Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 TALIFIN NAZARI NA 10

Kauna ga Jehobah Za Ta Sa Mu Yi Baftisma

Kauna ga Jehobah Za Ta Sa Mu Yi Baftisma

“Mene ne zai hana a yi mini baftisma?”​—A. M. 8:36.

WAƘA TA 37 Mu Riƙa Bauta wa Jehobah da Dukan Zuciya

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1-2. Kamar yadda aka nuna a Ayyukan Manzanni 8:​27-31 da 35-38, mene ne ya motsa wani Bahabashe ya yi baftisma?

KANA so ka yi baftisma ne don ka zama almajirin Kristi? Ƙauna da godiya sun sa mutane da yawa sun yi baftisma. Ka yi la’akari da misalin wani da ke yi wa sarauniyar Habasha hidima.

2 Bahabashen ya yi baftisma nan da nan da ya koya daga Nassosi cewa ya dace ya yi hakan. (Karanta Ayyukan Manzanni 8:​27-31, 35, 36, 38.) Mene ne ya motsa shi? Babu shakka, yana daraja Kalmar Allah domin yana karanta wasu ayoyi daga littafin Ishaya yayin da yake kan karusarsa zai koma gida. Kuma sa’ad da suka tattauna da Filibbus, mutumin ya nuna godiya don abin da Yesu ya yi masa. Amma me ya sa ma’aikacin ya je Urushalima? Domin yana ƙaunar Jehobah. Ta yaya muka sani? Ya je Urushalima ne don ya bauta wa Jehobah. Mai yiwuwa mutumin ya daina bin addininsa kuma ya soma bin al’ummar da ke bauta wa Allah na gaskiya. Ya tsai da shawara ya ɗauki wani mataki mai muhimmanci domin yana ƙaunar Jehobah. Ya yi baftisma kuma ya zama almajirin Kristi.​—Mat. 28:19.

3. Mene ne zai iya hana mutum yin baftisma? (Ka duba akwatin nan “ Yaya Yanayin Zuciyarka?”)

3 Ƙaunarka ga Jehobah za ta iya sa ka yin baftisma, kuma ƙauna za ta iya hana ka yin hakan. Ta yaya? Ga wasu misalai. Kana ƙaunar iyalanka da abokanka da ba sa bauta wa Jehobah. Hakan yana iya sa ka damu cewa idan ka yi baftisma, za su tsane ka. (Mat. 10:37) Ko kuma ƙila kana son halayen da ka san cewa Allah ba ya so, kuma daina  halayen yana maka wuya. (Zab. 97:10) Wataƙila ka yi girma kana yin bukukuwan da ke da alaƙa da addinin ƙarya, kuma kana farin ciki a duk lokacin da ka tuna yadda ka yi waɗannan bukukuwan a dā. Saboda haka, yana iya yi maka wuya ka daina bin al’adu da ke sa Jehobah baƙin ciki. (1 Kor. 10:​20, 21) Kana bukatar ka amsa tambayar nan, “Mene ne ko kuma waye ne na fi ƙauna?”

ƘAUNA MAFI MUHIMMANCI

4. Wane dalili mafi muhimmanci ne zai sa ka yi baftisma?

4 Kana da abubuwa da yawa masu kyau da kake so kuma kake nuna godiya domin su. Alal misali, kafin ka soma nazari da Shaidun Jehobah, wataƙila kana son ji game da Allah da kuma alherinsa a gare mu. Yanzu da ka san Shaidun Jehobah, kana iya jin daɗin yin cuɗanya da su. Amma son waɗannan abubuwan ba za su sa ka yi alkawarin bauta wa Jehobah kuma ka yi baftisma ba. Dalili mafi muhimmanci da zai sa ka yi baftisma shi ne don kana ƙaunar Jehobah. Idan kana ƙaunar Jehobah fiye da kome, ba za ka bar kome ko kuma wani ya hana ka bauta masa ba. Ƙaunarka ga Jehobah za ta sa ka yi baftisma kuma za ta taimaka maka ka kasance da aminci bayan ka yi baftisma.

