Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Nemi Dukiyar da Za ta Dawwama

Ka Nemi Dukiyar da Za ta Dawwama

“Ta wurin dukiya ta rashin gaskiya ku yi wa kanku abokai.”​—LUK. 16:9.

WAƘOƘI: 32, 154

1, 2. Me ya sa za a riƙa samun matalauta a duniyar Shaiɗan?

MUTANE suna shan wahala sosai saboda rashin tattalin arziki. Matasa suna neman aiki amma ba sa samuwa. Ban da haka ma, wasu suna sadakar da ransu don su je ƙasashen da ake samun kuɗi. Duk da haka, akwai talakawa ma a ƙasashen da suke da arziki. Mutane masu kuɗi suna daɗa arziki, talakawa kuma suna daɗa talaucewa. Wani bincike da aka yi kwanan nan ya nuna cewa idan aka tara arziki na kashi ɗaya na mutane da ke da arziki a duniya zai kai na sauran kashi casa’in da tara yawa. Ko da yake wasu mutane suna da kuɗi sosai, amma mutane masu yawan gaske, talakawa ne. Yesu ya fahimci hakan shi ya sa ya ce: “Kuna da fakirai kullum tare da ku.” (Mar. 14:7) Me ya sa wasu suke da kuɗi wasu kuma talakawa?

2 Yesu ya fahimci cewa Mulkin Allah ne kaɗai zai kawo ƙarshen matsalolin da ke tattare da tattalin arziki. “Dillalan” da aka ambata a Ru’ya ta Yohanna 18:3 na wannan duniyar ko masu kasuwanci da ’yan siyasa da kuma addinan ƙarya suna goyon bayan duniyar Shaiɗan. Ko da yake mutanen Allah ba sa yin siyasa kuma ba sa bin addinin ƙarya. Amma yawancinmu ba  za mu iya ware kanmu gabaki ɗaya daga kasuwanci na duniyar Shaiɗan ba.

3. Waɗanne tambayoyi ne za mu bincika?

3 Zai dace Kiristoci su bincika ra’ayinsu game da kasuwanci na duniyar nan ta wurin yi ma kansu waɗannan tambayoyi: ‘Ta yaya zan yi amfani da dukiyata don in bauta wa Allah da aminci? Ta yaya zan rage yawan kasuwanci a duniyar Shaiɗan? Waɗanne labarai ne suka nuna cewa bayin Allah sun dogara gare shi sosai?’

KWATANCIN WAKILI MARAR GASKIYA

4, 5. (a) Wane yanayi ne bawan nan da Yesu ya yi kwatanci da shi ya sami kansa? (b) Wace shawara ce Yesu ya ba wa mabiyansa?

4 Karanta Luka 16:​1-9. Kwatancin Yesu na bawa marar gaskiya zai sa mu yi tunani. An kai ƙararsa cewa yana ɓarnatar da dukiya, sai mai gidan ya ce zai kore shi. Da ya ga haka, sai ya yi wata dabara ko “hikima” kuma ya nemi ‘abokan’ da za su taimaka masa idan ya rasa aikinsa. * Ba wai Yesu yana ƙarfafa mabiyansa su riƙa cuci don su iya zama a wannan duniyar ba ne don ya ce irin wannan halin na “ya’yan zamanin nan” ne. A maimakon haka, yana son ya koya musu wani darasi mai muhimmanci ne.

5 Yesu ya san cewa mabiyansa suna bukatar su yi kasuwanci a wannan duniyar don su sami abin biyan bukata kamar yadda bawan nan ya yi sa’ad da ya sami kansa a saka mai wuya. Shi ya sa ya ƙarfafa su cewa: “Ta wurin dukiya ta rashin gaskiya ku yi wa kanku abokai, domin sa’anda ta kāsa, su [Jehobah da Yesu] su karɓe ku cikin bukkoki na har abada.” Wane darasi za mu iya koya daga wannan furucin?

