Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Jehobah Yana Kaunar Wadanda Suke Yin Wa’azi da Jimiri

Jehobah Yana Kaunar Wadanda Suke Yin Wa’azi da Jimiri

“Irin da suka fāɗi a ƙasa mai kyau kuwa, su ne . . . suka jimre suka ba da amfani.”​—LUK. 8:15.

WAƘOƘI: 68, 72

1, 2. (a) Me ya sa ’yan’uwa da suke wa’azi a yankunan da mutane ba sa son wa’azinmu suke ƙarfafa mu? (Ka duba hoton da ke shafin nan.) (b) Mene ne Yesu ya ce game da yin wa’azi a “garinsa”? (Ka duba ƙarin bayani.)

SERGIO DA OLINDA ma’aurata ne da suke zama a Amirka, ko da sun ba shekara 80 baya, har ila suna hidimar majagaba. Amma, kwanan nan ciwon ƙafa yana damun su sosai. Duk da haka, kamar yadda suka saba yi shekaru da yawa, a kowace safiya da ƙarfe bakwai, sukan taka zuwa wurin da jama’a suke a garinsu. Kuma su tsaya kusa da tashar mota su riƙa ba mutane da suke wucewa littattafanmu. Ma’auratan sukan kasance a wurin suna yi wa mutane da suka kalle su murmushi ko da yake yawancin mutanen ba su damu da su ba. Da rana kuma sai ma’auratan su taka a hankali su koma gida. Washegari kuma sai su dawo tashar motar da ƙarfe bakwai na safe. Haka suke yi kwanaki shida kowane mako har sai zagayowar shekara.

2 Akwai ’yan’uwa da yawa kamar Sergio da Olinda a faɗin  duniya da suke wa’azi shekaru da yawa a yankin da mutane ba sa sauraron su. Idan kana wa’azi a irin wannan yankin, muna yaba maka domin ka jimre kuma ka ci gaba da yin wa’azi ko da yake hakan ba shi da sauƙi. * Ƙari ga haka, kana ƙarfafa ’yan’uwa da yawa, har da waɗanda suka daɗe suna bauta wa Jehobah. Ga abin da wasu masu kula da da’ira suka ce game da masu wa’azi a irin wannan yanayin: “Sa’ad da na fita yin wa’azi da irin waɗannan ’yan’uwan, misalinsu yana ƙarfafa ni.” Wani kuma ya ce: “Amincinsu yana ƙarfafa ni in ci gaba da hidimata kuma in kasance da gaba gaɗi.” Wani ya daɗa cewa: “Misalinsu yana ƙarfafa ni sosai.”

3. Waɗanne tambayoyi uku ne za mu tattauna, kuma me ya sa?

3 Don mu ci gaba da yin aikin da Yesu ya ba mu, za mu tattauna amsoshin tambayoyin nan guda uku: Me zai iya sa mu sanyin gwiwa a wasu lokuta? Ta yaya za mu ci gaba da ba da amfani? Mene ne zai taimaka mana mu jimre sa’ad da muke wa’azi?

ME ZAI IYA SA MU SANYIN GWIWA?

4. (a) Ta yaya halin Yahudawa ya shafi Bulus? (b) Me ya sa Bulus ya ji hakan?

4 Idan kana sanyin gwiwa domin mutane a yankinku ba sa son su saurari wa’azinka, to ka san cewa ba ka kaɗaita ba. Manzo Bulus ma ya ji hakan. Bulus ya yi shekara 30 yana wa’azi kuma ya taimaki mutane da yawa su zama Kiristoci. (A. M. 14:21; 2 Kor. 3:​2, 3) Duk da haka, bai iya taimaka wa Yahudawa da yawa su zama Kiristoci ba. Maimakon haka, yawancinsu sun ƙi saurarar Bulus, wasu ma sun tsananta masa. (A. M. 14:19; 17:​1, 4, 5, 13) Ta yaya halin Yahudawa ya shafi Bulus? Ya ce: “Ina faɗin gaskiya cikin Almasihu, . . . ina da baƙin ciki ƙwarai, da kuma damuwa a kullum cikin zuciyata.” (Rom. 9:​1-3) Me ya sa Bulus ya ji hakan? Domin yana son wa’azi sosai kuma ya yi wa Yahudawa wa’azi domin ya damu da su. Saboda haka, ya yi baƙin ciki sa’ad da suka ƙi jinƙai da Allah ya nuna musu.

5. (a) Me yake sa mu yi wa maƙwabtanmu wa’azi? (b) Me ya sa muke sanyin gwiwa a wasu lokuta?

