Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 TALIFIN NAZARI NA 45

Yadda Ruhu Mai Tsarki Yake Taimaka Mana

Yadda Ruhu Mai Tsarki Yake Taimaka Mana

“Zan iya yin kome ta wurin Allah wanda yake ƙarfafa ni.”​—FILIB. 4:​13, New World Translation.

WAƘA TA 104 Allah Yana Ba Mu Ruhunsa Mai Tsarki

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1-2. (a) Mene ne yake taimaka mana mu ci gaba da jimre matsaloli? Ka bayyana. (b) Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

WATAƘILA za ka iya tuna wata matsala da ka taɓa fuskanta da ta sa ka ce: “Na san cewa in Jehobah bai taimaka mini ba, ba zan iya jimrewa ba.” Da yawa a cikinmu za mu iya tuna hakan. Wataƙila ka yi wannan tunanin ne sa’ad da ka sami ƙarfin jimrewa a lokacin da aka yi maka rasuwa ko kuma kana rashin lafiya. Sa’ad da ka tuna matsalar da ka fuskanta, ka fahimci cewa ruhun Jehobah ne ya ba ka “cikakken ikon” jimrewa.​—2 Kor. 4:​7-9.

2 Ban da haka, muna bukatar taimakon ruhu mai tsarki don mu guji bin ra’ayin mutanen duniya. (1 Yoh. 5:19) Ƙari ga haka, muna bukatar ƙarfi don mu yaƙi “mugayen ruhohi.” (Afis. 6:12) Yanzu, za mu tattauna hanyoyi biyu da ruhu mai tsarki yake taimaka mana mu jimre waɗannan matsalolin. Bayan haka, za mu tattauna abin da za mu iya yi don mu amfana sosai daga ruhu mai tsarki.

RUHU MAI TSARKI YANA SA MU YI ƘARFI

3. Ta yaya Jehobah yake taimaka mana mu jimre matsaloli?

3 Ruhu mai tsarki yana taimaka mana mu yi dukan ayyukan da muke bukatar mu yi duk da matsalolin da muke fuskanta. Manzo Bulus ya ci gaba da bauta wa Jehobah duk da matsalolin da ya fuskanta domin ya dogara ga “ikon Almasihu.” (2 Kor. 12:9) A ƙaro na biyu da Bulus ya je wa’azi a ƙasar waje, ya yi aiki don ya biya bukatunsa, duk da haka ya yi wa’azi da ƙwazo. Ya zauna a gidan Akila da Biriskilla a Koranti kuma da yake Bulus ya iya ɗinka tanti, ya yi aiki da su na ɗan lokaci. (A. M. 18:​1-4) Ruhu mai tsarki ya taimaka wa Bulus ya yi aiki don biyan bukatunsa kuma ya yi wa’azi da ƙwazo.

4. Kamar yadda 2 Korintiyawa 12:7b-9 suka nuna, wace matsala ce Bulus ya fuskanta?

 4 Karanta 2 Korintiyawa 12:7b-9. A ayar nan, mene ne Bulus yake nufi sa’ad da ya ce yana da “ƙaya a jiki”? Idan ƙaya ta maƙale a jikin mutum, zai yi masa zafi sosai. Don haka, Bulus yana magana ne game da matsalolin da yake fuskanta. Ya ce matsalolinsa kamar dai ‘ɗan aika ne wanda Shaiɗan ya aiko’ don ya riƙa wahalar da shi. Wataƙila Shaiɗan da aljanunsa ba su ne suka jawo wa Bulus wannan matsala da ke kamar ƙaya a jikinsa ba. Amma sa’ad da waɗannan mugayen ruhohi suka lura da matsalar da Bulus yake fuskanta, sun yi ƙoƙarin sa ya ƙara shan wahala, kamar dai suna daɗa tura ƙayar cikin jikinsa. Me Bulus ya yi?

5. Ta yaya Jehobah ya amsa addu’o’in Bulus?

5 Da farko, Bulus ya so Jehobah ya cire masa wannan “ƙayar.” Ya ce: “Sau uku na roƙi Ubangiji [Jehobah] domin in rabu da wannan abu.” Amma duk da addu’o’in da Bulus ya yi, ƙayar ba ta rabu da shi ba. Shin hakan yana nufin cewa Jehobah bai amsa addu’ar Bulus ba ne? A’a, ya amsa addu’o’in. Jehobah bai cire wa Bulus wannan ƙayar ba, amma ya ba shi ƙarfin jimrewa. Jehobah ya ce: ‘Ta wajen kāsawa ake ganin cikakken ikona.’ (2 Kor. 12:​8, 9) Da taimakon Allah, Bulus ya ci gaba da farin ciki kuma ya kasance da kwanciyar rai!​—Filib. 4:​4-7.