6. Ta yaya muka sani cewa Allah bai halicci mutane su riƙa kasuwanci ba?

6 Ko da yake Yesu bai bayyana dalilin da ya sa ya kira arzikin na “rashin gaskiya” ba, amma Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Allah ba ya so mutane su nemi riba ta wurin cucin mutane ba. Shi ya sa Allah ya biya bukatun Adamu da Hauwa’u a lambun Adnin. (Far. 2:15, 16) Daga baya, sa’ad da aka zuba wa shafaffun Kiristocin da ke ikilisiya a ƙarni na farko ruhu mai tsarki, “ba kuma waninsu da ya ce abin da ya mallaka nasa ne, sai dai kome nasu ne baki ɗaya.” (A. M. 4:32, Littafi Mai Tsarki) Annabi Ishaya ya ce lokaci yana zuwa da dukan mutane za su more amfanin duniya. (Isha. 25:6-9; 65:21, 22) Amma kafin lokacin, mabiyan Yesu suna bukata su kasance da “hikima” wajen yin amfani da “dukiya ta rashin gaskiya” a wannan duniyar sa’ad da suke ƙoƙarin faranta ran Allah.

YIN AMFANI DA DUKIYA TA RASHIN GASKIYA A HANYAR DA TA DACE

7. Wane umurni ne yake littafin Luka 16:​10-13?

7 Karanta Luka 16:​10-13. Bawan nan da Yesu ya yi kwatanci da shi ya nemi abokai da za su taimaka masa. Amma Yesu ya ƙarfafa mabiyansa su nemi abokai a sama ba don son kai ba ne. Ƙari ga haka, yana son mu fahimci cewa yadda muke yin amfani da dukiya ta “rashin gaskiya” zai iya nuna ko muna da aminci ga Allah ko a’a. Ta yaya za mu yi hakan?

8, 9. Ka ba da misalin yadda wasu suke nuna aminci ta wurin yin amfani da dukiyarsu.

8 Za mu iya nuna cewa mu masu aminci ne ta wajen ba da gudummawa don yin aikin da Yesu ya annabta cewa za a yi. (Mat. 24:14) Wata yarinya a ƙasar Indiya tana da wani asusun da take saka kuɗi a ciki, har ma da kuɗin da take so ta saya kayan wasa da su. Da asusun ya cika, sai  ta ba da kuɗin don tallafa wa wa’azin da muke yi. Wani ɗan’uwa da yake gonar kwakwa a Indiya, ya taɓa kawo gudummawar kwakwa da yawa zuwa ofishin fassara da ke Malayalam. Ɗan’uwan ya yi tunani cewa tun da ofishin suna sayan kwakwa, ba da gudummawar zai taimaka masu su rage kuɗin da suke kashewa. Babu shakka, ya yi tunani mai kyau. Hakazalika, ’yan’uwa a ƙasar Hellas suna kai wa iyalin Bethel gudummawar man zaitun da man shanu da kuma wasu kayan abinci.

9 Wani ɗan’uwa a ƙasar Sri Lanka da yanzu yake zama a ƙasar waje, ya ba da gidansa don ’yan’uwa su riƙa yin taro kuma ya zama masaukin masu hidima ta cikkaken lokaci. Ko da yake ɗan’uwan ya kashe kuɗi sosai, abin da ya yi ya taimaka wa ’yan’uwa talakawa. A ƙasashen da aka saka takunkumi a aikin Shaidun Jehobah, ’yan’uwa suna ba da gidajensu don a riƙa yin taro a ciki, kuma hakan yana taimaka wa majagaba da yawa da kuma wasu da ba su da kuɗi su sami wajen yin taro.

