Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 TALIFIN NAZARI NA 46

Kana Kula da ‘Garkuwarka’ Kuwa?

Kana Kula da ‘Garkuwarka’ Kuwa?

“Bari bangaskiya ta zama garkuwarku wadda za ku ɗauka.”​—AFIS. 6:16.

WAƘA TA 119 Wajibi Ne Mu Kasance da Bangaskiya

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1-2. (a) Kamar yadda Afisawa 6:16 ta nuna, me ya sa muke bukatar bangaskiya? (b) Wace tambaya ce za mu tattauna?

KANA da bangaskiyar da ke kamar ‘garkuwa’ kuwa? (Karanta Afisawa 6:16.) Babu shakka, kana da ita. Kamar yadda babbar garkuwa take kāre yawancin sashe na jikinmu, bangaskiyarmu za ta kāre mu daga lalata da mugunta da kuma abubuwan da suka saɓa wa ƙa’idodin Allah.

2 Amma muna rayuwa a “kwanakin ƙarshe,” kuma za a ci gaba da jarraba bangaskiyarmu. (2 Tim. 3:1) Saboda haka, ta yaya za mu bincika bangaskiyarmu don mu tabbata cewa tana nan da ƙarfi? Kuma ta yaya za mu iya riƙe garkuwarmu sosai? Bari mu tattauna amsoshin waɗannan tambayoyin.

KA BINCIKA GARKUWARKA SOSAI

Sojoji sun tabbatar da cewa sun gyara garkuwarsu bayan sun dawo daga yaƙi (Ka duba sakin layi na 3)

3. Mene ne sojoji suke yi wa garkuwarsu, kuma me ya sa?

3 A zamanin dā, sojoji suna yawan yin amfani da garkuwar da aka shimfiɗa fata a jikinta. Sojoji suna shafa wa garkuwar māi don kada fatar ta lalace kuma don kada ƙarfe da aka haɗa garkuwar da ita ya yi tsatsa. A duk lokacin da soja ya lura cewa garkuwarsa ta lalace, yana tabbata cewa ya gyara ta domin zai yi amfani da ita. Ta yaya misalin nan take da alaƙa da bangaskiyarmu?

4. Me ya sa ya kamata ka riƙa bincika bangaskiyarka, kuma yaya za ka yi hakan?

4 Kamar sojoji a zamanin dā, wajibi ne mu riƙa bincika da kuma kula da bangaskiyarmu a kai a kai domin mu kasance a shirye a kowane lokaci. A matsayinmu na Kiristoci, muna yin yaƙi da maƙiya da yawa, wato miyagun ruhohi da dai sauransu. (Afis. 6:​10-12) Babu wani da zai gyara mana garkuwarmu.  Mene ne za mu yi don mu tabbatar da cewa muna a shirye sa’ad da aka jarraba bangaskiyarmu? Na farko, dole ne mu riƙa yin addu’a don Allah ya taimaka mana. Sai mu yi amfani da Kalmar Allah don mu san yadda Allah yake ɗaukan mu. (Ibran. 4:12) Littafi Mai Tsarki ya ce: Ka “dogara ga Yahweh da dukan zuciyarka, kada ka dogara ga ganewarka.” (K. Mag. 3:​5, 6) Zai dace ka yi tunani a kan shawarwarin da ka yanke a kwana-kwanan nan. Alal misali, ka yi fama da rashin kuɗi ne? A lokacin, shin ka tuna alkawarin da Allah ya yi a Ibraniyawa 13:5 cewa: “Har abada ba zan bar ka ba”? Shin alkawarin ya sa ka yi imani cewa Jehobah zai taimaka maka? Idan ka yi haka, to garkuwarka, wato bangaskiyarka tana da lafiya.

5. Me za ka iya gani idan ka bincika bangaskiyarka?

5 Idan ka bincika bangaskiyarka, za ka iya yin mamaki sosai don abin da za ka gani. Wataƙila akwai wani abu da ka daɗe kana yi kuma ba ka sani ba. Alal misali, za ka iya lura cewa yawan alhini da ƙarairayi da kuma sanyin gwiwa sun raunana bangaskiyarka. Idan hakan ya faru da kai, wane mataki ne za ka iya ɗauka don kada bangaskiyarka ta lalace gabaki ɗaya?

