Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 3

Jehobah Yana Taimaka Maka don Ka Yi Nasara

Jehobah Yana Taimaka Maka don Ka Yi Nasara

‘Yahweh kuwa yana tare da Yusuf har ya zama mutum mai nasara cikin . . . , dukan abin da ya yi.’​—FAR. 39:​2, 3.

WAƘA TA 30 Jehobah Ubana, Allahna da Abokina

ABIN DA ZA A TATTAUNA a

1-2. (a) Me ya sa ba ma mamaki idan muna fuskantar matsaloli? (b) Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

 A MATSAYINMU na bayin Jehobah, ba ma mamaki idan muna fuskantar matsaloli. Kamar yadda aka faɗa a Littafi Mai Tsarki, “sai tare da azaba mai yawa za mu shiga Mulkin Allah.” (A. M. 14:22) Mun kuma san cewa ba dukan matsalolinmu ne za a magance su ba, sai Mulkin Allah ya zo inda “babu sauran mutuwa, ko baƙin ciki, ko kuka, ko azaba.”​—R. Yar. 21:4.

2 Jehobah ba ya kāre mu daga jarabobi, amma yana taimaka mana mu iya jimre musu. Ka lura da abin da manzo Bulus ya gaya wa Kiristoci da ke Roma. Ya fara ambata matsaloli da dama da shi da ꞌyanꞌuwansa suka fuskanta. Saꞌan nan ya rubuta cewa: “Mun wuce a ce da mu masu nasara kawai, wannan kuwa ta wurin shi wanda ya ƙaunace mu ne.” (Rom. 8:​35-37) Hakan yana nufin cewa Jehobah zai iya taimaka maka ka yi nasara idan kana fuskantar wata matsala. Bari mu ga yadda Jehobah ya taimaka wa Yusufu ya yi nasara da kuma yadda zai iya taimaka maka.

SAꞌAD DA ABUBUWA SUKA CANJA FARAT ƊAYA

3. Wane canji ne ya faru a rayuwar Yusufu farat ɗaya?

3 Yakubu ya nuna cewa yana ƙaunar ɗansa Yusufu sosai. (Far. 37:​3, 4) Saboda haka, sauran ꞌyaꞌyan Yakubu sun soma ƙishin ƙaninsu. Da sun sami zarafi, sai suka sayar da Yusufu ga wasu attajiran Midiya. Waɗannan attajiran sun kai Yusufu wata ƙasa mai nisa, wato ƙasar Masar, inda suka sake sayar da shi wa Fotifar, shugaban masu gādin Fir’auna. Rayuwar Yusufu ta canja nan da nan, daga zama wanda babansa yake ƙauna sosai zuwa bawan wani Ba-masari!​—Far. 39:1.

4. Waɗanne irin matsaloli ne za mu iya fuskanta?

4 Littafi Mai Tsarki ya faɗa cewa: ‘Lokaci da sa’a sukan same kowannenmu.’ (M. Wa. 9:11) A wasu lokuta, muna yawan fuskantar matsalolin da mutane suka “saba” fuskanta. (1 Kor. 10:13) Ko kuma za mu iya shan wahala domin mu mabiyan Yesu ne. Alal misali, ana iya yi mana baꞌa ko a tsananta mana domin bangaskiyarmu. (2 Tim. 3:12) Ko da wace matsala ce kake fuskanta, Jehobah zai iya sa ka yi nasara. Ta yaya Jehobah ya sa Yusufu ya yi nasara?

Jehobah ya taimaka wa Yusufu ya yi nasara har a lokacin da aka sayar da shi ya zama bawa a gidan Fotifar a ƙasar Masar (Ka duba sakin layi na 5)

5. Mene ne Fotifar yake ganin ke taimaka ma Yusufu ya yi nasara? (Farawa 39:​2-6)

5 Karanta Farawa 39:​2-6. Fotifar ya lura cewa Yusufu yana da ilimi sosai, kuma yana aiki da ƙwazo. Ya kuma san abin da ke taimaka wa Yusufu. Fotifar ya ga cewa “dukan abin da Yusuf ya yi, Yahweh yakan sa abin ya yalwata a hannunsa.” b Daga baya, Fotifar ya sa Yusufu ya zama shugaba bisa gidansa. Kuma duk abin da yake da shi, ya danƙa a hannun Yusufu. Mene ne sakamakon da ya samu? Fotifar ya tara dukiya.

