Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Me Ya Sa Za Mu ‘Yabi’ Jehobah?

Me Ya Sa Za Mu ‘Yabi’ Jehobah?

“Halleluyah! Gama ya yi kyau a raira yabbai ga Allahnmu.”​—ZAB. 147:1.

WAƘOƘI: 104, 152

1-3. (a) A wane lokaci ne wataƙila aka rubuta Zabura 147? (b) Kuma wane darasi za mu koya idan muka bincika Zabura 147?

ZAI dace mu yaba wa mutumin da ya yi aiki mai kyau ko kuma ya nuna wani halin da Littafi Mai Tsarki ya umurce mu mu kasance da shi. Idan mu mutane muna bukatar mu riƙa yaba wa wasu, Jehobah ma ya yi abubuwa da yawa da ya kamata mu riƙa yaba masa! Za mu iya yaba wa Jehobah saboda ikon da yake da shi, kamar yadda abubuwan da ya halitta suka bayana da yadda yake bi da mutane da kuma ɗansa da ya ba da hadaya domin ya fanshi ’yan Adam.

2 Mutumin da ya rubuta Zabura ta 147 ya yi hakan ne don yana son ya yabi Jehobah. Kuma ya ƙarfafa mutane su yabi Allah tare da shi.​—Karanta Zabura 147:​1, 7, 12.

3 Ba mu san wanda ya rubuta wannan zaburar ba, amma wataƙila ya yi rayuwa ne a lokacin da Jehobah ya dawo da Isra’ilawa daga bauta a Babila. (Zab. 147:2) Mai yiwuwa wannan mutumin da ya rubuta Zaburar don ya yabi Jehobah, ya yi hakan ne domin Allah ya dawo da mutanensa daga zaman bauta. Ban da haka ma, ya faɗi wasu dalilan da suka sa ya kamata a riƙa yabon Jehobah. Waɗanne dalilai ke nan? Wane dalili ne kake da shi na yabon Jehobah?​—Zab. 147:1.

 JEHOBAH YANA ƘARFAFA MASU BAƘIN CIKI

4. Yaya Isra’ilawa suka ji sa’ad da Sarki Sairus ya zo ya sāke su, kuma me ya sa?

4 Ka yi tunanin yadda Isra’ila suka ji sa’ad da suke zaman bauta a Babila. Mutanen da suka kai su zaman bauta suna zolayarsu suna cewa: “Ku raira mana ɗaya daga cikin waƙoƙin Sihiyona.” Don a lokacin ba mutane a birnin Urushalima da suke takama da ita. (Zab. 137:​1-3, 6) Yahudawa ba sa son su yi waƙa, don suna baƙin ciki kuma suna neman ƙarfafa. Amma kamar yadda Allah ya faɗa, Sarkin Fasiya mai suna Sairus ya zo kuma ya cece su. Ya hallaka Babila kuma ya ce: Jehobah ‘Allah . . . ya kuwa ƙarfafa ni in gina masa gida cikin Urushalima, . . . Kowanene da ke cikinku na dukan mutanensa, Ubangiji Allahnsa shi zauna tare da shi; shi tashi shi tafi can.’ (2 Laba. 36:23) Abin da ya yi ya taimaka wa Isra’ilawa da ke zaman bauta a Babila sosai kuma ya ƙarfafa su.

5. Mene ne wani marubucin zabura ya ce game da yadda Jehobah yake taimaka mana mu daina baƙin ciki?

5 Jehobah bai ƙarfafa al’ummar Isra’ila a matsayin rukuni kawai ba amma ya tabbata cewa ya ƙarfafa kowannensu. Haka ma yake a yau. Wani marubucin Zabura ya rubuta game da Jehobah, ya ce: “Yana warkar da masu-karyayyar zuciya, yana ɗaure raunukan su.” (Zab. 147:3) Babu shakka, Jehobah yana kula da waɗanda suke da kowace irin matsala. A yau, Jehobah yana ɗokin ƙarfafa mu kuma ya taimaka mana mu daina baƙin ciki. (Zab. 34:18; Isha. 57:15) Jehobah ya ba mu hikima da kuma ƙarfin jimre duk wata matsalar da muke fuskanta.​—Yaƙ. 1:5.

6. Ta yaya za mu amfana daga yadda marubucin zabura ya canja abin da yake magana a kai a Zabura 147:4? (Ka duba hoton da ke shafi na 17.)

