Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 TALIFIN NAZARI NA 35

Jehobah Yana Daraja Bayinsa Masu Saukin Kai

Jehobah Yana Daraja Bayinsa Masu Saukin Kai

“Yahweh yana . . . kula da masu sauƙin kai.”​—ZAB. 138:6.

WAƘA TA 48 Mu Riƙa Bauta wa Jehobah Kullum

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Yaya Jehobah yake ɗaukan masu sauƙin kai? Ka bayyana.

JEHOBAH yana ƙaunar mutane masu sauƙin kai. Mutane masu sauƙin kai ne kaɗai za su iya ƙulla abota da shi. Amma daga nesa ne yake gane “masu ɗaga kai.” (Zab. 138:6) Wajibi ne mu zama masu sauƙin kai da yake dukanmu muna so mu kasance da dangantaka mai kyau da Jehobah kuma muna so ya ƙaunace mu.

2. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

2 A wannan talifin, za mu amsa tambayoyin nan uku: (1) Mene ne sauƙin kai? (2) Me ya sa muke bukatar mu zama masu sauƙin kai? (3) Waɗanne yanayoyi ne za su nuna ko mu masu sauƙin kai ne? Za mu koya cewa idan muka nuna sauƙin kai, za mu faranta wa Jehobah rai kuma za mu amfana.​—K. Mag. 27:11; Isha. 48:17.

MENE NE SAUƘIN KAI?

3. Mene ne sauƙin kai?

3 Mutum mai sauƙin kai ba ya ganin cewa ya fi sauran mutane daraja. Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa duk masu sauƙin kai sun san cewa Jehobah ne mafi iko kuma suna daraja mutane. Mai sauƙin kai ya san cewa akwai fannin rayuwa da wani ya fi shi.​—Filib. 2:​3, 4.

4-5. Me ya sa muka ce ba a sanin mai sauƙin kai daga kallon fuskarsa?

4 Ana ganin wasu mutane kamar masu sauƙin kai. Wataƙila su masu jin kunya ne ko kuma suna nuna halaye masu kyau saboda al’adarsu ko yadda aka rene su. Amma idan an duba ciki-cikin zuciyarsu, su masu fahariya ne. A  kwana a tashi, wannan halin zai bayyana a ayyukansu.​—Luk. 6:45.

5 A wani ɓangare kuma, wasu mutane suna yawan furta ra’ayinsu, amma hakan ba ya nufin cewa su masu fahariya ne ba. (Yoh. 1:​46, 47) Ya kamata irin mutanen nan su yi hankali don kada su dogara ga iyawarsu. Ko da mu masu jin kunya ne ko a’a, ya kamata mu kasance da sauƙin kai.

Manzo Bulus yana da sauƙin kai kuma bai ɗauki kansa da muhimmanci ba (Ka duba sakin layi na 6) *

6. Kamar yadda 2 Korintiyawa 10:10 ta nuna, wane darasi ne za mu iya koya daga manzo Bulus?

6 Ka yi la’akari da misalin manzo Bulus. Jehobah ya yi amfani da shi sosai wajen kafa sababbin ikilisiyoyi a birane da yawa. Wataƙila ya fi sauran almajiran Yesu samun sakamako mai kyau a wa’azi. Duk da haka, Bulus bai yi girman kai ba. Ya yi wannan furucin cike da sauƙin kai: “Ni ne mafi ƙanƙanta a cikin manzannin Yesu, ban ma isa a ce da ni manzo ba, saboda na tsananta wa jama’ar masu bin Allah.” (1 Kor. 15:9) Sai Bulus ya ce alherin da Jehobah ya nuna masa ne ya sa yake da dangantaka mai kyau da shi ba don ayyukansa masu kyau ba. (Karanta 1 Korintiyawa 15:10.) Manzo Bulus ya kafa mana misali mai kyau a nuna sauƙin kai. A lokacin da ya rubuta wa Kiristoci a Korinti wasiƙa, bai furta abubuwa masu kyau game da kansa ba, duk da cewa wasu a ikilisiyar sun kushe shi.​—2 Kor. 10:10.

