Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 TALIFIN NAZARI NA 42

Yadda Za Ka Taimaki Dalibi Ya Yi Baftisma—Sashe na Biyu

Yadda Za Ka Taimaki Dalibi Ya Yi Baftisma—Sashe na Biyu

“Ka lura sosai da kanka da kuma koyarwarka.”—1 TIM. 4:16.

WAƘA TA 77 Haske a Duniya Mai Duhu

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Ta yaya muka san cewa yin wa’azi yana ceton mutane?

WA’AZIN da muke yi yana ceton rayukan mutane! Ta yaya muka san hakan? Sa’ad da Yesu ya ba da umurnin da ke Matiyu 28:19, 20, ya ce: “Ku je . . . ku sa su zama almajiraina, kuna yi musu baftisma.” Me ya sa yin baftisma yake da muhimmanci? Wajibi ne mu yi baftisma idan muna so mu sami ceto. Wajibi ne wanda yake so ya yi baftisma ya gaskata cewa zai sami ceto ne domin Yesu ya mutu a madadinmu. Shi ya sa manzo Bitrus ya gaya wa ’yan’uwansa Kiristoci cewa: ‘Baftisma tana cece ku a yanzu. . . . Saboda tashin Yesu Almasihu daga matattu.’ (1 Bit. 3:21) Saboda haka, mutumin da ya yi baftisma yana ɗokin yin rayuwa har abada.

2. Waɗanne irin malamai ne littafin 2 Timoti 4:1, 2 ya ce mu zama?

2 Don mu almajirtar da mutane, muna bukatar mu ƙware sosai a “koyarwa.” (Karanta 2 Timoti 4:1, 2.) Me ya sa? Domin Yesu ya umurce mu cewa: “Ku je . . . ku sa su zama almajiraina, kuna . . . koya musu.” Ban da haka, manzo Bulus ya ce mu “nace” domin idan muka yi haka, za mu ‘ceci kanmu da kuma masu jinmu.’ (1 Tim. 4:16) Muna bukatar mu ƙware a koyarwa kafin mu iya almajirtar da mutane.

3. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

3 Muna nazari da miliyoyin mutane a faɗin duniya. Kamar yadda aka ambata a talifin da ya gabata, muna so mu san yadda za mu taimaka wa mutane da yawa su zama mabiyan Yesu. A wannan talifin, za mu tattauna abubuwa biyar  da kowane malami yake bukata ya yi don ya taimaka wa ɗalibinsa ya cancanci yin baftisma.

KA YI AMFANI DA LITTAFI MAI TSARKI

Ka gaya wa wani da ya ƙware a koyarwa ya taimaka maka ka riƙa amfani da Littafi Mai Tsarki a koyarwarka (Ka duba sakin layi na 4-6) *

4. Me ya sa ya kamata mu guji yin dogon jawabi sa’ad da muke nazari da mutane? (Ka duba ƙarin bayani.)

4 Muna daraja abin da muke koya wa mutane daga Kalmar Allah. Saboda haka, za mu iya so mu yi dogon jawabi sa’ad a muke koyar da mutane. Amma bai kamata mu riƙa hakan ba sa’ad da muke gudanar da nazarin Hasumiyar Tsaro ko Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya ko kuma nazari da ɗalibinmu. Idan malami yana so ya yi amfani da Littafi Mai Tsarki a koyarwarsa, ya kamata ya mai da hankali don kada ya bayyana kome-da-kome da ya sani a kan wata aya ko kuma wani batu. * (Yoh. 16:12) Ka yi tunani a kan yawan ilimin da kake da shi sa’ad da ka yi baftisma da kuma wanda kake da shi yanzu. Babu shakka, ka koyi abubuwa masu sauƙi a lokacin. (Ibran. 6:1) Ka yi shekaru da yawa kafin ka koyi abubuwan da ka sani a yau. Saboda haka, kada ka yi ƙoƙarin koya wa ɗalibinka kome a lokaci ɗaya.

5. (a) Kamar yadda 1 Tasalonikawa 2:13 ta nuna, mene ne muke so ɗalibinmu ya fahimta daga nazarin da muke yi? (b) Ta yaya za mu ƙarfafa ɗalibinmu ya bayyana abubuwan da ya koya?