5. Mene ne za mu tattauna a talifin nan?

5 Yesu ya ce wajibi ne mu ƙaunaci Jehobah da dukan zuciyarmu da ranmu da hankalinmu da kuma ƙarfinmu. (Mar. 12:30) Ta yaya za ka ƙaunaci Jehobah kuma ka daraja shi sosai? Idan muka yi tunanin yadda Jehobah yake ƙaunar mu, hakan zai sa mu ƙaunace shi. (1 Yoh. 4:19) A talifin nan, za mu tattauna shawarwari da yawa da za su taimaka maka ka yi hakan. Kuma idan ka soma ƙaunar Jehobah sosai, waɗanne abubuwa ne za su biyo baya? *

6. Kamar yadda Romawa 1:20 ta nuna, wace hanya ɗaya ce za ka iya koya game da Jehobah?

6 Ka koya game da Jehobah daga halittunsa. (Karanta Romawa 1:20; R. Yar. 4:11) Ka yi tunani a kan shuke-shuke da dabbobi da Jehobah ya halitta da yadda suka nuna cewa shi mai hikima ne sosai. Ka lura da yadda aka halicce ka a hanya mai ban-mamaki. (Zab. 139:14) Kuma ka yi tunanin irin ƙarfin da Jehobah ya saka a rana. Rana tana cikin biliyoyin taurari da Jehobah ya halitta. * (Isha. 40:26) Za ka ƙara daraja Jehobah sa’ad da ka yi tunani a kan abubuwan da ya yi. Yana da muhimmanci mu san cewa Jehobah mai hikima ne kuma yana da iko sosai. Amma don ka ƙarfafa ƙaunarka ga Jehobah kuma ka zama abokinsa na kud da kud kana bukatar ka san shi sosai.

7. Don ka ƙaunaci Jehobah sosai, me ya kamata ka gaskata game da shi?

7 Kana bukatar ka kasance da tabbaci cewa Jehobah yana ƙaunar ka sosai. Yana maka wuya ka gaskata cewa Mahaliccin sama da duniya yana kula da kai? Idan haka ne, ka tuna cewa Jehobah “bai yi nesa da kowannenmu ba.” (A. M. 17:​26-28) Yana ‘bincika kowace zuciya’ kuma ya yi maka alkawari yadda Dauda ya yi wa Sulemanu cewa “idan ka neme shi, zai sa ka same shi.” (1 Tar. 28:9) Hakika, dalilin da ya sa kake nazarin Littafi Mai Tsarki  yanzu shi ne domin Jehobah ya ‘jawo ka wurinsa.’ (Irm. 31:3) Yayin da ka fahimci dukan abubuwan da Jehobah ya yi maka, za ka ƙara ƙaunar sa.

8. Ta yaya za ka nuna cewa kana godiya don alherin Jehobah?

8 Hanya ɗaya da za ka nuna cewa kana godiya don alherin Jehobah ita ce ta yin addu’a. Za ka ƙara ƙaunar Jehobah yayin da kake gaya masa damuwarka kuma ka gode masa don dukan abubuwan da ya yi maka. Kuma abokantakarku za ta yi danƙo yayin da kake ganin yadda yake amsa addu’o’inka. (Zab. 116:1) Za ka kasance da tabbaci cewa ya fahimce ka. Amma don ka kusaci Jehobah, kana bukatar ka san abubuwan da yake so da waɗanda ba ya so da kuma abin da yake bukata a gare ka. Hanya ɗaya da za ka san waɗannan abubuwan ita ce ta yin nazarin Kalmar Allah.

Yin nazarin Littafi Mai Tsarki ne hanya mafi kyau na kusantar Allah da kuma sanin abin da yake so a gare mu (Ka duba sakin layi na 9) *

9. Ta yaya za ka nuna cewa kana daraja Kalmar Allah?

9 Ka nuna kana daraja Kalmar Allah. A Littafi Mai Tsarki ne kaɗai za mu san gaskiya game da Jehobah da kuma nufinsa. Za ka nuna cewa kana godiya don Kalmar Allah ta wajen karanta ta kowace rana da yin shiri kafin ku yi nazari da kuma yin amfani da abubuwan da ka koya. (Zab. 119:​97, 99; Yoh. 17:17) Shin ka keɓe lokacin karanta Littafi Mai Tsarki kuwa? Kana karanta Littafi Mai Tsarki a kowace rana?