6. (a) Ta yaya Jehobah zai amsa addu’o’inmu? (b) Waɗanne alkawuran da ke ayoyin da aka ambata a sakin layin nan ne suka ƙarfafa ka?

6 Ka taɓa roƙan Jehobah ya cire maka wata matsala yadda Bulus ya yi? Wataƙila ka yi addu’a sosai game da matsalar amma ta ƙi-ci-ta-ƙi-cinyewa. Hakan ya sa ka tunanin cewa Jehobah yana fushi da kai ne? Idan haka ne, ka tuna misalin Bulus. Hakika, Jehobah zai amsa addu’o’inka yadda ya amsa na Bulus! Ƙila Jehobah ba zai cire matsalar ba. Amma zai ba ka ruhunsa don ka sami ƙarfin jimrewa. (Zab. 61:​3, 4) Za a iya ‘buge ka,’ amma Jehobah ba zai yasar ka kai ba.​—2 Kor. 4:​8, 9; Filib. 4:13.

RUHU MAI TSARKI NA SA MU CI GABA DA BAUTA WA JEHOBAH

7-8. (a) Ta yaya ruhu mai tsarki yake kama da iska? (b) Ta yaya Bitrus ya kwatanta yadda ruhu mai tsarki yake aiki?

7 A wace hanya ce kuma ruhu mai tsarki yake taimaka mana? Za mu iya kwatanta ruhu mai tsarki da iska. Iska za ta iya taimaka wa jirgin ruwa ya isa wurin da zai je ko da ana guguwa a tekun. Hakazalika, ruhu mai tsarki zai taimaka mana mu riƙa bauta wa Jehobah duk da matsalolin da muke fuskanta, har sai mun shiga aljanna.

8 Da yake manzo Bitrus yana aikin kamun kifi, ya san abubuwa da yawa game da jirgin ruwa. Wataƙila shi ya sa ya yi amfani da jirgin ruwa don ya kwatanta yadda ruhu mai tsarki yake taimaka mana. Ya ce: “Maganar annabci ba ta taɓa zuwa ta wurin nufin mutum ba. Ruhun Allah ne ya shiga zukatan mutane ya sa su su faɗa abin da suka karɓa daga wurin Allah.”​—2 Bit. 1:21.

9. Mene ne Bitrus yake so mutane su yi tunani a kai sa’ad da ya ce ruhu mai tsarki “ya sa” marubutan Littafi Mai Tsarki su yi aikin da aka ba su?

9 Mene ne Bitrus yake so mutane su yi tunani a kai sa’ad da ya yi amfani da furucin nan “ya sa”? Luka wanda ya rubuta littafin Ayyukan Manzanni ya yi amfani da kalma makamancin haka a Helenanci don ya bayyana yadda ‘iska take tura’ jirgi. (A. M. 27:15) Wani masani ya ce sa’ad da Bitrus ya rubuta cewa ruhu mai tsarki “ya sa” marubutan Littafi Mai Tsarki  su yi aikin da aka ba su, ya yi amfani da kalmomin da za su sa mutane tunanin jirgin ruwa. Bitrus yana magana ne cewa kamar yadda iska take tura jirgin ruwa zuwa wurin da zai je, haka ma ruhu mai tsarki ya sa marubutan Littafi Mai Tsarki su yi aikin da aka ba su. Wannan masanin ya ƙara da cewa: “Marubutan Littafi Mai Tsarki suna nan ne kamar jirgin ruwa mai fila-filai.” Jehobah ya yi tanadin “ruhu mai tsarki.” Marubutan Littafi Mai Tsarki kuma sun bi ja-gorancin ruhun sa’ad da suke yin aikin da aka ba su.

MATAKI NA 1: Ka riƙa yin ayyukan da Jehobah ya ba bayinsa

MATAKI NA 2: Ka yi iya ƙoƙarinka a hidimar Jehobah (Ka duba sakin layi na 11) *

10-11. Waɗanne abubuwa biyu ne muke bukatar mu yi don ruhu mai tsarki ya yi mana ja-goranci? Ka ba da misali.

10 A yau, Jehobah ba ya amfani da ruhu mai tsarki don ya sa mutane su rubuta Kalmarsa. Amma har yanzu yana amfani da ruhunsa don ya yi wa bayinsa ja-goranci. Jehobah yana taimaka mana. Ta yaya za mu amfana daga ruhun Allah? Muna bukatar mu tabbata cewa muna yin abin da Allah yake bukata a gare mu. Ta yaya za mu yi hakan?

