Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Kana Amfani da Abubuwan da Aka Rubuta Kuwa?

Kana Amfani da Abubuwan da Aka Rubuta Kuwa?

“Waɗannan al’amura . . . an rubuta su domin gargaɗi garemu, mu waɗanda matuƙan zamanu sun zo a kanmu.”1 KOR. 10:11.

WAƘOƘI: 11, 61

1, 2. Me ya sa za mu tattauna misalan sarakunan Yahuda guda huɗu?

IDAN ka ga cewa wani ya zame kuma ya faɗi, babu shakka za ka mai da hankali sosai idan kana bin wannan hanyar, ko ba haka ba? Hakazalika, yin la’akari da kuskuren da wasu suka yi zai taimaka mana mu guji yin irin waɗannan kura-kuran. Ƙari ga haka, zai taimaka mana a ibadarmu ga Jehobah. Alal misali, za mu koyi darussa daga kuskuren wasu har da waɗanda aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki.

2 Sarakunan Yahuda guda huɗu da muka tattauna a talifin da ya gabata sun bauta wa Jehobah da zuciya ɗaya. Duk da haka, sun yi kura-kurai masu tsanani. Mene ne za mu iya koya daga abin da ya faru da su, kuma yaya za mu guji kuskuren da suka yi? Yin bimbini a kan waɗannan misalan zai taimaka mana mu amfana daga abubuwan da aka rubuta a dā dominmu.Karanta Romawa 15:4.

BIN RA’AYIN MUTANE ZAI JAWO MANA BALA’I

3-5. (a) Ko da yake Asa ya miƙa zuciyarsa gaba ɗaya ga Jehobah, wace wahala ce ya sha? (b) Me ya sa Asa ya dogara ga mutane sa’ad da sarki Baasha ya kai wa Yahuda hari?

3 Za mu fara ne da Asa kuma mu ga yadda Kalmar Allah za  ta taimaka mana. Asa ya dogara ga Jehobah sa’ad da Habashawa miliyan ɗaya suka kai wa Yahuda hari, amma bai yi hakan ba sa’ad da Baasha sarkin Isra’ila ya soma gina katangar Ramah don ya kai wa Yahuda hari. Kuma Ramah wani birni ne da ke kusa da inda Asa yake sarauta. (2 Laba. 16:1-3) Bayan hakan, Asa ya dogara ga kansa kuma ya yi yarjejeniya da Ben-hadad Sarkin Suriya don ya yaƙi Baasha. Asa ya yi nasara kuwa? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Sa’anda Baasha ya ji wannan, ya bar ginin Ramah, ya fāsa aikinsa.” (2 Laba. 16:5) Wataƙila Asa yana ganin ya tsai da shawara mai kyau!

4 Amma, mene ne ra’ayin Jehobah game da matakin da Asa ya ɗauka? Allah ya tura annabinsa Hanani ya yi wa Asa gyara don bai dogara ga Allah ba. (Karanta 2 Labarbaru 16:7-9.) Hanani ya gaya masa: “Daga nan gaba za ka sha yaƙi.” Ko da yake Asa ya ƙwato birnin Ramah, amma a duk sarautarsa, shi da mutanensa sun yi ta yaƙi.

5 A talifin da ya gabata, Allah ya ce Asa ya bauta masa da zuciya ɗaya. (1 Sar. 15:14) A gaban Allah, Asa mai ibada ne sosai kuma ya yi abin da Jehobah yake so. Duk da haka, ya sha wahala don shawara marar kyau da ya tsai da. Me ya sa Asa ya dogara ga kansa da kuma sarki Ben-hadad maimakon Jehobah? Wataƙila ya yi tunani cewa zai iya yin amfani da diflomasiya ko sojojin da suka ƙware don ya ci yaƙin maimakon neman taimakon Jehobah. Ko kuma wataƙila ya saurari shawara marar kyau daga wasu.

