Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ku Sasanta Matsalolinku Cikin Kauna

Ku Sasanta Matsalolinku Cikin Kauna

“Ku zauna lafiya kuma da junanku.”—MAR. 9:50.

WAƘOƘI: 39, 77

1, 2. Waɗanne jayayya ko kuma saɓani tsakanin mutane ne aka ambata a cikin littafin Farawa, kuma ta yaya sanin hakan zai taimaka mana?

KA TAƁA yin tunani game da jayayya ko saɓani da ya faru tsakanin mutanen da aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki? Ga wasu misalai daga cikin surori na farko na littafin Farawa. Kayinu ya kashe Habila (Far. 4:3-8); Lamech ya kashe wani mutumin da ya buge shi (Far. 4:23); makiyayan Ibrahim (Abram) da na Lutu sun yi rigima (Far. 13:5-7); Hajaratu ta raina Saratu kuma hakan ya sa Saratu ta yi fushi da Ibrahim. (Far. 16:3-6) Ƙari ga haka, Littafi Mai Tsarki ya ce Isma’ila zai yi gāba da kowane mutum, kuma kowane mutum zai yi gāba da shi.—Far. 16:12.

2 Me ya sa Littafi Mai Tsarki ya ambaci waɗannan jayayyan ko kuma saɓani? Hakan zai taimaka mana mu san cewa yana da muhimmanci mu zauna lafiya da juna. Ƙari ga haka, waɗannan misalan za su taimaka mana mun san yadda za mu magance matsaloli. Za mu amfana idan muka karanta labaran Littafi Mai Tsarki game da mutanen da suka yi jayayya da juna. Muna koyan darasi daga yadda suka magance waɗannan matsalolin kuma muna amfani da darussan sa’ad da muka sami kanmu a irin wannan yanayin. Hakika, waɗannan abubuwan za su taimaka mana mu san yadda za mu zauna lafiya da mutane.—Rom. 15:4.

3. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

3 Za mu tattauna dalilin da ya sa ya kamata bayin Jehobah su  magance matsalolin da ke tsakaninsu da kuma yadda za su iya yin hakan. Ƙari ga haka, za mu tattauna ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da za su taimaka mana mu magance irin waɗannan matsalolin don mu kasance da dangantaka mai kyau da maƙwabtanmu da kuma Jehobah Allah.

ME YA BAYIN ALLAH SUKE BUKATA SU SASANTA MATSALOLINSU?

4. Wane irin hali ne ya zama ruwan dare a duniya, kuma mene ne sakamakon?

4 Shaiɗan ne tushin saɓani da kuma jayayya da ’yan Adam suke fama da su a yau. Ya yi da’awa a lambun Adnin cewa kowane mutum zai iya yanke shawara game da nagarta da mugunta ba tare da bin ja-gorar Allah ba, kuma ya rinjayi ’yan Adam su yi hakan. (Far. 3:1-5) Idan muka yi la’akari da abubuwan da suke faruwa a duniya a yau, za mu ga cewa irin wannan halin yana jawo matsaloli. Mutane da yawa suna ganin cewa suna da ’yanci su yanke shawara game da nagarta da mugunta kuma suna fahariya da girman kai da kuma kishi. Duk wanda yake yin irin wannan tunanin ya amince da abin da Shaiɗan ya yi da’awa cewa ya dace mu bi ra’ayinmu ko da yin hakan zai shafi wasu. Irin wannan halin son kai yana hadassa jayayya. Ya kamata mu tuna cewa “mutum mai-fushi ya kan tada husuma, mai-hasala kuma yana da yawan laifofi.”—Mis. 29:22.

5. Mene ne Yesu ya koya wa mutane game da yadda za su sasanta rigima?

5 Akasin haka, Yesu ya koya wa mutane cewa su yi sulhu, ko da yin hakan zai kawo musu illa. Yesu ya ba da shawarwari masu kyau game da yadda za mu bi da rigima ko kuma jayayya a huɗubar da ya bayar a kan dutse. Alal misali, ya shawarci almajiransa su kasance da tawali’u, su yi zaman lafiya da mutane kuma su guje wa duk wani abin da zai jawo ɓacin rai. Ƙari ga haka, ya umurce su su sasanta jayayya ba tare da ɓata lokaci ba kuma su ƙaunaci maƙiyansu.—Mat. 5:5, 9, 22, 25, 44.

6, 7. (a) Me ya sa yake da muhimmanci ka magance matsala tsakaninka da mutane ba tare da ɓata lokaci ba? (b) Waɗanne tambayoyi ne ya kamata dukan bayin Jehobah su yi wa kansu? 

