Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Kāre Kanka daga Karyace-Karyacen Shaidan

Ka Kāre Kanka daga Karyace-Karyacen Shaidan

AKWAI wani da yake kawo maka hari! Waye ke nan? Shaiɗan ne kuma yana amfani da wani makami da yake da lahani sosai. Wannan makamin da yake amfani da shi shi ne Farfaganda. Shaiɗan ya tsara wannan makamin don ya canja ra’ayinka ne ba don ya ji maka rauni ba.

Ko da yake manzo Bulus ya san wannan makamin da Shaiɗan yake amfani da shi, amma wasu Kiristoci ba su san da hakan ba. Alal misali, wasu a Koranti sun ga cewa ba za a iya yaudararsu ba don suna ganin cewa su masu ibada ne sosai. (1 Kor. 10:12) Wannan shi ne dalilin da ya sa Bulus ya yi musu kashedi ya ce: ‘Amma ina tsoro kada ya zamana, kamar yadda maciji ya yaudari Hawwa’u da makircinsa, ku ma a bauɗar da hankalinku daga sahihiyar biyayya amintacciya ga Almasihu.’​—2 Kor. 11:​3, Littafi Mai Tsarki.

Abin da Bulus ya faɗa ya nuna cewa bai kamata mu riƙa ganin mu masu ibada ne don haka, ba wanda zai iya yaudararmu. Amma idan ba ka son a yaudare ka, ya kamata ka san haɗarin wannan abin da Shaiɗan yake amfani da shi, wato farfaganda kuma ka kāre kanka.

YADDA FARFAGANDA TAKE DA HAƊARI

Mece ce ma’anar kalmar nan farfaganda? A wannan mahallin tana nufin wani irin ra’ayi na yaudara da Shaiɗan yake amfani da shi don ya rinjayi mutane ko kuma ya ɓata ra’ayinsu. Wani littafi mai suna Propaganda and Persuasion ya ce, farfaganda tana nufin “ƙarya da yaudara da dabara da ake yi don a ɓata ra’ayin mutane.”

Farfaganda tana da haɗari sosai don wannan ra’ayin zai iya rinjayar mutum ba tare da saninsa ba. Za a iya kwatanta wannan ra’ayin da gubar gas da ba za mu iya gani ko jin warinsa ba. Wani masani mai suna Vance  Packard ya ce farfaganda tana shafan yadda muke yin abubuwa “fiye da yadda muke zato.” Wani masani kuma ya ce farfaganda ce take sa mutane suke yin wasu abubuwa masu muni sosai har da kisan ƙare-dangi da yaƙi da tsananta wa mutane don yarensu ko kuma addininsu ya bambanta.​—Easily Led​—A History of Propaganda.

Idan mutane za su iya cusa mana ra’ayinsu, babu shakka, Shaiɗan zai iya yin fiye da hakan. Me ya sa? Ya san yadda mutane suke yin abubuwa tun da aka halicce su. Ban da haka ma, shi yake mulki da “duniya duka.” Don haka, zai iya yin amfani da kowane zarafin da ya samu don ya yaɗa ƙarya. (1 Yoh. 5:19; Yoh. 8:44) Shaiɗan ya ‘makantar da hankalin’ mutane da yawa kuma har ila yana “ruɗin dukan duniya.” (2 Kor. 4:4; R. Yoh. 12:9) Ta yaya za ku guji ra’ayinsa?

KA ƘARFAFA BANGASKIYARKA

Yesu ya nuna mana wata dabara mai sauƙi da za mu yi amfani da ita don mu guji wannan ra’ayin. Ya ce: “Ku san gaskiya, gaskiyar kuwa za ta ’yantar da ku.” (Yoh. 8:​31, 32) Idan ana yaƙi, sojoji suna hattara sosai da maganganun da suke ji don sun san cewa magabtansu za su iya yaɗa ƙarya da manufar yaudarar su. To, a ina ne za mu iya samun shawara da za mu tabbata da ita? Jehobah ya tanadar mana da hakan a cikin Kalmarsa Littafi Mai Tsarki. Idan muka karanta Kalmarsa, za mu san hanyoyin da za mu bi don mu guji wannan banzan ra’ayi na Shaiɗan.​—2 Tim. 3:​16, 17.