10. Waɗanne irin albarka ne muke samu idan muka kasance masu bayarwa?

10 Misalan da aka ambata ɗazu sun nuna mana cewa mutanen Allah suna da “aminci cikin ƙanƙanin abu,” don suna amfani da dukiyarsu don su taimaki wasu. (Luk. 16:10) Shin yaya suke ji game da irin abubuwan da suke yi don su taimaka? Babu shakka, sun fahimci cewa za su sami arzikin ‘gaske’ idan suna ba da kyauta. (Luk. 16:11) Wata ’yar’uwa da take tallafa wa aikinmu da gudummawa ta faɗi irin albarkar da take samu. Ta ce: “Kyautar da nake bayarwa tana inganta halina da kuma yadda nake cuɗanya da mutane. Yin hakan yana taimaka mini in riƙa gafarta wa mutane kuma ina haƙuri da su fiye da dā. Ban da haka ma, idan aka ba ni shawara ina bi.” Mutane da yawa sun fahimci cewa kasancewa masu bayarwa yana sa su riƙa ƙarfafa dangantakarsu da Jehobah.​—⁠Zab. 112:5; Mis. 22:⁠9.

11. (a) Ta yaya ba da gudummawa yake nuna cewa muna da “hikima”? (b) Mene ne bayin Allah suke yi a yau? (Ka duba hoton da ke shafi na 7.)

11 Wata hanya da za mu iya nuna cewa mu masu “hikima” ne ita ce yin amfani da dukiyarmu don mu tallafa ma wa’azin da muke yi. Yin hakan yana ba mu damar amfani da abin da muke da shi don mu taimaka ma wasu. ’Yan’uwan da suke da arziki amma ba su da damar yin hidima ta cikakken lokaci suna farin cikin sanin cewa ana yin amfani da gudummawar da suke bayarwa don a taimaka wa ’yan’uwan da suke yin wa’azi da ƙwazo. (Mis. 19:17) Ana yin amfani da gudummawar da ake bayarwa don a riƙa kai littattafai zuwa wasu ƙasashen da ake talauci sosai amma mutane da yawa suna son su koya game da Jehobah. Mutane sun yi shekaru da yawa suna sayan Littafi Mai Tsarki da tsada sosai a ƙasashe kamar su Kwango da Madagascar da kuma Rwanda. Saboda kuɗin sayan Littafi Mai Tsarki zai iya kai albashin sati ɗaya ko kuma wata ɗaya. Don haka, ’yan’uwa sukan zaɓi ko su saya abinci ko kuma su sayi Littafi Mai Tsarki.  Amma gudummawar da ake bayarwa tana sa a biya bukatar kowa. Kuma ƙungiyar Jehobah tana amfani da gudummawar don a fassara Littafi Mai Tsarki kuma a ba wa iyalai da mutanen da suke son koya game da Jehobah. (Karanta 2 Korintiyawa 8:13-15.) Don haka, kowa yana iya zama abokin Jehobah, waɗanda suke bayarwa har ma da waɗanda ake ba su.

TA YAYA ZA MU YI KASUWANCI YADDA YA KAMATA?

12. Ta yaya Ibrahim ya dogara ga Jehobah?

12 Idan muna so mu ci gaba da ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah, muna bukatar mu mai da hankali ga yadda muke kasuwanci kuma mu yi amfani da yanayinmu mu nemi dukiyar ‘gaske.’ A zamanin dā, Ibrahim ya yi biyayya ga Allah kuma ya bar ƙasar Ur da akwai arziki sosai don ya ƙarfafa dangantakarsa da Jehobah. (Ibran. 11:​8-10) Ya dogara ga Jehobah sosai kuma ya gaskata cewa Jehobah ne zai biya bukatunsa. Don hakan, bai yi ƙoƙarin nema wa kansa dukiya ba, amma ya ci gaba da dogara ga Jehobah. (Far. 14:22, 23) Yesu ya ƙarfafa mabiyansa su kasance da irin wannan bangaskiya kuma ya gaya ma wani matashi mai arziki cewa: “Idan kana so ka kamalta, sai ka tafi, ka sayar da abin da kake da shi, ka ba fakirai, za ka sami wadata a sama: ka zo kuma, ka biyo ni.” (Mat. 19:21) Wannan mutumin ba shi da bangaskiya kamar Ibrahim, amma akwai wasu mutanen da suka dogara ga Jehobah sosai.