6. Yaya Yusufu ya ji game da yanayinsa?

6 Ka yi tunanin yadda Yusufu ya ji. Mene ne ya fi so? Yana son Fotifar ya lura da aikin da yake yi kuma ya yi masa alheri ne? Ba mamaki, Yusufu ya so a sake shi domin ya koma wurin mahaifinsa. Balle ma, duk da ayyuka na musamman da yake yi a gidan Fotifar, har ila Yusufu bawa ne ga shugaban da ba ya bauta wa Jehobah. Jehobah bai sa Fotifar ya saki Yusufu ba. Kuma yanayin Yusufu zai daɗa muni.

IDAN YANAYIN YA DAƊA MUNI

7. A wace hanya ce yanayin Yusufu ya daɗa muni? (Farawa 39:​14, 15)

7 Kamar yadda aka ambata a Farawa 39, matar Fotifar ta soma son Yusufu kuma ta yi ƙoƙari ta rinjaye shi. Amma Yusufu yakan ƙi. Daga baya, ta yi fushi da Yusufu kuma ta zarge shi da son yi mata fyaɗe. (Karanta Farawa 39:​14, 15.) Da Fotifar ya ji hakan, sai ya saka Yusufu a kurkuku inda ya yi wasu shekaru. (Far. 39:​19, 20) Yaya yanayin kurkukun yake? Kalmar Ibrananci da Yusufu ya yi amfani da ita a matsayin “kurkuku” tana iya nufin “rami mai zurfi.” Hakan ya nuna cewa kurkukun na da duhu kuma Yusufu ya ji kamar ba shi da mafita. (Far. 40:15) Ƙari ga haka, Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa an ɗaure ƙafafun Yusufu da sarƙa, kuma an saka wuyarsa a cikin baƙin ƙarfe na ɗan lokaci. (Zab. 105:​17, 18) Hakika, yanayin Yusufu yana daɗa muni. Daga zama bawan da aka amince da shi, ya zama fursuna.

8. Mene ne za mu iya tabbatar da shi, ko da jarabawa da muke fuskanta ya yi tsanani?

8 Ka taɓa kasancewa a wani mawuyacin yanayi da ya daɗa muni duk da adduꞌoꞌinka? Hakan yana iya faruwa. Jehobah ba ya kāre mu daga jarabobi a duniyar Shaiɗan. (1 Yoh. 5:19) Duk da haka, za ka iya tabbata cewa Jehobah ya san duk abin da kake fuskanta kuma yana lura da kai. (Mat. 10:​29-31; 1 Bit. 5:​6, 7) Ƙari ga haka, ya yi alkawari cewa: “Har abada ba zan bar ka ba, sam sam ba zan yar da kai ba.” (Ibran. 13:5) Jehobah zai iya taimaka maka ka jimre ko da kana ganin kamar yanayinka ba shi da mafita. Bari mu ga yadda ya taimaka wa Yusufu.

Jehobah ya taimaka wa Yusufu har a lokacin da yake kurkuku, kuma hakan ya sa ya zama mai kula da dukan fursunoni (Ka duba sakin layi na 9)

9. Mene ne ya nuna cewa Jehobah yana tare da Yusufu a lokacin da yake kurkuku? (Farawa 39:​21-23)

9 Karanta Farawa 39:​21-23. Jehobah ya sa Yusufu ya yi nasara ko da yake yana cikin yanayi mai wuya a kurkuku. Ta yaya ya yi hakan? Da shigewar lokaci, Yusufu ya sami farin jini a gaban shugaban masu gādi kamar yadda ya samu a wurin Fotifar. Ba da daɗewa ba, shugaban masu gādin ya sa Yusufu ya riƙa kula da ꞌyan kurkuku. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Shugaban masu gadin ’yan kurkukun, bai damu ba a kan abubuwan da suke a ƙarƙashin Yusuf.” Yanzu Yusufu ya sami aikin da zai riƙa mai da hankali a kai. Wannan canji ne da bai yi tsammaninsa ba! Ta yaya fursunan da aka zarge shi da yi wa matar wani fyaɗe zai samu irin wannan babban matsayi? Amsa ɗaya ce kawai muke da ita. Kamar yadda Farawa 39:23 ta ce: “Yahweh yana tare da Yusuf. Kuma dukan abin da ya yi, Yahweh yakan ba shi nasara.”