Babu shakka, Shaiɗan ya san da hakan. Shi ya sa yake amfani da duniyarsa don ya janye hankalinmu ko kuma ya sa mu sanyin gwiwa idan muna son mu karanta kuma mu yi nazarin Littafi Mai Tsarki. Don haka, bai kamata mu faɗa a tarkon da Shaiɗan ya ɗana mana ba. (Afis. 6:11) Kuma abin da zai taimaka mana shi ne sanin Kalmar Allah da kyau. (Afis. 3:18) Saboda haka, muna bukata mu duƙufa wajen nazari don mu san Littafi Mai Tsarki da kyau. Wani masani mai suna Noam Chomsky ya ce: “Babu mutumin da zai buɗe ƙwaƙwalwarmu kuma ya zuba gaskiyar Littafi Mai Tsarki a ciki. Mu da kanmu ne za mu yi nazarinsa.” Don haka, ka dāge da koyo ta wurin “nazarin Littattafai [Littafi Mai Tsarki] kowace rana.”​—A. M. 17:11.

Idan ba ka son a yaudare ka, ya kamata ka san haɗarin abin da Shaiɗan yake amfani da shi, wato farfaganda kuma ka kāre kanka

 Bai kamata ka manta cewa Shaiɗan ba ya son ka yi tunani da kyau ko kuma ka kasance da ra’ayin da ya dace ba. Me ya sa? Littafin nan Media and Society in the Twentieth Century ya ce ra’ayin farfaganda “yana iya shafan mutum musamman idan ba ya tunani yadda ya dace.” Don haka, bai kamata mu amince da kowane irin magana da muke ji ba tare da yin tunani sosai ba. (Mis. 14:15) Allah ya halicce mu mu riƙa tunani da kyau don mu iya sanin gaskiyar Littafi Mai Tsarki.​—Mis. 2:​10-15; Rom. 12:​1, 2.

KU KASANCE DA HAƊIN KAI

Wasu sojoji suna amfani da ra’ayin farfaganda don su tsoratar da maƙiyansu kuma su ci yaƙi. Za su iya zuga sojojin su yi faɗa da juna ko kuma su zuga su su ware kansu daga sauran. Wani Janar a Jamus ya ce, wannan ita ce dabarar da aka yi amfani da ita don a tsoratar da mutanen Jamus kuma aka ci su a lokacin Yaƙin Duniya na Ɗaya. Haka ma yake a yau, Shaiɗan yana amfani da irin wannan ra’ayin don ya sa Kiristoci su riƙa faɗa da juna. Ban da haka ma, zai iya sa su ware kansu daga ƙungiyar Jehobah don suna ganin an yi musu rashin adalci ko kuma an yi musu abin da bai dace ba.

Kada ka yarda a yaudare ka amma ka riƙa bin abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa cewa mu “gafarta ma juna” kuma kada mu ɓata lokaci wajen sasantawa da juna idan muka samu saɓani da ’yan’uwanmu. (Kol. 3:​13, 14; Mat. 5:​23, 24) Kalmar Allah a kullum tana gaya mana cewa bai kamata mu ware kanmu daga ’yan’uwanmu ba. (Mis. 18:⁠1) Don haka, ya kamata ka bincika kanka ta wurin yin waɗannan tambayoyi: ‘A kwanan baya da na sami saɓani da wani ɗan’uwa, na ɗauki matakin da ya faranta ran Allah ne ko kuma na Shaiɗan?’​—Gal. 5:​16-26; Afis. 2:​2, 3.

KA CI GABA DA KASANCEWA DA AMINCI

Duk wani sojan da ba shi da aminci ga shugabansa ba zai iya yin yaƙi da kyau ba. Don haka, magabta sukan yi amfani da ra’ayin farfaganda don su sa sojoji su daina tabbatawa da shugabansu. Idan shugabanninsu sun yi wani kuskure, za su iya cewa: “Ba za ka iya tabbatawa da su ba sam!” kuma “Kada ka bi shawararsu don kada ka shiga wahala!” Haka ma Shaiɗan yake yi, yana ƙoƙari ya sa kada  mu riƙa tabbata ko yin biyayya da waɗanda Jehobah ya zaɓa su yi mana ja-goranci.

Mene ne zai taimaka maka ka kāre kanka? Ka tsai da shawara cewa ba abin da zai sa ka bar ƙungiyar Jehobah. Ban da haka ma, ka riƙa biyayya ga waɗanda suke mana ja-goranci ko da yake su ajizai ne. (1 Tas. 5:​12, 13) ’Yan ridda da wasu masu yaudara za su iya yin wasu maganganu don su ɓata ƙungiyarmu. Ko da muna gani kamar maganganun da suka yi gaskiya ne, bai kamata mu bar “hankalinmu” ya tashi ba. (2 Tas. 2:2; Tit. 1:10) Ka bi shawarar da aka ba wa matashin nan Timotawus. An gaya masa ya riƙe abin da ya koya daga Littafi Mai Tsarki da kyau kuma kada ya manta wurin da ya koye su. (2 Tim. 3:​14, 15) Babu shakka, kana da abubuwan da suka tabbatar maka da cewa Jehobah ne ya naɗa bawan nan da yake mana ja-goranci kusan shekaru ɗari yanzu kuma su suke nuna mana abin da za mu yi don mu sami rai na har abada.​—Mat. 24:​45-47; Ibran. 13:​7, 17.

