Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 TALIFIN NAZARI NA 29

‘Ku Je . . . Ku Sa A Zama Almajiraina’

‘Ku Je . . . Ku Sa A Zama Almajiraina’

“Ku je ku faɗa wa dukan al’umman duniya su bi ni, ku sa su zama almajiraina.”​—MAT. 28:19.

WAƘA TA 60 Domin Su Sami Ceto

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1-2. (a) Me ya sa aka kafa ikilisiyar Kirista kamar yadda Yesu ya faɗa a Matiyu 28:​18-20? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna a wannan talifin?

BABU SHAKKA, manzannin Yesu sun ɗan ruɗe sa’ad da Yesu ya ce su haɗu a kan dutse domin ba su san abin da zai faru ba. Yesu ya gaya masu haka ne bayan ya tashi daga matattu. (Mat. 28:16) Wataƙila a lokacin ne ya “bayyana ga ’yan’uwa fiye da ɗari biyar a lokaci guda.” (1 Kor. 15:6) Mene ne ya sa Yesu ya ce su haɗu? Yana so ya ba su wani aiki mai muhimmanci. Ya ce: “Ku je ku faɗa wa dukan al’umman duniya su bi ni, ku sa su zama almajiraina.”​—Karanta Matiyu 28:​18-20.

2 Waɗannan almajirai da suka ji furucin Yesu ne suka kasance cikin ikilisiyar Kirista ta ƙarni na farko. Ainihin dalilin da ya sa aka kafa ikilisiyar shi ne don a almajirtar da mutane. * A yau, akwai dubban ikilisiyoyi a faɗin duniya kuma dalilin da ya sa aka kafa su ɗaya ne da na ƙarni na farko. Za mu tattauna tambayoyi huɗu a wannan talifin: Me ya sa almajirtarwa yake da muhimmanci? Mene ne yin hakan ya ƙunsa? Dukan Kiristoci ne suke bukatar su yi wannan aikin? Kuma me ya sa muke bukatar haƙuri don mu cim ma wannan aikin?

 ME YA SA ALMAJIRTARWA YAKE DA MUHIMMANCI?

3. Kamar yadda Yohanna 14:6 da 17:3 suka nuna, me ya sa almajirtarwa yake da muhimmanci sosai?

3 Me ya sa almajirtarwa yake da muhimmanci sosai? Domin almajiran Yesu ne kaɗai za su iya zama abokan Allah. Ƙari ga haka, mabiyan Yesu suna kyautata salon rayuwarsu a yanzu kuma suna sa ran jin daɗin rayuwa a nan gaba. (Karanta Yohanna 14:6; 17:3.) Babu shakka, Yesu ya ɗanka mana hakki mai muhimmanci, amma ba ma yin wannan aiki da kanmu. Manzo Bulus ya ce shi da wasu abokan hidimarsa “abokan aiki na Allah ne.” (1 Kor. 3:9) Wannan babban gata ne da Jehobah da Kristi suka ba ʼyan Adam ajizai!

4. Wane darasi ne za mu iya koya daga labarin Ivan da Matilde?

4 Almajirtarwa yana sa mu farin ciki sosai. Ku yi la’akari da misalin Ivan da matarsa Matilde a ƙasar Kolombiya. Sun yi wa’azi ga wani mai suna Davier, kuma ya gaya musu cewa: “Ina so in yi canje-canje a rayuwata, amma hakan ya fi ƙarfina.” Davier ɗan dambe ne da ke shan miyagun ƙwayoyi, yana maye da giya kuma shi da budurwarsa Erika suna zaman dadiro. Ivan ya bayyana cewa: “Mun soma ziyartar sa a wani ƙauye mai nisa kuma muna tuƙa keke na sa’o’i da yawa kuma hanyarsu ba ta da kyau. Sa’ad da budurwarsa Erika ta lura cewa ya soma canja halayensa, sai ita ma ta soma nazarin Littafi Mai Tsarki.” Sannu a hankali, sai Davier ya daina shan ƙwayoyi da giya, kuma ya daina dambe. Ƙari ga haka, shi da Erika suka yi aure. Matilde ta ce: “A lokacin da Davier da Erika suka yi baftisma a shekara ta 2016, sun tuna cewa Davier yana yawan cewa, ‘Ina so in yi canje-canje, amma hakan ya fi ƙarfina.’ Mun yi murna sosai har muka soma zub da hawaye.” Babu shakka, muna matuƙar farin ciki sa’ad da muka taimaka wa mutane su zama almajiran Kristi.