5 Kamar Bulus, muna yi wa mutane wa’azi don mun damu da su. (Mat. 22:39; 1 Kor. 11:1) Me ya sa? Domin mun san cewa bauta wa Jehobah yana sa mu sami albarka sosai. Saboda haka, muna son mu taimaka ma mutane su ga cewa za su fi jin daɗin rayuwa idan suka bauta wa Jehobah. Shi ya sa muke ƙarfafa su su koya game da Jehobah da kuma nufinsa ga ’yan Adam. Yin hakan yana kamar mun kai musu kyauta mai tamani kuma muna roƙon su cewa: ‘Don Allah ku karɓa.’ Saboda haka, mukan yi baƙin ciki a ‘cikin zuciyarmu’ sa’ad da mutane suka ƙi wannan kyautar. Muna jin hakan domin muna ƙaunar mutane sosai ne ba don rashin bangaskiya ba. Duk da cewa mukan yi sanyin gwiwa a wasu lokuta, hakan ba ya hana mu wa’azi. Kuma mun yarda da abin da wata mai suna Elena da ta yi sama da shekara 25 tana hidimar majagaba ta ce: “Yin wa’azi yana min wuya, amma shi ne aikin da na fi so.”

TA YAYA ZA MU CI GABA DA BA DA AMFANI

6. Wace tambaya ce za mu tattauna, kuma yaya za mu yi hakan?

6 Me ya sa muke da tabbaci cewa wa’azin da muke yi yana sa Jehobah farin ciki ko da a wane yanki muke wa’azi? Don a  amsa wannan tambaya mai muhimmanci, za mu tattauna kwatancin Yesu guda biyu game da ba da “amfani.” (Mat. 13:23) Za mu soma da kwatancin itacen inabi.

7. (a) Wane ne “manomi” da “itacen inabi” da kuma “rassan”? (b) Wace tambaya ce muke so mu amsa?

7 Karanta Yohanna 15:​1-5, 8A wannan kwatancin, Yesu ya gaya wa manzanninsa cewa: “Ku haifar da halin rayuwa mai kyau wadda za ta nuna cewa ku almajiraina ne, kamar itacen da ya haifi ’ya’ya masu kyau, gama wannan ne yake ɗaukaka Ubana.” Yesu ya ce Jehobah ne “manomin,” shi kuma “itacen inabi na ainihi,” almajiransa ne “rassan.” * Saboda haka, wane irin ’ya’ya ne ya kamata mabiyan Kristi su bayar? A wannan kwatancin, Yesu bai ambata ’ya’yan ba, amma ya faɗi abubuwan da za su taimaka mana mu san amsar.

8. (a) A wannan kwatancin, me ya sa ba da ’ya’ya ba ya nufin yin almajirai? (b) Mene ne Jehobah yake bukata a gare mu?

8 Sa’ad da Yesu yake magana game da Ubansa, ya ce: ‘Kowane reshe a cikina da ba ya ba da ’ya’ya, sai ya yanke shi.’ Wato Yesu yana nufin cewa Jehobah zai ɗauke mu a matsayin bayinsa idan muna ba da ’ya’ya. (Mat. 13:23; 21:43) Saboda haka, a wannan kwatancin, ’ya’yan da ya wajaba kowane Kirista ya ba da ba ya nufin sa mutane su soma bauta wa Allah. (Mat. 28:19) Me ya sa? Domin akwai Shaidu masu aminci da yawa da ba su taɓa taimaka wa wani ya soma bauta wa Allah ba don suna wa’azi a yankin da mutane ba sa son saƙonmu. Hakika, ba za mu iya tilasta wa mutane su zama mabiyan Yesu ba. Ban da haka ma, Jehobah mai ƙauna ne, kuma ba zai ce mu yi abin da ya fi ƙarfinmu ba. A koyaushe, yana gaya mana mu yi abin da za mu iya yi.​—M. Sha. 30:​11-14.

9. (a) Ta yaya muke ba da ’ya’ya? (b) Wane kwatanci ne za mu tattauna, kuma me ya sa?

9 Wane ’ya’ya ne ya wajaba mu ba da? Hakika, hakan yana nufin duk abin da kowannenmu zai iya yi. Wane aiki ne Jehobah ya ba dukan bayinsa? Aikin shi ne wa’azi game da Mulkinsa. * (Mat. 24:14) Kwatancin mai shuki da Yesu ya ba da ne ya sa muka san hakan. Bari mu tattauna wannan kwatanci na biyu.

10. (a) A wannan kwatancin, mene ne iri da kuma ƙasa suke wakilta? (b) Wane irin amfani ne alkamar ta bayar?

