Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Gaskiya Ba ta Kawo ‘Salama, Amma Takobi’

Gaskiya Ba ta Kawo ‘Salama, Amma Takobi’

“Kada ku yi tsammani na zo domin in kawo wa duniya salama: A’a ban zo domin in kawo salama ba, amma takobi.”​—MAT. 10:34.

WAƘOƘI: 125, 135

1, 2. (a) Wace irin salama ce za mu iya morewa yanzu? (b) Amma me zai iya hana mu samun salama ta dindindin yanzu? (Ka duba hoton da ke shafin nan.)

BA WANDA yake son matsala sai dai kwanciyar hankali. Muna farin ciki cewa Jehobah ya ba mu damar kasancewa da ‘salamarsa,’ wato kwanciyar hankali da zai taimaka mana don kada mu riƙa yawan tunani ko baƙin ciki. (Filib. 4:​6, 7) Da yake mun yi alkawarin bauta wa Jehobah, muna more ‘salama wurin Allah,’ wato dangantaka mai kyau da shi.​—Rom. 5:1.

2 Amma lokaci bai yi da Allah zai kawo salama ta dindindin ba. Mutane suna faɗace-faɗace da kuma nuna halayen banza a waɗannan kwanaki na ƙarshe. (2 Tim. 3:​1-4) Ban da haka ma, muna bukatar mu yi ƙoƙari sosai don mu yi tsayayya da Shaiɗan da kuma koyarwarsa. (2 Kor. 10:​4, 5) Amma abin da zai fi sa mu baƙin ciki shi ne idan danginmu da ba Shaidu ba suka soma tsananta mana. Wasu za su iya zolayarmu saboda imaninmu, ko su ce muna raba iyali ko kuma su ce ba za su ƙara amincewa da mu a iyalin ba sai dai mun daina bauta wa Jehobah. Ta yaya ya kamata mu ɗauki wannan tsanantawa? Ta yaya za mu bi da waɗannan ƙalubale kuma mu yi zaman lafiya?

 ABIN DA ZA MU YI SA’AD DA DANGINMU SUKE TSANANTA MANA

3, 4. (a) Mene ne koyarwar Yesu zai iya sa mutane su yi? (b) A wane yanayi ne zai iya yi mana wuya mu bi Yesu?

3 Yesu ya san cewa koyarwarsa zai iya sa mutane su daina kasancewa da salama kuma mabiyansa suna bukatar ƙarfin hali don su ci gaba da bin sa sa’ad da ake tsananta musu. Kuma hakan zai shafi zaman lafiya da suke yi da danginsu da ’yan iyalinsu. Shi ya sa Yesu ya ce: “Kada ku yi tsammani na zo domin in kawo wa duniya salama: A’a ban zo domin in kawo salama ba, amma takobi. Gama na zo domin in haɗa mutum da ubansa, ’ya kuma da uwarta, surukuwa kuma da surukuwatata: Maƙiyan mutum za su kasance daga iyalin gidansa.”​—Mat. 10:​34-36.

4 Furucin Yesu cewa ‘Ka da ku yi tsammani na zo domin in kawo wa duniya salama,’ yana nufin cewa ya kamata almajiran Yesu su yi tunani sosai a kan abin da bin Yesu ya ƙunsa. Koyarwarsa za ta iya ɓata zumunci. Amma dai mun sani cewa Yesu ya yi wa’azin Kalmar Allah ce ba ɓata zumunci ba. (Yoh. 18:37) Duk da haka, bin koyarwar Kristi zai iya yi mana wuya idan abokanmu ko danginmu ko kuma ’yan iyalinmu suna tsananta mana.

5. Mene ne mabiyan Yesu suke fuskanta?

5 Yesu ya ambata cewa tsanantawa daga iyali ko dangi yana cikin wasu abubuwan da mabiyansa za su jimre da shi. (Mat. 10:38) Don su faranta wa Yesu rai, mabiyansa suna bukatar su jimre sa’ad da danginsu ko ’yan iyalinsu suke zolayarsu ko kuma suka yi watsi da su don imaninsu. Duk da haka, za su sami abubuwa da suka ɗara waɗanda suka yi hasararsu.​—Karanta Markus 10:​29, 30.

6. Me ya kamata mu tuna idan danginmu da ’yan iyalinmu suna tsananta mana don muna bauta wa Jehobah?

6 Ko da danginmu ko ’yan iyalinmu suna tsananta mana don muna bauta ma Jehobah, za mu ci gaba da ƙaunarsu, amma ya kamata mu tuna cewa ƙaunar da muke yi wa Allah za ta fi wadda muke musu. (Mat. 10:37) Ya kamata mu tuna cewa Shaiɗan zai nemi hanyoyin da zai sa mu daina kasancewa da aminci domin muna ƙaunar danginmu. Bari mu tattauna wasu hanyoyi da danginmu da ’yan iyalinmu za su iya tsananta mana da kuma yadda za mu jimre.