10. Wane abu ne ya sa Littafi Mai Tsarki ya yi dabam?

10 Wani abu kuma da ya sa Littafi Mai Tsarki ya yi dabam da sauran littattafai shi ne domin yana ɗauke da bayanai daga mutanen da suka ga Yesu. Shi ne kaɗai littafin da ya bayyana abin da Yesu ya yi dominka. Yayin da kake koyan abubuwan da Yesu ya yi da kuma faɗa, za ka so ka ƙulla abokantaka da shi.

11. Mene ne zai taimaka maka ka daɗa ƙaunar Jehobah?

11 Idan ka ƙaunaci Yesu, ƙaunarka ga Jehobah za ta daɗa ƙarfi. Me ya sa? Domin  Yesu yana yin koyi da halayen Ubansa sosai. (Yoh. 14:9) Don haka, yayin da kake koya game da Yesu, za ka daraja Jehobah sosai. Ka yi tunanin yadda Yesu ya tausaya wa talakawa da marasa lafiya da kuma marasa ƙarfi. Ƙari ga haka, ka yi tunanin shawarar da ya ba ka da kuma yadda za ka amfana idan kana bin shawarar.​—Mat. 5:​1-11; 7:​24-27.

12. Mene ne za ka yi yayin da kake koya game da Yesu?

12 Ƙaunarka ga Yesu za ta yi ƙarfi idan ka yi tunani sosai a kan fansar da ya yi don a gafarta zunubanka. (Mat. 20:28) Idan ka fahimci cewa Yesu ya ba da ransa dominka, hakan zai motsa ka ka tuba kuma ka roƙi Jehobah ya gafarta zunubanka. (A. M. 3:​19, 20; 1 Yoh. 1:9) Da zarar ka soma ƙaunar Jehobah da kuma Yesu, za ka so ka riƙa kasancewa da mutanen da suke ƙaunar sa.

13. Wane tanadi ne Jehobah ya yi maka?

13 Ka ƙaunaci mutanen da ke ƙaunar Jehobah. Iyalanka da kuma abokanka da ba sa bauta wa Jehobah ba za su fahimci dalilin da ya sa ka yi alkawarin bauta wa Jehobah ba. Suna iya tsananta maka. Jehobah zai taimaka maka ta wajen sa ’yan’uwa a ikilisiya su zama iyalinka. Idan ka kusaci ’yan’uwa, za su nuna maka ƙauna kuma su taimaka maka. (Mar. 10:​29, 30; Ibran. 10:​24, 25) Da shigewar lokaci, iyalanka suna iya soma bauta wa Jehobah da kuma bin ƙa’idodinsa.​—1 Bit. 2:12.

14. Kamar yadda 1 Yohanna 5:3 ta nuna, mene ne ka koya game da ƙa’idodin Jehobah?

14 Ka daraja ƙa’idodin Jehobah kuma ka yi amfani da su. Wataƙila kafin ka san Jehobah kana da naka ƙa’idodin, amma yanzu ka fahimci cewa ƙa’idodin Jehobah sun fi dacewa. (Zab. 1:​1-3; karanta 1 Yohanna 5:3.) Ka yi tunani a kan ƙa’idar Littafi Mai Tsarki ga magidanta da mata da iyaye da kuma yara. (Afis. 5:22–6:4) Iyalinka suna farin ciki domin kana bin wannan ƙa’idar? Sa’ad da ka bi umurnin Jehobah game da zaɓan abokan kirki, ka inganta halayenka? Kana farin ciki? (K. Mag. 13:20; 1 Kor. 15:33) Babu shakka, amsar ka e ce.

15. Mene ne za ka yi idan kana neman taimako don bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki?

15 A wasu lokuta, yana iya yi maka wuya ka yi amfani da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da kake koya. Shi ya sa Jehobah yake amfani da ƙungiyarsa don ya tanada maka abubuwan da za su taimake ka ka san abin da ya dace da wanda bai dace ba. (Ibran. 5:​13, 14) Idan ka karanta da kuma nazarta waɗannan abubuwan, za ka ga yadda za ka yi amfani da su a rayuwarka, kuma za ka so ƙungiyar Jehobah.

