Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Kana Daraja Kalmar Allah?

Kana Daraja Kalmar Allah?

“Sa’ad da kuka karɓi maganar jawabi daga gare mu,  . . . kuka karɓe ta . . . yadda take hakika, maganar Allah.”​—1 TAS. 2:13.

WAƘOƘI: 114113

1-3. Ta yaya Afodiya da Sintiki suka soma rigima, kuma ta yaya za mu iya hana irin waɗannan matsalolin faruwa? (Ka duba hoton da ke shafin nan.)

BAYIN JEHOBAH suna daraja Littafi Mai Tsarki sosai. Amma tun da yake mu ajizai ne, a wasu lokuta ana yin amfani da Littafi Mai Tsarki don a yi mana gyara. Mene ne za mu yi idan aka yi mana gyara? Ku yi la’akari da abin da ya faru tsakanin Afodiya da Sintiki a ƙarni na farko. Waɗannan mata biyun sun soma rigima sosai. Littafi Mai Tsarki bai gaya mana ko mece ce matsalar ba. Amma, wataƙila ga abin da ya faru tsakaninsu.

2 A ce Afodiya ta gayyaci wasu ‘yan’uwa zuwa gidanta don shaƙatawa, amma ba ta gayyaci Sintiki ba. Da Sintiki ta ji game da hakan, sai ta gaya wa kanta: ‘Lallai kam, Afodiya ta gayyaci ‘yan’uwa zuwa gidanta amma ta ƙi ta gayyace ni! Na ɗauka cewa mu abokai ne.’ Sintiki ta ji kamar Afodiya ta ci amanarta. Saboda haka ita ma ta gayyaci ‘yan’uwan da Afodiya ta gayyace su, amma ba ta gayyaci Afodiya ba! Abin da ya faru tsakanin Afodiya da Sintiki zai iya kawo matsala a cikin ikilisiya. Littafi Mai Tsarki bai gaya mana abin da ya faru daga baya ba, amma wataƙila waɗannan matan sun bi shawarar da manzo Bulus ya ba su.​—Filib. 4:​2, 3.

 3 Hakazalika a yau ma, irin wannan yanayin zai iya kawo matsala a cikin ikilisiya. Amma idan muna bin umurnin da ke cikin Kalmar Allah, za mu iya magance irin waɗannan matsalolin ko kuma mu hana su faruwa. Kuma idan muna daraja Kalmar Allah, za mu bi umurnin da ke cikin ta.​—⁠Zab. 27:⁠11.

KALMAR ALLAH TA GARGAƊE MU MU RIƘA KAME KANMU

4, 5. Wane umurni ne Kalmar Allah ta ba mu game da kame kanmu?

4 Ba shi da sauƙi mu kame kanmu sa’ad da aka ɓata mana rai ko kuma aka yi mana rashin adalci. Za mu yi baƙin ciki sosai idan aka wulaƙanta mu saboda yarenmu ko launin fatarmu ko kuma siffarmu. Idan wani ɗan’uwa Kirista ne ya yi hakan, zai daɗa sa mu baƙin ciki sosai! Shin Kalmar Allah za ta iya taimaka mana sa’ad da muke fuskantar irin wannan yanayin?

5 Jehobah ya san abin da zai iya faruwa idan ba mu kame kanmu ba. Fushi zai iya sa mu faɗi ko kuma mu yi wani abin da zai iya sa mu yi da-na-sani daga baya. Amma zai fi dacewa mu bi umurnin da Littafi Mai Tsarki ya ba mu cewa mu riƙa kame kanmu, kuma kada mu riƙa saurin fushi! (Karanta Misalai 16:32; Mai-Wa’azi 7:⁠9.) Babu shakka, dukanmu muna bukatar mu ci gaba da yafe wa juna. Jehobah da kuma Yesu sun ɗauki batun yafewa da muhimmanci sosai. (Mat. 6:​14, 15) Shin kana ganin ya kamata ka daɗa haƙuri da mutane kuma ka riƙa gafarta musu?

6. Mene ne zai iya faruwa idan ba mu kame kanmu ba?

6 Idan ba ma kame kanmu, za mu ci gaba da fushi har mu soma tsanan wanda muke fushi da shi. Idan muna da wannan halin mutane ba za su so su kusace mu ba, kuma za mu iya ɓata wasu a cikin ikilisiya. Wanda yake fushi da ɗan’uwansa zai iya ƙoƙarin ɓoye yadda yake ji, amma a kwana a tashi abin da yake zuciyarsa ‘zai bayyana ga mutane.’ (Mis. 26:​24-26) Dattawa za su iya taimaka wa irin wannan mutumin ya fahimci cewa bai kamata bayin Allah su yi fushi har ya wuce misali ko su ƙi juna ko kuma su ƙi gafarta wa juna ba. Jehobah ya bayyana hakan a cikin littafinsa. (Lev. 19:​17, 18; Rom. 3:​11-18) Ka amince da abin da ya ce?

