Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Zan “Yi Tafiya Cikin” Gaskiyarka

Zan “Yi Tafiya Cikin” Gaskiyarka

“Ya Yahweh, koya mini hanyarka, domin in yi tafiya cikin” gaskiyarka.​—ZAB. 86:11.

WAƘOƘI: 31, 72

1-3. (a) Yaya ya kamata mu ɗauki gaskiya? Ka ba da misali. (Ka duba hoton da ke shafin nan.) (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna a wannan talifin?

MUTANE suna yawan mayar da abin da suka sayo. An gano cewa a wasu ƙasashe, wajen kashi 9 na mutanen da suka sayi abu a dandalin cinikayya na Intane suna mayar da ita. Wajen kashin mutane 30 kuma a duniya suna mayar da abin da suka saya. Wataƙila mutanen sun lura cewa ba sa son abun ko kuma abun ba shi da kyau. Saboda haka, sai su yanke shawara su karɓi kuɗinsu ko kuma su musanya shi da wani abu dabam.

2 Ko da yake za mu iya mayar da kayan da muka saya a kanti, amma ba za mu so mu mayar ko kuma mu “sayar” da gaskiyar Littafi Mai Tsarki da muka ‘saya’ ba. (Karanta Karin Magana 23:23; 1 Tim. 2:4) Mun koya a talifi na farko cewa mun sadaukar da lokaci sosai don mu koyi gaskiya. Ƙari ga haka, wataƙila mun sadaukar da aikin da ake biyan mu albashi mai tsoka ko mun daina cuɗanya da wasu abokai. Wataƙila kuma mun yi wasu canje-canje a tunaninmu da halayenmu ko kuma mun daina yin wasu bukukuwa da bin wasu al’adu. Amma, albarkar da muka samu ta fi sadaukarwar da muka yi.

 3 Gaskiyar da muka koya tana sa mu ji kamar wani mutum da Yesu ya faɗa a kwatancinsa. Yesu ya ba da kwatancin don ya nuna yadda mutanen da ke neman gaskiya suke ji sa’ad da suka same ta. Kwatancin game da wani attajiri ne da ya nemi lu’u lu’u mai daraja sosai har ya same shi. Sai mutumin ya gaggauta “sayar” da dukan dukiyarsa don ya sayi lu’u lu’un. (Mat. 13:​45, 46) Hakazalika, gaskiyar da muka samu, wato gaskiya game da Mulkin Allah da kuma wasu abubuwan da muka koya a Kalmar Allah suna da daraja sosai a gare mu har muna a shirye mu yi sadaukarwa don mu same ta. Idan muna daraja wannan gaskiyar, ba za mu taɓa “sayar” da ita ba. Abin baƙin ciki ne cewa wasu bayin Allah sun daina daraja gaskiyar da suka koya, har ma sun sayar da ita. Kada mu yarda hakan ya faru da mu! Idan muna so mu nuna cewa muna daraja gaskiya sosai kuma ba za mu sayar da ita ba, wajibi ne mu bi umurnin nan a Littafi Mai Tsarki cewa mu riƙa “bin gaskiya.” (Karanta 3 Yohanna 2-4.) Bin gaskiya yana nufin cewa za mu bari ta zama abu mafi muhimmanci a rayuwarmu kuma za mu yi rayuwar da ta jitu da koyarwar Littafi Mai Tsarki. Yanzu bari mu tattauna waɗannan tambayoyin: Me ya sa wasu suka “sayar” da gaskiya kuma ta yaya suke yin hakan? Ta yaya za mu guji yin wannan kuskuren? Ta yaya za mu iya ƙuduri niyyar ci gaba da “bin gaskiya”?

ME YA SA WASU SUKE SAYAR DA GASKIYA, KUMA TA YAYA SUKE YIN HAKAN?

4. Me ya sa wasu a ƙarni na farko suka “sayar” da gaskiya?

4 A ƙarni na farko, wasu da suka karɓi gaskiya ba su ci gaba da bin ta ba. Alal misali, bayan da Yesu ya ciyar da wasu mutane, sun bi shi har ƙetaren Tekun Galili. Sai Yesu ya gaya musu wani abu da ya tayar musu da hankali. Ya ce: “In ba kun ci nama jikin Ɗan Mutum kun kuma sha jininsa ba, ba ku da rai a cikinku ke nan.” Maimakon su tambaye shi abin da hakan yake nufi, sai suka ce: “Wannan magana mai wuya ce, wa zai iya ya karɓe ta?” A sakamakon haka, “da yawa daga cikin mutanen da suke binsa suka bar shi, suka kuma daina binsa.”​—Yoh. 6:​53-66.