16. Yaya Jehobah ya tsara mutanensa?

16 Ka so ƙungiyar Jehobah kuma ka goyi bayanta. Jehobah ya tsara mutanensa a ikilisiya kuma Ɗansa Yesu ne yake yin ja-goranci. (Afis. 1:22; 5:23) Yesu ya naɗa ƙaramin rukunin maza shafaffu don su yi ja-goranci a aikin da yake so a yi a yau. Ya kira wannan rukunin “bawan nan mai aminci, mai hikima,” kuma suna ɗaukan hakkinsu na kāre da taimaka maka ka kusaci Jehobah da muhimmanci sosai. (Mat. 24:​45-47) Ɗaya daga cikin hanyoyin da bawan nan mai aminci yake kula da kai ita ce ta wajen tabbatar da cewa an naɗa dattawa don su kāre ka da kuma yi maka ja-goranci. (Isha. 32:​1, 2; Ibran. 13:17; 1 Bit. 5:​2, 3) Dattawa suna iya ƙoƙarinsu don su ƙarfafa ka kuma su taimaka  maka ka kusaci Jehobah. Amma abu mafi muhimmanci da suke yi shi ne su taimaka maka ka koya wa mutane game da Jehobah.​—Afis. 4:​11-13.

17. Kamar yadda Romawa 10:​10, 13, 14 suka nuna, me ya sa muke gaya wa mutane game da Jehobah?

17 Ka taimaka wa mutane su soma ƙaunar Jehobah. Yesu ya gaya wa mabiyansa cewa su riƙa yin wa’azi. (Mat. 28:​19, 20) Muna iya bin wannan umurnin domin mun san ya kamata mu yi hakan. Amma yayin da kake ƙara ƙaunar Jehobah, za ka kasance da irin ra’ayin manzo Bitrus da Yohanna da suka ce: “Ba za mu iya yin shiru a kan abin da muka ji, muka kuma gani ba.” (A. M. 4:20) Za mu yi farin ciki matuƙa idan muka taimaka ma wani ya ƙaunaci Jehobah. Babu shakka, Filibbus ya yi farin ciki sosai sa’ad da ya taimaka wa Bahabashen ya koyi gaskiya kuma ya yi baftisma! Idan ka yi koyi da Filibbus kuma ka yi wa’azi yadda Yesu ya umurce mu, za ka nuna cewa kana so ka zama Mashaidin Jehobah. (Karanta Romawa 10:​10, 13, 14.) A lokacin, za ka yi irin tambayar da Bahabashen ya yi cewa: “Mene ne zai hana a yi mini baftisma?”​—A. M. 8:36.

18. Mene ne za a tattauna a talifi na gaba?

18 Za ka tsai da shawara mafi muhimmanci a rayuwarka sa’ad da ka yanke shawarar yin baftisma. Domin shawara ce mai muhimmanci, kana bukatar ka yi tunani sosai game da abin da yin baftisma yake nufi. Mene ne kake bukatar ka sani game da baftisma? Mene ne kake bukatar ka yi kafin ka yi baftisma da kuma bayan hakan? Za a amsa waɗannan tambayoyi a talifi na gaba.

WAƘA TA 2 Jehobah Ne Sunanka

^ sakin layi na 5 Wasu da suke ƙaunar Jehobah ba su tabbata ko suna shirye su yi baftisma a matsayin Shaidun Jehobah ba. Idan kana jin hakan, wannan talifin zai taimaka maka ka bincika wasu abubuwa da za su taimaka maka ka yi baftisma.

^ sakin layi na 5 Dukanmu mun bambanta, saboda haka, wasu za su bi wani tsari sa’ad da suke bin shawarwari da aka ambata a wannan talifin.

^ sakin layi na 6 Ka duba talifofin nan Halittar Sa Aka Yi? da ake wallafawa a dandalin jw.org da manhajar JW Library.

^ sakin layi na 61 BAYANI A KAN HOTO: Wata ’yar’uwa tana ba wata matashiya warƙa a kasuwa.