JEHOBAH NE YAKE YI MANA JA-GORA

7, 8. (a) Ta yaya Jehobah yake ja-gorar bayinsa a duniya? (b) Waɗanne umurni ne ke cikin Kalmar Allah, kuma me ya sa ya kamata mu riƙa bin su?

7 Jehobah yana yi wa bayinsa a duniya ja-gora da kuma tanadin abin da zai taimaka musu su ƙarfafa dangantakarsu da shi. Yana yin hakan ta wajen amfani da “bawan nan mai-aminci, mai-hikima,” a ƙarƙashin ja-gorancin Yesu, wanda shi ne “kan ikilisiya.” (Mat. 24:​45-47; Afis. 5:23) Kamar hukumar da ke kula da ayyukan Kiristoci a ƙarni na farko, waɗannan bayin suna daraja Kalmar Allah sosai. (Karanta 1 Tasalonikawa 2:13.) Waɗanne ja-gora ko umurnin da ke cikin Littafi Mai Tsarki ne za su iya amfanar mu?

8 Littafi Mai Tsarki ya umurce mu mu riƙa halartan taro a koyaushe. (Ibran. 10:​24, 25) Ya umurce mu mu bi koyarwa ɗaya. (1 Kor. 1:10) Ya kuma ce mu saka al’amuran Mulkin Allah a kan gaba a rayuwarmu. (Mat. 6:33) Ƙari ga haka, Kalmar Allah ta nuna cewa wajibi ne mu yi wa’azi gida-gida, da kuma a inda jama’a suke, da duk inda muka sami damar yin wa’azi. (Mat. 28:​19, 20; A. M. 5:42; 17:17; 20:20) Kalmar Allah ta  umurci dattawa da su tabbatar da cewa ƙungiyar Jehobah ta kasance da tsabta. (1 Kor. 5:​1-5, 13; 1 Tim. 5:​19-21) Kuma Jehobah ya bukaci kowa a ƙungiyarsa ya kasance da tsabta da kuma dangantaka mai kyau da shi.​—⁠2 Kor. 7:⁠1.

9. Ta wace hanya ce Allah yake taimaka mana mu fahimci Kalmarsa?

9 Wasu suna iya yin tunanin cewa ba sa bukatar wani ya bayyana musu Littafi Mai Tsarki. Amma Yesu ya naɗa ‘bawan nan mai-aminci’ don ya riƙa yi wa bayin Allah tanadin abin da zai ƙarfafa dangantakarsu da Allah. Tun daga shekara ta 1919, Yesu ya soma yin amfani da wannan bawan don ya taimaka wa mabiyansa su fahimci Kalmar Allah kuma su bi umurnin da ke cikin ta. Idan muna bin umurnin da ke Littafi Mai Tsarki, hakan zai sa mu taimaka wa ikilisiyarmu ta kasance da tsabta da salama da kuma haɗin kai. Dukanmu muna bukatar mu tambayi kanmu, ‘Ina riƙe aminci ga Yesu ta wurin bin ja-gorar da wannan bawan yake bayarwa a yau?’

ANA SAMUN CI GABA SOSAI A ƘUNGIYAR JEHOBAH!

10. Ta yaya aka bayyana sashen ƙungiyar Jehobah ta sama a littafin Ezekiyel?

10 Ta wurin Kalmar Allah, mun koyi cewa Jehobah yana da ƙungiya a sama. Alal misali, a wani wahayi, annabi Ezekiyel ya ga wani karusa da take wakiltar sashen ƙungiyar Jehobah na sama. (Ezek. 1:​4-28) Jehobah ne yake ja-gorar wannan karusar kuma tana zuwa duk inda ruhunsa ya ce ta je. Kuma wannan sashen ƙungiyarsa ta sama tana ja-gorar ƙungiyarsa ta duniya. Babu shakka wannan karusar tana aiki sosai! A cikin shekaru goma da suka wuce, canje-canjen da ake yi a ƙungiyar Jehobah ta duniya ya nuna cewa Jehobah ne yake ja-gorar ƙungiyarsa. Nan ba da daɗewa ba, Yesu da mala’iku za su halaka wannan muguwar duniyar. Mutane za su daraja sunan Jehobah kuma ba za su ƙara yi masa rashin biyayya ko kuma su ƙi sarautarsa ba.

Muna farin ciki da waɗanda suke ba da kansu don yin aikin gine-gine! (Ka duba sakin layi na 11)

11, 12. Waɗanne abubuwa ne ƙungiyar Jehobah ta cim ma?