MIJI KO MATAR DA BA TA BAUTA WA JEHOBAH

7. Ta yaya waɗanda suke da mata ko maza da ba sa bauta wa Jehobah ya kamata su ɗauki yanayinsu?

7 Littafi Mai Tsarki ya yi mana kashedi cewa waɗanda suka yi aure “za su sha wahala a cikin jiki.” (1 Kor. 7:28) Idan kana da mata da ba ta bauta wa Jehobah, wahalar da za ka sha zai fi na sauran. Duk da haka, yana da muhimmanci ka ɗauki yanayinka yadda Jehobah yake ɗaukansa. Mutum ba zai iya barin matarsa ko mijinta ko kuma ya kashe aurensu don ɗayansu ba ya bauta wa Jehobah ba. (1 Kor. 7:​12-16) Ya kamata mu daraja mijinmu da ba ya bauta wa Jehobah ko da yake ba zai iya yin ja-goranci sa’ad da muke ayyukan ibada ba. Haka ma mijin da matarsa ba ta bauta ma Jehobah ya kamata ya riƙa ƙaunarta sosai ko da imaninsu ba ɗaya ba.​—Afis. 5:​22, 23, 28, 29.

8. Waɗanne tambayoyi ne mace za ta yi ma kanta idan maigidanta ya hana ta yin wasu ayyukan ibada a wasu ranaku?

8 Me za ki yi idan mijinki ya hana ki yin wasu ayyukan ibada a wasu ranaku? Alal misali, wani mutum ya ba matarsa da Mashaidiyar Jehobah ce ranakun da za ta riƙa fita wa’azi. Idan hakan ya faru da ke, zai dace ki tambayi kanki: ‘Shin maigidana ba ya son in riƙa bauta wa Jehobah ne? Idan ba haka ba, zan iya bin shawarar da ya ba ni?’ Idan kika yi la’akari da batun kuma kika ɗauki matakin da ya dace za ki guji wasu matsaloli.​—Filib. 4:5.

9. Ta yaya iyaye za su koyar da yaransu yadda za su riƙa girmama babansu ko mahaifiyarsu da ba Mashaidiyar Jehobah ba?

 9 Horar da yara ma zai iya zama mana ƙalubale idan matar ko miji ba ya bauta ma Jehobah. Alal misali, muna bukatar mu koyar da yaranmu su riƙa bin umurnin Littafi Mai Tsarki da ya ce: “Ka girmama ubanka da uwarka.” (Afis. 6:​1-3) Amma me za ku yi idan maigidanki ko matarka ba ta bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki? Ku kafa misali mai kyau wajen girmama matanku ko mazanku. Ku riƙa mai da hankali ga halayensu masu kyau kuma ku riƙa gode musu. Kuma bai kamata ku riƙa bakar magana game da mazanku ko matanku a gaban yaranku ba. A maimakon haka, kuna gaya wa yaran cewa kowane mutum ne yake da hakkin tsai da shawarar bauta wa Jehobah. Idan yaran suna da halin kirki, wataƙila hakan zai sa miji ko matar da ba ta bauta wa Jehobah ta soma yin hakan.

Ka koya wa yaranka Kalmar Allah idan da hali (Ka duba sakin layi na 10)

10. Ta yaya iyaye za su koya wa yaransu Littafi Mai Tsarki ko da ɗayansu ba sa bauta wa Jehobah?

10 A wasu lokuta, wasu iyaye da ba sa bauta ma Jehobah za su iya so yaransu su yi wasu bukukuwa da ba su dace ba tare da su ko kuma su koya musu koyarwar addinan ƙarya. Wasu ba za su so matansu su riƙa koya wa yaransu Littafi Mai Tsarki ba. Duk da haka, zai dace mace ta yi iya ƙoƙarinta don ta koya wa yaransu gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki. (A. M. 16:1; 2 Tim. 3:​14, 15) Alal misali, wani zai iya hana matarsa yin nazarin Littafi Mai Tsarki da yaransu ko kuma ya hana ta kai su taro. Duk da cewa za ta iya bin abin da maigidanta ya faɗa, za ta yi amfani da wasu zarafi don ta sa yaransu su san abubuwan da ta yi imani da su. Idan ta yi hakan, yaran za su iya koyan abubuwa game da Jehobah. (A. M. 4:​19, 20) Babu shakka, yaran ne suke da hakkin tsai  da shawarar bauta wa Jehobah.​—K. Sha. 30:​19, 20. *

