Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Shin ya dace Kirista ya mallaki makamai kamar bindiga don ya tsare kansa daga wasu mutane?

Ko da yake ba laifi ba ne Kiristoci su ɗauki mataki don su tsare kansu, amma ya kamata su yi hakan a hanyar da ta jitu da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. Wannan yana nufin cewa ba za su riƙe makamai irin su bindiga da sauransu ba. Bari mu bincika waɗannan ƙa’idodin:

Jehobah yana ɗaukan rai musamman na mutum da tamani. Dauda marubucin zabura ya san cewa Jehobah ne “mafarin dukan rai.” (Zab. 36:⁠9) Saboda haka, zai dace Kirista ya yi hattara don kada ya ɗauki alhakin jinin wasu sa’ad da yake ƙoƙarin tsare kansa ko dukiyarsa.​—K. Sha. 22:8; Zab. 51:14.

Ko da yake akwai wasu abubuwa da mutum zai yi amfani da su kuma ya jawo masa alhakin jini, amma bindiga tana sa ya kasance da sauƙi a kashe mutum, ko da an yi harbin da gangan ko da kuskure. * Ƙari ga haka, za a iya kashe wani idan wanda yake so ya kai hari ya ga cewa mutumin yana riƙe da makami kamar bindiga.

Sa’ad da Yesu ya gaya wa mabiyansa su riƙe takuba, ba wai yana nufin su riƙa kare kansu da su ba ne. (Luk. 22:​36, 38) A maimakon haka, Yesu ya ce su kawo takobi don ya koya musu wani muhimmin darasi, wato kada su ɗauki mataki ko su yi faɗa da maƙiyansu. (Luk. 22:52) A lokacin da Bitrus ya  zaro takobi ya yanke kunnen wani bawan babban firist, Yesu ya gaya wa Bitrus cewa: “Mayar da takobinka gidansa.” Sai Yesu ya faɗa masa wata muhimmiyar gaskiya wadda a yau ta zama ƙa’idar da mabiyansa suke bi: “Gama dukan waɗanda suka ɗauki takobi, da takobi za su lalace.”​—Mat. 26:​51, 52.

Kamar yadda aka ambata a Littafin Mikah 4:​3, bayin Allah za “su buga takubansu su zama garmuna, masunsu kuma su zama lauzuna.” Wannan halin Kiristoci ya jitu da abin da manzo Bulus ya faɗa cewa: ‘Kada ku sāka wa kowane mutum mugunta da mugunta. . . . Idan ya yiwu, ku zauna lafiya da dukan mutane.’ (Rom. 12:​17, 18) Duk da matsalolin da Bulus ya fuskanta kamar “hatsarin mafasa,” ya ci gaba da bin abin da ya faɗa kuma bai taka dokar Allah don ya kāre kansa ba. (2 Kor. 11:26) Maimakon haka, ya dogara da Allah da kuma hikimar da ke Kalmar Allah wato, hikima da “ta fi kayan yaƙi amfani.”​—M. Wa. 9:18.

Kiristoci sun ɗauki rai da tamani fiye da abubuwan duniya. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ba da yalwar dukiya da mutum yake da ita ransa ke tsayawa ba.” (Luk. 12:15) Idan Kiristoci suka yi iya ƙoƙarinsu su sasanta da ɗan fashi kuma suka kasa, sai su bi wannan shawarar Yesu: “Ba za ku yi tsayayya da wanda shi ke mugu ba.” Wataƙila yanayin zai bukaci mu ba shi wani abin mallakarmu. (Mat. 5:​39, 40; Luk. 6:29) * Abin da ya dace shi ne mu kāre kanmu. Idan muka guje wa “alfarmar banza” kuma mutane suka san mu da zaman lafiya da yake mu Shaidun Jehobah ne, wataƙila maƙiya ba za su so su yi mana ɓarna ko lahani ba.​—1 Yoh. 2:16; Mis. 18:10.

Kiristoci suna daraja ra’ayin wasu. (Rom. 14:21) Wasu a cikin ikilisiya za su iya yin sanyin gwiwa sa’ad da suka gano cewa wani ɗan’uwa yana da bindiga da yake kāre kansa da shi. Ba za mu so hakan ya faru ba don muna ƙaunar ’yan’uwanmu sosai ko da muna ganin cewa hakkin mu ne mu riƙe bindiga.​—1 Kor. 10:​32, 33; 13:​4, 5.

Kiristoci suna iya ƙoƙarinsu su kafa misali mai kyau. (2 Kor. 4:2; 1 Bit. 5:​2, 3) Bayan an shawarci Kirista ya bar riƙe bindiga don ya kāre kansa kuma ya ƙi ya bi shawarar, wannan ya nuna cewa ba ya kafa misali mai kyau. Ƙari ga haka, ba zai cancanci yin hidima a wata ikilisiya ba. Haka ma da Kiristan da aikinsa ya kunshi yin amfani da bindiga. Zai dace ya nemi aikin da ba a yin amfani da makami irin su bindiga. *

Kirista ne zai zaɓi yadda yake so ya kāre kansa da iyalinsa ko kuma dukiyarsa. Ban da haka ma, shi ne zai zaɓi irin aikin da zai yi. Ƙa’idodin da ke cikin Littafi Mai Tsarki suna nuna mana hikimar Allah da kuma ƙaunar da yake nuna mana. Kiristan da yake so ya kyautata dangantakarsa da Jehobah bai kamata ya yi amfani da bindiga don ya kāre kansa daga mutane ba. Ya san cewa idan muka dogara ga Allah kuma muka bi ƙa’idodin da ke cikin Littafi Mai Tsarki, Jehobah zai kāre mu.​—Zab. 97:10; Mis. 1:33; 2:​6, 7.

Kiristoci ba za su yi amfani da makamai don su kāre kansu a lokacin ƙunci mai girma ba, amma suna bukatar su dogara ga Jehobah

^ sakin layi na 3 Kirista zai iya tsai da shawarar samun makami kamar bindiga don ya yi farauta ko kuma ya tsare kansa daga dabbobin daji. Amma idan ba ya amfani da bindigar, ya kamata ya cire harsashi daga ciki kuma ya adana ta da kyau don kada ta jawo hatsari. Idan kana zama a ƙasar da aka haramta wa mutane mallakar bindiga, ya kamata Kiristoci su bi dokar ƙasar.​—Rom. 13:1.

^ sakin layi na 2 Don ƙarin bayani game da kāre kai daga fyaɗe, ku duba talifin nan “How to Prevent Rape” da ke Awake na 8 ga Maris, 1993 a Turanci.

^ sakin layi na 4 Don samun ƙarin bayani game da tambayar yin aikin da ya ƙunshi yin amfani da makami kamar bindiga, ka duba Hasumiyar Tsaro na 1 ga Nuwamba 2005, shafi na 31 da kuma 15 ga Yuli, 1983, shafuffuka na 25-26 a Turanci.