Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 TALIFIN NAZARI NA 40

Ka Ci Gaba da Kwazo a Karshen “Kwanaki na Karshe”

Ka Ci Gaba da Kwazo a Karshen “Kwanaki na Karshe”

“Ku tsaya daram, ku kafu, kullum kuna yalwata cikin aikin Ubangiji.”​—1 KOR. 15:58.

WAƘA TA 58 Muna Neman Mutane Masu Sauƙin Kai

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Me ya tabbatar mana da cewa muna rayuwa a “kwanaki na ƙarshe”?

IDAN an haife ka bayan shekara ta 1914, to, kana rayuwa ne a kwanaki na ƙarshe. (2 Tim. 3:1) Dukanmu muna jin abubuwan da Yesu ya annabta cewa za su faru a zamaninmu. Hakan ya ƙunshi yaƙe-yaƙe da rashin abinci da girgizar ƙasa da cututtuka iri-iri. Ya kuma ƙunshi yadda ɗabi’un mutane za su daɗa muni da kuma yadda za a tsananta wa bayin Jehobah. (Mat. 24:​3, 7-9, 12; Luk. 21:​10-12) Ƙari ga haka, muna ganin yadda mutane suke nuna halayen da manzo Bulus ya yi magana a kai. (Ka duba akwatin nan “ Halayen Mutane a Yau.”) A matsayinmu na bayin Jehobah, muna da tabbaci cewa muna rayuwa a kwanaki na ƙarshe.

2. Waɗanne amsoshi ne muke bukata?

2 Babu shakka, muna ƙarshen “kwanaki na ƙarshe” domin shekara ta 1914 ta daɗe da wucewa. Da yake ƙarshen zamanin nan ya yi kusa sosai, muna bukatar mu sami amsa ga tambayoyin nan masu muhimmanci: Waɗanne abubuwa ne za su faru a ƙarshen “kwanaki na ƙarshe”? Mene ne Jehobah yake so mu riƙa yi yayin da muke jira waɗannan abubuwan su faru?

MENE NE ZAI FARU A ƘARSHEN “KWANAKI NA ƘARSHE”?

3. Kamar yadda annabcin da ke 1 Tasalonikawa 5:​1-3 ya nuna, wace sanarwa ce al’ummai za su yi?

3 Karanta 1 Tasalonikawa 5:​1-3. Bulus ya ambata “ranar Ubangiji.” A wannan nassin, “ranar Ubangiji” tana nufin lokacin da za a kai hari ga “Babila Babba,” wato dukan addinan ƙarya kuma za a kammala hakan da yaƙin Armageddon. (R. Yar. 16:​14, 16; 17:5) Kafin haka ya faru, al’ummai za su sanar cewa an sami “zaman lafiya da salama!” Shugabannin  duniya suna yin amfani da wannan furuci a wasu lokuta sa’ad da suke magana game da kyautata dangantakarsu da sauran ƙasashe. * Amma wannan sanarwar “zaman lafiya da salama” da Littafi Mai Tsarki ya ambata zai yi dabam. Me ya sa? Domin idan aka yi sanarwar, mutane za su ɗauka cewa shugabannin duniya sun yi nasara wajen kawo zaman lafiya a duniya. Amma gaskiyar ita ce, “halaka za ta auko musu” kuma ƙunci mai girma za ta biyo baya.​—Mat. 24:21.

Kada mu bari sanarwa cewa an sami “zaman lafiya da salama” ta yaudare mu (Ka duba sakin layi na 3-6) *

4. (a) Me muke bukatar mu sani game da sanarwar “zaman lafiya da salama” da za a yi? (b) Mene ne muka sani game da sanarwar?

4 Mun san wasu abubuwa game da sanarwa da za a yi cewa an sami “zaman lafiya da salama.” Amma akwai abubuwan da ba mu sani ba. Ba mu san abin da zai sa a yi sanarwa ba ko kuma yadda za a yi sanarwar. Ƙari ga haka, ba mu san ko za a yi sanarwa ɗaya ne ko kuma sanarwa da yawa ba. Ko da me zai faru, mun san cewa: Shugabannin duniya ba za su iya kawo zaman lafiya a duniya ba. Saboda haka, ba za mu yarda sanarwar ta ruɗar da mu ba. Sanarwa ce da Kalmar Allah ta ce mu mai da wa hankali. Domin alama ce da za ta nuna cewa “ranar Ubangiji” tana gab da somawa!

