Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 TALIFIN NAZARI NA 12

Ku Nuna Kun Damu da Mutane

Ku Nuna Kun Damu da Mutane

“Dukanku . . . Kuna jin tausayin juna.”​—1 BIT. 3:8.

WAƘA TA 90 Mu Riƙa Ƙarfafa Juna

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Kamar yadda 1 Bitrus 3:8 ya nuna, me ya sa muke jin daɗin zama da mutanen da suka damu da mu da kuma yadda muke ji?

MUNA jin daɗin zama da mutanen da suka damu da mu da kuma yadda muke ji. Sukan lura cewa muna da bukata kuma su taimaka mana kafin mu nemi taimakonsu. Muna daraja mutane da suke nuna cewa suna jin ‘tausayinmu.’ *​—Karanta 1 Bitrus 3:8.

2. Me ya sa za mu yi iya ƙoƙarinmu don mu riƙa jin tausayin mutane?

2 Ya kamata dukanmu mu riƙa jin tausayin mutane kuma mu damu da yadda suke ji. Hakika, yin hakan ba shi da sauƙi. Me ya sa? Dalili ɗaya shi ne domin dukanmu ajizai ne. (Rom. 3:23) Saboda haka, wajibi ne mu yi ƙoƙari mu riƙa tunanin wasu ba kanmu kaɗai ba. Ƙari ga haka, yana yi ma wasu cikinmu wuya mu yi hakan domin yadda aka rene mu ko kuma abubuwa da muka fuskanta a rayuwa. Ban da haka, halin maƙwabtanmu yana iya shafan mu. A wannan kwanaki na ƙarshe, mutane da yawa ba sa damuwa da yadda mutane suke ji. Maimakon haka, suna “son kansu” kawai. (2 Tim. 3:​1, 2) Me zai taimaka mana mu magance waɗannan abubuwan?

3. (a) Ta yaya za mu ƙara jin tausayin mutane? (b) Mene ne za a tattauna a wannan talifin?

3 Za mu ƙara jin tausayin mutane ta wajen yin koyi da Jehobah da kuma Yesu Kristi. Jehobah, Allah ne mai ƙauna, kuma ya kafa mana misali mafi kyau a yadda za mu nuna mun damu da mutane. (1 Yoh. 4:8) Yesu ya yi koyi da  Jehobah sosai. (Yoh. 14:9) Sa’ad da Yesu yake duniya, ya nuna yadda ’yan Adam za su riƙa jin tausayi. A wannan talifin, za mu fara tattauna yadda Jehobah da Yesu suka nuna sun damu da mutane. Bayan hakan, za mu yi la’akari da yadda za mu bi misalansu.

YADDA JEHOBAH YAKE NUNA TAUSAYI

4. Ta yaya Ishaya 63:​7-9 ya nuna cewa Jehobah ya damu da yadda bayinsa suke ji?

4 Kalmar Allah ta koya mana cewa Jehobah ya damu da yadda bayinsa suke ji. Alal misali, ka yi la’akari da yadda Jehobah ya ji sa’ad da Isra’ilawa ta dā suke shan wahala. Littafi Mai Tsarki ya ce: “A cikin dukan damuwarsu shi ma ya damu.” (Karanta Ishaya 63:​7-9.) Daga baya, Jehobah ya sa annabi Zakariya ya gaya wa Isra’ilawa cewa sa’ad da suke shan wahala ya ji kamar shi ne yake shan wahala. Jehobah ya gaya wa bayinsa: “Duk wanda ya taɓa mutanena ya taɓa ƙwayar idona ne.” (Zak. 2:8) Wannan kwatancin ya nuna yadda Jehobah yake tausaya wa mutanensa!

Jehobah ya ’yantar da Isra’ilawa daga zaman bauta a ƙasar Masar don ya ji tausayin su (Ka duba sakin layi na 5)

5. Ka ba da misalin yadda Jehobah ya ɗauki mataki don ya taimaki bayinsa da suke shan wahala.

5 Jehobah yana jin tausayin bayinsa da suke shan wahala, kuma yana ɗaukan mataki don ya taimaka musu. Alal misali, Jehobah ya fahimci yadda Isra’ilawa suke ji sa’ad da suke shan wahala a ƙasar Masar, kuma hakan ya sa ya cece su. Jehobah ya gaya wa Musa cewa: ‘Na ga azabar jama’ata . . . , Na ji kukansu . . . Na san dukan wahalarsu. Saboda haka na sauka domin in kuɓutar da su daga hannun Masarawa.’ (Fit. 3:​7, 8) Jehobah ya ’yantar da mutanensa domin ya ji tausayin su. Bayan shekaru da yawa, magabtan Isra’ilawa sun kawo musu hari sa’ad da suke Ƙasar Alkawari. Wane mataki ne Jehobah ya ɗauka? Ya “ji tausayinsu saboda nishinsu da suka yi a hannun masu ba su wahala da masu yi musu danniya.” Jehobah ya taimaka wa mutanensa domin ya ji tausayinsu. Shi ya sa ya tura alƙalai su ceci Isra’ilawa daga magabtansu.​—Alƙa. 2:​16, 18.

