Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

“Mu Yi Kauna . . . da Aiki da Gaskiya Kuma”

“Mu Yi Kauna . . . da Aiki da Gaskiya Kuma”

‘Kada mu yi ƙauna da baki ko kuwa da harshe; amma da aiki da gaskiya kuma.’​—1 YOH. 3:18.

WAƘOƘI: 72, 124

1. Wace irin ƙauna ce ta fi muhimmanci, kuma ta yaya za ka kwatanta ta? (Ka duba hoton da ke shafin nan.)

ƘAUNA kyauta ce daga wurin Jehobah kuma shi ne tushen ta. (1 Yoh. 4:7) Wannan ƙaunar ce ta fi muhimmanci. An kwatanta irin wannan ƙaunar a Littafi Mai Tsarki da wata kalmar Helenanci da ake kira a·gaʹpe. Ko da yake irin wannan ƙaunar ta ƙunshi yin la’akari da mutane da kuma nuna mun damu da su, ta ƙunshi wani abu. Me ke nan? Ta ƙunshi nuna ƙauna ba tare da son kai ba don mutane su amfana. Ƙauna ce take sa mu taimaka wa mutane. Kuma idan muka yi hakan, muna farin ciki kuma rayuwarmu tana kasancewa da ma’ana.

2, 3. Ta yaya Jehobah ya nuna wa mutane ƙauna ba tare da son kai ba?

2 Jehobah ya nuna yana ƙaunar mutane tun kafin ya halicci Adamu da Hawwa’u. Ya halicci duniya don mutane su zauna kuma su ji daɗin rayuwa a cikinta sosai. Jehobah ya yi hakan ne ba don amfanin kansa ba, amma don mutane su amfana. Ƙari ga haka, da ya gama halittar duniya, sai ya halicce mutane ya albarkace su don su yi rayuwa a duniya har abada.

3 Amma da Adamu da Hawwa’u suka yi zunubi, sai Jehobah  ya nuna wata irin ƙauna da babu kamarta, wato ƙauna ba tare da son kai ba. Ta yaya ya yi hakan? Ta wurin tsai da shawarar ceto ’ya’yansu domin yana da tabbaci cewa wasu cikinsu za su kasance da aminci. (Far. 3:15; 1 Yoh. 4:10) A lokacin da Jehobah ya yi alkawari cewa akwai wani da zai ceci mutane, a ganinsa kamar an riga an ba da fansar. Amma bayan shekaru 4,000 ne Jehobah ya aiko da Ɗansa makaɗaici don ya ceci mutane. (Yoh. 3:16) Muna godiya don irin wannan ƙauna da Jehobah ya nuna mana, ko ba haka ba?

4. Me ya nuna cewa mutane ajizai za su iya nuna ƙauna ba tare da son kai ba?

4 Mu ma za mu iya nuna ƙauna ba tare da son kai ba domin Allah ya halicce mu yadda za mu iya yin koyi da halayensa. Za mu iya yin hakan ko da yake zunubin da muka gāda yana sa ya kasance mana da wuya mu riƙa nuna ƙauna. Habila ya nuna yana ƙaunar Allah ba tare da son kai ba, shi ya sa ya ba da hadaya mafi kyau. (Far. 4:​3, 4) Nuhu ma ya nuna irin wannan ƙaunar shi ya sa ya yi wa mutane wa’azi na shekaru da yawa ko da yake babu wanda ya saurare shi. (2 Bit. 2:5) Wani kuma shi ne Ibrahim wanda ya nuna yana ƙaunar Allah fiye da kansa a lokacin da aka gaya masa ya yi hadaya da ɗansa Ishaku. (Yaƙ. 2:21) Kamar waɗannan mutane masu aminci, mu ma muna bukatar mu nuna ƙauna ko da muna fuskantar matsaloli.

ƘAUNA TA GASKIYA DA KUMA TA JEBU

5. Ta yaya za mu nuna ƙauna ta gaskiya?

5 Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa ana nuna ƙauna ta gaskiya ba ‘da baki ko kuwa da harshe ba; amma da aiki da gaskiya.’ (1 Yoh. 3:18) Shin hakan yana nufin cewa ba za mu iya nuna ƙauna ta wurin furucinmu ba ne? A’a. (1 Tas. 4:18) Abin da wurin yake nufi shi ne cewa ba kawai da baki za mu riƙa nuna muna ƙaunar mutane ba, amma mu taimaka musu sa’ad da suke bukatar taimako. Alal misali, idan wani yana da bukata kuma yana neman taimako, ya kamata mu ba shi abin da yake bukata ba ƙarfafa shi kawai da baki ba. (Yaƙ. 2:​15, 16) Hakazalika, ƙaunar da muke nuna wa Allah da mutane za ta sa mu roƙi Allah ya turo mutanen da za mu yi wa’azi da su kuma mu ma mu riƙa yin iya ƙoƙarinmu a yin hakan.​—Mat. 9:38.