10. Ka bayyana abin da ya sa Yusufu zai iya tunani cewa bai yi nasara a kome ba.

10 Ka sake yin tunani a kan yadda Yusufu ya ji. Bayan da aka zarge shi kuma aka saka shi a kurkuku, kana ganin kamar ya ji cewa ya yi nasara a kome? Mene ne Yusufu ya fi so fiye da kome? Yana so ya samu farin jini a gaban shugaban masu gādin ꞌyan kurkukun ne? Babu shakka, Yusufu ya so a wanke shi a gaban mutane kuma a sake shi. Ya ma gaya ma wani fursuna da ake so a sake shi ya yi magana da Fir’auna a madadin shi don shi ma a sake shi. (Far. 40:14) Mutumin bai yi hakan nan da nan ba. Kuma hakan ya sa Yusufu ya sake yin shekaru biyu a kurkukun. (Far. 40:23; 41:​1, 14) Duk da haka, Jehobah ya sa ya ci gaba da yin nasara. Ta yaya ya yi hakan?

11. Wace baiwa ce Jehobah ya ba Yusufu, kuma ta yaya hakan ya sa aka cim ma nufin Jehobah?

11 Saꞌad da Yusufu yake kurkuku, Jehobah ya sa sarkin Masar ya yi mafarkai guda biyu da suka dame shi. Fir’auna ya so ya san maꞌanar mafarkan nan da nan. Da sarkin ya ji cewa Yusufu zai iya bayyana masa mafarkansa, sai ya aika a kawo shi. Da taimakon Jehobah, Yusufu ya bayyana mafarkan kuma ya ba Fir’auna shawarar da ta burge shi. Fir’auna ya lura cewa Jehobah yana taimaka wa Yusufu, don haka Fir’auna ya naɗa shi ya zama mai kula da harkar abinci a ƙasar Masar. (Far. 41:​38, 41-44) Daga baya, an yi yunwa mai tsanani a ƙasar Masar da kuma ƙasar Kan’ana, inda iyalin Yusufu suke zama. Yanzu Yusufu zai iya ya ceci iyalinsa, kuma ta hakan ne za a samu zuriyar da Almasihu zai fito.

12. A waɗanne hanyoyi ne Jehobah ya sa Yusufu ya yi nasara?

12 Ka yi tunanin irin abubuwan da suka faru a rayuwar Yusufu. Wane ne ya sa Fotifar ya lura da Yusufu duk da cewa shi bawa ne kawai? Wane ne ya sa Yusufu ya sami farin jini a gaban shugaban masu gādin yayin da yake kurkuku? Wa ya sa Fir’auna ya yi mafarkan da suka dame shi kuma ya sa Yusufu ya iya bayyana su? Wane ne ya sa Fir’auna ya naɗa Yusufu a matsayin mai kula da harkar abinci? (Far. 45:5) Hakika, Jehobah ne ya sa Yusufu ya yi nasara a duk abin da ya yi. Ko da yake ꞌyanꞌuwan Yusufu sun so su kashe shi, Jehobah ya canja yanayin don ya cim ma nufinsa.

YADDA JEHOBAH YAKE SA KA YI NASARA

13. Jehobah yana saka hannu a kowane yanayin da muke ciki? Ka bayyana.

13 Mene ne muka koya daga labarin Yusufu? Jehobah yana saka hannu a kowanne yanayin da mun same kanmu ne? Shin yana canja abubuwan da suka faru a rayuwarmu don dukan abubuwa marasa kyau su zama don dalili mai kyau? Hakan ba gaskiya ba ne, don Littafi Mai Tsarki bai yarda da wannan koyarwar ba. (M. Wa. 8:9; 9:11) Amma mun san cewa idan mun fuskanci jarabawa, Jehobah ya san da hakan kuma yana jin kukanmu na neman taimako. (Zab. 34:15; 55:22; Isha. 59:1) Ƙari ga haka, Jehobah zai iya taimaka mana mu jimre matsaloli. Ta yaya zai yi hakan?

14. Ta yaya Jehobah yake taimaka mana idan muna mawuyacin yanayi?

14 Hanya ɗaya da Jehobah yake taimaka mana ita ce, yana taꞌazantar da mu da kuma ƙarfafamu a daidai lokacin da muke bukatarsa. (2 Kor. 1:​3, 4) Abin da ya faru da Eziz ke nan, wani ɗanꞌuwa a ƙasar Turkmenistan wanda an yanke masa hukuncin yin shekaru biyu a kurkuku don imaninsa. Ɗanꞌuwan ya ce: “Da safe, a ranar da za a yanke min hukunci, wani ɗanꞌuwa ya nuna min Ishaya 30:15 da ta ce: ‘Cikin kwanciyar hankali da dogara gare ni za ku sami ƙarfi.’ Wannan ayar ta taimaka min in kasance da kwanciyar hankali kuma in dogara ga Jehobah a kome. Yin bimbini a kan wannan ayar ya taimaka min na tsawon lokacin da na yi a kurkuku.” Za ka iya tuna da wani lokaci a rayuwarka da Jehobah ya taimaka maka wajen ƙarfafa ka da taꞌazantar da kai saꞌad da ka fi bukatarsa?

