Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 TARIHI

Jehobah Ya Albarkace Ni Fiye da Yadda Na Yi Tsammani

Jehobah Ya Albarkace Ni Fiye da Yadda Na Yi Tsammani

‘NA SO yin hidimar majagaba, amma na ɗauka ba zan ji daɗin ta ba.’ Ina son aikin da nake yi a Jamus. Mukan kai abinci zuwa wurare dabam-dabam a Afirka, kamar su Dar es Salaam da Elisabethville da kuma Asmara. Ban taɓa yin tunanin cewa wata rana zan yi hidima ta cikakken lokaci a waɗannan wuraren da kuma wasu a Afirka ba!

Da na daina shakka kuma na soma hidimar majagaba, rayuwata ta canja a hanyar da ban taɓa tsammani ba. (Afis. 3:20) Kuna iya tunani cewa ta yaya hakan ya faru? Bari in ba ku labarin.

An haife ni a birnin Berlin a Jamus, ’yan watanni bayan an soma Yaƙin Duniya na Biyu a shekara ta 1939. Sa’ad da aka kusan daina yaƙin a shekara ta 1945, sojoji sun kawo wa Berlin hari kuma sun jefa bama-bamai daga jirgin sama. Akwai lokaci da bam ɗin ya faɗi a unguwarmu, amma ni da iyayena da ƙanwata mun gudu mun ɓuya. Bayan haka, sai muka gudu zuwa birnin Erfurt, wurin da aka haifi mahaifiyata don mu sami kāriya.

Ni da iyayena da ƙanwata a Jamus a wajen shekara ta 1950

Mahaifiyata ta yi ƙoƙari ta san gaskiya game da Allah. Don haka, ta karanta littattafan da ’yan ilimin falsafa suka wallafa, kuma ta bincika addinai da yawa, amma ba ta gamsu ba. A wajen shekara ta 1948, Shaidun Jehobah guda biyu sun zo gidanmu yin wa’azi. Mahaifiyata ta saurare su kuma ta yi musu tambayoyi da yawa. Bai kai awa guda ba, sai ta gaya wa ni da ƙanwata cewa, “Na sami gaskiya!” Nan ba da daɗewa ba, ni da mahaifiyata da kuma ƙanwata muka soma halartan taro a birnin Erfurt.

A shekara ta 1950, mun ƙaura zuwa birnin Berlin kuma muka soma halartan taro da ikilisiyar Berlin-Kreuzberg. Sa’ad da muka sake ƙaura zuwa wani wuri a Berlin, mun soma halartan taro a ikilisiyar Berlin-Tempelhof. Da shigewar lokaci, mahaifiyata ta yi baftisma, amma ni ban yi ba. Me ya sa?

YADDA NA DAINA JIN KUNYA

Ban saka ƙwazo a hidimar Jehobah ba, domin ina jin kunya sosai. Na ɗau shekara biyu ina fita wa’azi, amma bana yi wa mutane wa’azi. Abubuwa sun canja sosai sa’ad da na soma cuɗanya da ’yan’uwa maza da mata da suka riƙe amincinsu ga Jehobah. Wasu an saka su a kurkukun ’yan Nazi ko kuma kurkuku a Gabashin Jamus. Wasu kuma sun shigar da littattafai Gabashin Jamus duk da cewa za a iya  kama su kuma a saka su a kurkuku. Misalansu ya burge ni sosai. Na yi tunanin cewa idan waɗannan ’yan’uwa sun sadaukar da ransu da kuma ’yancinsu domin Jehobah da kuma ’yan’uwansu, ina bukatar in yi ƙoƙari don in daina jin kunya.

Na ɗan daina jin kunya sa’ad da na saka ƙwazo a wa’azi na musamman da aka yi a shekara ta 1955. A wata wasiƙa da aka wallafa a ƙasidar Informant, * Ɗan’uwa Nathan Knorr ya sanar cewa wannan wa’azi da za a yi shi ne mafi girma da ƙungiyarmu ta taɓa shiryawa. Ya ce idan duka masu shela suka yi himma, “wa’azi a watan zai zama mafi muhimmanci da aka taɓa yi a duniya.” Kuma abin da ya faru ke nan! Ba daɗewa ba, sai na yi alkawarin bauta wa Jehobah. A shekara ta 1956, ni da mahaifina da ƙanwata muka yi baftisma. Jim kaɗan bayan haka, na bukaci tsai da muhimmiyar shawara.