KA KĀRE KANKA DAGA YAWAN ALHINI DA ƘARAIRAYI DA KUMA SANYIN GWIWA

6. Waɗanne irin alhini ne suka dace?

6 Yin alhini a wasu lokuta yana da kyau. Alal misali, muna damuwa domin muna so mu faranta ran Jehobah da kuma Yesu. (1 Kor. 7:32) A lokacin da muka yi zunubi mai tsanani, muna damuwa domin muna so mu sulhunta da Allah. (Zab. 38:18) Muna kuma alhini domin muna so mu faranta ran matarmu ko mijinmu, muna so mu kula da iyalinmu kuma muna so mu mutunta ʼyan’uwanmu Kiristoci.​—1 Kor. 7:33; 2 Kor. 11:28.

7. Kamar yadda Karin Magana 29:25 ta nuna, me ya sa bai dace mu riƙa jin tsoron mutane ba?

7 Amma, yawan alhini zai iya raunana bangaskiyarmu. Alal misali, muna iya damuwa sosai game da samun isashen abinci da sutura. (Mat. 6:​31, 32) Don mu rage damuwar, muna iya soma neman abin duniya ruwa-a-jallo, kuma muna iya soma son kuɗi. Idan muka yarda hakan ya faru, bangaskiyarmu ga Jehobah za ta yi sanyi kuma abotarmu da shi za ta yi tsami. (Mar. 4:19; 1 Tim. 6:10) Muna kuma iya soma damuwa sosai game da yadda mutane suke ɗaukan mu. A sakamako, maimakon mu ji tsoron ɓata wa Jehobah rai, za mu iya jin tsoro don kada a yi mana ba’a ko kuma a tsananta mana. Idan muna so mu kāre kanmu daga wannan tarkon, dole ne mu roƙi Jehobah ya ba mu bangaskiya da kuma ƙarfin zuciyar jimrewa.​—Karanta Karin Magana 29:25; Luk. 17:5.

(Ka duba sakin layi na 8) *

8. Yaya ya kamata mu ɗauki ƙarairayi?

8 Shaiɗan wanda shi ne “uban ƙarya,” yana yin amfani da bayinsa wajen yaɗa ƙarairayi game da Jehobah da kuma ʼyan’uwanmu. (Yoh. 8:44) Alal misali, ʼyan ridda suna wallafa ƙarairayi game da ƙungiyar Jehobah a Intane da talabijin da kuma wasu kafofin yaɗa labarai. Ƙarairayin nan ɗaya ne cikin “kibiyoyi na wutar” da Shaiɗan yake amfani da ita. (Afis. 6:16) Me ya kamata mu yi idan wani ya soma gaya mana irin waɗannan ƙarairayin? Ya kamata mu yi tir da su! Me ya sa? Domin muna da imani ga Jehobah kuma mun yarda da ʼyan’uwanmu. Kada mu taɓa kuskura mu yi cuɗanya da ʼyan ridda. Kada  mu yarda wani abu ko mutum ko kuma karambani ya sa mu soma yin mūsu da su.

9. Ta yaya yin sanyin gwiwa zai iya shafan mu?

9 Yin sanyin gwiwa zai iya sa bangaskiyarmu ta yi sanyi. Ba za mu iya wayance cewa ba mu da matsaloli ba. Yin hakan zai nuna cewa ba mu san abin da muke yi ba. Kuma a wasu lokuta za mu iya yin sanyin gwiwa. Amma bai kamata mu ƙyale matsaloli su mamaye tunaninmu ba. Idan muka yi haka, za mu iya manta da dukan alkawura masu kyau da Jehobah ya yi mana. (R. Yar. 21:​3, 4) A sakamako, za mu iya yin sanyin gwiwa sosai har mu daina bauta wa Jehobah. (K. Mag. 24:10) Amma bai kamata mu yarda hakan ya faru da mu ba.

10. Wane darasi ne muka koya daga wasiƙar da wata ’yar’uwa ta rubuta?

10 Ku yi la’akari da yadda wata ’yar’uwa a Amirka take nuna bangaskiya yayin da take kula da maigidanta da ke rashin lafiya mai tsanani. Ta rubuta wasiƙa zuwa hedkwatarmu cewa: “A wasu lokuta, muna gajiya sosai kuma muna yin sanyin gwiwa, amma ba mu fid da rai ba. Ina matuƙar farin ciki don tanadodin da muke samu don mu ƙarfafa bangaskiyarmu. Muna bukatar waɗannan shawarwari da ƙarfafawa sosai. Suna taimaka mana don kada mu fid da rai kuma mu jimre jarrabawar Shaiɗan.” Labarin wannan ’yar’uwar ya koya mana cewa za mu iya magance yin sanyin gwiwa. A wace hanya? Ka tuna cewa Shaiɗan ne yake jarraba ka. Ka yi imani cewa Jehobah zai taimaka maka, kuma ka nuna godiya don tanadodin da yake mana mu ƙarfafa abotarmu da shi.