15-16. Mene ne ka koya daga labarin Tori?

15 Sau da yawa, sai mun shawo kan wata matsala ne muke ganin yadda Jehobah ya taimaka mana. Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Tori ta gano cewa hakan gaskiya ne. Yaronta mai suna Mason ya yi shekaru shida yana fama da ciwon kansa har ya mutu. Hakan ya sa Tori baƙin ciki sosai, kuma ta ce: “Ban tsammani akwai abin da ya fi sa ni baƙin ciki a matsayin mahaifiya kamar wannan ba.” Ta ƙara da cewa: “Na tabbatar iyaye za su yarda cewa sun fi damuwa idan suka ga yaronsu yana shan wahala, fiye da yadda za su damu idan a ce su ne.”

16 Ko da yake Tori ta yi baƙin ciki da ta ga ɗanta yana shan wahala sosai, daga baya ta yi tunanin yadda Jehobah ya taimaka mata ta iya jimrewa. Ta ce: “Idan na yi tunani a kan abin da ya faru a lokacin, nakan ga yadda Jehobah ya taimaka mini a lokacin da ɗana yake rashin lafiya. Alal misali, har a lokacin da ciwon Mason ya yi tsanani har ba ya iya ganin mutane, ꞌyanꞌuwa maza da mata sukan yi tafiya a mota na awa biyu don su ziyarce shi a asibitin. A kowane lokaci akwai mutum a wurin karɓan baƙi da yake a shirye ya taimaka mana. Kuma ꞌyanꞌuwa maza da mata sun tanadar mana da abubuwan da muke bukata. Ba mu rasa abin da muke bukata ba har a mawuyacin lokaci.” Jehobah ya tanada wa Tori da ɗanta Mason abin da suke bukata. Ka duba akwatin nan “ Jehobah Ya Ba Mu Ainihin Abin da Muke Bukata.”

KADA KA MANTA DA YADDA JEHOBAH YA TAIMAKA MAKA

17-18. A lokacin da muke fuskantar matsaloli, me zai taimaka mana mu ga yadda Jehobah yake taimaka mana? (Zabura 40:5)

17 Karanta Zabura 40:5. Burin mahayin dutse shi ne ya kai saman dutsen. Amma akwai lokuta da dama da zai iya dakatawa don ya ga wasu abubuwa masu ban shaꞌawa. Haka ma, zai dace ka riƙa dakatawa a kai a kai don ka yi tunanin yadda Jehobah yake yi maka albarka duk da cewa kana fuskantar matsaloli. A ƙarshen kowace rana, ka tambaye kanka: ‘A waɗanne hanyoyi ne Jehobah ya albarkace ni a yau? Duk da cewa Jehobah bai cire matsalolin da nake fuskanta ba, ta yaya yake taimaka mini in jimre?’ Ka yi laꞌakari sosai ko za ka iya ganin aƙalla hanya ɗaya da Jehobah ya albarkace ka.

18 Wataƙila kana adduꞌa cewa Jehobah ya cire matsalolinka. Yin hakan ba laifi ba ne. (Filib. 4:6) Amma kada mu manta da albarkun da muke morewa a yanzu. Jehobah ya yi mana alkawari cewa zai ƙarfafa mu kuma zai taimaka mana mu jimre. Saboda haka, a kowane lokaci, ka riƙa tuna cewa Jehobah yana taimaka maka. Idan ka yi hakan, za ka ga yadda Jehobah yake taimaka maka ka yi nasara, kamar yadda ya taimaka wa Yusufu a lokacin da yake fuskantar mawuyacin yanayi.​—Far. 41:​51, 52.

WAƘA TA 32 Mu Kasance da Aminci ga Jehobah!

a Idan muna fama da matsala, ba za mu ga cewa muna yin “nasara” ba. Sai mun magance matsalarmu ne mukan ga kamar mun yi nasara. Amma abubuwan da suka faru a rayuwar Yusufu sun koya mana darasi mai muhimmanci, cewa Jehobah zai iya taimaka mana mu yi nasara duk da matsalolinmu. Wannan talifin zai bayyana mana yadda hakan zai yiwu.

b Littafi Mai Tsarki ya ambata waɗannan canje-canje a rayuwar Yusufu a cikin ayoyi kaɗan ne kawai, amma mai yiwuwa, hakan ya ɗauki shekaru da yawa.