10 Karanta Luka 8:​5-8, 11-15. A kwatancin mai shuki, Yesu ya ce irin shi ne “kalmar Allah,” ko kuma wa’azi game da Mulkin Allah. Ƙasar kuma tana wakiltar zuciyar mutane. Irin da ya faɗi a ƙasa mai kyau ya yi jijiya, ya tsira kuma ya yi girma. Sai ya yi “tsaba ɗari-ɗari.” A ce irin da ya faɗi na alkama ne, wane irin ’ya’ya ne zai ba da? Shin ya fitar da ƙananan karar alkama ne? A’a, ya fitar da sabon iri wanda wataƙila zai yi girma. A wannan kwatancin, iri guda ne ya fitar da tsaba ɗari-ɗari. Ta yaya wannan fanni na kwatancin ya shafi hidimarmu?

Ta yaya muke jimrewa sa’ad da muke wa’azi? (Ka duba sakin layi na 11)

11. (a) Ta yaya kwatancin mai shuki yake da alaƙa da hidimarmu? (b) Ta yaya muke fitar da sabon iri?

11 Sa’ad da iyayenmu ko kuma wasu Shaidu suka koya mana game da Mulkin Allah, yana kamar sun shuka iri a ƙasa mai kyau. Sun yi farin ciki sosai sa’ad da muka amince da saƙon. Abin da suka shuka ya ci gaba da girma har ya yi ’ya’ya. Karar alkama da aka ambata ɗazu bai fitar  da sababbin kara ba, amma sabon iri. Hakazalika, ba ma yin sababbin almajirai, amma sabon iri na Mulkin. * Ta yaya muke yin hakan? A duk lokacin da muka yi wa’azi game da Mulkin Allah, yana kamar muna yaɗa irin da aka shuka a zuciyarmu. (Luk. 6:45; 8:1) Saboda haka, kwatancin nan ya koya mana cewa muddin mun ci gaba da yin shelar Mulkin Allah, muna “ba da amfani” da jimiri.

12. (a) Mene ne muka koya daga kwatancin mai shuki da kuma itacen inabi? (b) Ta yaya kwatancin ya shafe ka?

12 Mene ne muka koya daga kwatancin Yesu na mai shuki da kuma itacen inabi? Kwatancin ya koya mana cewa “ba da amfani” bai dangana ga yadda mutane suka saurare mu ba. Maimakon hakan, muna bukatar mu ci gaba da yin wa’azi. Bulus ya faɗi hakan sa’ad da ya ce: ‘Kowanne [mutum] zai sami ladansa bisa ga aikinsa.’ (1 Kor. 3:8) Za mu sami lada bisa aikin da muke yi, ba bisa sakamakon aikinmu ba. Wata mai suna Matilda da ta yi shekara 20 tana hidimar majagaba, ta ce: “Ina farin ciki sosai cewa Jehobah yana ba mu lada don ayyukanmu.”

YADDA ZA MU JIMRE YAYIN DA MUKE BA DA AMFANI

13, 14. Me Bulus ya ambata a littafin Romawa 10:​1, 2 da ya sa ya ci gaba da yi wa Yahudawa wa’azi ko da sun ƙi su saurare shi?

13 Mene ne zai taimaka mana mu jimre sa’ad da muke ba da amfani? Kamar yadda aka ambata ɗazu, Bulus ya yi sanyin gwiwa domin Yahudawa sun ƙi su saurari wa’azinsa. Duk da haka, Bulus bai daina yi musu wa’azi ba. Amma ya faɗi yadda yake ji a cikin wasiƙar da ya rubuta wa Kiristocin da ke Roma cewa: “Abin da na fi so fiye da kome shi ne Isra’ilawa su sami ceto. Addu’ar da nake yi wa Allah saboda su ke nan. Na dai shaida cewa suna da kishin bautar Allah, amma wannan kuwa ba tare da cikakken sani ba.” (Rom. 10:​1, 2) Me ya sa Bulus ya ci gaba da yin wa’azi?

14 Na farko, Bulus ya ce ya ci gaba da yi  wa Yahudawa wa’azi domin ‘abin da ya fi so’ ke nan. Hakika, yana son Yahudawa su sami ceto. (Rom. 11:​13, 14) Na biyu, Bulus ya yi addu’a ga Allah “saboda su.” Ya roƙi Allah ya taimaka musu su saurari saƙon Mulkin Allah. Na uku, Bulus ya daɗa cewa: “Suna da kishin bautar Allah.” Bulus ya ga cewa wasu mutane za su iya soma bauta wa Jehobah a nan gaba. Kuma ya san cewa waɗannan Yahudawa masu ƙwazo za su iya zama almajiran Yesu, yadda shi ma ya zama.