11 Ka yi la’akari da misalin nan. Idan matuƙin jirgin ruwa yana so ya amfana daga iska, yana bukatar ya yi abubuwa biyu. Na farko, yana bukatar ya saka jirginsa a wurin da akwai iska. Jirgin ba zai yi tafiya ba idan matuƙin ya bar jirgin a gaɓar teku. Na biyu, yana bukatar ya buɗe fila-filan jirgin da kyau. Babu shakka, jirgin zai yi tafiya ne idan iska ta bugi fila-filan. Hakazalika, za mu ci gaba da bauta wa Jehobah idan ruhunsa yana taimaka mana. Idan muna so mu amfana daga ruhu mai tsarki, muna bukatar mu yi abubuwa biyu. Na farko, wajibi ne mu bi ja-gorancin ruhu mai tsarki. Na biyu, muna bukatar mu “buɗe fila-filanmu da kyau,” wato mu yi iya ƙoƙarinmu a hidimar Jehobah. (Zab. 119:32) Idan muka yi abubuwan nan, ruhu mai tsarki zai sa mu ci gaba da  bauta wa Jehobah da aminci kuma za mu shiga aljanna.

12. Mene ne za mu tattauna yanzu?

12 Mun tattauna hanyoyi biyu da ruhu mai tsarki yake taimaka mana. Yana ba mu ƙarfi kuma yana taimaka mana mu riƙe aminci sa’ad da muke fuskantar matsaloli. Yana mana ja-goranci kuma yana taimaka mana mu yi aikin da Jehobah ya ba mu don mu sami rai na har abada. Yanzu, za mu tattauna abubuwa huɗu da muke bukata mu yi don mu amfana sosai daga ruhu mai tsarki.

YADDA ZA MU AMFANA SOSAI DAGA RUHU MAI TSARKI

13. Kamar yadda 2 Timoti 3:​16, 17 suka nuna, mene ne Kalmar Allah za ta yi mana, amma me muke bukatar yi?

13 Na farko, ka yi nazarin Kalmar Allah. (Karanta 2 Timoti 3:​16, 17.) Idan muka karanta Kalmar Allah kuma muka yi tunani a kan abin da muka karanta, umurnan Allah za su shiga zuciyarmu. Umurnan za su sa mu yi canje-canje a rayuwarmu don mu faranta ran Jehobah. (Ibran. 4:12) Amma don mu amfana sosai daga ruhu mai tsarki, muna bukatar mu keɓe lokaci don yin nazari da kuma tunani sosai a kan abin da muka nazarta. Yin haka zai sa Kalmar Allah ta shafi ayyukanmu da furucinmu.

14. (a) Me ya sa za mu iya cewa ruhu mai tsarki yana kasancewa a taronmu? (b) Ta yaya za mu amfana sosai daga ruhu mai tsarki sa’ad da muka halarci taro?

14 Na biyu, mu riƙa bauta wa Jehobah tare da ’yan’uwanmu. (Zab. 22:22) Ruhu mai tsarki yana kasancewa a taron ikilisiya. (R. Yar. 2:29) Me ya sa muka ce hakan? Domin sa’ad da muke taro da ’yan’uwanmu Kiristoci, muna yin addu’a cewa Jehobah ya ba mu ruhu mai tsarki. Muna rera waƙoƙi da aka ɗauko daga Kalmar Allah kuma muna saurarar jawabai daga Littafi Mai Tsarki da ’yan’uwan da ruhu mai tsarki ya naɗa suke yi. Ƙari da haka, ruhu mai tsarki yana taimaka wa ’yan’uwa mata su shirya ayyukan da aka ba su a taro. Don mu amfana sosai daga ruhu mai tsarki, muna bukatar mu yi shiri don mu yi kalami a taro. Idan mun yi hakan, muna a shirye mu amfana daga ruhu mai tsarki kamar jirgin ruwan da fila-filansa yake a buɗe.

15. Ta yaya ruhu mai tsarki yake taimaka mana a wa’azi?

15 Na uku, ka riƙa yin wa’azi. Idan muka yi amfani da Littafi Mai Tsarki sa’ad da muke wa’azi da kuma koyarwa, muna barin ruhu mai tsarki ya taimaka mana a hidimarmu. (Rom. 15:​18, 19) Amma don mu amfana sosai daga ruhu mai tsarki, dole ne mu yi wa’azi a kai a kai kuma mu riƙa amfani da Littafi Mai Tsarki a duk lokacin da muka sami zarafi. Hanya ɗaya da za mu iya ratsa zukatan mutane a wa’azi ita ce ta wajen yin amfani da shawarar da ke Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu.