6. Ka ba da misalin da ya nuna cewa Jehobah ya damu da mutanen da ra’ayinsu bai dace ba.

6 Jehobah ya nuna ya damu da yadda  mutanensa suke ji har a lokacin da ra’ayinsu bai dace ba. Alal misali, Jehobah ya tura annabi Yunana ya sanar wa mutanen Nineba cewa zai halaka su. Amma Allah bai halaka su ba don sun tuba. Hakan ya sa Yunana baƙin ciki, kuma “ya yi fushi” sosai domin abin da ya faɗa bai faru ba. Duk da haka, Jehobah ya yi haƙuri da Yunana kuma ya taimaka masa ya canja ra’ayinsa. (Yona 3:10–4:11) Da shigewar lokaci, Yunana ya fahimci darasin da Jehobah yake so ya koya masa. Ƙari ga haka, Jehobah ya sa Yunana ya rubuta labarinsa don mu amfana.​—Rom. 15:4. *

7. Mene ne yadda Jehobah ya yi sha’ani da bayinsa ya tabbatar mana?

7 Yadda Jehobah ya yi sha’ani da mutanensa ya tabbatar mana da cewa yana jin tausayin bayinsa. Ya san da azaba da wahalar da kowannenmu yake sha. Jehobah ya “san tunanin zuciyar mutum.” (2 Tar. 6:30) Ya san abin da ke zuciyarmu da tunaninmu da kuma kasawarmu. Ƙari ga haka, ‘ba zai bari a gwada mu fiye da ƙarfinmu ba.’ (1 Kor. 10:13) Babu shakka, wannan alkawarin ya ƙarfafa mu sosai!

YADDA YESU YA NUNA TAUSAYI

8-10. Waɗanne yanayoyi ne suka taimaka wa Yesu ya ji tausayin mutane?

8 Yesu ya ji tausayin mutane sosai sa’ad da yake duniya. Abubuwa uku ne suka taimaka masa ya damu da mutane. Na farko, kamar yadda aka ambata ɗazu, Yesu ya yi koyi da Jehobah sosai. Kamar Jehobah, Yesu yana ƙaunar mutane. Ko da yake yana farin ciki don dukan abubuwan da Jehobah ya yi, ya fi son “ ’yan Adam.” (K. Mag. 8:31) Yesu ya damu da yadda mutane suke ji domin yana ƙaunar su.

9 Na biyu, Yesu yana kamar Jehobah don ya san abin da ke zuciyar mutane. Ya san muradin mutane da kuma yadda suke ji. (Mat. 9:4; Yoh. 13:​10, 11) Saboda haka, idan ya lura cewa mutane suna baƙin ciki sosai, yakan ƙarfafa su domin yana jin tausayin su.​—Isha. 61:​1, 2; Luk. 4:​17-21.

10 Na uku, Yesu ya fuskanci wasu ƙalubalen da mutane suke fuskanta. Alal misali, iyayen da suka rene shi talakawa ne. Yesu ya koyi yin aiki mai wuya daga wurin Yusufu. (Mat. 13:55; Mar. 6:3) Ƙari ga haka, kamar dai Yusufu ya mutu kafin Yesu ya soma hidimar sa a duniya. Hakan ya nuna cewa Yesu ya san yadda mutane suke ji sa’ad da aka yi musu rasuwa. Ban da haka, Yesu ya san abin da mutum yake fuskanta idan yana cikin iyali da wasu ba sa bauta wa Jehobah. (Yoh. 7:5) Irin wannan yanayin da wasu sun taimaki Yesu ya fahimci ƙalubalen da talakawa suke fuskanta da kuma yadda suke ji.