Na san cewa ina bukatar in soma yin hidimar majagaba, amma na yi tunanin cewa zan yi hakan a nan gaba. Da farko, na tsai da shawarar koyan sana’ar sayan abubuwa a Berlin da kuma sayar da su a wasu ƙasashe. Na so in ci gaba da yin wannan sana’ar don in ƙware sosai kafin in zama majagaba. Don haka, a shekara ta 1961, sai na soma aiki a Hamburg, birnin da babban tashan jirgin ruwa a Jamus take. Ina son wannan sana’ar sosai, kuma hakan ya hana ni soma yin hidimar majagaba. Mene ne zan yi?

Ina farin ciki Jehobah ya yi amfani da ’yan’uwa don ya taimaka mini in fahimci cewa bauta masa ita ce abu mafi muhimmanci a rayuwa. Abokaina da yawa sun soma yin hidimar majagaba kuma sun kafa mini misali mai kyau. Ƙari ga haka, Ɗan’uwa Erich Mundt wanda aka taɓa saka a kurkuku, ya ƙarfafa ni in dogara ga Jehobah. Ɗan’uwan ya gaya mini cewa sa’ad da suke kurkuku, ’yan’uwan da suka dogara ga kansu sun karaya. Amma waɗanda suka dogara ga Jehobah sun riƙe aminci kuma daga baya sun taimaka wa ƙungiyar Jehobah.

A lokacin da na soma yin hidimar majagaba a 1963

Ban da haka, Ɗan’uwa Martin Poetzinger wanda daga baya ya yi hidima a matsayin memban Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu, ya ci gaba da ƙarfafa ’yan’uwan, ya ce, “Ƙarfin zuciya shi ne hali mafi muhimmanci da kuke bukata!” Bayan na yi tunani sosai a kan kalmomin nan, sai na yi murabus kuma na soma yin hidimar majagaba a watan Yuni 1963. Wannan ne shawara mafi kyau da na taɓa tsai da! Bayan watannin biyu, kafin in soma neman aiki, an ce in yi hidimar majagaba na musamman. Bayan ʼyan shekaru, Jehobah ya albarkace ni fiye da yadda na yi tsammani. An gayyace ni in halarci aji na 44 na Makaranta Gilead.

NA KOYI DARASI MAI MUHIMMANCI A GILEAD

Ɗaya daga cikin darussa masu muhimmanci da na koya, musamman daga wurin Ɗan’uwa Nathan Knorr da Lyman Swingle shi ne cewa, “Kada ku yi sanyi gwiwa a hidimarku.” Sun ƙarfafa mu mu ci gaba da yin hidimarmu ko da mun fuskanci matsaloli. Ɗan’uwa Nathan ya ce: “Mene ne za ku mai da wa hankali? Za ku mai da hankali ne ga dattin wurin ko ƙwari ko talaucin da mutanen ke fama da shi? Ko kuma za ku mai da hankali ga bishiyoyi da furanni da kuma yadda mutanen ke farin ciki? Ku ƙaunaci mutanen!” Akwai wata rana sa’ad da Ɗan’uwa Swingle yake gaya mana dalilan da ke sa wasu su karaya, sai idanunsa suka cika da hawaye. Sai ya ɗan dakata don hankalinsa ya kwanta. Hakan ya sosa zuciyata sosai kuma na ƙuduri niyyar cewa ba zan taɓa sa Yesu ko ’yan’uwansa masu aminci baƙin ciki ba.​—Mat. 25:40.