6. Mene ne za mu iya koya daga kuskuren da Asa ya yi? Ka ba da misali.

6 Mene ne za mu iya koya daga kuskuren da Asa ya yi? Sa’ad da muke fuskantar matsalolin da muke ganin sun fi ƙarfinmu, zai iya yi mana sauƙi mu dogara ga Jehobah. Amma me za mu yi idan muna tsai da shawara a kan abubuwan da ba su da muhimmanci sosai a rayuwarmu? Shin muna bin ra’ayin mutane ko kuma muna yin ƙoƙari mu magance su yadda muke ganin ya dace? Ko kuma muna bin da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki kuma mu yi amfani da su don mu magance matsalolin? Alal misali, a ce iyalinka suna hana ka halartan taron ikilisiya ko kuma manyan taro. Shin za ka gaya Jehobah ya taimaka maka ka san abin da za ka yi a yanayin nan? Idan ka rasa aikinka kuma fa, kuma ka daɗe kana neman aiki? Idan ka samu wanda yake son ya ɗauke ka aiki, shin har ila za ka gaya masa cewa za ka riƙa halartan taro a kowane mako? Ko da wace irin matsala ce muke fuskanta, muna bukatar mu bi shawarar marubucin wannan zaburar da, ya ce: “Ka danƙa wa Ubangiji tafarkinka; ka dogara gare shi, shi kuma za ya tabbatar da shi.”Zab. 37:5.

ME ZAI FARU IDAN KANA TARAYYA DA ABOKAN BANZA?

7, 8. Wane kuskure ne Jehoshaphat ya yi, kuma da wane sakamako? (Ka duba hoton da ke shafi na 23.)

7 Bari mu duba misalin Jehoshaphat ɗan Asa. Yana da halaye da yawa masu kyau. Kuma sa’ad da ya dogara ga Jehobah, ya yi abubuwa da yawa masu kyau. Duk da haka, ya tsai da wasu shawarwarin da ba su dace ba. Alal misali, ya sa ɗansa ya auri ‘yar mugun Sarkin nan Ahab. Kuma bayan haka, Jehoshaphat ya bi Ahab yin yaƙi da Suriyawa, duk da cewa annabi Micaiah ya hana shi yin hakan. A yaƙin, da kyar Jehoshaphat ya tsira. (2 Laba. 18:1-32) Sa’ad da ya koma Urushalima sai annabi Jehu ya tambaye shi: “Ya kamata ka taimaki miyagu, ka ƙaunaci waɗanda suke ƙin Ubangiji?”Karanta 2 Labarbaru 19:1-3.

 8 Jehoshaphat ya koyi darasi kuwa daga abin da ya faru da shi da kuma gargaɗin da annabin ya ba shi? Ko da yake yana ƙaunar Jehobah kuma yana son faranta masa rai, bai koyi darasi daga abin da ya faru da shi ba. Jehoshaphat ya soma abokantaka da maƙiyin Jehobah. Wato mugun Sarki Ahaziah, ɗan sarki Ahab. Jehoshaphat da Ahaziah sun gina jiragen ruwa tare, amma jiragen sun lalace kafin a yi amfani da su.2 Laba. 20:35-37.

9. Ta yaya yin tarayya da abokan banza zai iya shafan mu?

9 Ya kamata karanta labarin Jehoshaphat ya sa mu bincika irin rayuwar da muke yi. Ta yaya? Jehoshaphat ya yi abin da ya dace kuma “ya biɗi Ubangiji da dukan zuciyarsa.” (2 Laba. 22:9) Duk da haka, ya yi tarayya da abokan banza kuma hakan ya jawo masa matsaloli sosai. Ka tuna abin da Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ka yi tafiya tare da masu-hikima, kai kuwa za ka yi hikima: Amma abokin tafiyar wawaye za ya cutu dominsa.” (Mis. 13:20) Saura kaɗan Jehoshaphat ya rasa ransa saboda abotarsa da Ahab. Ko da yake ya kamata mu koya wa mutane game da Jehobah, duk da haka, za mu iya faɗawa cikin matsalar idan muka yi abokantaka na kud da kud da mutanen da ba sa bauta wa Jehobah.

10. (a) Wane darasi ne za mu iya koya daga Jehoshaphat a batun yin aure? (b) Me ya kamata mu tuna sa’ad da muke fuskantar batun yin tarayya da abokan banza?

10 Wane darasi ne za mu iya koya daga abin da ya faru da Jehoshaphat? Ɗan’uwa zai iya soma sha’awar wadda ba ta bauta wa Jehobah a zuciyarsa don yana ganin ba zai sami wadda ta dace da shi a cikin ƙungiyar Jehobah ba. Wataƙila dangin wani ɗan’uwa da ba sa bauta wa Jehobah suna matsa masa ya yi aure kafin ya tsufa. Ƙari ga haka, wasu suna iya jin yadda wata ‘yar’uwa ta ji kuma ta ce: “Jehobah ya halicce mu don mu so mutane kuma mutane su so mu.” Mene ne Kirista zai yi a irin wannan yanayin? Yin bimbini a kan abin da ya faru da Jehoshaphat zai taimaka masa. Jehoshaphat ya roƙi Jehobah ya yi masa ja-gora. (2 Laba. 18:4-6) Amma mene ne ya faru sa’ad da Jehoshaphat ya soma  tarayya da Ahab, wanda ba ya ƙaunar Jehobah? Ya kamata Jehoshaphat ya tuna cewa Jehobah yana amincewa da waɗanda suke bauta masa da zuciya ɗaya. A zamaninmu, idanun Allah “suna kai da kawowa a cikin dukan duniya” kuma yana so ya taimaka mana. (2 Laba. 16:9) Ya san yanayinmu kuma yana ƙaunarmu. Shin ka gaskata cewa Allah zai taimake ka don ka samu matar da ta dace da kai kuma ku yi rayuwa tare? Ka kasance da tabbaci cewa zai yi hakan!