MENE NE YIN HAKAN YA ƘUNSA?

5. Wane mataki ne muke bukatar mu fara ɗauka don mu almajirtar da mutane?

5 Mataki na farko da za mu ɗauka don mu almajirtar da mutane shi ne mu “nemi” mutanen da suke son saƙonmu. (Mat. 10:11) Yin wa’azi ga dukan mutanen da muka haɗu da su zai nuna cewa mu Shaidun Jehobah ne. Bin umurnin da Yesu ya bayar cewa mu riƙa wa’azi zai nuna mu mabiyansa ne.

6. Mene ne zai iya taimaka mana mu yi nasara a wa’azi?

6 Mutane da yawa suna so su koyi gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki, amma wasu ba sa so. Saboda haka, za mu bukaci mu sa su saurare mu. Idan muna so mu yi nasara, wajibi ne mu yi shiri sosai. Ku zaɓi batutuwan da mutane a yankinku za su so ji. Sai ku yi tunani a kan hanyoyin da za ku gabatar da batun.

7. Me za mu iya tattaunawa da mutane, kuma me ya sa yake da muhimmanci mu daraja su?

7 Alal misali, za ku iya tambayar maigida cewa: “Zan so in san ra’ayinka a kan wannan batun. Matsaloli da yawa da muke fama da su a yau suna shafan mutane a faɗin duniya. Kana ganin gwamnatin ʼyan Adam za ta iya magance matsalolin kuwa?” Bayan haka, sai ku karanta littafin Daniyel 2:44. Kuna kuma iya cewa: “Mene ne zai iya  taimaka mana mu tarbiyyar da yaranmu sosai? Zan so in ji ra’ayinka?” Sai ku tattauna Maimaitawar Shari’a 6:​6, 7. Ko da wane batu ne kuke so ku tattauna da maigida, zai dace ku tattauna batun da za su so su saurara. Ku yi tunani a kan yadda za su amfana don koyan gaskiyar da ke Littafi Mai Tsarki. Sa’ad da kuke tattaunawa da su, zai dace ku saurare su sosai kuma ku daraja ra’ayinsu. Yin hakan zai taimaka muku ku fahimce su sosai kuma za su so su saurare ku.

8. Me ya sa za mu iya ziyartar mutum sau da yawa kafin ya yarda a yi nazari da shi?

8 Kafin mutum ya yarda mu yi nazarin Littafi Mai Tsarki da shi, za mu bukaci mu koma ziyara wurinsa sau da yawa. Me ya sa? Domin wataƙila ba za mu tarar da su a gida ba. Ƙari ga haka, wataƙila za ka koma ziyara sau da yawa kafin maigidan ya yarda a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da shi. Ku tuna cewa idan muka shuka iri, za mu bukaci mu riƙa zuba masa ruwa a kai a kai don ya yi girma. Hakazalika, mutanen da muka yi musu wa’azi za su ƙaunaci Jehobah da kuma Yesu idan muna tattauna Kalmar Allah da su a kai a kai.

DUKAN KIRISTOCI NE SUKE BUKATAR SU ALMAJIRTAR DA MUTANE?

Shaidu a faɗin duniya suna saka hannu wajen neman mutanen da ke so su bauta wa Allah (Ka duba sakin layi na 9-10) *

9-10. Me ya sa muka ce dukanmu muna saka hannu wajen taimaka wa wani ya zama mabiyin Yesu?

9 Kowane Kirista yana da hakkin neman mutane masu son gaskiya. Za mu iya kwatanta wannan aikin da neman ƙaramin yaron da ya ɓace. A wace hanya? Ku yi la’akari da labarin wani ɗan shekara uku da ya ɓace. Mutane wajen 500 sun fita neman yaron amma sun rasa. Bayan wajen awa 20 da ɓacewar yaron, sai wani mutum ya gan shi a wani  fili. Mutumin bai yarda cewa shi ne ya samo yaron ba. Ya ce: “Ɗarurruwan mutane ne suka samo shi.”