6, 7. (a) Mece ce ƙauna “marar-riya”? (b) Waɗanne misalai na nuna ƙauna ta jebu ne muke da su?

6 Manzo Bulus ya ce wajibi ne mu riƙa nuna ƙauna ‘ta aiki da gaskiya.’ Saboda haka, ya kamata ƙaunar da muke nuna wa ya zama na gaskiya ko “marar-riya.” (Rom. 12:9; 2 Kor. 6:6) A wasu lokuta mutane sukan yi wasu abubuwa don a ce suna ƙaunar mutane. Amma irin wannan ƙaunar ta gaskiya ce kuwa? Wace manufa ce za ta iya sa mutum ya yi hakan? Mutum ba zai nuna ƙauna ta munafurci kuma ya yi tunanin cewa ƙaunarsa ta gaskiya ce ba. Irin wannan ƙauna jebu ce.

7 Bari mu bincika wasu misalan ƙauna ta jebu. A lokacin da Shaiɗan ya zo ya ruɗi Hawwa’u, ya yi kamar yana son ya taimaka mata ne amma a gaskiya yana da muguwar manufa. (Far. 3:​4, 5) A zamanin Sarki Dauda, Ahitofel ya nuna cewa abokantakarsa da Dauda ba ta ƙwarai ba ce. Domin daga baya Ahitofel ya ci amanar Dauda don ya sami riba. (2 Sam. 15:31) Haka ma a yau, ’yan ridda da kuma wasu suna sa ’yan’uwa su kasance da rashin haɗin kai a ikilisiya ta wurin “daɗin baƙinsu” don mutane su ga cewa suna ƙaunarsu, amma a gaskiya suna da muguwar manufa.​—Rom. 16:​17, 18.

8. Wace tambaya ce za mu yi wa kanmu?

8 Da yake manufar ƙauna ta jebu ita ce a sa mutane su ga kamar mu masu nuna ƙauna ne, a ƙarshe hakan yakan jawo kunya  sosai. Mutane ne kawai za mu iya ruɗa da irin wannan ƙaunar, ba Jehobah ba. Hakika, Yesu ya ce za a hukunta waɗanda suke munafurci da “dūka ƙwarai.” (Mat. 24:51) Amma mu Shaidun Jehobah ba ma so mu riƙa nuna irin wannan ƙaunar. Don haka, zai dace mu tambayi kanmu, ‘Shin ƙauna da nake nuna wa ta gaskiya ce ko ta munafurci ne?’ Bari mu bincika hanyoyi tara da za su nuna muna nuna ƙauna “marar-riya” ko ta gaskiya.

YADDA ZA “MU YI ƘAUNA . . . DA AIKI DA GASKIYA KUMA”

9. Mece ce ƙauna ta gaskiya za ta motsa mu mu yi?

9 Ka riƙa farin cikin nuna ƙauna ko da ba wanda yake ganinka. Ya kamata mu riƙa yi wa ’yan’uwanmu alheri ko da mutane ba sa ganin lokacin da muke yin hakan. (Karanta Matta 6:​1-4.) Hananiya da Safiratu ba su yi hakan ba sam. Sun nuna ƙauna irin ta munafurci kuma suka yi ƙarya, don haka, an hukunta su saboda halinsu. (A. M. 5:​1-10) Amma idan muna ƙaunar ’yan’uwanmu da gaske, za mu riƙa ƙaunarsu da kuma musu alheri ba tare da son mutane su san abin da muke yi ba. Alal misali, ’yan’uwa da suke taimaka wa Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah wajen shirya littattafan da suke ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah ba sa son mutane su riƙa girmama su. Ban da haka ma, ba sa gaya wa mutane irin littattafan da suka yi aiki a kai.

10. Ta yaya za mu zama a kan gaba wajen girmama mutane?

10 Mu zama kan gaba wajen girmama mutane. (Karanta Romawa 12:10.) Yesu ya kafa mana misalin yadda za mu riƙa girmama mutane ta wurin yin wasu ayyukan da mutane ba sa son su yi. (Yoh. 13:​3-5, 12-15) Kafin mu iya girmama mutane kamar yadda Yesu ya yi, sai mun kasance da sauƙin kai. Sai da almajiran Yesu suka sami ruhu mai tsarki kafin suka fahimci dalilin da ya sa Yesu ya yi hakan. (Yoh. 13:7) Za mu iya girmama wasu idan ba ma ɗaukan kanmu da muhimmanci ainun domin ilimin da muke da shi ko arziki ko kuma wata hidima da muke yi a ibadarmu ga Jehobah. (Rom. 12:3) Kuma maimakon mu riƙa kishin wasu da ake yaba musu, ya kamata mu taya su murna ko da muna ganin cewa matsayinmu ɗaya ne ko kuma tare muka yi aikin da ya sa ake yaba musu.