5 Muna son ɗalibinmu ya san cewa abubuwan da yake koya daga Kalmar Allah ne. (Karanta 1 Tasalonikawa 2:13.) Ta yaya za mu yi hakan? Ka ƙarfafa ɗalibin ya riƙa wa’azi game da abubuwan da yake koya. Maimakon ka riƙa yi wa ɗalibin bayani a kowane lokaci, ka gaya masa ya bayyana maka abin da ya fahimta. Ka taimaka wa ɗalibin ya san yadda Kalmar Allah ta shafe shi. Ka yi masa tambayoyin da za su taimaka masa ya bayyana ra’ayinsa game da ayar da ya karanta. (Luk. 10:25-28) Alal misali, ka tambaye shi: “Ta yaya wannan nassin ya taimaka maka ka ga ɗaya daga cikin halayen Jehobah?” “Ta yaya abubuwan da ka koya daga Littafi Mai Tsarki za su taimaka maka?” “Mene ne ra’ayinka game da abin da ka koya?” (K. Mag. 20:5) Abin da ya fi muhimmanci shi ne yadda ɗalibin yake son abubuwan da yake koya kuma yake amfani da su.

6. Me ya sa yake da kyau mu kai mai shela da ya ƙware nazari da ɗalibinmu?

6 Kana kai masu shela da suka ƙware wurin ɗalibinka kuwa? Idan haka ne, kana iya tambayar ra’ayinsu game da  yadda kake gudanar da nazarin, kuma kana iya tambayar su ko ka yi amfani da Littafi Mai Tsarki yadda ya dace a nazarin. Kana bukatar ka kasance da sauƙin kai idan kana so ka ƙware a koyarwa. (Ka gwada Ayyukan Manzanni 18:24-26.) Bayan haka, ka tambayi mai shelar ko yana ganin cewa ɗalibin yana fahimtar abin da yake koya. Kana iya gaya wa mai shelar ya yi nazari da ɗalibin idan za ka yi tafiya na mako ɗaya ko fiye da hakan. Yin hakan zai sa a riƙa yin nazari da ɗalibin a kai a kai kuma zai nuna wa ɗalibin cewa yin nazari yana da muhimmanci. Kada ka yi tunani cewa shi “ɗalibinka ne” kuma babu wanda zai iya yin nazari da shi. Me ya sa? Domin kana so ɗalibin ya ci gaba da koya game da Jehobah.

KA NUNA CEWA KA GASKATA DA ABIN DA KAKE KOYARWA

Ka faɗa wa ɗalibinka labarai da za su taimaka masa ya fahimci yadda zai yi amfani da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki (Ka duba sakin layi na 7-9) *

7. Mene ne zai taimaka wa ɗalibi ya soma son abubuwan da yake koya?

7 Ɗalibinka yana bukatar ya ga cewa kana son koyarwar Littafi Mai Tsarki kuma ka gaskata da su. (1 Tas. 1:5) Hakan zai sa ya riƙa farin ciki game da abin da yake koya. Idan zai yiwu, ka gaya masa yadda bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki suka taimaka maka. Hakan zai taimaka masa ya ga cewa zai amfana daga bin shawarwarin Littafi Mai Tsarki.

8. Mene ne za ka iya yi don ka taimaka wa ɗalibinka, kuma me ya sa?

8 Sa’ad da kuke nazari, ka ba ɗalibin misalin mutanen da suka fuskanci irin matsalolin da yake fuskanta da kuma yadda suka shawo kansu. Kana iya kai wani ɗan’uwa daga ikilisiya wanda ɗalibin zai iya yin koyi da shi. Ko kuma ka nemo labarai masu ƙarfafawa da ke sashen nan “Littafi Mai Tsarki Yana Gyara Rayuwar Mutane” a dandalin jw.org. * Irin waɗannan talifofin da bidiyoyi za su taimaka wa ɗalibinka ya ga cewa bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki za su kyautata rayuwarsa.

9. Ta yaya za ka ƙarfafa ɗalibinka ya riƙa yi wa iyalinsa da abokansa wa’azi?

9 Idan ɗalibin yana da aure, matarsa tana nazari kuwa? Idan ba ta yi, ka gayyace ta ta bi ku yin nazarin. Ka ƙarfafa ɗalibinka ya riƙa yi wa iyalinsa da kuma abokansa wa’azi game da abubuwan da yake koya. (Yoh. 1:40-45) Kana iya tambayar sa cewa: “Ta yaya za ka bayyana wa iyalinka wannan koyarwar?” ko kuma  “Wace aya ce za ka yi amfani da ita don ka bayyana wa abokinka wannan batun?” Ta yin hakan, kana koya wa ɗalibin ya zama malami. Bayan haka, zai cancanci soma wa’azi tare da ’yan’uwa a ikilisiya. Kana iya tambayar ɗalibin ko ya san wani da yake so a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da shi. Idan ya sani, ka tuntuɓi mutumin nan da nan kuma ka ce za ka yi nazari da shi. Ka nuna masa bidiyon nan Yaya Ake Gudanar da Nazarin Littafi Mai Tsarki? *

KA ƘARFAFA ƊALIBIN YA SAMI ABOKAI A IKILISIYA

Ka ƙarfafa ɗalibin ya ƙulla abokantaka da ’yan’uwa a ikilisiya (Ka duba sakin layi na 10-11) *