5. Ta yaya 1 Tasalonikawa 5:​4-6 za su taimaka mana mu yi shiri don “ranar Ubangiji”?

5 Karanta 1 Tasalonikawa 5:​4-6. Shawarar da Bulus ya bayar ta koya mana yadda za mu nuna cewa muna shirye don zuwan “ranar Ubangiji.” Kada mu “yi barci yadda waɗansu suke yi.” Muna bukatar mu kasance a faɗake. Alal misali, muna bukatar mu mai da hankali don mu guji saka hannu a harkokin duniya da na siyasa. Idan muka saka hannu a abubuwan nan, za mu iya zama “na duniya” ne. (Yoh. 15:19) Mun san cewa Mulkin Allah ne kaɗai zai sa mutane su zauna lafiya.

6. Mene ne muke bukatar mu taimaka wa mutane su yi, kuma me ya sa?

6 Ban da kasancewa a faɗake, muna bukatar mu taimaka wa mutane su san abubuwan da Littafi Mai Tsarki ya ce za su faru a duniyar nan. Muna bukatar mu yi hakan yanzu, domin idan ƙunci mai girma ya soma, zai yi wa mutane wuya su soma bauta wa Jehobah. Don haka, yana da muhimmanci mu yi wa’azi yanzu! *

KU CI GABA DA YIN WA’AZI DA ƘWAZO

Yayin da muke yin wa’azi a yau, muna nuna cewa Mulkin Allah ne kaɗai zai kawo zaman lafiya da salama (Ka duba sakin layi na 7-9)

7. Mene ne Jehobah yake so mu yi a yanzu?

7 A wannan ɗan ƙanƙanin lokaci da ya rage kafin “ranar” Jehobah ta soma, Jehobah yana so mu ci gaba da yin wa’azi da himma. Muna bukatar mu tabbata cewa muna yin ƙwazo sosai a “aikin Ubangiji.” (1 Kor. 15:58) Yesu ya annabta abin da muke bukatar mu yi. Sa’ad da ya yi magana  game da abubuwan da za su faru a kwanaki na ƙarshe, ya ƙara da cewa: “Kuma za a ba da wannan labari mai daɗi na mulkin sama domin shaida ga dukan al’umma.” (Mar. 13:​4, 8, 10; Mat. 24:14) Ka yi tunani: A duk lokacin da ka fita wa’azi, kana sa annabcin nan ya cika!

8. Ta yaya muka san cewa muna yin nasara a wa’azi?

8 Muna yin nasara a wa’azi kuwa? A kowace shekara, mutane da yawa suna saurarar wa’azin Mulkin Allah. Alal misali, ka yi tunanin yadda masu shela suka ƙaru a faɗin duniya a kwanaki na ƙarshe. A shekara ta 1914, masu shela guda 5,155 ne kawai a ƙasashe 43. A yau, akwai masu shela wajen 8,500,000 a ƙasashe 240! Duk da haka, aikinmu bai ƙare ba. Muna bukatar mu ci gaba da yin wa’azi cewa Mulkin Allah ne kaɗai zai magance matsalolinmu.​—Zab. 145:​11-13.

9. Me ya sa muke bukatar mu ci gaba da yin wa’azin Mulkin Allah?

9 Wa’azin da muke yi ba zai ƙare ba har sai Jehobah ya ce hakan. Kwanaki nawa ne ya rage wa mutane su koya game da Jehobah da kuma Yesu? (Yoh. 17:3) Ba mu sani ba. Amma mun san cewa kafin a soma ƙunci mai girma, mutanen da ke da “zuciya ta samun rai na har abada” suna iya jin wa’azinmu kuma su soma bauta wa Jehobah. (A. M. 13:​48, NW ) Ta yaya za mu taimaka wa mutanen nan kafin lokaci ya ƙure musu?