Kana kula da ‘garkuwarka’ kuwa? (Ka duba sakin layi na 8, 11) *

11. Waɗanne tambayoyi ne za su taimaka mana mu san ko bangaskiyarmu tana da lafiya?

11 Shin ka ga wani sashe na garkuwarka da ke bukatar gyara? A watanni da suka wuce, ka rage yawan alhini kuwa? Ka guji saurarar ’yan ridda da kuma yin mūsu da su game da ƙarairayin da suke yaɗawa? Kuma ka daina yin sanyin gwiwa kuwa? Idan haka ne, to bangaskiyarka tana da lafiya. Amma ya kamata mu yi hankali sosai domin ba waɗannan ne kaɗai tarkunan da  Shaiɗan yake amfani da su ba. Bari mu tattauna ɗaya cikinsu.

KA KĀRE KANKA DAGA SON ABIN DUNIYA

12. Mene ne neman abin duniya zai iya sa mu yi?

12 Abin duniya zai iya raba hankalinmu kuma ya sa mu yi watsi da bangaskiyarmu da ke kamar garkuwa. Manzo Bulus ya ce: “Ai, babu sojan da yake a kan aiki wanda zai sa kansa cikin al’amuran farin hula, gama niyyar soja ita ce ya faranta wa shugabansa rai.” (2 Tim. 2:4) A zamanin dā, aikin soja ne kawai aka yarda sojojin Roma su riƙa yi. Mene ne zai iya faruwa idan ɗaya cikin sojojin ya ƙi bin umurnin nan?

13. Me ya sa bai dace soja ya yi abin da zai raba hankalinsa ba?

13 Ka yi tunani a kan wannan misalin. Wasu sojoji sun wuni suna horar da kansu, amma ɗaya cikinsu ba ya nan. Yana cikin gari yana sayar da abinci a kasuwa. Da yamma kuma, sojojin suka kwashe sa’o’i suna gyara makamansu. Amma wancan sojan da ke sana’a ya dawo kuma yana shirya kayan da zai kai kasuwa washegari. Abin mamaki, sai maƙiya suka kawo musu hari washegari. Kuna gani wanne cikin sojojin ne zai ɗauki matakin da ya dace kuma ya faranta ran shugabansa? Kuma idan kana cikin sojojin nan, wanne cikinsu ne za ka so ya tsaya kusa da kai? Za ka so wanda ke kasuwanci ne ko kuwa wanda yake wuni yana horar da kansa?

14. Mene ne ya fi muhimmanci a gare mu a matsayinmu na sojojin Yesu?

14 Hakazalika, muna kamar ƙwararen soja domin ba ma barin kome ya raba hankalinmu daga faranta ran Shugabanninmu, wato Jehobah da kuma Yesu. Faranta ransu ya fi kome a duniyar Shaiɗan muhimmanci a gare mu. Muna tabbatar da cewa muna da lokaci da kuzarin da muke bukata don mu bauta wa Jehobah kuma mu kyautata bangaskiyarmu da ke kamar garkuwa. Ƙari ga haka, muna kuma kula da sauran makaman da muke amfani da su don mu yaƙi Shaiɗan.

15. Wane gargaɗi ne Bulus ya yi mana, kuma me ya sa?

 15 Ya kamata mu riƙa kasancewa a faɗake a kowane lokaci! Me ya sa? Domin manzo Bulus ya yi gargaɗi cewa “waɗanda suke marmarin yin arziki” za su “rabu da bangaskiyarsu.” (1 Tim. 6:​9, 10) Furucin nan “rabu” ya nuna cewa neman tattara abin duniya zai iya raba hankalinmu. A sakamakon haka, za mu iya barin “mugayen sha’awace-sha’awace iri-iri na banza” su shiga zuciyarmu. Maimakon mu yarda sha’awace-sha’awacen nan su shiga zukatanmu, ya kamata mu san cewa makamai ne da Shaiɗan yake yin amfani da su don ya raunana bangaskiyarmu.