Yesu ya fitar da wani kurma daga wurin da jama’a suke kafin ya warkar da shi (Ka duba sakin layi na 11)

11. A wane lokaci ne musamman Yesu ya ji tausayin mutane? Ka bayyana. (Ka duba hoton da ke bangon gaba.)

11 Yesu ya nuna ya damu da mutane musamman sa’ad da yake yin mu’ujizai. Ba ya yin mu’ujizai domin wajibi ne ya yi hakan. Yesu ya yi hakan ne domin yana jin ‘tausayin’ waɗanda suke shan wahala. (Mat. 20:​29-34; Mar. 1:​40-42) Alal misali, ka yi tunanin yadda ya ji sa’ad da ya ja wani kurma gefe ɗaya kafin ya warkar da shi. Yaya kake ganin ya ji sa’ad da ya ta da ɗa tilo na wata gwauruwa daga mutuwa? (Mar. 7:​32-35; Luk. 7:​12-15) Babu shakka, Yesu ya ji tausayin waɗannan mutanen kuma ya so ya taimaka musu.

12. Ta yaya Yohanna 11:​32-35 ya nuna cewa Yesu ya damu da Marta da Maryamu?

 12 Yesu ya nuna ya damu da Marta da Maryamu. Sa’ad da ya ga suna kuka domin mutuwar ɗan’uwansu Li’azaru, “sai Yesu ya yi hawaye.” (Karanta Yohanna 11:​32-35.) Ba rasuwar amininsa ba ne kawai ya sa Yesu kuka ba. Me ya sa? Domin ya san zai ta da Li’azaru. Amma, ya yi kuka domin ya fahimci yadda ’yan’uwansa suke baƙin ciki domin Li’azaru ya rasu.

13. Ta yaya sanin cewa Yesu ya ji tausayin mutane ya ƙarfafa mu?

13 Sanin cewa Yesu yana jin tausayin mutane ya ƙarfafa mu sosai. Hakika, mu ba kamiltattu ba ne kamar shi, amma duk da haka, muna ƙaunar sa don yadda ya ji tausayin mutane. (1 Bit. 1:8) Muna farin ciki da yake mun san cewa yanzu Yesu Sarkin Mulkin Allah ne. Ba da daɗewa ba, zai cire dukan wahalar da muke sha. Domin Yesu ya taɓa zama a duniya, zai fi taimaka wa mutane su daina shan mugun azaba da kuma wahala domin sarautar Shaiɗan. Hakika, an albarkace mu domin mun samu Sarki da zai iya tausaya mana domin “kāsawarmu.”​—Ibran. 2:​17, 18; 4:​15, 16.

KU BI MISALIN JEHOBAH DA NA YESU

14. Mene ne Afisawa 5:​1, 2, ya motsa mu mu yi?

14 Idan muka yi la’akari da yadda Jehobah da Yesu suka ji tausayin mutane, hakan zai motsa mu mu riƙa nuna tausayi. (Karanta Afisawa 5:​1, 2.) Jehobah da Yesu ne kaɗai suke sanin abin da ke cikin zuciyar mutum. Duk da haka, za mu yi ƙoƙari mu fahimci yadda mutane suke ji. (2 Kor. 11:29) Bai kamata mu yi koyi da mutane masu girman kai ba. Saboda haka, mu ƙoƙarta don ‘kada mu kula da kanmu kaɗai, amma mu kula da waɗansu kuma.’​—Filib. 2:4.

(Ka duba sakin layi na 15-19) *

15. Su waye ne musamman suke bukatar su riƙa jin tausayin ’yan’uwa?

15 Ya kamata dattawa musamman su riƙa jin tausayin mutane. Don Jehobah yana bukatar su riƙa kula da ’yan’uwa sosai. (Ibran. 13:17) Idan dattawa suna jin tausayin ’yan’uwa, hakan zai sa su taimaka musu. Mene ne zai taimaka wa dattawa su riƙa yin hakan?

16. Mene ne dattijo da ya damu da ’yau’uwa zai riƙa yi, kuma me ya sa hakan yake da muhimmanci?

16 Dattijon da ya damu da ’yan’uwa zai riƙa keɓe lokaci don ya kasance da su. Zai yi musu tambayoyi kuma ya saurare su sosai. Zai yi hakan musamman idan wani ɗan’uwa da ke fama yana ƙoƙarin gaya masa abin da ke damunsa. (K. Mag. 20:5) Idan dattijo yana keɓe lokaci don ya kasance da ’yan’uwa, hakan zai sa ’yan’uwa su amince da shi. Ƙari ga haka, za su zama abokansa kuma su ƙaunace shi.​—A. M. 20:37.