Ni da ɗan’uwa Claude da Heinrich sa’ad da muke wa’azi a ƙasar waje a Lubumbashi da ke Kwango a 1967

Sa’ad da muka sauke karatu, wasu a Bethel sun tambaye mu uku inda aka tura mu yin hidima. Sun yi kalami masu daɗi sa’ad da ’yan ajinmu suke gaya musu inda aka tura su. Amma da ya zo kaina sai na ce: “Kwango (Kinshasa).” Ba su ce kome ba sai, “Kwango, to! Jehobah ya kāre ka!” A wannan lokacin, ana yaɗa labarai sosai game da faɗa da kashe-kashe da ake yi a Kwango. Amma abin da nake tunani shi ne abubuwan da na koya a Gilead. Jim kaɗan bayan mun sauke karatu a watan Satumba 1967, ni  da Ɗan’uwa Heinrich Dehnbostel da Claude Lindsay, muka tafi Kinshasa, babban birnin ƙasar Kwango.

WURI MAI KYAU DA MUKA KOYI DARASI

Sa’ad da muka isa Kinshasa, mun ɗau watanni uku muna koyan Faransanci. Sai muka je birnin Lubumbashi wanda a dā ake kira Elisabethville da ke kusa da iyakar ƙasar Zambiya ta kudancin Kwango. Mun je masauƙin ’yan’uwan da ke wa’azi a ƙasar waje a tsakiyar birnin.

Da yake ba a taɓa yin wa’azi a wurare da yawa a Lubumbashi ba, mun yi farin ciki sosai cewa mu ne za mu fara yi wa mutane wa’azi game da Mulkin Allah a wuraren. Nan ba da daɗewa ba, mun sami ɗalibai da yawa har ba mu da lokacin yin nazari da wasu. Ban da haka, mun yi wa hukumomi wa’azi. Da yawa daga cikinsu suna daraja Kalmar Allah da kuma wa’azin da muke yi. Yaren da yawancin mutanen ke yi shi ne Swahili. Don haka, ni da ɗan’uwa Claude Lindsay mun koyi wannan yaren. Bayan haka, sai aka tura mu ikilisiyar da ake yaren Swahili.

Ko da yake mun ji daɗin hidimarmu, mun fuskanci matsaloli sosai. Sau da yawa, sojoji ko kuma ’yan sanda da suka bugu suna tuhumarmu da laifin da ba mu aikata ba. Akwai wata rana da ’yan sanda da yawa suka shigo masauƙin masu wa’azi a ƙasar waje sa’ad da muke taro kuma suka kai mu ofishinsu. Sun sa mu zauna a ƙasa har sai wajen ƙarfe goma na dare kafin suka bar mu mu tafi.

A shekara ta 1969, na soma yin hidimar mai kula mai ziyara. Sa’ad da nake wannan hidimar, nakan yi tafiya mai nisa a cikin laka da  dogayen ciyayi. A wani ƙauyen da na kai ziyara, kaza da ’ya’yanta suna kwana a ƙarƙashin gadona. Ba zan taɓa manta da yadda suke tashe ni daga barci da asuba ba. Kuma na tuna yadda ni da ’yan’uwan da yamma mukan zauna muna shan ɗumi kuma muna taɗi.

Wata babbar matsala da muka fuskanta ita ce mutanen da suka yi da’awar su Shaidun Jehobah ne, amma magoya bayan ƙungiyar Kitawala ne. * Wasu daga cikinsu sun yi baftisma kuma sun zama dattawa a ikilisiya. ’Yan’uwa sun fallasa asirin da yawa cikin mutanen nan. (Yahu. 12) Jehobah ya cire su daga ikilisiya. Bayan haka, mutane da yawa sun soma bauta wa Jehobah.

A shekara ta 1971, an tura ni yin hidima a ofishinmu da ke Kinshasa. A wurin, na yi hidimomi dabam-dabam kamar su rubuta wasiƙu da odar littattafai da kuma magance matsalolin da masu hidima suke fuskanta. A Bethel, na koyi yadda zan tsara ayyukanmu a ƙasar da ke fama da talauci. A wasu lokuta, littattafan da muke tura wa ikilisiyoyi ta jirgin sama yakan ɗau watanni kafin ya isa. Bayan haka, sai a saukar da littattafan daga jirgin sama kuma a loda su a jirgin ruwa. Sau da yawa, jirgin yana maƙalewa a cikin ciyayin da ke girma a ruwa. Duk da haka, mun cim ma hidimarmu.