6 Hidimomin da muke yi a bautar Allah, wato yin addu’a da halartan taro da fita wa’azi da kuma wasu abubuwan da suka shafi ibada za su zama aikin banza idan muka ƙi sasantawa da mutane. (Mar. 11:25) Ba za mu kasance da dangantaka mai kyau da Allah ba idan ba ma gafarta wa mutane laifuffukan da suka yi mana.—Karanta Luka 11:4; Afisawa 4:32.

7 Kowane Kirista yana bukatar ya yi tunani da kyau game da yadda zai riƙa gafarta wa mutane kuma ya yi zaman lafiya da su. Shin kana saurin gafarta wa ’yan’uwa masu bi? Kana farin cikin yin tarayya da su ko da sun ɓata maka rai? Jehobah yana son bayinsa su riƙa gafarta wa juna. Idan ka ga cewa kana bukatar yin gyara a wannan fannin, ya kamata ka yi addu’a ga Jehobah don ya taimake ka ka yi wannan gyarar. Ubanmu wanda yake sama zai saurari irin wannan addu’a da aka yi da zuciya ɗaya kuma ya amsa.—1 Yoh. 5:14, 15.

ZA KA IYA YAFE LAIFIN DA WANI YA YI MAKA?

8, 9. Mene ne ya kamata mu yi idan aka ɓata mana rai?

8 Da yake dukanmu ajizai ne, wani zai iya yin ko faɗi abin da zai ɓata maka rai. Ba za mu iya guje wa irin wannan yanayin ba. (M. Wa. 7:20; Mat. 18:7) Idan hakan ya faru, mene ne za ka yi? Ka yi la’akari da wani abin da ya taɓa faruwa: A wani liyafa da wasu Shaidun Jehobah suka halarta, wata ’yar’uwa ta gai da wasu ’yan’uwa maza biyu. Ɗaya daga cikinsu yana ganin ba ta gaishe su yadda ya dace ba. Sa’ad da  ’yan’uwa biyun suke tare, wanda ya ɓata rai a cikinsu ya soma kūshe ’yar’uwan don abin da ta yi da kuma faɗa. Amma ɗayan ya tuna masa cewa ta yi shekaru 40 tana bauta wa Jehobah a mawuyacin yanayi kuma ya tabbata cewa ba ta da wani mugun anniya. Ɗan’uwan da ya yi fushi ya sake nazari a kan batun, sai ya ce: “Gaskiyar ka.” Saboda haka, ba su sake ta da zancen ba.

9 Wane darasi ne za mu koya daga wannan labarin? Idan wani ya ɓata mana rai, muna da zaɓi game da yadda za mu bi da yanayin. Mutum mai ƙauna yana gafarta wa mutane. (Karanta Misalai 10:12; 1 Bitrus 4:8.) Mutum mai “ƙyale laifi” yana da daraja a gaban Jehobah. (Mis. 19:11; M. Wa. 7:9) Saboda haka, tambaya ta farko da mutum zai iya yi wa kansa sa’ad da wani ya ɓata masa rai ita ce, ‘Zan iya yafe wannan laifin? Shin ina bukata in ci gaba da tunani a kan wannan batun?’

10. (a) Yaya wata ’yar’uwa ta ji da farko sa’ad da wasu suka yi sūkar ta? (b) Wace shawarar Littafi Mai Tsarki ce ta taimaka wa ’yar’uwar ta kasance da kwanciyar hankali?

10 Idan wani ya yi sūkar mu, bi da yanayin bai da sauƙi. Bari mu yi la’akari da wata ’yar’uwa mai suna Lucy. [1] Wasu sun yi maganganun da bai dace ba game da hidimarta da kuma yadda yake amfani da lokacinta. Abin ya dami Lucy sosai, sai ta nemi shawara daga wasu ’yan’uwa da suka manyanta. Ta ce: “Shawarar da suka ba ni daga Littafi Mai Tsarki ta taimaka mini in kasance da ra’ayin da ya dace game da abin da mutane suka faɗa kuma in mai da hankali ga Jehobah don ra’ayinsa ne ya fi muhimmanci.” Ta sami ƙarfafa sa’ad da ta karanta Matta 6:1-4. (Karanta.) Waɗannan ayoyin sun sa ta tuna cewa faranta wa Jehobah rai shi ne ya fi muhimmanci. Ta daɗa cewa: “Ko da wasu suna yin maganganun da ba su dace ba game da hidimata, ina farin ciki, don na san cewa ina yin iya ƙoƙarina don in sami albarkar Jehobah.” Bayan Lucy ta yi wannan tunanin, sai ta daina damuwa game da maganganun da mutane suka yi game da ita.