Ɗan’uwa Karl F. Klein mai sauƙin kai ne, kuma shi memban Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu ne a dā (Ka duba sakin layi na 7)

7. Ta yaya wasu ʼyan’uwa a zamaninmu suka nuna sauƙin kai? Ka ba da misali.

7 Bayin Jehobah da yawa sun sami ƙarfafawa daga labarin Ɗan’uwa Karl F. Klein, wanda shi memban Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu ne kafin ya rasu. A labarinsa, ya faɗi ƙalubale da yawa da ya kwashi shekaru yana fama da su. Alal  misali, a shekara ta 1922, yin wa’azi gida-gida yana masa wuya sosai. Bayan ya yi wa’azi a lokaci na farko, bai sake yi ba sai bayan shekara biyu. A lokacin da yake hidima a Bethel, ya riƙe wani ɗan’uwa a zuciya saboda gargaɗin da ya yi masa. Bugu da ƙari, ya yi fama da ciwon baƙin ciki mai tsanani, amma ya warke daga baya. Duk da waɗannan matsalolin, ya sami gata sosai a ƙungiyar Jehobah. A bayyane yake cewa shi mai sauƙin kai ne don abubuwan nan da ya rubuta game da kansa. ʼYan’uwa maza da mata da yawa suna tunawa da Ɗan’uwa Klein da labarinsa. *

ME YA SA MUKE BUKATAR MU ZAMA MASU SAUƘIN KAI?

8. Ta yaya 1 Bitrus 5:6 ta sa mu ga cewa nuna sauƙin kai yana faranta ran Jehobah?

8 Dalili mafi muhimmanci da ya sa muke nuna sauƙin kai shi ne domin hakan yana faranta ran Jehobah. Manzo Bitrus ya bayyana hakan sarai. (Karanta 1 Bitrus 5:6.) Littafin nan “Come Be My Follower” ya yi wannan bayanin game da furucin Bitrus: “Girman kai yana kamar guba. Yana jawo mugun sakamako. Ko da mutum yana da iyawa sosai, idan shi mai girman kai ne, ba shi da amfani a wurin Allah. Amma idan wani yana da sauƙin kai, ko da ba a san da shi ba, Jehobah yana daraja shi sosai. . . . Jehobah zai albarkace ka idan kana da sauƙin kai.” * Babu shakka, abu mafi muhimmanci shi ne mu sa Jehobah farin ciki.​—K. Mag. 23:15.

9. Ta yaya nuna sauƙin kai yake sa mutane su kusace mu?

9 Ban da haka, muna samun sakamako masu kyau idan muka nuna sauƙin kai. Nuna sauƙin kai yana sa mutane su kusace mu. Me ya sa? Ka yi tunani a kan irin mutanen da kake so su zama abokanka. (Mat. 7:12) Yawancinmu ba za mu so mu zama abokan mutanen da suke nace a bi nasu ra’ayin ba, amma ba sa so su yi abin da abokansu suke so. Hakazalika, muna jin daɗin yin cuɗanya da ʼyan’uwanmu idan suna ‘jin tausayin juna, suna kuma ƙaunar ’yan’uwa, suna nuna halin taimakon juna ba tare da ɗaga kai ba.’ (1 Bit. 3:8) Idan muna son mutane masu irin halayen nan, su ma za su so mu.

10. Ta yaya sauƙin kai yake sa rayuwarmu ta yi sauƙi?

 10 Sauƙin kai yana kuma sa rayuwarmu ta yi sauƙi. A wasu lokuta, muna iya ganin abubuwan da ba su dace ba. Sarki Sulemanu ya ce: “Na taɓa ganin bayi a kan dawaki, ’ya’yan sarki suna takawa da ƙafa kamar bayi.” (M. Wa. 10:7) A wasu lokuta, ba a girmama mutanen da suke da iyawa sosai. Amma ana girmama mutanen da ba su da iyawa. Sulemanu ya ce kada mu yi fushi idan mun fuskanci irin wannan yanayin domin yanayin rayuwa ke nan. (M. Wa. 6:9) Idan muna da sauƙin kai, za mu amince da abubuwan da suka faru ko da ba ma son su.

WAƊANNE YANAYOYI NE ZA SU NUNA KO MU MASU SAUƘIN KAI NE?