10 Za mu iya kamanta mutane da yawa a wannan duniyar da yaron nan da ya ɓace. Suna cikin tsaka mai wuya kuma suna bukatar taimako. (Afis. 2:12) Mu Shaidun Jehobah fiye da miliyan takwas ne muke aiki tuƙuru don mu nemi mutanen da ke so su bauta wa Jehobah. Zai yiwu cewa ba ka sami zarafin yin nazari da wani ba. Amma wasu masu shela da kuke wa’azi tare, za su iya samun mutanen da ke so a yi nazarin Kalmar Allah da su. Sa’ad da wani ɗan’uwa ko ’yar’uwa ta taimaka wa wani ya zama almajirin Yesu, dukanmu muna murna domin mun yi aikin tare.

11. A waɗanne hanyoyi ne za ka iya almajirtar da mutane ko da ba ka yin nazari da wani?

11 Ko da ba ka da wani da kake nazarin Littafi Mai Tsarki da shi yanzu, za ka iya taimaka wajen almajirtarwa a waɗansu hanyoyi. Alal misali, za ka iya marabtar sababbin mutanen da suka halarci taronmu kuma ka zama abokinsu. Idan ka yi haka, za ka sa su kasance da tabbaci cewa Kiristoci na gaskiya suna ƙaunar juna. (Yoh. 13:​34, 35) Kalaminka a taro ko da gajere ne zai taimaka musu su furta abin da suka yi imani da shi a hanyar da kowa zai amfana. Za ka kuma iya fita wa’azi tare da sabon mai shela kuma ka koya masa yin amfani da Nassosi a wa’azi. Idan ka yi haka, za ka koya masa ya yi koyi da Kristi.​—Luk. 10:​25-28.

12. Muna bukatar baiwa ta musamman kafin mu almajirtar da mutane? Ka bayyana.

12 Bai kamata kowannenmu ya yi tunani cewa yana bukatar baiwa ta musamman kafin ya zama almajirin Yesu ba. Me ya sa? Ka yi la’akari da misalin wata mai suna Faustina da ke zama a ƙasar Bolivia. A lokacin da Shaidun Jehobah suka soma nazari da ita, ba ta iya karatu ba. Sai ta soma koyon karatu, amma ba ta iya sosai ba. A yanzu ta yi baftisma kuma tana jin daɗin koyar da mutane. Tana nazari da mutane biyar a kowane mako. Ko da yake ba ta iya karatu kamar ɗalibanta ba, amma ta taimaka wa mutane shida su yi baftisma.​—Luk. 10:21.

13. Ko da muna aiki tuƙuru, ta yaya za mu iya amfana idan muna wa’azi?

13 Kiristoci da yawa suna aiki tuƙuru. Duk da haka, suna keɓe lokaci don su gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane kuma suna murna sosai. Ku yi la’akari da misalin wata mai suna Melanie da ke zama a jihar Alaska tare da ʼyarta mai shekara takwas. Tana aiki na cikakken lokaci kuma tana kula  da babanta da ke fama da cutar kansa. Melanie ce kaɗai Mashaidiya a garinsu. Tana yawan yin addu’a cewa Allah ya ba ta ƙarfi ta fita wa’azi duk da sanyin da ake yi a garin domin tana so ta sami ɗalibi. Daga baya, sai ta haɗu da wata mai suna Sara wadda ta yi farin ciki sa’ad da ta koya cewa sunan Allah Jehobah ne. Bayan ɗan lokaci, sai Sara ta yarda a yi nazari da ita. Melanie ta ce: “Ina gajiya sosai a ranakun Jumma’a da yamma, amma ni da ʼyata mun amfana sosai don muna zuwa gudanar da nazari da ita. Ni da ʼyata muna jin daɗin yin bincike a kan tambayoyin da Sara ta yi, kuma mun yi farin cikin ganin yadda ta zama abokiyar Jehobah.” Sara ta jimre da tsanantawa, ta daina zuwa coci kuma ta yi baftisma.

ME YA SA MUKE BUKATAR HAƘURI DON MU CIM MA HIDIMARMU?

14. (a) Me ya sa almajirtarwa yake kamar aikin kamun kifi? (b) Mene ne furucin Bulus da ke 2 Timoti 4:​1, 2, za su motsa ka ka yi?

