Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Yadda Za Ka Sa Nazarin Littafi Mai Tsarki Ya Kara Dadi da Kuma Inganci

Yadda Za Ka Sa Nazarin Littafi Mai Tsarki Ya Kara Dadi da Kuma Inganci

DA AKWAI wani ƙalubalen da Yoshuwa ya fuskanta. Yana bukatar ya yi wa al’ummar Isra’ila ja-goranci zuwa Ƙasar Alkawari duk da matsalolin da zai fuskanci. Amma Jehobah ya ƙarfafa shi kuma ya tabbatar masa da cewa zai yi nasara. Ya ce: ‘Ka yi ƙarfin zuciya ƙwarai! Ka kiyaye dukan Koyarwar da bawana Musa ya ba ka. Amma za ka yi tunani a kansa dare da rana domin ka tabbata ka aikata duk abin da aka rubuta a ciki. Gama ta haka za ka yi ta albarka cikin hanyarka, ta haka kuma za ka yi nasara.’​—Josh. 1:​7, 8.

Muna rayuwa a “kwanakin ƙarshe” shi ya sa muke fuskantar matsaloli sosai. (2 Tim. 3:1) Amma kamar Yoshuwa, za mu yi nasara idan muka bi shawarwarin da Jehobah ya ba shi. Mu riƙa karanta Littafi Mai Tsarki kowace rana, kuma mu yi amfani da abubuwan da muka koya don yanke shawarwarin da suka dace.

Amma wasu ’yan’uwa ba su iya nazari ba, ko kuma ba sa jin daɗin yin hakan. Duk da haka, nazarin Littafi Mai Tsarki yana da muhimmanci sosai. Ka yi amfani da akwatin nan “ Ka Gwada Bin Waɗannan Shawarwarin” don ka sa nazarinka ya ƙara daɗi da kuma inganci.

Wani marubucin Zabura ya ce: ‘Ka bishe ni cikin hanyar umarnanka, gama suna faranta mini rai.’ (Zab. 119:35) Babu shakka, kai ma za ka yi farin ciki sosai idan kana yin nazarin Kalmar Allah. Akwai abubuwa masu tamani da za ka iya koya idan kana nazarin Littafi Mai Tsarki.

Ba za ka yi wa al’umma ja-goranci kamar yadda Yoshuwa ya yi ba, amma kai ma kana fuskantar wasu matsaloli. Don haka, kamar Yoshuwa, ka riƙa yin nazarin Littafi Mai Tsarki kuma ka lura da abubuwan da aka rubuta da za su amfane ka. Idan ka yi hakan, kai ma za ka yi nasara kuma ka yi hikima.