13. (a) Wane umurni ne Bulus ya ba Timotawus? (b) Ta yaya za mu bi umurnin Bulus?

13 Wani mutum mai bangaskiya kuma shi ne Timotawus. Bulus ya kira shi “mayaƙin kirki na Kristi Yesu.” Ƙari ga haka, ya ce: “Mayaƙin da ke a kan sha’anin yaƙi ba za ya nannaɗe kansa da al’amuran wannan rai ba; gama yana so ya gami wanda ya rubuta shi mayaƙi.” (2 Tim. 2:​3, 4) A yau, mabiyan Yesu da kuma masu hidima ta cikakken lokaci fiye da miliyan ɗaya suna yin iya ƙoƙarin su don su bi umurnin da Bulus ya bayar. Suna guje wa tallace-tallacen wannan duniyar saboda suna bin shawarar nan cewa: “Mai cin bashi kuma bawa ne ga mai ba da bashi.” (Mis. 22:7) Shaiɗan yana son mu mai da hankalinmu ga neman abin duniya. Wasu ma suna cin bashi don sayan gida ko don su biya kuɗin makaranta ko su sayi mota mai tsada ko kuma su yi bikin auren a zo a gani. Yin hakan yana iya sa mutane su riƙa biyan bashi har tsawon shekaru da yawa. Idan muna so mu nuna hikima muna bukatar mu sauƙaƙa salon rayuwarmu kuma mu rage cin bashi, don yin hakan zai ba mu damar bauta wa Allah ba wannan duniyar ba.​—1 Tim. 6:10.

14. Mene ne ya kamata mu ƙudiri aniyar yi? Ka ba da misali.

14 Muna bukatar mu sauƙaƙa salon rayuwarmu don mu saka Mulkin Allah a kan gaba. Akwai wasu ma’aurata da suke kasuwanci kuma suna samun riba sosai. Amma burinsu shi ne su koma yin hidima ta cikakken lokaci. Don haka, sai suka daina sana’ar da suke yi kuma suka sayar da jirgin ruwansu da kuma wasu abubuwan da suka mallaka. Bayan haka, sai suka ba da kansu don su taimaka da aikin gini da ake yi a hedkwatarmu da ke Warwick, a jihar New York. Wannan aikin yana da muhimmanci a gare su saboda za su yi hidima tare da ’yarsu da kuma mijinta a Bethel. Ban da haka ma, za su kasance tare da surukansu da suka je yin aikin. Wata ’yar’uwa majagaba a jihar Colorado da ke Amirka, ta sami aiki na ɗan lokaci a banki. Ma’aikatan bankin sun ji daɗin aikinta, don haka suka ce za su riƙa biyanta albashi mai tsoka idan ta ci gaba da aiki  da su. Amma da yake aikin ba zai ba ta damar mai da hankali ga hidimarta ba, sai ta ƙi. Waɗannan kaɗan ne daga cikin misalan bayin Jehobah da suka ba da kansu. Idan muka saka al’amuran Mulkin Allah a kan gaba, hakan zai nuna cewa mun ɗauki dangantakarmu da Jehobah da tamani sosai fiye da abin duniya.

SA’AD DA DUKIYA TA ƘARE

15. Wace irin dukiya ce ta fi sa mutum farin ciki?

15 Kasancewa masu dukiya ba ya nufin cewa Jehobah ya amince da mu. Amma Jehobah yana albarkar “mawadata cikin kyawawan ayyuka.” (Karanta 1 Timotawus 6:17-19.) Alal misali, da wata mai suna Lucia * ta ji cewa ana bukatar masu wa’azi a ƙasar Albaniya, sai ta bar ƙasarta Italiya kuma ta je wurin a shekara ta 1993. Ko da yake ba ta da wani kuɗin kirki, ta je don ta dogara ga Jehobah. Ta koyi yaren mutanen Albaniya kuma ta taimaka wa mutane fiye da 60 su koya game da Jehobah har suka yi baftisma. Ba dukanmu ba ne muke samun wannan damar taimaka wa mutane har su soma bauta wa Jehobah, amma idan muka yi iya ƙoƙarinmu don mu taimaka ma wasu su koya game da Jehobah don su sami rai na har abada, hakan babban gata ne.​—Mat. 6:⁠20.