10. Kamar yadda 1 Tasalonikawa 2:7, 8 suka nuna, ta yaya malami zai iya yin koyi da Bulus?

10 Wajibi ne malamai su nuna cewa sun damu da ɗalibansu. Ku san cewa za su iya zama ’yan’uwa a ikilisiya nan ba da daɗewa ba. (Karanta 1 Tasalonikawa 2:7, 8.) Ba zai yi musu sauƙi su daina cuɗanya da abokansu na dā ba ko kuma su yi canje-canje don su bauta wa Jehobah ba. Muna bukatar mu taimaka musu su sami abokan kirki a ikilisiya. Ka riƙa cuɗanya da ɗalibinka a wasu lokuta, ba a lokacin da za ku yi nazari kaɗai ba. Kiran sa ta waya ko tura masa saƙo ko kuma ziyartar sa zai nuna masa cewa ka damu da shi.

11. Mene ne muke so ɗalibanmu su samu a ikilisiya, kuma me ya sa?

11 Masu iya magana sun ce: “Hannu ɗaya ba ya ɗaukan jinka.” Hakazalika, “ana bukatar kowa a ikilisiya don a almajirtar da mutum.” Shi ya sa malaman da suka ƙware suke taimaka wa ɗalibansu su san ’yan’uwa a ikilisiya. Waɗannan ’yan’uwan za su taimaka musu su zama abokan Jehobah kuma su ƙarfafa su sa’ad da suke fuskantar matsaloli. Muna so ɗalibinmu ya san cewa muna ƙaunar sa kuma yana cikin iyalinmu na faɗin duniya. Muna so ɗalibinmu ya ƙulla abokantaka da ’yan’uwa a ikilisiya. Hakan zai sa ya yi masa sauƙi ya daina cuɗanya da abokan banza. (K. Mag. 13:20) Idan abokansa na dā suka daina cuɗanya da shi, ya san cewa zai sami abokan kirki a ƙungiyar Jehobah.—Mar. 10:29, 30; 1 Bit. 4:4.

KA RIƘA GAYA MASA GAME DA YIN ALKAWARIN BAUTA WA ALLAH DA BAFTISMA

Sannu-a-hankali ɗalibinka zai cim ma burinsa na yin baftisma! (Ka duba sakin layi na 12-13)

12. Me ya sa muke bukatar mu riƙa yin magana game da alkawarin bauta wa Jehobah da kuma baftisma da ɗalibinmu?

12 Kana bukatar ka riƙa gaya masa muhimmancin yin alkawarin bauta wa Jehobah da kuma baftisma. Domin maƙasudinmu na yin nazari da mutum shi ne  mu taimaka masa ya soma bauta wa Jehobah. ’Yan watanni bayan mun soma nazari a kai a kai da ɗalibin kuma ya soma halartan taro, ya kamata ya fahimci cewa muna so mu taimaka masa ya zama Mashaidin Jehobah.

13. Waɗanne abubuwa ne ɗalibi zai yi don ya cancanci yin baftisma?

13 Akwai abubuwa da yawa da ɗalibin da yake son yin baftisma yake bukatar yi! Na farko, yana bukatar ya san Jehobah sosai, ya ƙaunace shi kuma ya yi imani da shi. (Yoh. 3:16; 17:3) Hakan zai sa ɗalibin ya ƙulla dangantaka da Jehobah kuma ya soma cuɗanya da ’yan’uwa a ikilisiya. (Ibran. 10:24, 25; Yaƙ. 4:8) Ɗalibin zai yi da-na-sani don ayyukansa na dā kuma zai tuba. (A. M. 3:19) Ban da haka, zai riƙa yi wa mutane wa’azi game da abubuwan da ya yi imani da su. (2 Kor. 4:13) Sai ya yi alkawarin bauta wa Jehobah kuma ya yi baftisma. (1 Bit. 3:21; 4:2) Kowa zai yi farin ciki a wannan ranar! Yayin da ɗalibin yake cim ma maƙasudansa, ka riƙa yaba masa da kuma ƙarfafa shi ya ci gaba da yin waɗannan abubuwan.

KA RIƘA LURA DA YADDA ƊALIBIN YAKE SAMUN CI GABA

14. Ta yaya malami zai bincika don ya san ko ɗalibinsa yana samun ci gaba?

14 Muna bukatar mu zama masu haƙuri yayin da muke taimaka wa ɗalibinmu ya sami ci gaba, har ya yi alkawarin bauta wa Allah da kuma baftisma. Amma lokaci zai kai, da za mu bukaci mu bincika ko yana so ya bauta wa Jehobah. Shin akwai alama cewa ɗalibin yana so ya bi umurnin Yesu? Ko kuma kawai yana so ya koya abubuwa masu ban-sha’awa daga Littafi Mai Tsarki ne?