16. Waɗanne tambayoyi ne ya kamata littafin Markus 10:​17-22 ya motsa mu mu yi la’akari da su?

16 A ce muna da kuɗi sosai, shin za mu yi laifi idan muka saya abubuwa da ba ma bukata sosai? Ba lallai ba. Amma ku yi la’akari da waɗannan tambayoyi: Ko da muna da kuɗin sayan wani abu, mun tabbata cewa muna da lokaci da kuma kuzarin yin amfani da shi kuwa? Kuma za mu iya soma son abubuwan da muka tattara sosai? Son abin duniya zai iya sa mu zama kamar wani saurayi da ya ƙi zama mabiyin Yesu ne? (Karanta Markus 10:​17-22.) Zai fi dacewa mu yi rayuwa mai sauƙi kuma mu yi amfani da lokacinmu da kuma kuzarinmu don yin nufin Allah!

 KA RIƘE GARKUWARKA SOSAI

17. Mene ne bai kamata mu manta da shi ba?

17 Wajibi ne mu tuna cewa muna bakin dāga kuma mu riƙa kasancewa a shirye mu yaƙi Shaiɗan kullum. (R. Yar. 12:17) ʼYan’uwanmu maza da mata ba za su iya taya mu ɗaukan garkuwarmu ba. Wajibi ne mu riƙe shi sosai.

18. Me ya sa sojoji a zamanin dā suke riƙe garkuwarsu gam-gam?

18 A zamanin dā, ana yaba wa soja sosai idan shi jarumi ne. Amma zai zama masa abin kunya idan ya dawo gida ba tare da garkuwarsa ba. Wani masanin tarihi ɗan Roma mai suna Tacitus ya ce: “Abin kunya ne sosai soja ya gudu ya bar garkuwarsa a bakin dāga.” Shi ya sa sojoji suke riƙe garkuwarsu gam-gam.

Wata ʼyar’uwa tana riƙe da garkuwarta sosai ta wajen karanta Kalmar Allah da yin addu’a don ta iya bin shawarar, da halartan taro da kuma yin wa’azi a kai a kai (Ka duba sakin layi na 19)

19. Me zai taimaka mana mu riƙe garkuwarmu sosai?

19 Za mu nuna cewa muna riƙe da bangaskiyarmu da ke kamar garkuwa idan muna halartar taro a kai a kai kuma muna wa’azi game da sunan Jehobah da kuma Mulkinsa. (Ibran. 10:​23-25) Ƙari ga haka, mu riƙa karanta Kalmar Allah kowace rana kuma mu yi addu’a cewa Jehobah ya taimaka mana mu bi dukan shawarwarin da muka karanta. (2 Tim. 3:​16, 17) Idan muka yi haka, Shaiɗan bai isa ya jawo mana la’ani na dindindin ba. (Isha. 54:17) ‘Bangaskiyarmu’ da ke kamar ‘garkuwa’ za ta kāre mu. Za mu ci gaba da yin aiki tare da ʼyan’uwanmu da ƙarfin zuciya. Bugu da ƙari, Shaiɗan ba zai iya raunana bangaskiyarmu ba. Mafi muhimmanci kuma, za mu goyi bayan Yesu a lokacin da ya ci nasara a kan Shaiɗan da mabiyansa.​—R. Yar. 17:14; 20:10.

WAƘA TA 118 Ka “Ƙara Mana Bangaskiya”

^ sakin layi na 5 Sojoji suna yin amfani da garkuwa don su kāre kansu. Bangaskiyarmu tana kamar garkuwa. Kuma muna bukatar mu riƙa kula da bangaskiyarmu yadda muke kula da garkuwarmu. Wannan talifin yana ɗauke da abubuwa da za mu iya yi don mu tabbatar da cewa ‘garkuwarmu’ tana da lafiya.

^ sakin layi na 58 BAYANI A KAN HOTO: Wasu Shaidu sun kashe talabijin ɗinsu ba tare da ɓata lokaci ba sa’ad da ʼyan ridda suke yaɗa ƙarairayi game da Shaidun Jehobah.

^ sakin layi na 60 BAYANI A KAN HOTO: Bayan haka, magidancin ya yi amfani da Littafi Mai Tsarki don ya ƙarfafa bangaskiyarsu a lokacin ibada ta iyali.