11 Ka yi tunani a kan abubuwan da sashen ƙungiyar Jehobah ta duniya take cim ma wa a wannan kwanaki na ƙarshe. Gine-gine. ‘Yan’uwa da yawa sun yi aiki tuƙuru don gina hedkwatar Shaidun Jehobah a garin Warwick da ke Amirka. Ofishin da ke Kula da Yin Gini da Zanen Gini yana ja-gorar ‘yan’uwa da yawa da suka ba da kansu da yardan rai kuma suke aiki tuƙuru a kan yadda za su riƙa gina Majami’un Mulki da kuma ofisoshin Shaidun Jehobah. Muna gode wa waɗanda suka ba da kansu kuma suke aiki tuƙuru don su ga cewa an yi waɗannan gine-ginen! Kuma bayin Jehobah a dukan faɗin duniya suna tallafawa ta wajen ba da gudummawarsu, kuma Jehobah yana musu albarka.​—⁠Luk. 21:​1-4.

 12 Ilimantarwa. Jehobah yana so ya ilimantar da mutanensa. (Isha. 2:​2, 3) Ka yi la’akari da makarantun da muke da su. Muna da Makarantar Hidima ta Majagaba da Makarantar Koyar da Masu Hidima da Makarantar Littafi Mai Tsarki ta Gileyad da Makarantar Sababbi Masu Hidima a Bethel da Makaranta Don Masu Kula Masu Ziyara da Matansu da Makarantar Hidima ta Mulki da kuma Makaranta Don Mambobin Kwamitin da Ke Kula da Ofishin Shaidun Jehobah da Matansu. Wannan ya nuna mana cewa Jehobah yana so ya ilimantar da mutanensa! Ƙari ga haka, a dandalinmu na jw.org/⁠ha za a iya samun Littafi Mai Tsarki da kuma littattafan da ke bayyana Littafi Mai Tsarki a harsuna da yawa. Kuma akwai sashe don yara da sashe don iyali da kuma sashen labarai. Shin kana amfani da jw.org/⁠ha sa’ad da kake wa’azi da kuma ibadarka ta iyali?

KA RIƘE AMINCI GA JEHOBAH KUMA KA BI JA-GORAR ƘUNGIYARSA

13. Wane hakki ne muke da shi a matsayinmu na bayin Jehobah?

13 Babban gata ne cewa muna cikin ƙungiyar Jehobah! Da yake mun san abin da Allah yake so mu yi, muna bukatar mu yi masa biyayya kuma mu riƙa yin abin da ya dace. Ko da mutane suna son yin abubuwan da ba su da kyau, muna bukatar mu “ƙi mugunta” kamar yadda Jehobah ma ya ƙi mugunta. (Zab. 97:10) Kada mu yi tarayya da waɗanda suke cewa: “Mugunta nagarta; nagarta kuma mugunta” ce. (Isha. 5:20) Domin muna so mu faranta wa Jehobah rai, za mu ci gaba da kasancewa da tsabta da kuma dangantaka mai kyau da shi. (1 Kor. 6:​9-11) Idan muna ƙaunar Jehobah kuma mun dogara gare shi, za mu kasance da aminci ta wajen bin ƙa’idodinsa da suke cikin Littafi Mai Tsarki. Ƙari ga haka, muna iya ƙoƙarinmu mu riƙa bin waɗannan ƙa’idodin a gidanmu, a cikin ikilisiya da wajen aikinmu da makaranta da kuma duk inda muke. (Mis. 15:⁠3) Ka yi la’akari da wasu hanyoyin da za mu iya nuna amincinmu ga Jehobah.

14. Ta yaya iyaye za su iya nuna amincinsu ga Jehobah?

14 Renon yara. Kiristoci suna nuna aminci ga Jehobah sa’ad da suke renon yaransu kamar yadda Kalmar Allah ta umurce su. Iyaye da suke bauta wa Jehobah ba sa bukatar su bi yadda mutanen duniya suke renon yaransu ko kuma bisa ga al’adarsu. (Afis. 2:⁠2) Alal misali, a wasu wurare wani mahaifi zai iya yin tunanin cewa, ‘A nan mata ne suke koyar da yara.’ Littafi Mai Tsarki ya bayyana mana cewa: “Ubanni, . . . ku goye [yaranku] cikin horon Ubangiji da gargaɗinsa.” (Afis. 6:⁠4) Iyayen da suke tsoron Allah suna son yaransu su zama kamar Sama’ila, wanda Jehobah ya kasance da shi sa’ad da yake girma.​—⁠1 Sam. 3:⁠19.