5, 6. (a) Me ya sa wasu suka daina bin gaskiya a kwana-kwanan nan? (b) Ta yaya mutum zai iya barin gaskiya sannu a hankali?

5 Abin baƙin ciki ne cewa wasu a yau sun yi watsi da gaskiyar da suka koya. Wasu sun daina bin gaskiya saboda wata gyarar da aka yi ga koyarwar Littafi Mai Tsarki ko kuma don abin da wani ɗan’uwa da ya manyanta ya ce ko kuma ya yi. Wasu sun yi fushi don gargaɗin da aka yi musu ko kuma don sun sami saɓani da wani a ikilisiya. Wasu kuma sun goyi bayan ’yan ridda da suke yaɗa ƙaryace-ƙaryace game da mu. A sakamakon haka, wasu sun “juya baya” ga Jehobah da kuma ikilisiya da gangan. (Ibran. 3:​12-14) Da ya dace su bi misalin manzo Bitrus. Sa’ad da mutane suka daina bin Yesu don abin da ya faɗa, Yesu ya tambayi almajiransa in su ma suna so su daina bin sa. Amma Bitrus ya amsa da gaggawa, ya ce: “Ubangiji, wurin wane ne za mu je? Ai, kai ne kake da magana mai ba da rai na har abada.”​—Yoh. 6:​67-69.

6 Wasu sun bar gaskiya sannu a hankali, wataƙila ma ba tare da saninsu ba. Mutumin da hakan ya faru da shi yana kamar jirgin ruwan da iska ta ture shi a hankali daga gaɓar teku. Littafi Mai  Tsarki yana kiran irin wannan aukuwar ‘zakuɗawa.’ (Ibran. 2:​1, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe) Mutumin da ya zakuɗa daga gaskiya ba ya yin hakan da gangan. Amma, ya ɓata dangantakarsa da Jehobah kuma zai iya yin hasarar ta. Me za mu iya yi don kada hakan ya faru da mu?

TA YAYA ZA MU GUJI SAYAR DA GASKIYA?

7. Mene ne zai taimaka mana kada mu sayar da gaskiya?

7 Idan muna so mu ci gaba da bin gaskiya, wajibi ne mu yi biyayya ga dukan dokokin Jehobah. Dole ne mu sa gaskiya ta zama abu mafi muhimmanci a rayuwarmu kuma mu yi rayuwar da ta jitu da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. Sarki Dauda ya yi alkawari ga Allah cewa: Zan ‘yi tafiya cikin’ gaskiyarka. (Zab. 86:11) Dauda ya ƙuduri niyyar yin hakan. Ya kamata mu ma mu ƙuduri niyyar ci gaba da bin gaskiya. Idan ba mu yi haka ba, za mu iya soma yin da-na-sani don gaskiyar da muka saya. Wataƙila ma mu soma neman a mayar mana da abubuwan da muka sadaukar don mu koye ta. Amma, ba za mu iya zaɓan gaskiyar Littafi Mai Tsarki da za mu gaskata da su ba da kuma waɗanda ba za mu gaskata da su ba. Wajibi ne mu bi ‘dukan gaskiya.’ (Yoh. 16:13) Yanzu, bari mu yi la’akari da abubuwa biyar da muka sadaukar don mu koyi gaskiya. Yin hakan zai ƙarfafa mu mu san cewa sadaukarwar da muka yi sun dace kuma ba za mu taɓa koma gidan jiya ba.​—Mat. 6:19.

8. Ta yaya yadda muke yin amfani da lokacinmu zai iya sa mu zakuɗa daga gaskiya? Ka ba da misali.

8 Lokaci. Idan ba ma so mu zakuɗa daga gaskiya, wajibi ne mu yi amfani da lokacinmu yadda ya dace. Idan ba mu yi hankali ba, za mu iya ɓata lokacinmu muna yin nishaɗi da kallon talabijin da kuma yin amfani da Intane. Ko da yake yin waɗannan abubuwan ba laifi ba ne, amma za su iya cinye lokacin da muke amfani da ita wajen yin nazari da kuma wasu abubuwan da ke da alaƙa da ibadarmu. Ka yi la’akari da abin da ya faru da wata ’yar’uwa mai suna Emma. * ’Yar’uwar tana son hawan doki sosai. A duk sa’ad da take da lokaci, tana zuwa hawan doki. Bayan wani lokaci, sai ta soma yin da-na-sani don lokacin da take ɓatawa tana hawan doki. Ta yi gyara kuma a sakamako, ta daina ɓata dukan lokacinta tana yin nishaɗi. Wani abu kuma da ya taimaka mata ta yi wannan canjin shi ne labarin wata mai suna Cory Wells da ke hawan dawakai a dā. * A yau, Emma tana yin amfani da lokacinta sosai wajen bauta wa Jehobah da kasancewa tare da abokanta da kuma ’yan’uwa a ikilisiya. Dangantakarta da Jehobah tana da danƙo sosai kuma tana farin ciki don sanin cewa tana amfani da lokacinta yadda ya dace.