Me ya sa yake da wuya mu nuna sauƙin kai a irin wannan yanayin? (Ka duba sakin layi na 11-12) *

11. Yaya ya kamata mu ji idan wani ya yi mana gargaɗi?

11 Muna samun zarafi a kowace rana don mu nuna cewa mu masu sauƙin kai ne. Ku yi la’akari da wasu misalai. Idan wani ya gargaɗe mu. Ya kamata mu tuna cewa idan wani ya yi mana gargaɗi, hakan yana nufin cewa mun wuce gona da iri. Za mu iya ƙin amincewa da gargaɗin. Muna iya ganin laifin mutumin da ya yi mana gargaɗin ko kuma mu ƙi yarda da furucinsa. Amma, za mu kame kanmu idan muna da sauƙin kai.

12. Kamar yadda Karin Magana 27:​5, 6 suka nuna, me ya sa ya dace mu nuna godiya ga ɗan’uwan da ya gargaɗe mu? Ka ba da misali.

12 Mutumin da ke da sauƙin kai ba ya ƙin gargaɗi. Alal misali: A ce kana cikin taron Kirista. Bayan ka tattauna da ʼyan’uwa da yawa, sai ɗaya cikinsu ya kira ka gefe, kuma ya gaya maka cewa wani abu ya maƙale a haƙorinka. Babu shakka, za ka ji wani iri. Amma za ka yi fushi da shi domin ya gaya maka cewa abu ya maƙale a haƙorinka? A’a. Wataƙila za ka gwammace an gaya maka tun da wuri. Hakazalika, ya kamata mu nuna godiya ga ɗan’uwanmu da ya gargaɗe mu a lokacin da ya dace. Zai dace mu ɗauke shi a matsayin abokinmu ba maƙiyinmu ba.​—Karanta Karin Magana 27:​5, 6; Gal. 4:16.

Me ya sa muke bukatar sauƙin kai sa’ad da aka ba wasu ƙarin gata? (Ka duba sakin layi na 13-14) *

13. Ta yaya za mu nuna sauƙin kai sa’ad da wani ya sami ƙarin gata?

13 Sa’ad da aka ba wani ƙarin gata. Wani dattijo mai suna Jason ya ce: “A wasu lokuta, idan na ga an ba wani gata, ina tunanin dalilin da ya sa ba a ba ni gatan ba.” Ka taɓa jin haka kuwa? Yin “marmarin” samun ƙarin aiki a cikin  ikilisiya ba laifi ba ne. (1 Tim. 3:1) Amma, ya kamata mu yi hattara. Idan ba mu yi hankali ba, za mu soma girman kai. Alal misali, wani ɗan’uwa zai iya soma yin tunani cewa shi ne ya fi ƙwarewa ya yi wani aiki a ikilisiya. Ko kuma wata mace Kirista tana iya soma tunani cewa, ‘Ai maigidana ya fi wane-da-wane ƙwarewa!’ Amma idan muna da sauƙin kai da gaske, ba za mu yi irin wannan tunanin ba.

14. Wane darasi ne za mu iya koya daga yadda Musa ya ji sa’ad da aka ba wasu ƙarin gata?

14 Za mu iya koyan darasi daga yadda Musa ya ji sa’ad da wasu suka sami ƙarin gata. Musa ya ji daɗin aikin da yake yi na yi wa Isra’ilawa ja-goranci. Amma yaya Musa ya ji sa’ad da Jehobah ya naɗa wasu su taya shi yin hidima? Bai yi ƙishin su ba. (L. Ƙid. 11:​24-29) Ya nuna sauƙin kai ta wajen barin mutanen su shari’anta al’ummar. (Fit. 18:​13-24) Mazan da aka naɗa sun taimaka wa Isra’ilawa da suke neman taimako su samu da sauri. Ta hakan, Musa bai fi daraja gatarsa a kan mutanen ba. Hakika, wannan misali ne mai kyau sosai! Ya kamata mu tuna cewa idan muna so Jehobah ya riƙa yin amfani da mu, wajibi ne mu zama masu sauƙin kai. A wurin Jehobah, sauƙin kai ya fi ƙwarewa muhimmanci. Ko da yake Jehobah “yana can sama, yakan kula da masu sauƙin kai.”​—Zab. 138:6.

