HASUMIYAR TSARO—NA NAZARI Nuwamba 2019

Wannan fitowar tana dauke da talifofin nazari da za a yi daga ranar 30 ga Disamba, 2019–2 ga Fabrairu, 2020.

Ku Yi Abokan Kirki Kafin Karshe Ya Zo

Za mu iya koyi darussa da yawa daga labarin Irmiya, wanda abokansa suka taimaka masa gab da halakar Urushalima.

Yadda Ruhu Mai Tsarki Yake Taimaka Mana

Ruhu mai tsarki zai iya taimaka mana mu jimre matsaloli. Amma don mu amfana daga taimakonsa, muna bukatar daukan matakai hudu.

Kana Kula da ‘Garkuwarka’ Kuwa?

Bangaskiyarmu tana kāre mu kamar garkuwa. Mene ne za mu yi don mu tabbata cewa bangaskiyarmu tana da karfi?

Darussan da Za Mu Iya Koya Daga Littafin Firistoci

Littafin Firistoci yana dauke da dokokin da Jehobah ya ba Isra’ilawa a zamanin dā. A matsayinmu na Kiristoci, ba ma bin wadannan dokokin a yau, amma ta yaya za mu iya amfana daga dokokin.

“Ku Gama Abin da Kuka Fara”

Ko da mun yanke shawara mai kyau, yana iya yi mana wuya mu aiwatar da shawarar. Ka yi la’akari da hanyoyin da za mu iya gama abin da muka fara.

Ka Sani?

Mene ne aikin wakili a zamanin dā?