Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Taron yankin da aka yi a Nyzhnya Apsha da ke Yukiren a 2012

An Girbe Amfani Mai Yawa!

An Girbe Amfani Mai Yawa!

YESU ya yi annabci cewa a kwanaki na ƙarshe, mabiyansa za su girbe amfani mai yawan gaske. (Mat. 9:37; 24:14) Bari mu yi la’akari da yadda annabcin nan ya cika a wata hanya ta musamman a yankin Transcarpathia da ke ƙasar Yukiren. A garurruka guda uku da suke kusa da juna, da akwai ikilisiyoyi 50 da kuma masu shela fiye da 5,400. * Hakan yana nufin cewa idan aka haɗa dukan garurrukan nan, mutum ɗaya cikin mutane huɗu Mashaidin Jehobah ne.

Wane irin hali ne mutanen yankunan suke da shi? Wani ɗan’uwa mai suna Vasile ya ce: “Mutanen suna daraja Littafi Mai Tsarki, suna son adalci kuma suna da haɗin kai sosai a iyalinsu. Ban da haka ma, suna iya ƙoƙarinsu don su taimaka ma juna. Ba a kowane lokaci ba ne suke yarda da abin da muka yi imani da shi ba, amma idan muka nuna musu a Littafi Mai Tsarki, suna saurara sosai.”

Da yake masu shela suna da yawa a yankin, ’yan’uwa suna fuskantar ƙalubale. Alal misali a wata ikilisiya, akwai masu shela 134, amma gidaje 50 ne kawai suke yankin. Ta yaya masu shela suke wa’azi a wannan yankin?

’Yan’uwa da yawa suna yin wa’azi a wasu yankuna da ake bukatar masu shela sosai. Wani ɗan’uwa ɗan shekara 90 mai suna Ionash, ya ce: “A yankin da ikilisiyarmu take wa’azi, mutum ɗaya zai iya wa’azi a gida biyu kawai. A lokacin da nake da ƙoshin lafiya sosai, ina zuwa wasu ƙauyuka yin wa’azi. Ban da haka, ina yin tafiyar mil 100 zuwa yanki da ba a sanya ma kowa yin wa’azi ba don in yi wa’azi da yaren Hungary.” Wajibi ne masu shela su yi sadaukarwa sosai don zuwa wa’azi a wasu yankuna. Ɗan’uwa Ionash ya ƙara cewa: “Ina tashiwa ƙarfe 4:00 da asuba don in shiga jirgin ƙasa, kuma nakan yi wa’azi har ƙarfe 6:00 na yamma don a lokacin ne jirgin yake komawa. Nakan yi hakan sau biyu ko uku a mako.” Yaya yake ji don ƙwazon da ya sa a wa’azi? Ɗan’uwan ya ce: “Ina jin daɗin yin irin wannan wa’azin. Ina farin ciki don na taimaka wa wata iyali da ke zama a inda babu ikilisiya su koya game da Jehobah.”

Ba kowa ba ne a ikilisiyar da ke wannan yankin ba ne zai iya yin tafiya mai nisa ba. Amma dukansu har ma da tsofaffi suna yin iya ƙoƙarinsu don su yi wa dukan mutane wa’azi a yankinsu. A sakamakon haka, a shekara ta 2017, waɗannan garurruka uku sun haɗu don su yi taron Tuna da Mutuwar Yesu. Kuma mutanen da suka halarci taron sun ninka dukan masu shela a garurrukan sau biyu. Ko kuma a ce rabin dukan mutanen da suke garurrukan ne suka halarci taron. Hakika, wannan ya nuna mana cewa a duk inda muke hidima, da akwai ayyuka da yawa da za mu iya yi a “aikin Ubangiji.”​—1 Kor. 15:58.

^ sakin layi na 2 Sunayen garurrukan su ne, Hlybokyy Potik da Serednye Vodyane da kuma Nyzhnya Apsha.