9. Ta yaya biɗan kayan duniya zai iya sa wasu su daina bin gaskiya?

9 Kayan duniya. Idan muna so mu ci gaba da bin gaskiya, bai kamata kayan duniya ya fi muhimmanci a gare mu ba. Sa’ad da muka koyi gaskiya, al’amura na Mulkin Allah sun zama abu na farko a rayuwarmu. Muna farin ciki cewa mun sadaukar da kayan duniya don mu bi gaskiya. Amma da shigewar lokaci, za mu iya lura cewa wasu suna sayan sababbin na’urori da wasu abubuwa da dama. Hakan za iya sa mu soma ji cewa an bar mu a baya kuma za mu iya soma biɗan kayan  duniya ruwa a jallo. Hakan ya tuna mana da abin da ya faru da Demas. “Ƙaunar duniyar nan” ya sa shi ya yi watsi da hidimar da shi da manzo Bulus suke yi. (2 Tim. 4:10) Me ya sa Demas ya daina bin Bulus? Littafi Mai Tsarki bai faɗi ainihin dalilin ba. Wataƙila ya soma son kayan duniya fiye da abubuwa na ibada ko kuma ba ya so ya ci gaba da yin sadaukarwa don ya yi hidima da Bulus. Babu shakka, bai kamata mu yarda son kayan duniya ya janye hankulanmu daga bin gaskiya ba.

10. Wace jarrabawa ce ya kamata mu guje wa idan muna so mu ci gaba da bin gaskiya?

10 Yin abota da mutane. Idan muna so mu ci gaba da bin gaskiya, bai kamata mu faɗa cikin jarrabawa ba. Sa’ad da muka soma bin gaskiya, dangantakarmu da abokanmu da kuma danginmu da ba Shaidu ba ba ta kamar dā. Wataƙila wasu cikinsu ba su tsananta mana ba, amma wasu sun tsananta mana sosai. (1 Bit. 4:4) Ko da yake muna iya ƙoƙarinmu don mu bi da danginmu yadda ya kamata, amma bai kamata mu ƙarya dokar Jehobah domin muna so mu sa su farin ciki ba. Ya kamata mu bi gargaɗin da ke cikin littafin 1 Korintiyawa 15:33. Ayar ta ce mu yi abota da mutanen da suke ƙaunar Jehobah kaɗai.

11. Ta yaya za mu guji yin abubuwan da ba su dace ba?

11 Hali da tunanin banza. Wajibi ne masu bin gaskiya su kasance da tsarki. (Isha. 35:8; karanta 1 Bitrus 1:​14-16.) Sa’ad da muka koyi gaskiya, dukanmu mun yi canje-canje don rayuwarmu ta jitu da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. Wasu sun yi canji na musamman. Amma ya kamata mu yi hankali don kada lalata ta wannan duniyar ta gurɓata mu. Me zai taimaka mana don kada mu yi lalata? Ka yi la’akari a kan tanadin da Jehobah ya yi don mu kasance da tsarki, wato jinin Ɗansa, Yesu Kristi. (1 Bit. 1:​18, 19) Don mu kasance da tsabta, ya kamata mu riƙa tuna cewa hadayar fansar da Yesu ya yi tana da tamani sosai.

12, 13. (a) Me ya sa yake da muhimmanci mu kasance da ra’ayin Jehobah game da bukukuwa? (b) Mene ne za mu tattauna a sakin layi na gaba?

12 Bukukuwa da al’adun da ba su dace ba. Danginmu da abokan aikinmu da kuma abokan makarantarmu suna iya neman su sa mu bi su yin wasu bukukuwa. Mene ne zai taimaka mana don kada mu saka hannu a bukukuwa da al’adun da Jehobah ba ya so? Sanin yadda Jehobah yake ɗaukan waɗannan abubuwan zai taimaka mana. Yin nazarin talifofin da ke littattafanmu da suka nuna tushen bukukuwan zai taimaka. Idan muka tuna wa kanmu dalilan da Allah ya bayar cikin Kalmarsa na nisanta kanmu daga bukukuwan, za mu kasance da tabbaci cewa muna yin abin da ya “gamshi Ubangiji.” (Afis. 5:10) Idan mun dogara ga Jehobah da kuma Kalmarsa, ba za mu riƙa “jin tsoron mutum” ba.​—K. Mag. 29:25.

13 Bin gaskiya abu ne da muke bukatar mu ci gaba da yi har abada. Mene ne zai taimaka mana mu ƙuduri niyyar ci gaba da yin hakan? Bari mu tattauna hanyoyi uku.