15. Ta yaya za mu iya yin koyi da Bulus? Ka ba da misalai.

15 Ta yaya za mu iya yin koyi da Bulus? Na ɗaya, muna bukatar mu riƙa neman mutanen da suke son “samun rai na har abada.” Na biyu, ya kamata mu roƙi Jehobah ya taimaka wa mutane su saurari wa’azin da muke yi. (A. M. 13:48; 16:14) Wata mai suna Silvana da ta yi kusan shekara 30 tana hidimar majagaba, ta ce: “Kafin na shiga wani gida a yankinmu, nakan yi addu’a ga Jehobah ya taimaka mini in kasance da ra’ayin da ya dace.” Ƙari ga haka, ya dace mu yi addu’a cewa mala’iku su taimaka mana mu sami mutanen da za su saurare mu. (Mat. 10:​11-13; R. Yar. 14:6) Wani mai suna Robert da ya yi fiye da shekara 30 yana hidimar majagaba, ya ce: “Ina farin ciki sosai cewa ina hidima tare da mala’iku da suka san abin da mutane suke fuskanta a rayuwa.” Na uku, ya kamata mu san cewa mutane za su iya soma bauta wa Jehobah a nan gaba. Wani dattijo mai suna Carl da ya yi baftisma fiye da shekara 50 yanzu, ya ce: “Nakan nemi wata alamar da ta nuna cewa mutumin yana so ya saurari saƙonmu. Wataƙila ta yadda ya yi murmushi ko kuma tambayar da ya yi.” Hakika, za mu iya yin koyi da Bulus ta wajen ba da amfani da jimiri.

“KADA KA NAƊA HANNUWANKA”

16, 17. (a) Wane darasi ne za mu iya koya daga abin da ke littafin Mai-Wa’azi 11:6? (b) Ka ba da misalin yadda wa’azinmu zai iya shafan waɗanda suke lura da abin da muke yi.

16 Ko da muna ganin kamar ba wanda yake saurarar mu, bai kamata mu manta cewa wa’azin da muke yi yana shafan rayukan mutane ba. (Karanta Mai-Wa’azi 11:6.) Hakika, mutane da yawa ba sa saurarar mu, amma suna lura da abin da muke yi. Sukan lura cewa muna ado da kyau, muna da halin kirki kuma mu masu fara’a ne. Da shigewar lokaci, halinmu zai sa wasu da ba sa son saƙonmu su canja ra’ayinsu. Abin da ya faru da Sergio da Olinda da aka ambata ɗazun ke nan.

17 Sergio ya ce: “Akwai wani lokaci da muka ɗan jima ba mu fita wa’azi ba domin muna rashin lafiya. Amma da muka dawo tashar da muke tsayawa, mutane sun tambaye mu, ‘Me ya faru da ku? Mun yi kewar ku.’ ” Olinda ta daɗa cewa cike da murmushi: “Direbobi sun ɗaga mana hannu kuma wasu suka ce da babbar murya, ‘Sannunku da aiki!’ Sun ma ce mu ba su mujallunmu.” Ma’auratan sun yi mamaki sa’ad da wani mutum ya zo wurin da suke wa’azi da amalanke kuma ya ba su kwandon furanni, ya gode musu don aikin da suke yi.

18. Me ya sa ka ƙuduri niyyar ci gaba da jimrewa sa’ad da kake wa’azi?

18 Hakika, idan ba mu ‘naɗa hannuwanmu’ ba ko kuma ba mu ƙi gaya wa mutane game da Mulkin Allah ba, muna yin aiki mai muhimmanci na yin “shaida ga dukan al’umma.” (Mat. 24:14) Ƙari ga haka, muna murna sosai domin mun san cewa muna sa Jehobah farin ciki. Jehobah yana ƙaunar dukan waɗanda “suka jimre suka ba da amfani”!

^ sakin layi na 2 Yesu ma ya ce yin wa’azi a “garinsa” yana da wuya. Duk marubutan littattafan Linjila guda huɗu sun faɗi hakan.​—Mat. 13:57; Mar. 6:4; Luk. 4:24; Yoh. 4:44.

^ sakin layi na 7 Ko da yake rassan da ke kwatancin nan yana nufin Kiristocin da za su je sama, amma dukan bayin Allah za su koyi darussa masu kyau daga kwatancin.

^ sakin layi na 9 Furucin nan “ba da amfani” yana iya nufin kasancewa da “halin da ruhun Allah yake haifar” da shi. A wannan talifin da kuma na gaba, za mu mai da hankali a kan yadda za mu riƙa “yabon” Allah, ta wajen yin wa’azi game da Mulkinsa.​—Gal. 5:​22, 23; Ibran. 13:15.

^ sakin layi na 11 A wasu wurare, Yesu ya yi amfani da misalan shuki da girbi don ya kwatanta aikin yin almajirai.​—Mat. 9:37; Yoh. 4:​35-38.