15. Waɗanne abubuwa ne za su nuna cewa ɗalibi yana samun ci gaba?

15 Ka riƙa bincika don ka san ko ɗalibin yana samun ci gaba. Alal misali, yana faɗin yadda yake ji game da Jehobah? Yana addu’a ga Jehobah? (Zab. 116:1, 2) Yana jin daɗin karanta Littafi Mai Tsarki? (Zab. 119:97) Yana halartan taro a kai a kai? (Zab. 22:22) Ya yi canje-canje a rayuwarsa da suka nuna cewa yana yin amfani da abubuwan da yake koya? (Zab. 119:112) Ya soma gaya wa iyalinsa da abokansa abubuwan da yake koya?  (Zab. 9:1) Mafi muhimmanci ma, yana so ya zama Mashaidin Jehobah? (Zab. 40:8) Idan ɗalibin ba ya samun ci gaba a waɗannan hanyoyin, ka yi ƙoƙari ka san dalilin kuma ka tattauna batun da shi don ya san inda ya kamata ya yi gyara. *

16. A wane lokaci ne ya kamata ka daina yin nazari da wani?

16 Ka riƙa tambayar kanka a wasu lokuta ko zai dace ka ci gaba da yin nazari da wani ɗalibi. Ka tambayi kanka: ‘Shin ɗalibin yana shiri don nazarin? Yana son halartan taro kuwa? Har yanzu yana da halayen banza ne? Har yanzu yana cuɗanya da addinin ƙarya?’ Idan amsar e ce, ci gaba da yin nazari da shi yana kamar koya wa mutumin da ba ya so ruwa ya taɓa jikinsa, yin iyo! Babu amfanin ci gaba da nazari da ɗalibin, idan ba ya son abubuwan da yake koya kuma bai yi shirin yin canje-canje ba.

17. Kamar yadda 1 Timoti 4:16 ta nuna, mene ne dukan malaman Littafi Mai Tsarki za su yi?

17 Ya kamata mu ɗauki almajirtarwa da muhimmanci sosai, kuma mu so taimaka wa ɗalibanmu su cancanci yin baftisma. Shi ya sa muke amfani da Littafi Mai Tsarki a koyarwarmu kuma muke nuna cewa mun gaskata da abin da muke koyarwa. Za mu ƙarfafa ɗalibin ya sami abokai a ikilisiya. Za mu nuna masa muhimmanci yin alkawarin bauta wa Jehobah da kuma baftisma. Ban da haka, mu riƙa bincika ko yana samun ci gaba. (Ka duba akwatin nan a shafi na 13, “ Abin da Za Mu Yi Don Ɗalibanmu Su Cancanci Yin Baftisma.”) Muna farin ciki cewa muna da damar saka hannu a wannan aikin da ke ba mutane damar samun rai! Muna bukatar mu yi iya ƙoƙarinmu don mu taimaka wa ɗalibanmu su cancanci yin baftisma.

WAƘA TA 79 Mu Koya Musu Su Kasance da Aminci

^ sakin layi na 5 Sa’ad da muke nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane, muna da zarafin taimaka musu su koyi abubuwan da Jehobah yake so su yi. Wannan talifin zai taimaka mana mu inganta koyarwarmu.

^ sakin layi na 4 Ka duba talifin nan “Ka Guji Abubuwan Nan Sa’ad da Kake Nazarin Littafi Mai Tsarki” a Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu na Satumba 2016.

^ sakin layi na 8 Ka shiga sashen GAME DA MU > LABARAI.

^ sakin layi na 9 A jw.org, ka shiga sashen LABURARE > BIDIYOYI > TARO DA HIDIMARMU > ABUBUWAN YIN WA’AZI.

^ sakin layi na 15 Ka duba talifofin nan “Ƙauna ga Jehobah Za Ta Sa Mu Yi Baftisma” da kuma “Ka Shirya Yin Baftisma Kuwa?” a Hasumiyar Tsaro na nazari ta Maris 2020.

^ sakin layi na 77 BAYANI A KAN HOTUNA: Bayan sun kammala nazarin, ’yar’uwa da ta ƙware tana taimaka wa ʼyar’uwar da ta gudanar da nazarin ta koyi yadda za ta guji yin dogon jawabi.

^ sakin layi na 79 BAYANI A KAN HOTUNA: A lokacin nazarin, ɗalibar ta koyi yadda za ta zama matar kirki. Daga baya, ta gaya wa mijinta abubuwan da ta koya.

^ sakin layi na 81 BAYANI A KAN HOTUNA: Ɗalibar da maigidanta sun kai ziyara gidan wasu ’yan’uwa ma’aurata da suka haɗu da su a Majami’ar Mulki.