KADA KA TSORATA

Shaiɗan har ila yana ƙoƙari ya yaudari mutane suna-ji-suna-gani. A wasu lokuta yakan tsoratar da su. Littafin nan Easily Led​—A History of Propaganda ya ce tsoratar da mutane dabara ce da ake amfani da ita da daɗewa don a yaudari mutane. Alal misali, wani farfesan Biritaniya mai suna Philip M. Taylor ya ce Assuriyawa sun yi amfani da dabarar tsoratar da mutane da kuma wasu dabaru don su shawo kan magabtansu. Haka ma Shaiɗan yake yi, yana yin amfani da tsoron mutane ko tsanani da kuma tsoron mutuwa don ya sa mu daina bauta wa Jehobah.​—Isha. 8:12; Irm. 42:11; Ibran. 2:15.

Kada ka bar Shaiɗan ya yi nasara a kanka! Yesu ya ce: “Kada ku ji tsoron waɗanda ke kisan jiki, daga baya ba su da sauran wani abin da za su yi ba.” (Luk. 12:4) Ka tabbata cewa Jehobah zai cika alkawarinsa na kulawa da kai kuma zai ba ka “mafificin girman iko” da zai taimaka maka ka guji dabarun Shaiɗan.​—⁠2 Kor. 4:​7-9; 1 Bit. 3:⁠14.

Hakika, a wasu lokuta za ka iya yin sanyin gwiwa ko kuma ka ji tsoro. Amma ka riƙa tunawa da ƙarfafar da Jehobah ya yi wa Joshua, ya ce: “Ka ƙarfafa; ka yi ƙarfin zuciya kuma; kada ka tsorata, kada ka yi fargaba kuma: gama Ubangiji Allahnka yana tare da kai dukan inda ka nufa.” (Josh. 1:⁠9) Saboda haka, a duk lokacin da kake fuskantar wata matsala, ka yi addu’a ga Jehobah nan da nan. Idan ka yi hakan, babu shakka ‘salama kuwa ta Allah, . . . za ta tsare zuciyarka da tunaninka cikin Kristi Yesu.’​—Filib. 4:​6, 7, 13.

Ka tuna da farfaganda ko dabarar da wakilin Assuriyawa mai suna Rabshakeh ya yi amfani da ita don ya yaudari mutanen Allah? Kamar dai yana cewa, ‘Babu wanda zai iya kāre ku daga hannun Assuriyawa. Ko Allahnku Jehobah ba zai iya kāre ku ba.’ Ƙari ga haka, da gaba gaɗi ya gaya musu cewa: ‘Jehobah ne ya aike mu mu hallakar da wannan ƙasar.’ Amma mene ne Jehobah ya faɗa? Ya ce: “Kada ka ji tsoron zancen da ka ji, zancen da bayin sarkin Assyria sun saɓe ni da shi.” (2 Sar. 18:​22-25; 19:6) Sai Jehobah ya aiko mala’ika ya hallaka Assuriyawa “ɗari da tamanin da biyar” a dare ɗaya!​—2 Sar. 19:35.

KA ZAMA MAI HIKIMA, KA RIƘA SAURARAR SHAWARAR JEHOBAH

Ka taɓa kallon wani fim kuma ka ga ana yaudarar wani ba tare da saninsa ba? Babu shakka, wataƙila kana ta faɗa a zuciyarka: ‘Kada ka yarda da su! Ƙarya suke yi maka!’ Haka mala’iku suke gaya mana: “Kada ku yarda Shaiɗan ya yaudare ku!”

Saboda haka, kada ka amince da ƙaryar da Shaiɗan yake yi maka. (Mis. 26:​24, 25) Ka riƙa yi wa Jehobah biyayya kuma ka riƙa dogara gare shi. (Mis. 3:​5-7) Ka yi abin da wannan ayar ta ce: “Ɗana, ka yi hikima, ka fa faranta zuciyata.” (Mis. 27:11) Babu shakka, idan ka yi hakan za ka kāre kanka daga ƙaryace-ƙaryacen Shaiɗan!