YADDA ZA A BI DA LAIFUFFUKA MASU TSANANI

11, 12. (a) Wane mataki ne ya kamata Kirista ya ɗauka idan ya tabbata cewa ɗan’uwansa “yana da wani abu game da” shi? (b) Wane darasi za mu iya koya daga yadda Ibrahim ya sasanta wata matsala? (Ka duba hoton da ke shafi na 3.)

11 “Dukanmu mukan yi tuntuɓe” sau da yawa. (Yaƙ. 3:2) Alal misali, a ce ka ji cewa wani abin da ka yi ko kuma faɗa ya ɓata wa wani ɗan’uwa rai sosai. Mene ne ya kamata ka yi? Yesu ya ce: ‘Idan . . . kana cikin miƙa baikonka a wurin bagadi, can ka tuna ɗan’uwanka yana da wani abu game da kai, sai ka bar baikonka can a gaban bagadi, ka yi tafiyarka, ka sulhuntu da ɗan’uwanka tukuna, kāna ka zo ka miƙa baikonka.’ (Mat. 5:23, 24) Saboda haka, ka je ka sami ɗan’uwanka don ku tattauna. Maƙasudinka shi ne ku yi sulhu, ba ka nuna masa cewa shi ne mai laifi ba. Zaman lafiya da ’yan’uwa masu bi shi ne abin da ya fi muhimmanci.

12 Littafi Mai Tsarki ya nuna mana yadda za mu magance matsalar da za ta iya tasowa tsakanin ’yan’uwa. Alal misali, Ibrahim da Lutu sun mallaki dabbobi da yawa. Hakan ya sa makiyayansu rigima a kan filin kiwo. Da yake Ibrahim yana so su yi zaman lafiya, sai ya ba wa Lutu damar zaɓan filin da shi da ’yan gidansa za su zauna. (Far. 13:1, 2, 5-9) Ibrahim ya kafa mana misali mai kyau don bai nuna son kai ba, amma ya biɗi zaman lafiya da mutane. Shin ya rasa wani abu ne don wannan hali mai kyau da ya nuna? A’a. Ba da daɗewa ba bayan haka, Jehobah ya yi wa Ibrahim alkawari cewa zai albarkace shi sosai. (Far. 13: 14-17) Hakan ya nuna mana cewa Jehobah zai albarkace mu ko da mun rasa wani abu saboda bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki kuma muka yi sulhu cikin ƙauna. [2]

13. Mene ne wani mai kula da taron yanki ya yi sa’ad da aka yi masa baƙar magana kuma me za mu iya koya daga misalinsa?

13 Ka yi la’akari da abin da ya faru kwanan baya. Sa’ad da wani sabon mai kula da taron yanki ya kira wani ɗan’uwa kuma ya tambaye shi ko zai iya yin wani aiki a taron, sai ɗan’uwan ya yi masa baƙar magana kuma ya kashe wayar. Ya yi hakan ne saboda saɓani da suka samu da mai kula da taron yanki na dā. Sabon mai kula da taron yanki bai yi fushi a kan abin da ɗan’uwan ya yi ba amma bai bar maganar haka ba. Bayan awa guda, sai ya sake kiran ɗan’uwan kuma ya gaya masa cewa suna bukatar su magance matsalar da ke tsakaninsa da mai kula da taron yanki na dā. Sati ɗaya bayan haka, waɗannan ’yan’uwa biyu sun haɗu a wata Majami’ar Mulki don su tattauna batun. Bayan sun yi addu’a, sai suka yi magana na awa ɗaya. Hakan ya sa ɗan’uwan da aka yi masa laifi ya faɗi abin da ya faru da shi. Mai kula da taron yanki ya saurari wannan ɗan’uwan sosai kuma ya ba shi wasu shawarwari daga Littafi Mai Tsarki. Hakan ya sa ’yan’uwan sun sasanta kuma suka yi aiki tare a taron. Ɗan’uwan ya yi farin ciki sosai cewa wannan mai kula da taron yanki ya bi da shi cikin ƙauna.

LOKACIN DA YA KAMATA KA GAYA WA DATTAWA

14, 15. (a) A wane lokaci ne ya kamata mu bi shawarar da ke cikin littafin Matta 18:15-17? (b) Waɗanne matakai uku ne Yesu ya ambata, kuma sa’ad da muke bin waɗannan matakan, wane buri ne ya kamata mu kasance da shi?