16. (a) Mene ne zai faru da kasuwancin da ake yi a duniyar nan? (b) Kuma ta yaya sanin abin da zai faru a nan gaba zai shafi yadda muke ɗaukan abin duniya?

16 Yesu ya ce lokaci yana zuwa da mutane za su daina kasuwancin da ake yi a wannan duniyar. Ya ce sa’ad da dukiyar ta ƙare, ba wai idan wataƙila ta ƙare ba. (Luk. 16:9) A waɗannan kwanaki na ƙarshe, tattalin arzikin ƙasashe da wasu bankuna sun faɗi. Ƙari ga haka, nan ba da daɗewa ba, yanayin da duniya take ciki zai yi muni sosai. Kuma siyasa da addinan ƙarya da kuma kasuwanci na duniyar nan za su rugurguje. Annabi Ezekiyel da kuma Zafaniya sun annabta cewa zinariya da azurfa da kuma kasuwanci duk za su zama banza. (Ezek. 7:19; Zaf. 1:18) Yaya za mu ji a lokacin da muka tsufa kuma muka fahimci cewa mun ɓata lokaci muna neman dukiyar da ba ta da amfani? Babu shakka, za mu ji kamar mutumin da ya yi amfani da dukan rayuwarsa yana aiki don ya tara kuɗi amma daga baya ya gano cewa duk kuɗinsa jebu ne. (Mis. 18:11) Hakika, dukiyar duniyar nan za ta durƙushe. Don haka, zai dace mu yi amfani da damar da muke da ita yanzu mu zama ‘abokan’ Jehobah da Yesu. Duk wata sadaukarwa da muka yi saboda Mulkin Allah za ta sa mu farin ciki.

17, 18. Wace albarka ce abokan Allah za su samu?

17 Za a daina haya da karɓan bashin kuɗi don a sayi gida a lokacin da Mulkin Allah zai soma sarauta. Ban da haka ma, za a samu abinci a ko’ina kuma ba za mu sake sayan magani ba. Mutane za su ji daɗin rayuwa a duniya. Za a yi ado da azurfa da zinariya da makamantansu maimakon a riƙa ajiyarsu don samun riba. Mutane ba za su sake sayan kayan gini kamar su katako da duwatsu da kuma kwano don su gina gidaje masu kyau ba. Abokanmu za su taimaka mana kuma ba za su karɓi kuɗi ba. Kowa zai more duk wani abin da ke duniya.

18 Wannan kaɗan ne daga cikin abubuwan da mutane za su more idan suka zama abokan Jehobah. Waɗanda suke bauta wa Jehobah za su yi murna sa’ad da suka ji muryar Yesu, yana cewa: “Ku zo, ku masu-albarka na Ubana, ku gaji mulkin da an shirya dominku tun kafawar duniya.”​—Mat. 25:34.

^ sakin layi na 4 Yesu bai faɗa ko ƙarar da aka kawo game da bawan gaskiya ce ko a’a ba. Amma kalmar Helenanci da aka fassara zuwa furucin nan “kai ƙararsa” a Luka 16:1 yana iya nufin cewa sharri aka yi masa. Kuma Yesu ya mai da hankali a kan yadda bawan ya kasance da hikima ne, ba abin da ya sa aka kore shi ba.

^ sakin layi na 15 Za ka iya karanta labarin Lucia Moussanett a Awake! na 22 ga Yuni, 2003 shafuffuka na 18-22.