DANGINMU DA BA SA SON IBADAR DA MUKE YI

11. Me zai iya jawo saɓani tsakaninka da danginka ko ’yan gidanku da ba sa bauta wa Jehobah?

11 Da farko, ba za mu iya gaya ma danginmu ko ’yan gidanmu cewa mun soma tarayya da Shaidun Jehobah ba. Amma idan bangaskiyarmu ta yi ƙarfi sosai, za mu iya gaya musu abin da muka yi imani da shi. (Mar. 8:38) Saboda haka, idan shawarar da ka tsai da na bauta wa Jehobah tana sa ka sami saɓani da danginka ko iyalinka da ba Shaidu ba, ka bincika wasu matakan da za ka ɗauka don ka rage wasu matsaloli kuma ka ci gaba da kasancewa da aminci.

12. Me ya sa danginmu za su iya tsananta mana, amma ta yaya za mu yi ƙoƙari mu fahimci yadda suke ji?

12 Ka yi ƙoƙari ka fahimci yadda danginka ko ’yan gidanku suke ji. Ko da yake da farko za mu yi farin ciki game da abubuwan da muka koya daga Littafi Mai Tsarki, danginmu ko ’yan gidanmu za su iya gani kamar an yaudare mu ne ko kuma mun shiga wata ƙungiyar asiri. Za su ga kamar ba ma ƙaunarsu don ba ma yin wasu bukukuwa tare da su. Ƙari ga haka, za su iya jin tsoro cewa wani abu zai iya faruwa da mu. Zai dace mu yi ƙoƙari mu san yadda suke ji kuma mu saurare su don mu san dalilin da ya sa suke gaya mana hakan. (Mis. 20:5) Manzo Bulus ya yi ƙoƙari ya “zama dukan abu ga dukan mutane” don ya iya yi musu bishara. Idan mu ma muka yi hakan, za mu taimaka wa mutane da yawa.​—1 Kor. 9:​19-23.

13. Ta yaya za mu gaya wa danginmu ko ’yan gidanmu da ba Shaidu ba game da imaninmu?

13 Ka riƙa magana yadda ya dace. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Bari zancenku kullum ya kasance tare da alheri.” (Kol. 4:6) Za mu iya roƙan Allah ya ba mu ruhu mai tsarki don mu iya nuna halaye masu kyau sa’ad da muke gaya wa danginmu ko ’yan gidanmu game da imaninmu. Bai kamata mu yi jayayya da su game da koyarwar ƙarya da suka yi imani da ita ba. Idan suka faɗi ko yi wani abu da ya ɓata mana rai, zai dace mu bi misalin manzanni. Bulus ya ce: “Ana zaginmu, muna sa albarka; ana tsanantanmu, muna haƙuri; ana yi mana ƙire, muna ba da haƙuri.”​—1 Kor. 4:​12, 13.

14. Me ya sa kasancewa da halin kirki yake da muhimmanci?

14 Ka kasance da halin kirki. Ko da yake yin magana yadda ya dace yana sa ku yi zaman lafiya da danginku ko ’yan gidanku da ba Shaidu ba, halinmu mai kyau ya fi muhimmanci. (Karanta 1 Bitrus 3:​1, 2, 16.) Ta misalinka ka nuna wa danginka, cewa Shaidun Jehobah suna jin daɗin aurensu da renon yaransu kuma suna yin rayuwar da ta jitu da ƙa’idodin Allah don yin hakan yana sa su yin farin ciki a rayuwa. Ko da ’yan gidanmu ba su zama Shaidu ba, za mu yi farin ciki kuma za mu sami albarka don mun kasance da aminci.

15. Ta yaya za mu yi shiri don mu guji yin jayayya da danginmu ko ’yan iyalinmu?

15 Ka yi shiri. Ka yi tunanin wasu abubuwan da za su iya sa ku yi jayayya kuma ka shirya yadda za ka bi da batun. (Mis. 12:​16, 23) Wata ’yar’uwa a Ostareliya ta ce: “Baban maigidana ya tsananta mana sosai don muna bauta wa Jehobah. Kafin mu kira shi ta waya, ni da maigidana mukan yi addu’a don Jehobah ya taimaka mana mu yi magana yadda ya dace idan ya ɓata mana rai. Muna shirya irin batutuwan da za mu tattauna da shi don kada mu riƙa jayayya. Don mu guji tattaunawa na dogon lokaci da zai iya sa mu riƙa jayayya game da addini, muna tsara lokacin da ya kamata mu yi hira da shi.”

