Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Rika Jin Tausayin “Dukan Mutane”

Ka Rika Jin Tausayin “Dukan Mutane”

SA’AD DA Yesu yake koya wa almajiransa yadda za su yi wa’azi, ya gaya musu cewa ba dukan mutane ba ne za su saurare su ba. (Luk. 10:​3, 5, 6) Haka yake a yau, wasu mutane sukan zage mu ko kuma su wulaƙanta mu. Kuma hakan yana iya sa ya yi mana wuya mu riƙa jin tausayin mutane sa’ad da muke wa’azi.

Mutum mai tausayi yakan lura cewa mutane suna bukatar taimako kuma sai ya taimaka musu. Amma ba za mu riƙa ƙwazo ba da kuma taimaka wa mutane ba idan muka daina jin tausayin mutanen da muke wa wa’azi. Alal misali, idan muna so wuta ta riƙa ci sosai muna bukatar mu riƙa saka itace. Hakazalika, idan muna so mu kasance da ƙwazo sosai muna bukatar mu riƙa nuna wa mutane juyayi sa’ad da muke wa’azi!​—1 Tas. 5:19.

Me zai taimaka mana mu riƙa jin tausayin mutane ko da yin hakan yana da wuya? Bari mu tattauna misalin mutane uku da za mu iya yin koyi da su. Wato na Jehobah da Yesu da kuma manzo Bulus.

KA RIƘA JIN TAUSAYIN MUTANE KAMAR JEHOBAH

Mutane sun yi shekaru da yawa suna faɗin ƙarya game da Jehobah. Duk da haka, shi “mai alheri ne ga mutanen da ba sa godiya da kuma mugaye.” (Luk. 6:35) Jehobah yana hakan ta wurin yin haƙuri da su. Me ya sa? Don yana son “dukan mutane” su sami ceto. (1 Tim. 2:​3, 4) Duk da cewa Allah ya tsani mugunta, mutane suna da tamani a gare shi kuma ba ya son kowannensu ya mutu.​—2 Bit. 3:9.

Jehobah ya san cewa Shaiɗan gwani ne wajen yaudarar mutane. (2 Kor. 4:​3, 4) An koya wa mutane da yawa ƙaryace-ƙaryace game da Allah tun suna ƙanana. Kuma hakan zai sa ya yi musu wuya su saurare mu. Amma Jehobah yana son ya taimaka wa irin waɗannan mutanen. Ta yaya muka sani?

Alal misali, ka yi la’akari da yadda Jehobah ya ɗauki mutanen Nineba na dā. Duk da cewa su mugaye ne, Jehobah ya gaya wa Yunana cewa: “Ashe, ni kuwa ba zan ji tausayin Nineba babban birnin nan ba? Birnin da yake da ’yan yara marasa alhaki fiye da dubu ɗari da ashirin (120,000) a cikinsa?” (Yon. 4:11) Jehobah ya ji tausayin waɗannan mutanen da ba su san shi ba. Shi ya sa ya tura Yunana ya yi musu gargaɗi.

Kamar Jehobah, muna ɗaukan mutane da tamani sosai. Muna iya yin koyi da Jehobah ta wajen son taimaka wa mutane su koya game da shi. Har ma a lokacin da ba sa son su saurari wa’azinmu.

KA RIƘA JIN TAUSAYIN MUTANE KAMAR YESU

Kamar Jehobah, Yesu ya ji tausayin mutanen da ba su san Allah ba. Shi ya sa “da ya ga jama’a sun taru da yawa, sai ya ji tausayinsu, gama suna shan wahala kuma ba mai taimako, kamar tumakin da ba su da makiyayi.” (Mat. 9:36) Yesu ya fahimci abin da ya sa suke cikin wannan yanayin. Ya san cewa malamansu ba sa koyarwar da ta jitu da Kalmar Allah kuma suna wulaƙanta su. Ko da Yesu ya san cewa mutane da yawa da suka saurare shi ba za su zama almajiransa ba, amma ya “koya musu abubuwa da yawa.”​—Mar. 4:​1-9.

Kada ka yi baƙin ciki idan wani ya ƙi ya saurari wa’azinka

Idan yanayin mutane ya canja, suna iya son su saurari wa’azi

Idan mutane sun ƙi su saurare mu, ya kamata mu yi ƙoƙari mu san dalilin da ya sa suka yi  hakan. Wataƙila ba sa son Littafi Mai Tsarki ko kuma don mugayen abubuwan da suka ga wasu Kiristoci suke yi. Mai yiwuwa wasu sun ji abin da ba daidai ba game da imaninmu. Ban da haka ma, wasu suna jin tsoron danginsu ko kuma suna ganin maƙwabtansu za su yi musu ba’a idan sun saurare mu.

Wataƙila wasu mutane da muke haɗuwa da su ba sa son su saurare mu don suna sha wahala sosai. Wata da take wa’azi a ƙasar waje mai suna Kim ta ce: “A wasu wurare a yankinmu, mutane da yawa suna shan wahala don yaƙi da aka yi kuma sun yi hasarar dukan dukiyarsu. Ba su da bege, saboda haka suna baƙin ciki kuma ba sa amincewa da kowa. Mutane a wannan yankin ba so su saurare mu. Akwai lokacin da aka kawo mini hari sa’ad da nake wa’azi.”