14 Kada ka yi sanyin gwiwa ko da ba ka taimaka wa wani ya zama almajirin Yesu ba. Ka tuna cewa Yesu ya kamanta almajirtarwa da sana’ar kamun kifi. Masu kamun kifi suna iya yin sa’o’i da yawa kafin su sami kifi. Suna yawan zuwa aiki da tsakar dare ko kuma da asuba, kuma a wasu lokuta, suna yin tafiya mai nisa. (Luk. 5:5) Hakazalika, masu aikin almajirtarwa suna kwashe sa’o’i da yawa wajen neman mutane a wurare dabam-dabam da kuma lokuta dabam-dabam. Me ya sa? Domin suna so su haɗu da mutane. ʼYan’uwa da ke yin iya ƙoƙarinsu  suna yawan haɗuwa da mutanen da ke son saƙonmu. Zai dace ku riƙa zuwa wa’azi a lokaci da kuma wuraren da za ku fi samun mutane a gida.​—Karanta 2 Timoti 4:​1, 2.

Ku taimaka wa ɗalibanku su san Jehobah, su ƙaunace shi kuma su yi masa biyayya (Ka duba sakin layi na 15-16) *

15. Me ya sa muke bukatar haƙuri sa’ad da muke nazari da mutane?

15 Me ya sa muke bukatar haƙuri sa’ad da muke nazari da mutane? Dalili ɗaya shi ne domin muna bukatar mu taimaka wa ɗalibanmu su san koyarwar Littafi Mai Tsarki kuma su so koyarwar. Kuma muna bukatar mu taimaka musu su ƙaunaci Mawallafin Littafi Mai Tsarki, wato Jehobah. Ƙari ga haka, muna bukatar mu koya wa ɗalibanmu umurnin Yesu ga almajiransa da kuma yadda za su bi umurnin. Ya kamata mu yi haƙuri da su yayin da suke ƙoƙari su bi ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. Wasu suna iya canja halayensu cikin ʼyan watanni. Wasu kuma suna kwashe shekaru da yawa kafin su yi canje-canje.

16. Mene ne ka koya daga labarin Raúl?

16 Wani mai wa’azi a ƙasar Peru ya shaida abin da ya sa haƙuri yake da muhimmanci. Ya ce: “Akwai lokacin da na yi nazari da wani mai suna Raúl, har mun kammala littattafai biyu. Duk da haka, yana fama da matsaloli sosai. Yana samun matsaloli a aurensa, yana zage-zage kuma yaransa ba sa masa ladabi. Mutumin ba ya fasa halartan taro. Saboda haka, na ci gaba da ziyartar sa domin in taimaka wa shi da iyalinsa. Fiye da shekara uku bayan farkon haɗuwarmu, sai ya yi baftisma.”

17. Mene ne za mu tattauna a talifi na gaba?

17 Yesu ya umurce mu cewa: “Ku je ku faɗa wa dukan al’umman duniya su bi ni, ku sa su zama almajiraina.” Sa’ad da muke yin wannan aikin, muna yawan haɗuwa da mutanen da tunaninsu da kuma ra’ayinsu ya bambanta da namu. A wasu lokuta, muna ma haɗuwa da mutanen da ba su da addini ko kuma ba su yarda da wanzuwar Allah ba. A talifi na gaba, za mu tattauna yadda za mu iya yi wa waɗannan mutanen wa’azi.

WAƘA TA 68 Mu Taimaki Mutane Su Bauta wa Jehobah

^ sakin layi na 5 Ainihin dalili da ya sa aka kafa ikilisiyar Kirista shi ne don a taimaka wa mutane su zama almajiran Yesu. Wannan talifi yana ɗauke da shawarwari masu kyau da za su taimaka mana mu cim ma hidimarmu.

^ sakin layi na 2 MA’ANAR WASU KALMOMI: Ba koyan abubuwan da Yesu ya koyar kaɗai ba ne almajiransa suke yi ba. Suna aikata abin da suke koya. Suna yin iya ƙoƙarinsu don su bi misalin Yesu a rayuwarsu.​—1 Bit. 2:21.

^ sakin layi na 52 BAYANI A KAN HOTO: Wani mutum da zai je hutu ya karɓi warƙa daga wurin Shaidu a tashar jirgin sama. Daga baya, ya sake ganin wasu Shaidu suna wa’azi da amalanke sa’ad da yake yawon buɗe ido. Bayan ya dawo gida, sai wasu Shaidu suka je su yi masa wa’azi a gidansa.

^ sakin layi na 54 BAYANI A KAN HOTO: Mutumin ya yarda a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da shi. Daga baya, ya yi baftisma.