10. Ta yaya Jehobah yake taimaka mana mu koya wa mutane gaskiya?

10 Jehobah yana yin amfani da ƙungiyarsa don ya tanada mana dukan abubuwan da muke bukata mu koya wa mutane gaskiya. Alal misali a kowace mako, ana koyar da mu a taron tsakiyar mako. A taron, ana koya mana yadda za mu yi wa’azi a ƙaro na farko da koma ziyara da kuma gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki. Ban da haka, ƙungiyar Jehobah ta yi tanadin Kayan Aiki don Koyarwa. Abubuwan nan na taimaka mana mu . . .

 • soma tattaunawa da mutane,

 • yi wa’azi a hanya mai daɗi,

 • motsa su su so ci gaba da koyo game da Allah,

 • koya wa mutane gaskiyar Littafi Mai Tsarki sa’ad da muke nazari da su, kuma

 •   gayyaci mutanen da ke son wa’azinmu su shiga dandalinmu kuma su zo Majami’ar Mulki.

Hakika, muna bukatar mu riƙa yin amfani da kayan aikin nan. * Alal misali, bayan mun tattauna da wani da ke son saƙonmu, kuma muka ba shi warƙa ko mujalla, zai ci gaba da karanta shi kafin mu sake dawowa. Hakkinmu ne mu ci gaba da yin ƙwazo a wa’azi kowane wata.

11. Me ya sa aka shirya shafin nan Online Bible Study Lessons?

11 Shafin nan Online Bible Study Lessons a jw.org® wata hanya ce da Jehobah yake taimaka wa mutane su koyi gaskiyar da ke Kalmarsa. * (Ka duba ƙarƙashin BIBLE TEACHINGS > ONLINE LESSONS.) Me ya sa aka shirya wannan shafin? A kowane wata, dubban mutane a faɗin duniya suna bincika Intane don koyan darussa daga Littafi Mai Tsarki. Shafin da ke koya wa mutane darussa daga Littafi Mai Tsarki a dandalinmu zai iya taimaka wa mutane su soma koyan gaskiya da ke Kalmar Allah. Wataƙila wasu cikin mutanen da kake haɗuwa da su a wa’azi suna jinkirin soma yin nazarin Littafi Mai Tsarki. Idan haka ne, ka nuna musu wannan shafin da ke dandalinmu ko kuma ka tura musu adireshin, idan zai yiwu ka tura musu adireshin dandalin jw.org a yarensu.

12. Mene ne mutum zai iya koya daga shafin Online Bible Study Lessons?

12 A shafin Online Bible Study Lessons da ke dandalinmu, an tattauna waɗannan batutuwan: “Littafi Mai Tsarki da Kuma Mawallafinsa,” da “Mutanen da Aka Ambata a Littafi Mai Tsarki,” da kuma “Saƙon Littafi Mai Tsarki da Ke Sa A Kasance da Bege.” Waɗannan batutuwan za su taimaka wa mutum ya san:

 • Yadda Littafi Mai Tsarki zai taimaka masa

 • Jehobah da Yesu da kuma mala’iku

 • Dalilin da ya sa Allah ya halicci ’yan Adam

 • Dalilin da ya sa mutane ke shan wahala da kuma abin da ya sa mugaye suke ko’ina

Ƙari ga haka, an tattauna yadda Jehobah zai . . .

 • cire wahala da kuma mutuwa

 • yadda zai ta da matattu da kuma

 • yadda zai kawar da gwamnatin ’yan Adam kuma ya kafa Mulkinsa.

13. Shafin online study lessons ya sauya yin nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane ne? Ka bayyana.

13 Wannan shafin da aka shirya ba ya nufin cewa ba za mu riƙa yin nazarin Littafi Mai Tsarki da ɗalibanmu ba. Yesu ya ba mu gatan almajirtar da mutane. Muna fatan cewa mutanen da ke son wa’azinmu za su yi nazarin waɗannan darussa a dandalinmu, su so abubuwan da suka koya kuma su ci gaba da koyo. Idan hakan ya faru, wataƙila za su so a yi nazari da su. A ƙarshen kowane darasi, ana ce wa mai karatu ya cika fom idan zai so wani ya zo ya riƙa yin nazarin Littafi Mai Tsarki da shi. Ta dandalinmu, mutane fiye da 230 a faɗin duniya suna turo saƙo a kowace rana cewa suna so a yi nazari da su! Yin nazarin Littafi Mai Tsarki fuska da fuska yana da muhimmanci sosai!

