Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

3Idan mutane biyu da ba ma’aurata ba suka kwana a gida ɗaya su kaɗai ba tare da wani ƙwaƙƙwarar dalili ba, shin hakan zai bukaci dattawa su kafa musu kwamitin shari’a?

E, idan babu wata ƙwaƙƙwarar dalilin da ya sa suka yi haka, za a kafa musu kwamitin shari’a domin da akwai alama cewa sun yi lalata.​—1 Kor. 6:18.

Rukunin dattawa za su yi la’akari da yanayin sosai don su gani ko ya cancanci a kafa kwamitin shari’a. Alal misali: Su biyu suna fita zance ne? An taɓa yi musu gargaɗi game da dangantakarsu da juna kuwa? Mene ne ya faru da ya sa suka kwana a gida ɗaya? Sun shirya yin hakan ne? Shin suna da mafita ne ko kuwa da akwai abin da ya faru da ya jawo haka, wataƙila wata larura ta faru da ya sa ya wajaba su kwana a gida ɗaya? (M. Wa. 9:11) Shin sun kwana ne a kan gado ɗaya? Tun da kowane yanayin dabam ne, dattawa za su bukaci yin la’akari sosai.

Bayan dattawan sun gama binciken, rukunin dattawa za su duba ko ya kamata a kafa musu kwamitin shari’a.