KA ƘUDURI NIYYAR YIN TAFIYA A CIKIN GASKIYA

14. (a) Ta yaya ci gaba da sayan gaskiya zai taimaka mana mu ƙuduri niyyar ƙin sayar da ita? (b) Me ya sa hikima da horo da kuma ganewa suke da muhimmanci?

14 Da farko, ka ci gaba da yin nazarin Kalmar Allah da kuma bimbini a kan abin da ka koya. Ka keɓe lokaci don ka  ci gaba da koyan gaskiyar da ke cikin Kalmar Allah. Hakan zai hana ka sayar da gaskiya. Littafin Karin Magana 23:23 ta ce mu sayi “hikima da horarwa da ganewa.” Ban da sanin Kalmar Allah, muna bukatar mu riƙa yin amfani da abubuwan da muke koya a rayuwarmu. Ƙari ga haka, ganewa za ta taimaka mana mu fahimci dukan abubuwan da Jehobah yake bukata a gare mu. Hikima kuma za ta motsa mu mu yi abin da muka koya. A wasu lokuta, Littafi Mai Tsarki yana horar da mu da kuma taimaka mana mu san canje-canjen da muke bukatar mu yi. Bari mu ci gaba da daraja wannan taimakon domin Littafi Mai Tsarki ya ce yana da tamani fiye da azurfa.​—K. Mag. 8:10.

15. Ta yaya ɗamarar gaskiya take kāre mu?

15 Na biyu, ka ƙuduri niyyar bin gaskiya kowace rana, kuma ta zama ɗamararka. (Afis. 6:14) A zamanin dā, ɗamarar sojoji tana taimaka musu da kuma kāre su. Amma idan soja yana so ɗamarar ta kāre shi, yana bukatar ya ɗaure ta da ƙarfi sosai. Idan bai ɗaure ɗamarar yadda ya kamata ba, ba za ta taimaka masa ba. Ta yaya ɗamarar gaskiya take kāre mu? Idan muka ci gaba da bin gaskiya, hakan zai taimaka mana mu guji tunanin banza kuma zai taimaka mana mu riƙa tsai da shawarwarin da suka dace. A lokacin da muke fuskantar gwaji, gaskiyar Littafi Mai Tsarki za ta sa mu yi abin da ya dace. Kamar yadda soja ba zai taɓa zuwa yaƙi ba tare da ɗamararsa ba, muna bukatar mu ƙuduri niyyar cewa ba za mu kwance ɗamara ta gaskiya ba. A maimakon haka, za mu yi iya ƙoƙarinmu don mu ɗaure ɗamarar da ƙarfi ta wajen yin abubuwan da suka jitu da koyarwar Kalmar Allah. Ƙari ga haka, soja yana iya rataye takobinsa a ɗamararsa. Bari mu ga yadda za mu iya yin hakan yayin da muke bin gaskiya.

16. Ta yaya koya wa mutane gaskiya yake taimaka mana mu ci gaba da tafiya a cikinta?

16 Na uku, ka yi ƙoƙarin koyar da gaskiyar da kake koya daga Littafi Mai Tsarki. Ta yin hakan, za ka riƙe takobin Ruhu, wato “Kalmar Allah” yadda ya dace. (Afis. 6:17) Dukanmu muna bukatar mu yi iya ƙoƙarinmu don mu zama malamai nagari yayin da muke “koyar da kalmar gaskiya daidai.” (2 Tim. 2:15) Idan muka ci gaba da koya wa mutane gaskiyar da ke Littafi Mai Tsarki, hakan zai taimaka mana mu san gaskiyar sosai. Ta hakan, muna ƙarfafa ƙudurinmu na ci gaba da yin tafiya a cikin gaskiya.

17. Me ya sa gaskiya take da muhimmanci a gare ka?

17 Gaskiya kyauta ce mai tamani da Jehobah ya ba mu. Wannan kyautar ta taimaka mana mu ƙulla dangantaka mai kyau da Ubanmu na sama. Jehobah ya koya mana abubuwa da yawa, amma wannan soma taɓi ne! Allah ya yi alkawari cewa zai ci gaba da koyar da mu har abada. Saboda haka, bari mu ci gaba da ɗaukan gaskiyar da tamani sosai. Mu ci gaba da sayan ‘gaskiya, kada mu sayar’ da ita. Kamar Dauda, za ka cika wannan alkawari cewa: Zan “yi tafiya cikin” gaskiyarka.​—Zab. 86:11.

^ sakin layi na 8 An canja sunan.

^ sakin layi na 8 Ka shiga Tashar JW kuma ka duba ƙarƙashin GANAWA DA LABARAI > GASKIYA TA CANJA RAYUKA.