Kada ku soma soyayya da wanda ba ya bauta wa Jehobah (Ka duba sakin layi na 10)

KADA KA ZAMA MAI GIRMAN KAI

11, 12. (a) Ta yaya Hezekiya ya nuna abin da ke zuciyarsa? (b) Me ya sa Allah ya gafarta wa Hezekiya?

11 Wane darasi ne za mu iya koya daga misalin Hezekiya? Akwai lokacin da Jehobah ya nuna abin da ke zuciyar Hezekiya. (Karanta 2 Labarbaru 32:31.) Sa’ad da Hezekiya ya soma rashin lafiya sosai, Allah ya gaya masa cewa zai warke kuma ya nuna masa alama cewa hakan zai faru. Wataƙila sarakunan Babila sun turo mutane ne don ya bayyana musu mu’ujizar da ta faru, wato inuwar da ta koma baya. (2 Sar. 20:8-13; 2 Laba. 32:24) Sa’ad da Allah ya “bar shi,” Hezekiya ya nuna abin da ke zuciyarsa kuma ya nuna wa Babiloniyawa “dukan gidan kayansa masu-daraja.” Wannan wawancin da Hezekiya ya yi ya nuna “dukan abin da ke cikin zuciyarsa.”

12 Littafi Mai Tsarki bai faɗi abin da ya sa Hezekiya ya canja halinsa ba. To me ya sa ya zama mai girman kai? Shin ya yi hakan ne domin nasarar da ya yi a kan Assuriyawa ko kuma domin Allah ya warkar da shi? Ko kuma don yana da “dukiya da daraja da yawa ƙwarai?” Saboda ya zama mai girman kai Hezekiya, bai nuna godiya don “alherin da aka yi masa ba.” Abin baƙin ciki shi ne, ko da yake Hezekiya ya gaya wa Allah cewa ya bauta masa da dukan zuciyarsa, akwai lokacin da ya ɓata wa Jehobah rai. Amma daga baya, “Hezekiah ya ƙasƙantar da kansa” kuma Allah ya gafarta masa.2 Laba. 32:25-27; Zab. 138:6.

13, 14. (a) Wane yanayi ne zai nuna abin da yake zuciyarmu? (b) Mene ne za mu yi sa’ad da wasu suka yaba mana don abin da muka yi?

13 Ta yaya za mu amfana daga karanta da kuma yin bimbini a kan labarin Hezekiya? Ka tuna cewa Hezekiya ya soma girman kai bayan Jehobah ya taimaka masa ya yi nasara a kan Sennacherib kuma ya warkar da shi. Saboda haka, mene ne za mu yi idan muka cim ma wani abu ko kuma sa’ad da mutane suka yabe mu? Alal misali, wani ɗan’uwa zai iya shirya jawabinsa sosai kuma ya ba da jawabin a gaban jama’a mai girma. Mutane da yawa kuma su yaba masa don jawabin da ya ba da. Mene ne zai yi sa’ad da aka yabe shi?

14 Ya kamata mu riƙa tuna da abin da Yesu ya faɗa: “Sa’anda kun yi dukan abin da aka umurce ku, sai ku ce, Mu bayi marasa-amfani ne; mun yi abin da ya wajaba garemu.” (Luk. 17:10) Ka tuna cewa Hezekiya ya zama mai girman kai don bai nuna godiya ga “alherin da aka yi masa ba.” Yin bimbini a kan abubuwan da Allah ya yi mana zai sa mu guji halin da Jehobah ya tsana, kuma za mu riƙa yaba masa. Ballantana ma, shi ne ya ba mu Littafi Mai Tsarki da kuma ruhu mai tsarki don su taimaka wa mutanensa.