Yadda ’yan’uwan suke tsara manyan taro duk da cewa ba su da kuɗi sosai ya burge ni. Suna mayar da gidan gara ya zama dakalin magana, sai su yi amfani da zana don su yi shinge da kuma ƙera wurin zama. Suna yin amfani da itacen bamboo don gina gida, sai su jinke ta da zana ko kuma su yi teburi da ita. Ƙari ga haka, suna yin amfani da ɓawon itace maimakon kūsa. Waɗannan ’yan’uwan sun burge ni sosai. Na ƙaunace su sosai. Na yi kewar su sa’ad da aka tura ni yin hidimar a wani wuri!

YIN HIDIMA A KENYA

A shekara ta 1974, an tura ni zuwa ofishinmu da ke birnin Nairobi a Kenya. Muna da ayyuka sosai domin ofishin da ke Kenya ne ke kula da ƙasashe goma da ke kusa da ita. Amma an saka wa aikinmu taƙunƙumi a wasu daga cikin waɗannan ƙasashe. Sau da yawa an tura ni in ziyarci waɗannan ƙasashen, musamman a Habasha inda ake tsananta wa ’yan’uwan sosai a wannan lokacin. Ana wulaƙanta ’yan’uwa da yawa ko kuma a saka su a kurkuku, wasu ma har kashe su aka yi. Duk da haka, sun jimre don suna da dangantaka mai kyau da Jehobah da kuma ’yan’uwansu.

A shekara ta 1980, wani abu na musamman ya faru da ni sa’ad da na auri Gail Matheson. Muna aji ɗaya da ita a Makarantar Gilead kuma ita ’yar ƙasar Kanada ce. Muna rubuta wa juna wasiƙa. Gail tana wa’azi a ƙasar waje a Bolivia. Bayan shekaru 12, sai muka sake haɗuwa a birnin New York. Ba da daɗewa ba bayan haka, sai muka yi aure a Kenya. Ina godiya domin Gail tana da dangantaka mai kyau da Jehobah kuma ta gamsu da abubuwan da take da shi. Har yanzu tana taimaka mini kuma tana ƙauna ta.

A shekara ta 1986, ni da matata mun soma yin hidimar mai kula mai ziyara da kuma hidima a matsayin Memban Kwamitin da Ke Kula da Ofishinmu a ƙasar. Hidimar mai kula mai ziyara da muka yi ya ƙunshi ziyartar ƙasashen da ofishin Kenya ke kula da su.

Ina ba da jawabi a taron yanki a Asmara a 1992

Ba zan manta da yadda na tsara taron yanki a ƙasar Asmara (yanzu Eritrea) a shekara ta 1992 ba, kuma a lokacin an saka wa aikinmu taƙunƙumi. Abin takaici, wurin da muka samu don yin taron ba shi da kyaun gani musamman ma cikin. A ranar taron, na yi mamaki sosai don yadda ’yan’uwan suka gyara wurin da kyau don mu bauta wa Jehobah. Iyalai da yawa sun kawo kayan ado kuma suka rufe dukan wani abin da bai da kyaun gani. Mun ji daɗin taron kuma mutane 1,279 ne suka halarta.

 Hidimar mai kula mai ziyara ya yi dabam sosai domin ana canja mana masauƙi a kowane mako. Akwai wani lokacin da muka zauna a wani gida mai kyau a kusa da teku, a wani lokacin kuma mun zauna a gidan kwano kuma bayan gidan yana da nisa fiye da kafa 300. Amma abubuwan da ba za mu manta da su ba shi ne yadda muke fita wa’azi tare da ’yan’uwa da kuma majagaba masu ƙwazo sosai. Sa’ad da aka canja hidimarmu, mun yi kewar abokanmu sosai.