KU CI GABA DA ƘOƘARIN ALMAJIRTAR DA MUTANE

14. Bisa ga umurnin da Yesu ya ba da a Matiyu 28:​19, 20, mene ne muke ƙoƙarin yi, kuma me ya sa?

14 Karanta Matiyu 28:​19, 20. Yayin da muke nazari da ɗalibanmu, muna bukatar  mu ƙoƙarta mu taimaka musu su zama almajiran Yesu kuma mu ‘koya musu su yi biyayya da dukan abubuwan da [Yesu] ya umarce mu.’ Muna bukatar mu taimaka wa mutane su san cewa yana da muhimmanci su soma bauta wa Jehobah kuma su goyi bayan Mulkinsa. Hakan yana nufin cewa, za mu yi iya ƙoƙarinmu mu taimaka musu su riƙa yin abin da suke koya, su yi alkawarin bauta wa Jehobah kuma su yi baftisma. Yin hakan ne kaɗai zai sa su tsira.​—1 Bit. 3:21.

15. Mene ne ba za mu ɓata lokaci muna yi ba, kuma me ya sa?

15 Kamar yadda aka ambata ɗazu, kwanakin da suka rage kafin wannan zamanin ya ƙare ba su da yawa. Don haka, ba za mu ɓata lokaci muna yin nazari da mutanen da ba sa so su zama mabiyan Kristi ba. (1 Kor. 9:26) Aikinmu yana da gaggawa sosai! Akwai mutane da yawa da suke bukatar su ji saƙon Mulkin Allah kafin lokaci ya ƙure.

KA GUJE WA ADDININ ƘARYA

16. Kamar yadda Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 18:​2, 4, 5, 8 suka nuna, mene ne muke bukatar mu yi? (Ka duba ƙarin bayani.)

16 Karanta Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 18:​2, 4, 5, 8Waɗannan ayoyin sun nuna wani abu kuma da Jehobah yake so bayinsa su riƙa yi. Dukan Kiristoci na gaskiya suna bukatar su nuna cewa akwai bambanci tsakanin su da Babila Babba. Wataƙila kafin wani ɗalibi ya koyi gaskiya, yana bin addinin ƙarya. Ƙila yana yin ibada tare da su kuma yana saka hannu a harkokinsu. Ko kuma yana ba ƙungiyar gudummawar kuɗi. Saboda haka, kafin a yarda ɗalibin Littafi Mai Tsarki ya zama mai shela da bai yi baftisma ba, dole ne ya cire hannunsa daga duk wani abin da ya shafi addinin ƙarya. Yana bukatar ya rubuta wasiƙa ga cocinsu na dā ko kuma duk wata ƙungiyar da take da alaƙa da addinin ƙarya da yake a dā cewa ya daina tarayya da su. *

17. Waɗanne irin ayyuka ne Kirista yake bukatar ya guje wa, kuma me ya sa?

17 Kirista na gaskiya yana bukatar ya tabbata cewa aikin da yake yi ba ta da alaƙa da Babila Babba. (2 Kor. 6:​14-17) Alal misali, ba zai yi aiki a coci ba. Ƙari ga haka, ba zai dace Kirista da yake aiki a wata masana’anta ya yi aiki sosai a ginin da ake amfani da shi don goyon bayan addinin ƙarya ba. Kuma idan yana da nasa sa’ana, hakika ba zai dace ya nemi ko kuma ya amince ya yi aiki a wurin da ke da alaƙa da Babila Babba ba. Me ya sa muke ɗaukan wannan  matakin? Ba ma so mu saka hannu a ayyukan addinan ƙarya da kuma zunubansu domin ba su da tsabta a gaban Allah.​—Isha. 52:11. *

18. Ta yaya wani ɗan’uwa ya bi ƙa’idar Littafi Mai Tsarki a aikinsa?

18 Shekaru da yawa da suka shige, wani ɗan’uwa da yake aikin gine-gine ya sami aikin kafinta a wani coci a garin da yake. Mutumin da ya ba ɗan’uwan aiki ya san cewa ɗan’uwan ya saba faɗa cewa ba zai yi aiki a coci ba. Amma mutumin yana neman wanda zai yi aikin da gaggawa. Duk da haka, ɗan’uwan ya bi ƙa’idar Littafi Mai Tsarki kuma ya ƙi yin aikin. Bayan mako guda, sai aka wallafa labari a jarida kuma aka nuna hoton wani kafinta yana saka giciye a cocin. Da a ce wannan ɗan’uwan ya ƙi bin ƙa’idar Littafi Mai Tsarki, da hotonsa za a saka a wannan jaridar. Ka yi tunanin yadda hakan zai ɓata sunansa a gaban ’yan’uwansa Kiristoci! Ban da haka, ka yi tunanin yadda Jehobah zai ji.