KA MAI DA HANKALI SA’AD DA KAKE YANKE SHAWARA

15, 16. Mene ne Josiah ya yi da ya jawo mutuwarsa?

15 A ƙarshe, mene ne za mu koya daga labarin Josiah? Ko da yake Josiah sarki  ne mai kirki, ya yi kuskuren da ya kai ga mutuwarsa. (Karanta 2 Labarbaru 35:20-22.) Mene ne ya faru? Josiah “ya fita yaƙi” da Neko Sarkin Masar, ko da yake sarkin ya gaya wa Josiah cewa ba shi ya zo ya yaƙa ba. Littafi Mai Tsarki ya ce abin da Neko ya faɗa ya fito daga “bakin Allah” ne. To, me ya sa Josiah ya yaƙi Neko? Littafi Mai Tsarki bai faɗi dalilin ba.

16 Amma ta yaya, Josiah zai sani cewa abin da Neko ya faɗa daga bakin Jehobah ne? Da ya tambayi Irmiya, ɗaya daga cikin annabawa masu aminci. (2 Laba. 35:23, 25) Amma babu inda aka ambata cewa ya yi hakan. Ƙari ga haka, Neko na kan hanyarsa na zuwa Carchemish ne don ya yaƙi wata al’umma, ba Urushalima ba. Ban da haka ma, Neko bai zagi Jehobah ko mutanensa ba. Josiah bai yi tunani sosai a kan waɗannan abubuwan kafin ya yanke shawara ba. Wane darasi ne muka koya daga wannan labarin? Sa’ad da muke fuskantar wata matsala, ya kamata mu fara yin la’akari da abin da Jehobah zai so mu yi.

17. Ta yaya za mu guji yin kuskuren da Josiah ya yi sa’ad da muke cikin matsala?

17 Idan wata matsala ta taso, ya kamata mu yi la’akari da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da suka shafi batun kuma mu yi amfani da su a hanyar da ta dace. A wasu lokatai, muna iya yin bincike a littattafanmu ko kuma mu nemi shawarar dattawa. Suna iya taimaka mana mu yi tunani a kan wasu ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. Alal misali, wata ‘yar’uwa ta san cewa ya kamata ta yi wa’azi. (A. M. 4:20) Amma, a ce ta yi shirin fita wa’azi wata rana, sai mijinta da ba Mashaidi ba ne ya ce ta zauna a gida. Ya ce sun daɗe ba su yi abubuwa tare ba, zai so su shaƙata kuma su fita yawo. ‘Yar’uwar tana iya yin la’akari da wasu ayoyin Littafi Mai Tsarki da za su taimaka mata ta tsai da shawara mai kyau. Ta san cewa wajibi ne ta yi wa Allah biyayya kuma Yesu ya umurce mu mu yi wa’azi. (Mat. 28:19, 20; A. M. 5:29) Amma sai ta tuna cewa ya kamata matar aure ta yi wa mijinta biyayya kuma ya dace bayin Allah su zama masu sanin yakamata. (Afis. 5:22-24; Filib. 4:5) Shin mijinta yana ƙoƙarin ya hana ta zuwa wa’azi ne ko kuma yana so su kasance tare a ranar ne kawai? A matsayinmu na bayin Jehobah, ya kamata mu tsai da shawarwarin da suka dace kuma mu faranta masa rai.

KA BAUTA WA JEHOBAH DA ZUCIYA ƊAYA DON KA YI FARIN CIKI

18. Ta yaya yin la’akari da labaran sarakuna huɗu da aka ambata a wannan talifin za su amfane mu?

18 Da yake mu ajizai ne, a wasu lokatai mu ma muna iya yin kuskuren da waɗannan sarakuna huɗu da muka tattauna suka yi. Muna iya (1) dogara ga ra’ayinmu, na (2) muna iya soma yin tarayya da abokan banza na (3) muna iya zama masu girman kai, ko kuma (4) mu tsai da shawarwari ba tare da yin la’akari da ra’ayin Allah ba. Jehobah yana ganin nagargarun ayyukan da muke yi kamar yadda ya ga ayyuka masu kyau da waɗannan sarakuna huɗu suka yi. Ƙari ga haka, Jehobah ya san cewa muna ƙaunarsa kuma muna son mu bauta masa da gaske. Shi ya sa ya yi tanadin waɗannan misalan don mu guji yin kura-kurai masu tsanani. Bari mu ci gaba da yin bimbini a kan waɗannan labaran Littafi Mai Tsarki kuma mu riƙa nuna godiya cewa Jehobah ya yi mana tanadinsu.