MUN SAMI ALBARKA A HABASHA

A shekara ta 1987 zuwa wajen 1992, ƙasashe da yawa sun cire taƙunƙumin da suka saka wa aikinmu. A sakamakon haka, an kafa ofisoshi a ƙasashen. A shekara ta 1993, an tura mu yin hidima a ofishinmu da ke Addis Ababa a Habasha wurin da aka ɗau shekaru da yawa muna yin aikinmu a ɓoye, amma gwamnati ta cire taƙunƙumin.

A lokacin da nake yin hidimar mai kula mai ziyara a Habasha a 1996

Jehobah ya albarkaci aikin da aka yi a Habasha. ’Yan’uwa da yawa sun soma yin hidimar majagaba. Fiye da kashi 20 na masu shela a ƙasar suna yin hidimar majagaba kowace shekara tun 2012. Ƙari ga haka, Makarantun ƙungiyar Jehobah suna kan horar da ’yan’uwan kuma an gina Majami’ar Mulki fiye da 120. A shekara ta 2004, iyalin Bethel sun ƙaura zuwa sabon ofishi. Ƙari ga haka, ’yan’uwan suna amfana sosai daga sabon Majami’ar Babban Taron da aka gina.

Da shigewar lokaci, ni da matata mun ƙulla abokantaka da ’yan’uwanmu a Habasha. Muna ƙaunar su sosai domin suna ƙaunar mu kuma suna da alheri. Yanzu ba mu da ƙoshin lafiya, don haka, an tura mu ofishinmu da ke Turai na Tsakiya. Ana kula da mu sosai a nan, amma muna kewar abokanmu da suke Habasha.

JEHOBAH YA SA AN SAMI ƘARUWA

Mun ga yadda Jehobah ya sa aikinsa ya sami ci gaba sosai. (1 Kor. 3:​6, 9) Alal misali, a lokacin da na fara yi wa wani ɗan Ruwanda da ya zo Kwango haƙa jan ƙarfe wa’azi, babu wanda yake bauta Jehobah a ƙasarsu. Amma yanzu akwai sama da mutane 30,000 da ke bauta wa Jehobah a ƙasar. A shekara ta 1967, akwai wajen mutane 6,000 da suke bauta wa Jehobah a Kwango (Kinshasa.) Amma yanzu da akwai wajen mutane 230,000, kuma mutane fiye da miliyan ɗaya ne suka halarci taron Tunawa da Mutuwar Yesu a shekara ta 2018. Dukan ƙasashen da ofishinmu da ke Kenya ke kula da su an sami ƙaruwar masu shela fiye da 100,000.

Fiye da shekaru 50 da suka shige, Jehobah ya yi amfani da ’yan’uwa da yawa don ya taimaka mini na soma yin hidima ta cikakken lokaci. Ko da yake har yanzu ni mutum ne mai jin kunya, na koyi in dogara ga Jehobah da dukan zuciyata. Abubuwan da na fuskanta a Afirka su taimaka mini na zama mai haƙuri kuma na sami gamsuwa. Yadda ’yan’uwan suke nuna karimci da yadda suke jimre matsaloli da kuma yadda suke dogara ga Jehobah, yana burge ni da matata. Ina yi wa Jehobah matuƙar godiya don wannan gata da ya ba ni. Babu shakka, Jehobah ya albarkace ni fiye da yadda na yi tsammani.​—Zab. 37:4.

^ sakin layi na 11 Daga baya ana kiran sa Hidimarmu ta Mulki, amma yanzu ana kiran sa Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu.

^ sakin layi na 23 An ɗauko kalmar nan “Kitawala” daga yaren Swahili kuma yana nufin “mulki ko shugabanci ko kuma gwamnati.” Manufar mutanen nan shi ne su sami ’yanci daga ƙasar Belgium. Sun karɓi littattafan Shaidun Jehobah, sun nazarta su kuma sun rarraba littattafan. Sun canja koyarwar Littafi Mai Tsarki don su goyi bayan ra’ayinsu na siyasa da al’adunsu da kuma salon rayuwarsu da bai dace ba.