Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Kai Mai Hikima Ne?

Kai Mai Hikima Ne?

AKWAI wani yaro da yake zama a wani ƙauye. Shi talaka ne kuma mutanen ƙauyen suna masa dariya don suna ganin cewa ba shi da wayo. Idan baƙi suka zo ƙauyen, sai mutanen su riƙa yi masa dariya a gaban abokansu. Sai su ba shi kwandala guda biyu, ɗaya na azurfa ɗaya kuma na zinariya kuma su ce masa: “Ka ɗauki wanda kake so.” Sai yaron ya ɗauki na azurfa kuma ya gudu.

Wata rana, sai wani baƙon da ya zo ƙauyen ya tambayi yaron, “Kai ba ka san cewa kwandalar zinariya ta fi na azurfa ba?” Yaron ya yi murmushi kuma ya ce: “E, na sani.” Sai baƙon ya tambaye shi, “To me ya sa kake ɗaukan na azurfa? Za ka fi samun kuɗi idan ka ɗauki na zinariyar!” Sai yaron ya ce: “Amma idan na ɗauki na zinariyar, mutane za su daina wasa da ni kuma ba za su ƙara ba ni kwandalar ba. Ka san kwandalar azurfa guda nawa na tara?” Wannan yaron yana da hikima kuma wannan hali ne da zai iya taimaka wa mutane.

Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ka kiyaye sahihiyar hikima da hankali kuma: Sa’annan za ka bi tafarƙinka a lafiya, ƙafarka ba za ta yi tuntuɓe ba.” (Mis. 3:​21, 23) Saboda haka, sanin mece ce “hikima” da kuma yadda za mu iya zama masu hikima zai taimaka mana sosai. Hikima tana hana ‘ƙafarmu’ daga yin tuntuɓe, wato tana taimaka mana mu guji duk wani abin da zai ɓata dangantakarmu da Allah.

MECE CE HIKIMA?

Da akwai bambanci tsakanin hikima da ilimi da kuma fahimi. Wanda yake nazari da kuma bincike sosai a kan abubuwa zai zama mai ilimi. Wanda yake da fahimi yana ganin alaƙar abin da ya koya da abin da ya sani a dā da kuma yadda hakan zai amfane shi. Amma wanda yake da hikima yana yin abin da ya koya a rayuwarsa.

Alal misali, wani yana iya karanta da kuma fahimtar littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? cikin ƙanƙanin lokaci. Yana iya ba da amsa daidai sa’ad da ake nazari da shi. Ƙari ga haka, yana iya soma halartan taro da kuma ba da kalamai masu ƙarfafawa. Waɗannan abubuwan suna nuna cewa yana samun ci gaba. Amma hakan yana nufin cewa yana da hikima ne? A’a. Wataƙila shi mai saurin fahimtar abubuwa ne. Amma zai zama mai hikima ne idan yana yin abin da yake koya kuma yana yanke shawarwari masu kyau a kan wasu batutuwa.

Littafin Matta 7:​24-27 ta ambaci kwatancin da Yesu ya yi game da wasu mutane biyu da suka gina gida. An ce ɗaya daga cikinsu “mai hikima” ne. Wannan mutumin ya yi tunani sosai a kan abin da zai iya faruwa da gidansa a nan gaba, don haka ya gina gidan a kan dutse. Bai yi tunanin cewa zai fi masa sauƙi da kuma araha idan ya gina gidansa a kan yashi ba. Amma ya yi tunanin abin da zai iya faruwa idan ya gina gidansa a kan yashi. Don haka, gidansa bai rushe ba sa’ad da aka yi wata guguwa mai ƙarfi. Yanzu tambayar ita ce, ta yaya za mu zama masu hikima kuma mu kiyaye ta?

TA YAYA ZAN ZAMA MAI HIKIMA?

Da farko, ka lura da abin da littafin Mikah 6:9 ta ce: “Hikima ce ƙwarai a ji tsoron sunan [Allah].” (Littafi Mai Tsarki) Idan muna daraja Allah, hakan zai sa mu jin tsoron sunansa. Kuma hakan yana nufin cewa za mu daraja abin da sunansa  take wakilta da kuma ƙa’idodinsa. Kafin ka soma daraja wani, kana bukatar ka san shi sosai. Bayan haka, za ka iya gaskatawa da shi kuma ka koyi abubuwa daga wurinsa. Bayan haka, za ka soma bin misalinsa. Za mu nuna cewa muna da hikima idan muna tunanin yadda shawarwarin da muka yanke za su shafi dangantakarmu da Jehobah, kuma idan muna iya ƙoƙarinmu don mu yi abubuwan da suka jitu da ƙa’idodinsa.

Na biyu, littafin Misalai 18:1 ta ce: “Mutumin da ya kula da kansa kaɗai ba ya jituwa da kowa, ko wani ya faɗi maganar da ke daidai ba zai yarda ba.” Idan ba mu mai da hankali ba, za mu soma nisanta kanmu daga Jehobah da kuma mutanensa. Maimakon mu riƙa ware kanmu, ya kamata mu riƙa kasancewa tare da waɗanda suke jin tsoron sunan Allah kuma suna bin ƙa’idodinsa. Ya kamata mu riƙa halartan taro a Majami’ar Mulki da kuma yin tarayya da ‘yan’uwa a cikin ikilisiya. Sa’ad da muka halarci taro, zai dace mu riƙa sauraron abin ake faɗa a taron kuma mu bar abin da muka ji ya ratsa zuciyarmu.