6 Bayan haka, marubucin ya mai da hankali ga abubuwan da Jehobah ya halitta a sama kuma ya ce: Jehobah “yana ƙididigan yawan taurari” dukansu yana kiransu da “sunayensu.” (Zab. 147:4) Amma me ya sa marubucin Zaburar ya canja abin da yake magana a kai kuma ya mai da hankali ga halittun sama? Bari mu yi la’akari da wannan: Marubucin yana ganin taurari da idanunsa, amma bai san yawan su ba. A yau muna ganin taurari da yawa fiye da yadda muke yi a dā. Wasu suna ganin cewa da akwai biliyoyin taurari a damin tauraro da ake kira Milky Way galaxy kaɗai. Kuma irin wannan damin taurarin ba su da iyaka. A gare mu taurari ba su da iyaka, amma wanda ya halicce su ya ba dukansu sunaye ko kuma abin da zai riƙa sanin su da shi. Hakan yana nufin cewa kowane tauraro yana da muhimmanci a wurin Jehobah. (1 Kor. 15:41) Mutane da ya halitta a duniya kuma fa? Allah da ya san sunayen kowane tauraro ya san ka, ya san inda kake, ya san yadda kake ji kuma ya san abin da kake bukata a kowane lokaci.

7, 8. (a) Mene ne Jehobah ya sani game da mu? (b) Ka bayyana yadda Jehobah yake taimaka wa mutane don yana da tausayi.

7 Jehobah ya san abin da kake fuskanta, kuma yana da ikon taimaka maka ka jimre da matsalolinka. (Karanta Zabura 147:5.) Babu shakka, kana iya ji kamar matsalolinka sun fi ƙarfinka kuma ba za ka iya jimrewa ba. Amma Allah ya san kasawarka, don yana ‘tuna kai turɓaya ne.’ (Zab. 103:14) Da yake mu ajizai ne mukan yi kuskure a kai a kai, kuma hakan yana iya sa mu yi sanyin gwiwa. Ban da haka ma, muna iya yin da-na-sanin wani abin da muka faɗa, ko wata sha’awa da bai dace ba da muke yi, ko kuma halinmu na kishin wasu. Jehobah ba shi da irin wannan kasawar amma ya san yadda muke ji.​—Isha. 40:28.

8 Wataƙila Jehobah ya taɓa taimaka  maka ka magance wata matsala. (Isha. 41:​10, 13) Ku yi la’akari da misalin wata ’yar’uwa majagaba mai suna Kyoko da ta yi sanyin gwiwa bayan da aka tura ta hidima a wani wuri dabam. Ta yaya Jehobah ya nuna ya fahimci matsalolin da take fuskanta? A ikilisiyar da Kyoko ta koma, ta haɗu da ’yan’uwan da suke fuskantar irin matsalar da take fuskanta kuma sun san yadda take ji. Hakan ya sa ta ji kamar Jehobah yana gaya mata cewa: “Ba kawai don ke majagaba ba ce ya sa nake ƙaunarki amma don ke ’yata ce kuma kina bauta min da ƙwazo. Don haka, ina son ki ji daɗin rayuwarki a matsayin Mashaidiyata!” Kai kuma fa, ta yaya Jehobah ya nuna cewa “fahiminsa marar-iyaka ne” a gare ka?

JEHOBAH YANA BIYAN BUKATUNMU

9, 10. A wace hanya mafi muhimmanci ce Jehobah yake taimaka mana? Ka ba da misali.

9 Dukanmu muna bukatar abubuwa kamar su abinci da kaya da kuma wurin kwana. Don haka, a wasu lokuta muna iya damuwa ko za mu iya samun isashen abinci. Amma Jehobah ya halicce duniyar nan a hanyar da za ta iya tsiro da abincin da zai ciyar da mutane har da ‘hankaki a lokacin da suke kuka.’ (Karanta Zabura 147:​8, 9.) Da yake Jehobah yana ciyar da hankaki a kowane lokaci, babu shakka zai iya biyan dukan bukatunmu.​—Zab. 37:25.