15. Ta yaya za mu nuna cewa muna da aminci ga Jehobah?

15 Yanke shawarwari masu muhimmanci. Hanya ɗaya da za mu nuna amincinmu ga Jehobah ita ce ta wajen neman taimakon Littafi Mai Tsarki sa’ad da muke so mu yanke shawarwari masu muhimmanci a rayuwa. Alal misali, ka yi la’akari da abubuwan da suke shafe iyalai da yawa. A wasu wurare, mutane sukan bar ƙasarsu zuwa wata ƙasa kuma su tura yaransu wajen iyayensu don su ci gaba da yin aiki a wannan ƙasar da suke. Ko da yake ma’aurata ne za su yanke wannan shawarar, amma suna bukatar su tambaye kansu, ‘Ya Jehobah zai ji game da wannan shawarar?’ (Karanta Romawa 14:12.) Zai dace mu yi  tunani a kan abin da Littafi Mai Tsarki ya ce kafin mu yanke shawarar da za ta shafi iyalinmu da kuma aikinmu. Babu shakka, muna bukatar taimakon Jehobah don mu yanke shawara mai kyau.​—Irm. 10:23.

16. Sa’ad da wata mata ta haifi ɗanta, wace shawara ce ta yanke, kuma mene ne ya taimaka mata ta yanke shawara mai kyau?

16 Wata mata da ke zama a wata ƙasa ta haifi ɗa kuma ta yanke shawarar cewa za ta tura shi wajen iyayenta don su kula da shi. A wannan lokacin, sai ta soma nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah, kuma ta soma yin abin da take koya. Ban da haka ma, matan ta koyi cewa Jehobah ya ba ta hakkin kula da kuma renon yaronta. (Zab. 127:3; Mis. 22:⁠6) Sai ta yi addu’a ga Jehobah kuma ta nemi ja-gorarsa kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya umurce mu mu yi. (Zab. 62:​7, 8) Ta tattauna batun da ‘yar’uwar da ke nazari da ita da kuma wasu ‘yan’uwa a cikin ikilisiya. Duk da matsin da ‘yan’uwanta da kuma abokanta suka yi mata cewa ta tura yaron wurin iyayen, ta yanke shawarar cewa ba za ta tura ɗanta gida ba. Sa’ad da maigidanta ya ga yadda ‘yan’uwa a ikilisiya suka taimaka mata da yaron, sai ya amince a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da shi kuma ya soma halartan taro tare da matarsa da kuma yaronsu. Hakika wannan matar za ta ji cewa Jehobah ya amsa addu’arta.

17. Wace shawara ce aka ba mu game da ɗalibanmu na Littafi Mai Tsarki?

17 Bin ja-gora. Wata hanya mai muhimmanci da za mu nuna aminci ga Jehobah ita ce bin ja-gorar da ƙungiyar Jehobah take bayarwa. Alal misali, ka yi la’akari da wasu shawarwarin da aka ba mu game da nazarin da muke yi da ɗalibanmu. An ce da zarar mun soma nazarin littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? da mutumin, sai mu ɗauki ‘yan mintoci don mu koya wa ɗalibin game da ƙungiyarmu ta wurin yin amfani da bidiyon nan Me Ake Yi a Majami’ar Mulki? da kuma ƙasidar nan Su Wane Ne Suke Yin Nufin Jehobah a Yau? An kuma ba da shawarar cewa mu soma nazarin littafin nan “Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah” da zarar mun kammala nazarin littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? da ɗalibin ko da ya yi baftisma. Ƙungiyar ta ba da wannan shawarar ne don a taimaka wa sababbi su ‘kafu cikin bangaskiyarsu.’ (Kol. 2:⁠7) Kana bin wannan shawarar da aka ba da kuwa?

18, 19. Waɗanne dalilai ne suka sa ya kamata mu riƙa gode wa Jehobah?

18 Akwai dalilai da yawa da suka sa ya kamata mu riƙa gode wa Jehobah! Shi ne ya ba mu rai. (A. M. 17:​27, 28) Ya ba mu kyauta mai tamani, wato Littafi Mai Tsarki. Kamar yadda Kiristocin da ke Tasalonika suka karɓi Kalmar Allah, haka ma muna farin cikin bin abin da Allah ya ce a cikin Kalmarsa.​—⁠1 Tas. 2:⁠13.

19 Littafi Mai Tsarki ya taimaka mana mu kusaci Allah kuma shi ma zai kusace mu. (Yaƙ. 4:⁠8) Ubanmu na sama ya ba mu babban gatan kasancewa a cikin ƙungiyarsa, kuma ya kamata mu gode masa don hakan! Marubucin wannan zabura ya ce: “Ku yi godiya ga Ubangiji; gama nagari ne: Gama jinƙansa har abada ne.” (Zab. 136:⁠1) A littafin Zabura na 136, an ambata furucin nan “jinƙansa har abada ne” sau ashirin da shida. Idan muka kasance da aminci ga Jehobah da kuma ƙungiyarsa, Jehobah zai ba mu rai na har abada kuma zai kasance da aminci ga bayinsa!