Ƙari ga abin da aka ambata, muna bukatar mu riƙa addu’a ga Jehobah don yin hakan zai sa mu kusace shi sosai. (Mis. 3:​5, 6) Idan muka mai da hankali sosai sa’ad da muke karanta Littafi Mai Tsarki da kuma littattafan da ƙungiyar Jehobah take wallafawa, hakan zai sa mu san yadda  shawarwarin da muke yankewa za su shafe mu a nan gaba. Kuma muna bukatar mu saurari shawarar da dattawa suke ba mu. (Mis. 19:20) Idan muka ci gaba da yin waɗannan abubuwan, za mu zama masu hikima.

TA YAYA HIKIMA ZA TA TAIMAKA WA IYALINA?

Hikima tana taimaka wa iyalai sosai. Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya umurci mace ta riƙa daraja maigidanta. (Afis. 5:33) Mene ne mijin zai iya yi da zai sa matarsa ta daraja shi? Idan ya tilasta wa matarsa ta riƙa yin hakan, ba za ta daraja shi sosai ba. Domin ba ta son masifa, matar tana iya daraja shi sa’ad da suke tare. Amma ba za ta daraja shi ba idan ba ya nan. Mijin yana bukatar ya yi tunani a kan abin da zai sa matarsa ta ci gaba da daraja shi. Idan ya koyi nuna ‘ya’yan ruhu kamar ƙauna da kuma alheri, hakan zai sa matarsa ta daraja shi sosai. Hakika, mace tana bukatar ta riƙa daraja mijinta ko da ya cancanci hakan ko a’a.​—Gal. 5:​22, 23.

Littafi Mai Tsarki ya ce ya kamata miji ya ƙaunaci matarsa. (Afis. 5:​28, 33) Matar tana iya tunanin cewa idan tana son mijinta ya ƙaunace ta sosai, tana bukatar ta ƙi gaya masa kuskuren da ta yi duk da cewa mijin ya kamata ya san da hakan. Amma hakan ya dace ne? Mene ne zai faru idan daga baya mijin ya san da hakan? Zai ci gaba da ƙaunar ta ne? A’a. Maimakon hakan, zai fi kyau matar ta nemi lokacin da ya dace don ta bayyana masa abin da ta yi kuma mijin zai ji daɗin cewa ta faɗi gaskiya. Hakan zai sa mijinta ya ci gaba da ƙaunar ta.

Yadda kuka horar da yaranku zai shafi yadda za ku riƙa tattaunawa da su a nan gaba

Yara suna bukatar su yi wa iyayensu biyayya kuma iyaye su yi musu horo yadda Jehobah ya umurta. (Afis. 6:​1, 4) Hakan ba ya nufin cewa iyayen za su jera dokoki da yawa da suke so yaransu su bi. Ban da dokokin da yaran za su bi ko kuma horon da za a yi musu idan suka yi laifi, iyaye masu hikima suna gaya wa yaransu dalilin da ya sa ya kamata su yi musu biyayya.

A ce wani yaro ya yi wa iyayensa reni. Idan iyayen suka daka masa tsawa ko kuma horo, hakan zai sa yaron ya yi shiru. Amma a cikin zuciyarsa yana fushi kuma zai daina gaya wa iyayensa matsalolinsa.

Iyaye masu hikima suna tunani a kan yadda horon da suke yi wa yaransu zai shafe su a nan gaba. Kada ku yi fushi nan da nan don yaronku ya kunyatar da ku. Kuna iya kiran sa kuma ku tattauna da shi cikin kwanciyar hankali. Kuna iya gaya masa cewa Jehobah ya ce ya riƙa daraja iyayensa don yin hakan zai amfane shi sosai har a nan gaba. Idan ya daraja iyayensa, kamar yana daraja Jehobah ne. (Afis. 6:​2, 3) Yin hakan zai ratsa zuciyar yaronku. Zai ga cewa iyayensa suna ƙaunarsa kuma zai ci gaba da daraja su. Kuma hakan zai sa yaron ya nemi taimakon iyayensa a nan gaba.

Wasu iyayen ba sa son su ɓata wa yaransu rai, shi ya sa ba sa yi musu horo. Amma mene ne zai faru idan yaron ya girma? Shin yaron zai ji tsoron Jehobah kuma ya bi ƙa’idodinsa? Zai saurari abin da Jehobah yake gaya masa ne ko kuma zai nisanta kansa daga gare shi?​—Mis. 13:1; 29:21.

Mai ƙera abubuwa da ya gwaninta sosai yana yin shiri tun da wuri a kan abin da yake so ya ƙera. Ba ya ƙera duk abin da ya ga dama kuma ya riƙa fatan cewa abin zai yi kyau. Hakazalika, iyaye masu hikima suna yin amfani da lokacinsu don su koyi da kuma bi ƙa’idodin Jehobah. Ta hakan, suna jin tsoron sunansa. Ƙari ga haka, ba sa nisanta kansu daga Jehobah da kuma ƙungiyarsa, amma suna kasancewa da hikima kuma suna amfani da ita don su ƙarfafa iyalinsu.

A kowace rana, muna yanke shawarwarin da za su iya shafan rayuwarmu a nan gaba. Maimakon mu yanke shawara nan da nan a kan wani batu, muna bukatar mu dakata kuma mu yi tunani sosai. Ƙari ga haka, ya kamata mu yi la’akari da sakamakon da shawarwarin da muka yanke za su kawo. Mu roƙi Jehobah ya yi mana ja-gora kuma mu bi shawarwarinsa. Idan muka yi waɗannan abubuwan, za mu zama masu hikima kuma hikimar ce za ta sa mu sami rai na har abada.​—Mis. 3:​21, 22.