10 Abin da ya fi muhimmanci ma shi ne Jehobah yana yi mana tanadin abin da zai riƙa ƙarfafa dangantakarmu da shi, kuma waɗannan abubuwan suna taimaka mana mu kasance da “salama kuwa ta Allah.” (Filib. 4:​6, 7) Ku yi la’akari da misalin Mutsuo da matarsa da Jehobah ya taimaka musu sa’ad da suka fuskanci tsunami a shekara ta 2011 a ƙasar Jafan. Sun tsira don sun hau rufin gidansu. Amma sun yi hasarar kusan dukan abubuwan da suke da su. Sun kwana a bene na biyu na gidansu a cikin duhu da kuma sanyi. Da gari ya waye, sun nemi abin da za su karanta don ya ƙarfafa su, amma abin da suka samu shi ne littafin nan 2006 Yearbook of Jehovah’s Witnesses. Da suka buɗe, jigon da Mutsuo ya gani shi ne “The Deadliest Tsunamis Ever Recorded” wato tsunami mafi muni da aka taɓa yi a duniya. Wannan labari ne game da girgizan ƙasar da ta faru a yankin Sumatra a shekara ta 2004 kuma ta jawo tsunami mafi muni sosai. Mutsuo da matarsa sun zub da hawaye sa’ad da suka karanta labarin wasu, kuma sun ji kamar Jehobah yana ƙarfafa su a lokacin da suke bukatar hakan. Ban da haka ma, Jehobah ya yi musu tanadin abin biyan bukata. ’Yan’uwa sun tura musu kayan agaji. Amma abin da ya fi ƙarfafa su shi ne ziyarar da wakilan ƙungiyar Jehobah suka kai wa ikilisiyoyi da ke wurin. Mutsuo ya ce: “Na ji kamar Jehobah yana tare da kowanenmu kuma yana kula da mu, hakan ya ƙarfafa ni sosai!” Da farko Jehobah yana yi mana tanadin abin da zai riƙa ƙarfafa dangantakarmu da shi, bayan haka, sai ya biya bukatunmu.

YADDA MUKE AMFANA DAGA TAIMAKON JEHOBAH

11. Me waɗanda suke so su amfana daga taimakon Jehobah suke bukatar su yi?

11 Jehobah yana shirye ya tallafa wa “masu-tawali’u” a koyaushe. (Zab. 147:6a) Amma ta yaya za mu amfana daga yadda Jehobah yake taimaka mana? Muna bukatar mu kasance da dangantaka mai kyau da shi. Amma kafin mu yi hakan, muna bukatar mu zama masu tawali’u. (Zaf. 2:⁠3) Masu tawali’u suna dogara ga Jehobah ya magance duk wani rashin adalci da aka yi musu. Kuma Jehobah yana amincewa da irin waɗannan mutanen.

12, 13. (a) Idan muna so Jehobah ya taimaka mana, mene ne za mu guje wa? (b) Su waye ne Jehobah yake amincewa da su?

 12 Ban da haka, Allah yana “ragargaza mugaye har ƙasa.” (Zab. 147:6b, LMT) Babu shakka, waɗannan kalmomin suna da zafi sosai! Ba ma son hakan ya faru da mu, amma muna so Jehobah ya amince da mu. Saboda haka, muna bukatar mu tsani abin da ya tsana. (Zab. 97:10) Alal misali, muna bukatar mu guji fasikanci. Ƙari ga haka, ya kamata mu guji duk wani abin da zai iya kai mu ga yin abin da bai dace ba, kuma wannan ya ƙunshi kallon hotunan batsa. (Zab. 119:37; Mat. 5:28) Guje wa irin waɗannan abubuwan ba shi da sauƙi, amma idan muka yi hakan, Jehobah zai albarkace mu.

13 Idan muna so mu yi nasara muna bukatar mu dogara ga Jehobah ba ga kanmu ba. Shin Jehobah zai yi farin ciki ne idan muka dogara ga “ƙarfin doki” wato inda mutane suke zuwa neman taimako? A’a! Ban da haka ma, ba ma bukatar mu dogara ga “ƙafafun mutum,” wato, mu dogara ga kanmu ko kuma wasu. (Zab. 147:10) A maimakon haka, muna bukatar mu roƙi Jehobah ya taimaka mana. Mutane suna gajiya idan ana yawan neman taimako daga wurinsu, amma Jehobah ba ya gajiya da jin addu’armu a duk lokacin da muka nemi taimakonsa. Jehobah “yana jin daɗin waɗanda ke tsoronsa, su waɗanda ke kafa bege ga jinƙansa.” (Zab. 147:11) Da yake muna iya dogara ga Jehobah kuma yana ƙaunarmu, mun san cewa zai taimaka mana mu shawo kan duk wasu sha’awoyin da ba su dace ba.