11. Me ya sa za mu yaba wa mutane daga zuciyarmu?

11 Ka riƙa yaba wa ’yan’uwanka da zuciya ɗaya. Zai dace mu nemi hanyoyin da za mu yaba ma wasu domin hakan yana ƙarfafa ’yan’uwanmu sosai. (Afis. 4:29) Amma ya kamata mu yi hakan daga zuciyarmu ba da munafurci ba. Domin idan muna munafurci sa’ad da muke yaba musu, idan suna bukatar gyara, ba za mu iya faɗa musu ba. (Mis. 29:5) Mu munafukai ne idan muna yaba wa mutane sa’ad da muke tare da su amma idan ba ma tare, sai mu riƙa baƙar magana game da su. Manzo Bulus bai fāɗa a wannan tarkon ba, shi ya sa ya kafa mana misali mai kyau wajen yaba wa mutane. Alal misali, ya yaba wa Kiristoci a Koranti don wasu abubuwa masu kyau da suka yi. (1 Kor. 11:2) Amma idan suka yi wani abin da bai dace ba, yana ba su shawara da sanin yakamata.​—1 Kor. 11:​20-22.

Taimaka wa ’yan’uwanmu da suke da bukata yana cikin hanyoyin da muke nuna ƙauna da kuma karɓan baki (Ka duba sakin layi na 12)

12. Ta yaya za mu nuna ƙauna ta gaskiya sa’ad da muke taimaka ma wasu?

12 Mu riƙa karɓan baki. Jehobah ya umurce mu mu riƙa karɓan baki da kuma taimaka wa ’yan’uwanmu. (Karanta 1 Yohanna 3:17.) Amma ya kamata mu yi hakan da ra’ayi mai kyau ba da son kai ba. Saboda haka, za ka iya yi wa kanka wannan tambayar: ‘Shin ina nuna karimci ga abokaina ne kaɗai ko waɗanda suka  shahara da kuma masu arziki da za su iya taimaka min wata rana? Ko kuma ina nuna karimci ga ’yan’uwa da ban sani ba ko talakawa da ba za su iya taimaka min ba?’ (Luk. 14:​12-14) Me za mu yi idan wani ɗan’uwa yana bukatar taimako don bai yanke shawarar da ta dace ba ko kuma bai gode mana saboda taimakon da muka masa ba? A irin wannan yanayin, zai dace mu bi wannan shawarar cewa: “Ku yi wa junanku gyaran baƙi, ba kuwa da gunaguni ba.” (1 Bit. 4:9) Idan ka bi wannan shawarar za ka samu albarka kuma za ka yi farin ciki.​—A. M. 20:35.

13. (a) A wane lokaci ne muke bukatar yin haƙuri sosai? (b) Waɗanne abubuwa za mu yi don mu taimaka ma marasa ƙarfi?

13 Mu riƙa taimaka ma waɗanda suka yi sanyin gwiwa. Umurnin da ke Littafi Mai Tsarki cewa ku riƙa taimaka wa “marasa-ƙarfi, ku yi haƙuri da kowa” zai iya taimaka mana mu gane ko ƙaunar da muke nuna wa ta gaskiya ce ko a’a. (1 Tas. 5:14) ’Yan’uwa da yawa a dā ba su da bangaskiya sosai, amma yanzu suna da ƙwazo a ibada. Har ila, akwai wasu da ya kamata mu riƙa haƙuri da su sa’ad da muke taimaka musu. Amma ta yaya za mu taimaka musu? Muna iya yin hakan ta wurin ƙarfafa su da Littafi Mai Tsarki ko mu ce su yi wa’azi tare da mu ko kuma mu saurare su sa’ad da suke gaya mana damuwarsu. Ban da haka ma, bai kamata mu riƙa tunani cewa bangaskiyar ’yan’uwanmu ba ta da ƙarfi ba. Maimakon haka, ya kamata mu san cewa dukanmu muna da kasawarmu da kuma inda muka ƙware. Manzo Bulus ma ya san da hakan. (2 Kor. 12:​9, 10) Saboda haka, dukanmu za mu amfana idan muna tallafa wa juna.