17. Wane hali ne ’yan’uwa da yawa suka ce sun fi so dattawa su kasance da shi? Ka ba da misali.

17 ’Yan’uwa da yawa sun ce sun fi son dattawan da suka damu da yadda suke ji. Me ya sa? Adelaide ta ce: “Ya fi sauƙi ka yi musu magana, domin ka san za su fahimce ka.” Ta daɗa cewa: “Za ka lura cewa suna jin tausayinka ta abin da suke yi sa’ad da kake tattaunawa da su.” Wani ɗan’uwa da yake farin ciki don yadda wani dattijo ya bi da shi ya ce: “Na ga hawaye ya cika idanun wani dattijo sa’ad da nake gaya masa abin da nake fuskanta. Ba zan taɓa manta da wannan ba.”​—Rom. 12:15.

18. Ta yaya za mu nuna mun damu da ’yan’uwa?

18 Hakika, ba dattawa ba ne kaɗai za su riƙa jin tausayin ’yan’uwa ba. Dukan mu  za mu iya yin hakan. Ta yaya? Ku yi ƙoƙari ku fahimci matsalolin da membobin iyalinku ko kuma ’yan’uwa suke fuskanta. Ku riƙa nuna kun damu da matasa da ke ikilisiyarku da masu rashin lafiya da tsofaffi da kuma waɗanda aka yi musu rasuwa. Ka tambaye su yadda suke fama da matsalolin, kuma ka saurare su da kyau sa’ad da suke gaya maka yadda suke ji. Ka sa su san cewa ka damu da su sosai, kuma ka yi ƙoƙari ka taimaka musu. Idan muka yi waɗannan abubuwan, muna nuna cewa muna ƙaunar ’yan’uwanmu sosai.​—1 Yoh. 3:18.

19. Me ya sa ya kamata mu kasance da sanin yakamata sa’ad da muke ƙoƙari mu taimaka wa ’yan’uwa?

19 Zai dace mu kasance da sanin yakamata sa’ad da muke ƙoƙarin taimaka wa mutane. Me ya sa? Domin mutane suna bi da matsaloli a hanyoyi dabam-dabam. Wasu suna son gaya wa mutane matsalolinsu, wasu kuma ba sa so. Saboda haka, ko da yake muna son mu taimaka wa mutane, bai kamata mu riƙa yin tambayoyin da zai kunyatar da su ba. (1 Tas. 4:11) Ko da wasu sun gaya mana matsalolinsu, za mu ga cewa ba a kowane lokaci ba ne muke amincewa da ra’ayinsu ba. Duk da haka, ya kamata mu tuna cewa suna faɗin yadda suke ji ne. Kuma ya kamata mu yi saurin saurarar su amma ba saurin magana ba.​—Mat. 7:1; Yaƙ. 1:19.

20. Mene ne za mu tattauna a talifi na gaba?

20 Duk da cewa ya dace mu riƙa nuna mun damu da mutane a ikilisiya, ya kamata mu riƙa nuna wannan halin sa’ad da muke wa’azi. Ta yaya za mu nuna muna jin tausayin mutane sa’ad da muke wa’azi? Za mu tattauna wannan batun a talifi na gaba.

WAƘA TA 130 Mu Riƙa Gafartawa

^ sakin layi na 5 Jehobah da Yesu sun damu da yadda mutane suke ji. A wannan talifin, za mu tattauna abin da muka koya daga misalansu. Ban da haka, za mu tattauna dalilin da ya sa za mu riƙa jin tausayin mutane da kuma yadda za mu iya yin hakan.

^ sakin layi na 1 MA’ANAR WASU KALMOMI: Jin “tausayi” yana nufin cewa za mu yi ƙoƙari mu fahimci yadda mutane suke ji kuma mu riƙa tausaya musu. (Rom. 12:15) A wannan talifin, jin “tausayi” da kuma “damuwa” suna da ma’ana ɗaya.

^ sakin layi na 6 Jehobah ya ji tausayin bayinsa masu aminci da suka yi sanyin gwiwa ko kuma suka ji tsoro. Ka yi tunanin labarin Hannatu (1 Sam. 1:​10-20) da Iliya (1 Sar. 19:​1-18) da kuma Ebed-melek (Irm. 38:​7-13; 39:​15-18).

^ sakin layi na 65 BAYANI A KAN HOTUNA: Taro a Majami’ar Mulki yana ba mu zarafin yin cuɗanya da ’yan’uwa. Mun ga (1) wani dattijo yana magana da wani matashi da mahaifiyarsa, (2) wani mahaifi da ’yarsa suna taimaka ma wata ’yar’uwa tsohuwa ta shiga mota, kuma (3) dattawa biyu suna saurarar wata ’yar’uwa da take neman taimako.