimaka mana yau da kullum.

17. Ta yaya ƙaunar da muke nunawa za ta iya shafan mutane?

17 Muna taimaka wa mutane su zama almajiran Yesu ta wajen nuna musu ƙauna ko da suna da addini ko a’a. (1 Kor. 13:1) Yayin da muke koyar da su, maƙasudinmu shi ne mu nuna cewa Allah yana ƙaunar mu kuma yana so mu ƙaunace shi. A kowace shekara, dubban mutanen da a dā babu ruwansu da addini suna yin baftisma domin sun soma ƙaunar Allah. Saboda haka, ku kasance da ra’ayin da ya dace kuma ku nuna kun damu da dukan mutane. Ku saurare su kuma ku fahimci ra’ayinsu. Ƙari ga haka, ku yi amfani da misalanku masu kyau wajen koya musu su zama almajiran Yesu.

WAƘA TA 76 Yin Wa’azi Na Sa Mu Murna

^ sakin layi na 5 A yau, za mu iya haɗuwa da mutanen da ba su da addini fiye da yadda muke haɗuwa da su a dā. A wannan talifin, an tattauna yadda za mu iya koya musu gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki da yadda za mu iya taimaka musu su amince da Littafi Mai Tsarki kuma su yi imani da Jehobah.

^ sakin layi na 1 Binciken da aka yi ya nuna cewa wasu cikin ƙasashen su ne: Albaniya, Ostareliya, Austriya, Azarbajan, Kanada, Caina, Jamhuriyar Czech, Denmark, Faransa, Jamus, Hong Kong, Ireland, Isra’ila, Japan, Holan, Norway, Koriya ta Kudu, Sifen, Sweden, Siwizalan, Britaniya, da Vietnam.

^ sakin layi na 53 BAYANI A KAN HOTO: Wani ɗan’uwa da ke aiki a asibiti ya yi wa abokin aikinsa wa’azi, daga baya, mutumin ya shiga dandalin jw.org.