14. Me ya kamata mu yi don mu yi zaman lafiya da juna?

14 Ku yi zaman lafiya da juna. Ya kamata mu yi iya ƙoƙarinmu don mu yi zaman lafiya da juna ko da muna ganin mutane ba su fahimce mu ba ko kuma ba sa bi da mu yadda ya kamata. (Karanta Romawa 12:​17, 18.) Kuma idan muka ɓata ma wani rai, zai dace mu nemi gafara da gaske. Alal misali, maimakon ka ce, “Ka yi haƙuri idan kana ganin abin da na faɗa ya ɓata maka rai,” zai fi kyau ka ce, “Ka yi haƙuri, na san na ɓata maka rai.” Faɗin hakan zai nuna cewa ka yarda kai ne ka jawo matsalar. Zaman lafiya tana da muhimmanci musamman ma a aure. Bai kamata ma’aurata su riƙa nuna suna ƙaunar juna a cikin jama’a ba amma a gida su ƙi yi wa juna magana, suna zage-zage da kuma faɗa da juna.

15. Ta yaya za mu nuna cewa muna gafarta wa mutane daga zuciya?

15 Ku riƙa gafarta wa juna. Idan wani ya yi mana laifi, zai dace mu gafarta masa kuma mu manta da batun. Ta yaya za mu yi hakan? Ta wurin ‘haƙuri da junanmu cikin ƙauna; muna ƙwazo mu kiyaye ɗayantuwar Ruhu cikin ɗaurin salama,’ ya kamata mu riƙa gafarta ma waɗanda suka ɓata mana ba da saninsu ba. (Afis. 4:​2, 3) Idan muna son mu gafarta wa mutane da  gaske, zai dace mu kame kanmu don kada mu ‘riƙe’ su a zuci. (1 Kor. 13:​4, 5, Littafi Mai Tsarki) Idan muka riƙe mutane a zuci, za mu ɓata dangantakarmu da ’yan’uwa da kuma Jehobah. (Mat. 6:​14, 15) Ban da haka ma, zai dace mu nuna cewa muna gafarta wa mutane daga zuci ta wurin yin addu’a a madadin waɗanda suka mana laifi.​—Luk. 6:​27, 28.

16. Yaya ya kamata mu ɗauki hidimomi da muke yi a ƙungiyar Jehobah?

16 Kada ka yi son kai. Idan kana da gatan yin wasu hidimomi a ƙungiyar Jehobah, zai dace ka yi hakan ba don ka ‘biɗa ma kanka ba, amma abin da za ya amfani maƙwabcinka.’ (1 Kor. 10:24) Alal misali, ana bukatar ’yan atenda da suke ba da wurin zama su kasance a inda ake taron kafin wasu. Bai kamata waɗannan ’yan’uwan su yi amfani da wannan damar su kama wurin zama mai kyau ma kansu da iyalinsu, a maimakon haka, sai sun ba wasu wuraren zama kafin su zauna. Ta yin hakan suna nuna cewa ba sa son kai, amma suna ƙaunar ’yan’uwansu da gaske. Ta yaya za mu yi koyi da su?

17. Idan wani ya yi zunubi mai tsanani kuma shi mai nuna ƙauna ta gaskiya ce, me zai yi?

17 Ka faɗi zunubanka kuma ka daina yin zunubi a ɓoye. Wasu Kiristoci da suka yi zunubi mai tsanani sun ƙi su faɗa don ba sa son su sha kunya ko kuma su sa wasu baƙin ciki. (Mis. 28:13) Amma hakan bai da kyau don zai iya yi wa mai zunubin da kuma wasu illa. Ban da haka ma, zai iya sa ruhu mai tsarki ya daina aiki a ikilisiya kuma ya sa ’yan’uwa su daina kasancewa da haɗin kai. (Afis. 4:30) Ƙauna ta gaskiya tana sa waɗanda suka yi zunubi mai tsanani su gaya wa dattawa don su taimaka musu.​—Yaƙ. 5:​14, 15.

18. Ta yaya ƙauna ta gaskiya take da muhimmanci?

18 Ƙauna ce ta fi wasu halaye muhimmanci. (1 Kor. 13:13) Wannan halin yana sa mutane su gane cewa mu mabiyan Yesu ne kuma muna koyi da Jehobah wanda shi ne tushen ƙauna. (Afis. 5:​1, 2) Manzo Bulus ya ce: “Idan . . . ba ni da ƙauna, ni ba komi ba ne.” (1 Kor. 13:2) Don haka, zai dace mu ci gaba da nuna ƙauna ba kawai da “baki” ba amma ta “aiki da gaskiya kuma.”