16. Ta yaya za ka guji ra’ayin nan cewa za ka ɓata ran danginku da ’yan gidanku da ba Shaidu ba?

 16 Hakika, ba zai yiwu ka ce ba za ka sami saɓani sam sam da danginka ko ’yan gidanku da ba Shaidu ba. Kuma idan hakan ya faru, za ka iya yin baƙin ciki don kana ƙaunar danginku kuma ba ka son ka ɓata musu rai. Idan kana jin hakan, ya kamata ka tuna cewa faranta wa Jehobah rai ya fi faranta ran danginka muhimmanci. Wannan matakin da ka ɗauka zai taimaka musu su san cewa bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ya fi muhimmanci. Ban da haka ma, zai dace ka sani cewa ba za ka sa mutane dole su bauta wa Jehobah ba. Amma halinka zai iya taimaka musu su san muhimmancin bauta wa Jehobah. Da yake Jehobah mai ƙauna ne, ya ba su damar zaɓa ko za su bauta masa ko a’a kamar yadda mu ma muke da wannan zarafin yin zaɓi.​—Isha. 48:​17, 18.

IDAN DANGINMU YA DAINA BAUTA WA JEHOBAH

17, 18. Me zai taimaka maka ka jimre sa’ad da danginka ko ’yan iyalinku suka daina bauta ma Jehobah?

17 Za mu yi baƙin ciki sosai idan an yi ma danginmu ko ’yan iyalinmu yakan zumunci ko sun daina bauta wa Jehobah. Ta yaya za mu jimre da hakan?

18 Ka ci gaba da ayyukan ibada. Ka shirya yadda za ka riƙa karanta Littafi Mai Tsarki a kai a kai da shirya taro da fita wa’azi da kuma yin addu’a don ka jimre. (Yahu. 20, 21) Me za ka yi bayan ka yi waɗannan abubuwan amma har ila kana baƙin ciki? Kada ka fid da rai! Idan ka mai da hankali ga bautar Jehobah, a hankali za ka shawo kan waɗannan matsalolin. Abin da ya faru da marubucin Zabura ta 73 ke nan. Akwai lokacin da ya kasance da ra’ayin da bai dace ba kuma ya soma baƙin ciki. Me ya taimaka masa? Ya kasance da ra’ayin da ya dace sa’ad da ya je haikalin Jehobah. (Zab. 73:​16, 17) Kai ma za ka iya yin hakan idan kana bauta wa Jehobah da aminci.

19. Ta yaya za ka goyi bayan Jehobah sa’ad da aka yi ma wani horo?

19 Ka amince da horon da Jehobah yake mana. Jehobah ya san cewa horon da yake mana zai amfane mu har da wanda aka masa yankan zumunci. Ko da yake da farko mutum zai iya yin baƙin ciki, horon zai taimaka wa mai zunubin ya tuba. (Karanta Ibraniyawa 12:11.) Alal misali, Jehobah ya gaya mana ‘kada mu yi tarayya da’ mutanen da suka ƙi tuba. (1 Kor. 5:​11-13) Ko da yake muna baƙin ciki don sun bar Jehobah, bai kamata mu riƙa musu waya ko tura musu saƙon tes ko rubuta musu wasiƙa ko kuma mu riƙa hira ta intane ba.

20. Wane bege ya kamata ka kasance da shi?

20 Kada ka fid da rai! Ƙauna tana da “bege ga abu duka,” don hakan muna sa rai cewa waɗanda suka daina bauta ma Jehobah za su iya dawowa. (1 Kor. 13:7) Idan ka ga cewa wani danginku ko ɗan iyalinku da aka masa yankan zumunci yana ayyukan da suka cancanci a dawo da shi, ka yi masa addu’a don ya sami taimako daga Kalmar Allah kuma ya ji roƙon Jehobah cewa: “Ka komo wurina.”​—Isha. 44:22.

21. Me za ka yi idan kuna samun saɓani a iyalinku don matakin da ka ɗauka na zama almajirin Yesu?

21 Yesu ya ce wajibi ne mu yi ƙaunarsa fiye da kowane ɗan Adam. Kuma ya tabbata cewa almajiransa za su sami ƙarfin halin kasancewa da aminci a gare shi duk da cewa za a tsananta musu. Idan shawarar da ka tsai da na bauta wa Jehobah ya kawo maka “takobi” a iyalinku, ka dogara ga Jehobah don ya taimaka maka ka jimre da matsalolin da kake fuskanta kuma ka yi nasara. (Isha. 41:​10, 13) Sanin cewa Jehobah da Yesu suna murna da matakin da ka ɗauka na bauta wa Jehobah zai sa ka yi farin ciki don ka tabbata cewa za ka sami albarka a nan gaba.

^ sakin layi na 10 Don ƙarin bayani a kan yadda za mu horar da yara ko da matar ko mijin ba sa bauta wa Jehobah, ka dubi “Questions From Readers” da ke Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Agusta, 2002 a Turanci.