14. Mene ne ya ƙarfafa wani marubucin zabura?

14 Jehobah ya ba mu tabbacin cewa zai taimaka mana a lokacin da muke bukatar hakan. Sa’ad da Isra’ilawa suka dawo Urushalima, wani marubucin zabura ya yi tunanin yadda Jehobah ya taimaka musu kuma ya ce: “Shi yake riƙe da ƙofofinki da ƙarfi, yakan sa wa jama’arki albarka. Yakan kiyaye kan iyakar ƙasarki lafiya.” (Zab. 147:​13, 14, LMT) Babu shakka, sanin cewa Jehobah zai ƙarfafa kofar birnin don ya kāre bayinsa ya ƙarfafa marubucin zaburar nan sosai.

Ta yaya Kalmar Allah za ta taimaka mana sa’ad da muke cikin matsala? (Ka duba sakin layi na 15-17)

15-17. (a) A wasu lokuta yaya za mu riƙa ji game da matsalolinmu, amma ta yaya Jehobah yake amfani da Kalmarsa don ya taimaka mana? (b) Ka ba da misalin yadda Kalmar Allah “takan yi gudu da sauri ƙwarai.”

15 Wataƙila kana damuwa saboda matsalolin da kake fuskanta. Amma Jehobah zai iya ba ka hikimar jimre su. Wani marubucin zabura ya yi magana game da Jehobah kuma ya ce: “Ya aike da umurninsa a bisa duniya; maganarsa takan yi gudu da sauri ƙwarai.” Bayan ya faɗi wannan, marubucin ya ƙara magana game da Jehobah ya ce: Jehobah “yana ba da snow [dusar ƙankara] kamar farin ulu; yana warwatsa raɓa kamar toka. Yakan jefa [ƙankara] nasa kamar ƙasashi.” Bayan haka, marubucin ya yi tambaya ya ce: “Wa ke da iko ya tsaya gaban sanyi nasa?” Ya daɗa cewa Jehobah ‘yakan aike da maganarsa, ya narkar da su.’ (Zab. 147:​15-18) Allah mai iko da ya san kome zai iya taimaka maka ka magance duk wata matsala da kake fuskanta tun da yake yana iya ba wa ƙanƙara umurni.

16 A yau, Jehobah yana yin amfani da Littafi Mai Tsarki don ya yi mana ja-goranci. Kuma ‘maganarsa takan yi gudu da sauri ƙwarai’ ma’ana yana yi mana ja-goranci a lokacin da muke bukatar hakan. Ka yi tunanin yadda ka amfana daga karanta Littafi Mai Tsarki, yin nazarin littattafan da “bawan nan mai-aminci” yake mana tanadinsu. Ban da hakan ma, muna amfana daga kallon shirye-shiryen JW Broadcasting da shiga dandalinmu na jw.org da tattaunawa da dattawa da kuma yin cuɗanya da ’yan’uwa. (Mat. 24:45) Shin waɗannan abubuwan ba sa nuna  maka cewa Jehobah ba ya ɓata lokaci wajen yi maka ja-goranci?

17 Wata ’yar’uwa mai suna Simone ta ga yadda Kalmar Allah ta taimaka mata. A dā ba ta ɗaukan kanta da daraja, har ma tana shakkar ko Allah zai amince da ita. Amma a duk lokacin da ta yi sanyin gwiwa, takan yi addu’a sosai kuma ta roƙi Jehobah ya taimaka mata. Ban da haka, ta duƙufa a yin nazarin Littafi Mai Tsarki. ’Yar’uwar ta ce, “Ban taɓa samun kaina a wani yanayin da na ji cewa Jehobah bai ƙarfafa ni ko kuma yi mini ja-goranci ba.” Kuma hakan ya taimaka mata ta kasance da ra’ayin da ya dace.

18. Me ya sa kake ganin Jehobah ya yi maka albarka, kuma wane dalili kake da shi na yabonsa?

18 Wannan marubucin zaburar ya san a dukan al’umman duniya, Jehobah ya zaɓi Isra’ilawa su zama mutanensa. Su ne kaɗai Allah ya ba Kalmarsa da kuma ‘farillansa da hukuncinsa.’ (Karanta Zabura 147:​19, 20.) A yau, babban gata ce da ake kiranmu da sunan nan Shaidun Jehobah. Saboda mun bar Kalmar Jehobah ta gyara rayuwarmu, hakan ya sa mun ƙulla dangantaka mai kyau da shi. Kuma kamar marubucin Zabura 147, muna da dalilin yabon Jehobah kuma mu ƙarfafa wasu ma su yi hakan.