Me ya taimaka wa Kim ta ci gaba da jin tausayin mutane duk da cewa sun wulaƙanta ta? Ta ce: “Ina ƙoƙari in riƙa tuna da abin da ke littafin Karin Magana 19:​11, inda aka ce: ‘Hankali yakan sa mutum ya danne fushinsa.’ Sa’ad da na tuna irin wahalar da mutanen da ke yankinmu suke sha, hakan yana taimaka mini in ji tausayinsu. Kuma ba kowa ba ne yake ƙin mu, don a wannan yankin muna nazari da wasu da suke son saƙonmu sosai.”

Muna iya tambayar kanmu, ‘Da a ce ni ba Mashaidi ba ne, mene ne zan yi idan Shaidun Jehobah suka zo wa’azi?’ Alal misali, a ce an gaya mini ƙarya game da Shaidu Jehobah fa? Wataƙila da mu ma ba mu saurari wa’azi ba, kuma za mu so a nuna mana juyayi. Yesu ya ce wajibi ne mu yi wa mutane abin da muke so a yi mana. Saboda haka, ya kamata mu yi iya ƙoƙarinmu mu fahimci yanayin mutane kuma mu ji tausayinsu, ko a lokacin da yin hakan yake da wuya.​—Mat. 7:12.

KA RIƘA NUNA TAUSAYI KAMAR BULUS

Manzo Bulus ya nuna juyayi ga mutanen da suka kai masa hari sa’ad da yake wa’azi. Me ya sa? Don ya tuna da halinsa a dā. Ya ce: “A dā ni mai saɓon Allah ne, mai tsananta masa, kuma mai wulaƙanta shi. Amma duk da haka, na sami jinƙai saboda duk abin na aikata na yi ne cikin rashin sani da rashin bangaskiya.” (1 Tim. 1:13) Ya san cewa Jehobah da Yesu sun nuna masa juyayi. Wataƙila ya fahimci ra’ayin mutanen da suke son su sa ya daina wa’azi domin shi ma yana da irin ra’ayinsu a dā.

A wasu lokuta, Bulus ya haɗu da mutanen da suka yi imani sosai da koyarwar ƙarya. Yaya ya ji? Littafin Ayyukan Manzanni 17:16 ya ce sa’ad da Bulus yake birnin Atina, “ya yi baƙin ciki ƙwarai da ya ga garin ya cika da gumaka.”  Duk da haka, Bulus ya yi amfani da abin da ya sa shi baƙin ciki wajen koyar da mutanen. (A. M. 17:​22, 23) Ya daidaita wa’azinsa ga yanayin mutane dabam-dabam domin ‘ko ta yaya ya cece waɗansu.’​—1 Kor. 9:​20-23.

Muna iya bin misalin Bulus sa’ad da muka haɗu da mutanen da suka ƙi saurarar wa’azinmu, ko kuma waɗanda suka yi imani da koyarwar ƙarya. Za mu iya yin amfani da abin da muka sani game da su don mu koya musu “labari mai daɗi.” (Isha. 52:7) Wata ’yar’uwa mai suna Dorothy ta ce: “A yankinmu an koya wa mutane da yawa cewa Allah yana tsananta wa mutane da kuma kushe musu sosai. Ina yaba musu don sun yi imani da Allah, bayan haka sai in nuna musu abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da halayen Jehobah da kuma alkawuran da ya yi.”

“KU YI NASARA A KAN MUGUNTA TA WURIN AIKATA ABIN DA YAKE MAI KYAU”

Da yake muna cikin “kwanakin ƙarshe,” halayen mutane za su “ƙara muni” sosai. (2 Tim. 3:​1, 13) Amma kada mu bar hakan ya hana mu jin tausayi ko kuma ya hana mu yin farin ciki. Jehobah zai ba mu ƙarfin yin “nasara a kan mugunta ta wurin aikata abin da yake mai kyau.” (Rom. 12:21) Wata majagaba mai suna Jessica ta ce: “Ina yawan haɗuwa da mutane marasa sauƙin kai kuma suna rena wa’azinmu. Hakan yana ba ni haushi a wasu lokuta. Amma idan na soma tattaunawa da mutumin, ina addu’a ga Jehobah a zuciyata don ya taimaka mini in ɗauki mutumin kamar yadda Allah ya ɗauke shi. Hakan yana taimaka mini in daina mai da hankali ga ra’ayina kuma in soma tunanin yadda zan taimaka wa mutumin.”

Ka ci gaba da neman waɗanda suke son su koya game da Allah

A ƙarshe, wasu mutane suna iya saurarar mu kuma su koya game da Allah

Muna bukatar mu yi tunanin yadda za mu ƙarfafa ’yan’uwan da muke wa’azi tare da su. Jessica ta ce: “Sa’ad da muke wa’azi kuma aka wulaƙanta abokiyar wa’azina, ba na mai da hankali ga abin da ya faru. A maimakon haka, ina mai da hankali ga abubuwan da wa’azinmu ke cim ma duk da cewa wasu mutane ba sa saurara.”

Jehobah ya san cewa a wasu lokuta muna fuskantar ƙalubale sa’ad da muke wa’azi. Amma yana farin ciki sosai idan muka bi misalinsa na nuna juyayi. (Luk. 6:36) Babu shakka, ba zai nuna juyayi da kuma haƙuri ga mugaye har abada ba. Ya kamata mu kasance da tabbaci cewa ya san daidai lokacin da zai kawo ƙarshen wannan mugun zamani. Amma kafin wannan lokacin, muna bukatar mu ci gaba da yin wa’azi. (2 Tim. 4:2) Bari mu ci gaba da yin wa’azi da ƙwazo kuma mu riƙa nuna tausayi ga “dukan mutane.”