15. Wane yanayi ne wasu ʼyan’uwa suka fuskanta?

15 Sa’ad da muka fuskanci sabon yanayi. A kwana-kwanan nan, an canja hidimar ʼyan’uwa da yawa da suka ƙware sosai. Alal misali, a shekara ta 2014, an canja hidimar masu kula da gunduma da kuma matansu. Ƙari ga haka, idan mai kula da da’ira ya kai shekara 70, zai daina hidimarsa. Kuma idan mai tsara ayyukan rukunin dattawa ya kai ɗan shekara 80,  zai daina wannan hidimar. Bugu da ƙari, cikin shekaru da yawa yanzu, an canja hidimar wasu ʼyan’uwan da ke hidima a Bethel. Wasu masu hidima a Bethel da majagaba na musamman da masu gina majami’un taro da masu kula da shi da kuma masu kula da da’ira sun daina hidimarsu sanadiyyar rashin lafiya ko matsaloli a iyalinsu da dai sauransu.

16. Ta yaya ʼyan’uwanmu suka nuna sauƙin kai sa’ad da suka sami canji a hidimarsu?

16 Bai kasance wa ʼyan’uwan nan da sauƙi su yi waɗannan canje-canjen ba. Babu shakka, suna son hidimarsu ta dā sosai, wataƙila sun daɗe suna yin hidimar. Wasu sun yi baƙin ciki sosai sa’ad da suka sami canjin hidima. Amma da sannu-sannu, sun yi canje-canje. Me ya sa? Musamman domin suna ƙaunar Jehobah. Sun san cewa sun yi alkawarin bauta wa Jehobah domin suna ƙaunar sa ba don hidimar da suke yi ba ko kuma don suna son yin suna ba. (Kol. 3:23) Suna farin cikin ci gaba da bauta wa Jehobah a kowace hidimar da ya ba su. Sun ‘danƙa masa dukan damuwarsu,’ cike da tabbaci cewa yana kula da su.​—1 Bit. 5:​6, 7.

17. Me ya sa muke farin ciki cewa Jehobah ya ƙarfafa mu mu zama masu sauƙin kai?

17 Babu shakka, muna farin ciki sosai cewa Jehobah ya ƙarfafa mu mu zama masu sauƙin kai. Idan muka nuna wannan halin, za mu amfani kanmu da kuma mutane. Kuma zai fi kasance mana da sauƙi mu bi da matsalolin rayuwa. Mafi muhimmanci ma, za mu kusaci Ubanmu da ke sama. Muna farin cikin sanin cewa ko da yake Jehobah yana “zaune a can sama” kuma shi “Maɗaukaki” ne, yana ƙaunar bayinsa masu sauƙin kai kuma yana daraja su.​—Isha. 57:15.

WAƘA TA 45 Abubuwan da Nake Tunani a Kai

^ sakin layi na 5 Sauƙin kai hali ne mafi muhimmanci da muke bukatar mu kasance da shi. Amma mene ne sauƙin kai? Me ya sa muke bukatar mu kasance da sauƙin kai? Kuma me ya sa nuna halin nan zai iya kasancewa da wuya a wasu lokuta? Za a tattauna muhimman tambayoyin nan a wannan talifin.

^ sakin layi na 7 Ka duba talifin nan “Jehovah Has Dealt Rewardingly With Me” a Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Oktoba, 1984.

^ sakin layi na 8 Ka duba babi na 3, sakin layi na 23.

^ sakin layi na 53 BAYANI A KAN HOTO: Sa’ad da manzo Bulus yake gidan ʼyan’uwansa, ya yi cuɗanya da dukansu har da yara.

^ sakin layi na 57 BAYANI A KAN HOTO: Wani ɗan’uwa yana wa wani da ya girme shi gargaɗi.

^ sakin layi na 59 BAYANI A KAN HOTO: Ɗan’uwa da aka yi wa gargaɗi bai yi ƙishin wancan ɗan’uwan cewa yana da gata a ikilisiya fiye da shi ba.