16. Ta wace hanya mafi muhimmanci ce za mu iya samun ruhu mai tsarki?

16 Na huɗu, ka yi addu’a ga Jehobah. (Mat. 7:​7-11; Luk. 11:13) Hanya mafi muhimmanci da za mu sami ruhu mai tsarki ita ce ta wajen roƙon Jehobah ya ba mu ruhunsa. Babu abin da zai iya hana Jehobah jin addu’armu ko kuma ba mu ruhu mai tsarki. Shaiɗan bai isa ba kuma kasancewa a kurkuku ba zai iya hana shi ba. (Yaƙ. 1:17) Ta yaya za mu yi addu’a don mu amfana sosai daga ruhu mai tsarki? Don mu amsa tambayar nan, bari mu tattauna darasin da za mu iya koya game da  addu’a daga wani kwatancin da ke littafin Luka kaɗai. *

KA NACE DA YIN ADDU’A

17. Wane darasi ne za mu iya koya game da addu’a daga kwatancin Yesu da ke Luka 11:​5-9, 13?

17 Karanta Luka 11:​5-9, 13. Kwatanci da Yesu ya ba da ya nuna yadda za mu roƙi Jehobah ya ba mu ruhu mai tsarki. A kwatancin, mutumin ya sami abin da yake bukata domin “ya yi ta roƙo.” Bai ji tsoron gaya wa abokinsa ya taimaka masa ba duk da cewa da tsakar dare ne. (Luk. 11:8) * Wane darasi ne Yesu ya ce za mu iya koya daga kwatancin nan? Ya ce: “Ku yi ta roƙo za a ba ku. Ku yi ta nema za ku samu. Ku yi ta ƙwanƙwasawa, za a buɗe muku.” Don mu sami taimakon ruhu mai tsarki, muna bukatar mu yi ta roƙon Jehobah a addu’a.

18. Kamar yadda kwatancin Yesu ya nuna, me ya tabbatar mana da cewa Jehobah zai ba mu ruhu mai tsarki?

18 Kwatancin Yesu ya taimaka mana mu ga dalilin da ya sa Jehobah zai ba mu ruhu mai tsarki. A kwatancin, mutumin yana so ya kula da wani baƙo. Ya lura cewa baƙon yana bukatar abinci duk da cewa dare ya yi kuma ba shi da abinci. Yesu ya ce maƙwabcin mutumin ya taimaka masa ne domin ya nace ya ba shi burodi. Wane darasi ne Yesu yake so mu koya? Idan mutum ajizi yana a shirye ya taimaka wa maƙwabcinsa da ya yi ta roƙonsa, za mu iya kasancewa da tabbaci cewa Ubanmu da ke sama zai ba waɗanda suka ci gaba da roƙan sa ruhu mai tsarki! Saboda haka, mu tabbata cewa Jehobah zai amsa addu’o’inmu idan muka roƙe shi ya ba mu ruhu mai tsarki.​—Zab. 10:17; 66:19.

19. Me ya sa muke da tabbaci cewa za mu iya jimrewa?

19 Mu kasance da tabbaci cewa duk da harin da Shaiɗan yake kawo mana, za mu iya jimrewa. Me ya sa? Domin ruhu mai tsarki yana taimaka mana a hanyoyi biyu. Na farko, yana ba mu ƙarfin da muke bukata don mu jimre matsaloli. Na biyu, yana taimaka mana mu ci gaba da bauta wa Jehobah har sai mun shiga aljanna. Bari mu ƙuduri niyyar amfana sosai daga taimakon ruhu mai tsarki!

WAƘA TA 41 Allah Ka Ji Roƙona

^ sakin layi na 5 A wannan talifin, an bayyana yadda ruhu mai tsarki zai iya taimaka mana mu jimre matsaloli. Ƙari ga haka, an tattauna yadda ruhu mai tsarki zai taimaka mana.

^ sakin layi na 16 Luka ya fi kowane marubucin Linjila nanata cewa addu’a tana da muhimmanci sosai ga Yesu.​—Luk. 3:21; 5:16; 6:12; 9:​18, 28, 29; 18:1; 22:​41, 44.

^ sakin layi na 60 BAYANI A KAN HOTUNA: MATAKI NA 1: Wasu ma’aurata sun halarci taro a Majami’ar Mulki. Ta halartan taro da ’yan’uwansu Kiristoci, ma’auratan suna wurin da akwai ruhu mai tsarki. MATAKI NA 2: Sun yi shiri don su yi kalami a taro. Matakan nan biyu sun shafi sauran abubuwan da aka ambata a talifin nan, wato yin nazarin Kalmar Allah da yin wa’azi da kuma addu’a ga Jehobah.