14 Ya kamata Kiristoci su sasanta yawancin matsalolin da ke tsakaninsu da kansu. Amma, Yesu ya ambata cewa da akwai wasu matsalolin da ake bukata a gaya  wa dattawa. (Karanta Matta 18:15-17.) Mene ne za a yi idan wanda yake da laifi ya ƙi ya saurari ɗan’uwansa da shaidun da aka kira da kuma dattawa? Za a bi da shi “kamar Ba-al’ummi ko mai-karɓan haraji.” A yau, za mu ce ya kamata a yi masa yankan zumunci. Idan aka ɗauki wannan matakin, ya nuna cewa wannan “zunubin” ba ƙaramin abu ba ne. A maimakon haka, (1) zunubi ne da mutane biyu da suke rigima za su iya sasantawa da kansu amma (2) idan ba su sasanta ba, zai zama zunubi mai tsanani da zai iya sa a yi wa mutum yankan zumunci. Irin wannan zunubin ya ƙunshi zamba ko kuma ɓata sunan mutum. A irin wannan yanayin ne za a bi waɗannan matakai uku da Yesu ya ambata. Amma bai ƙunshi zunubi kamar zina da luwaɗi da ridda da bautar gumaka da wasu zunubai masu tsanani da ake bukata a gaya wa dattawan ikilisiya ba tare da ɓata lokaci ba.

A wani lokaci, zai dace ka tattauna da ɗan’uwanka sau da sau don ku sulhunta (Ka duba sakin layi na 15)

15 Yesu ya ba da wannan shawarar saboda mu taimaka wa ɗan’uwanmu don muna ƙaunar sa. (Mat. 18:12-14) Da farko, ya kamata a yi ƙoƙarin sasanta wata matsala ba tare da mutane su ji game da batun ba. Zai dace ka tattauna batun da mai laifin ba sau ɗaya ba. Idan ka ɗauki wannan matakan kuma ba ku sasanta ba har ila, sai ka yi magana da wanda yake da laifi a gaban shaidun ko kuma wasu mutanen da za su taimaka don a tabbatar da laifin. Idan kuka sasanta ta wurin taimakon su, hakan yana nufin cewa “ka ribato ɗan’uwanka.” Za a gaya wa dattawa ne kawai idan ba a iya sasanta matsalar ba duk da ƙoƙarin da aka yi don a taimaki wanda yake da laifi.

16. Me ya nuna cewa bin shawarar Yesu yana da amfani kuma hakan ya nuna cewa muna ƙaunar ɗan’uwanmu?

16 Ba a cika samun irin yanayin da zai sa a bi dukan matakai da aka ambata a Matta 18:15-17. Hakan abin ƙarfafa ne, don ya nuna cewa ana sasantawa kafin yanayin ya kai wanda zai sa a yi wa mai laifin yankan zumunci. A yawancin lokaci, mai laifin yakan fahimci kuskurensa kuma ya yi gyara. Wanda aka yi masa laifi zai iya gani cewa gafartawa ya fi a maimakon ya ci gaba da nanata laifin da ɗan’uwansa ya yi. Ko yaya yanayin yake, abin da Yesu ya faɗa ya nuna cewa bai kamata dattawa su yi saurin saka baki a wani saɓani tsakanin ’yan’uwa ba. Dattawa za su saka baki ne kawai idan an ɗauki mataki na farko da na biyu kuma idan za a iya ba da hujja cewa an yi rashin adalci.

17. Wace albarka ce za mu samu idan muka “biɗi” zaman lafiya da juna?

17 Da yake muna rayuwa ne a zamanin Shaiɗan, za mu ci gaba da yi wa juna laifi don mu ajizai ne. Shi ya sa almajiri Yakubu ya ce: “Idan wani bai yi tuntuɓe a wajen magana ba, wannan cikakken mutum ne, mai-ikon sarafta dukan jiki.” (Yaƙ. 3:2) Idan muna so mu sasanta matsalolin da ke tsakaninmu, wajibi ne mu “biɗi” zaman lafiya da juna. (Zab. 34:14) A matsayinmu na masu son zaman lafiya, za mu kasance da dangantaka ta kud da kud da ’yan’uwanmu masu bi kuma haɗin kai zai ƙaru a cikin ikilisiya. (Zab. 133:1-3) Mafi muhimmanci, za mu kasance da dangantaka ta kud da kud da Jehobah, “Allah na salama.” (Rom. 15:33) Wannan shi ne albarkar da waɗanda suke sasanta jayayya cikin ƙauna za su samu.

^ [1] (sakin layi na 10) An canja sunan.

^ [2] (sakin layi na 12) Wasu da suka magance matsaloli cikin lumana sun haɗa da Yakubu da Isuwa (Far. 27:41-45; 33:1-11); Yusuf da ’yan’uwansa (Far. 45:1-15); da kuma Gideon da mutanen Ifraimu. (Alƙa. 8:1-3) Wataƙila, za ka iya tuna da wasu misalai da aka rubuta a cikin Littafi Mai Tsarki.