ME MUKA KOYA?

19-20. (a) Mene ne muka koya? (b) Mene ne za mu ƙara koya?

19 Littafi Mai Tsarki ya gaya mana annabci mai muhimmanci da zai cika nan ba daɗewa ba. Annabcin shi ne sanarwar da shugabannin duniya za su yi cewa an sami “zaman lafiya da salama.” Domin abubuwan da Jehobah ya koya mana, mun san cewa al’ummai ba za su sami cikakkiyar salama ba. Mene ne muke bukatar mu yi kafin wannan abu ya faru kuma halaka ta biyo bayan haka? Jehobah yana so mu ci gaba da yin ƙwazo a wa’azin Mulkinsa kuma mu ƙoƙarta don mu almajirtar da mutane. Ƙari ga haka, muna bukatar mu guji saka hannu a ayyukan da suka shafi addinan ƙarya. Hakan ya ƙunshi ƙin karɓan aikin da ke goyon bayan Babila Babba.

20 Akwai ƙarin abubuwan da za su faru a waɗannan “kwanaki na ƙarshe.” Akwai kuma wasu abubuwa da Jehobah yake so mu riƙa yi. Waɗanne abubuwa ke nan, kuma ta yaya za mu yi shiri don abubuwan da za su faru a nan gaba? Za mu tattauna hakan a talifi na gaba.

WAƘA TA 71 Mu Rundunar Jehobah Ne!

^ sakin layi na 5 Nan ba da daɗewa ba, shugabannin duniya za su sanar cewa an sami “zaman lafiya da salama!” Wannan ita ce alamar da za ta nuna cewa ƙunci mai girma ya kusan somawa. Mene ne Jehobah yake so mu yi yanzu da kuma a lokacin da aka yi sanarwar? Wannan talifin zai taimaka mana mu sami amsar.

^ sakin layi na 3 Alal misali, Majalisar Ɗinkin Duniya ta rubuta a dandalinta cewa tana “sa al’ummai su kasance da zaman lafiya da kuma salama.”

^ sakin layi na 10 Don ƙarin bayani game da yadda za mu yi amfani da Kayan Aiki don Koyarwa, ka duba talifin nan “Ka Riƙa Koyar da Gaskiya” a Hasumiyar Tsaro ta Oktoba 2018.

^ sakin layi na 11 Za a iya samun wannan shafin a Turanci da yaren Portuguese da kuma wasu yaruka.

^ sakin layi na 16 Ƙari ga haka, muna bukatar mu guji abubuwa kamar su ƙungiyoyin matasa ko kuma wuraren shaƙatawa da suke da alaƙa da addinan ƙarya. Alal misali a wasu wurare, ƙungiyoyin da ke da alaƙa da addinan ƙarya suna gina wuraren wasa da na motsa jiki da dai sauransu. Duk da cewa ƙungiyoyin nan suna iya yin da’awa cewa ba su da wata alaƙa da addinan ƙarya, amma gaskiyar ita ce, suna goyon bayan addinan ƙarya.

^ sakin layi na 17 Don samun cikakken bayani game da ra’ayin Allah a kan yin aiki a ƙungiyar da take da alaƙa da addinin ƙarya, ka duba “Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu” a Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Afrilu, 1999, na Turanci.

^ sakin layi na 83 BAYANI A KAN HOTUNA: Mutane a shagon shayi suna saurarar “Labarai da Ɗumi-Ɗuminsa” a talabijin game da sanarwar cewa an sami “zaman lafiya da salama.” Wasu Shaidu ma’aurata da suke hutawa bayan sun dawo daga wa’azi ba su damu da sanarwar ba.