Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Kasance da Bangaskiya Kuma Ka Tsai da Shawara Mai Kyau!

Ka Kasance da Bangaskiya Kuma Ka Tsai da Shawara Mai Kyau!

“Bari shi yi roƙo da bangaskiya, ba da shakkar komi ba.”YAƘ. 1:6.

WAƘOƘI: 81, 70

1. Me ya sa Kayinu ya yanke shawara da ba ta dace ba kuma wane sakamako ya samu?

KAYINU yana da shawarar da yake bukatar ya tsai da. Idan ya kame kansa zai sami sakamako kyau da kuma zaman lafiya amma idan ya ƙi yin hakan, zai sami mummunar sakamako. Kowace shawara da ya tsai da a wannan batun zai iya shafar dukan rayuwarsa. Kayinu bai tsai da shawara mai kyau ba kuma hakan ya sa ya kashe Habila ɗan’uwansa mai aminci. Ban da haka ma, shawarar da ya yanke ta ɓata dangantakarsa da Mahaliccinsa.Far. 4:3-16.

2. Me ya sa yake da muhimmanci mu riƙa tsai da shawarwari masu kyau?

2 Mu ma muna da shawarwari da yawa da ya kamata mu tsai da a rayuwa. Wasu shawarwarin suna da muhimmanci wasu kuma ba su da muhimmanci. Ƙari ga haka, wasu shawarwari da muke tsai da wa za su iya shafan mu a rayuwa. Amma idan muka tsai da shawarwari masu kyau, za mu zauna lafiya kuma ba za mu kasance da matsaloli da yawa ba. Idan muka tsai da shawarar da ba su dace ba kuma, za mu fuskanci matsaloli masu yawa kuma ba za mu yi zaman lafiya ba.Mis. 14:8.

3. (a) Mene ne ya kamata mu gaskata da shi idan muna son mu yanke shawarwari masu kyau? (b) Waɗanne tambayoyi za mu tattauna?

 3 Me zai taimaka mana mu riƙa tsai da shawarwari masu kyau? Muna bukatar mu kasance da bangaskiya cewa Allah zai taimaka mana mu zama masu hikima. Ban da haka ma, ya kamata mu gaskata da abin da Jehobah ya faɗa a Kalmarsa da kuma yadda yake yin abubuwa. (Karanta Yaƙub 1:5-8.) Idan muka kusaci Allah kuma muna ƙaunarsa sosai, hakan zai taimaka mana mu gaskata cewa ya san abin da ya dace da mu. Ƙari ga haka, za mu riƙa bincika Kalmar Allah kafin mu tsai da shawara. Amma ta yaya za mu kyautata yadda muke yanke shawara? Kuma ya kamata mu canja wasu shawarwarin da muka riga muka yanke?

MUNA BUKATAR MU RIƘA TSAI DA SHAWARWARI

4. Wace shawara ce Adamu ya yanke, kuma wane sakamako ya samu?

4 Tun da farko, an yi mutane su riƙa tsai da shawarwari masu muhimmanci a rayuwa. Adamu yana bukatar ya tsai da shawarar ko zai saurari Mahaliccinsa ko kuma matarsa Hauwa’u. Amma wace shawara ya tsai da? Matarsa ta sa ya yanke wata shawarar da ba ta dace ba, don haka, ya yi hasarar Aljanna har ma da ransa. Ban da haka ma, Allah ya kore su daga Aljanna. Mu ma muna shan wahala ne don shawarar da Adamu ya yanke.

5. Ta yaya ya kamata mu ɗauki ‘yancin yanke shawarwari?

5 Wasu suna ganin cewa za su ji daɗin rayuwa idan ba sa yanke shawarwari. Kai fa, haka kake ji? Ya kamata mu tuna cewa Jehobah bai halicce mu kamar ‘yar tsana da ba sa iya tunani ko kuma tsai da shawara ba. Littafi Mai Tsarki ya koya mana yadda za mu iya tsai da shawarwari da suka dace. Jehobah yana son mu riƙa tsai da shawarwari domin ya san cewa za mu amfana. Bari mu bincika wasu misalai da suka nuna hakan.

6, 7. Wane zaɓi ne Isra’ilawa suke da shi, kuma me ya sa ya kasance musu da wuya su yi zaɓi mai kyau? (Ka duba hoton da ke shafi na 13.)

6 A lokacin da Isra’ilawa suka soma zama a Ƙasar Alkawari suna bukata su yi zaɓi. Suna da zaɓin ko su bauta wa Jehobah ko kuma su bauta ma wasu alloli. (Karanta Joshua 24:15.) Yin hakan ba wani abu mai wuya ba ne. Duk da haka, shawarar da za su tsai da za ta iya sa su sami rai ko kuma su halaka. A zamanin Alƙalawa, Isra’ilawa sun yi ta tsai da shawarwarin da ba su dace ba. Sun daina bauta wa Allah kuma suka soma bauta wa allolin ƙarya. (Alƙa. 2:3, 11-23) A zamanin annabi Iliya kuma, bayin Allah sun bukaci su tsai da shawarar ko za su bauta wa Allah ko kuma su bauta wa Baal. (1 Sar. 18:21) Iliya ya tsauta wa mutanen don sun kasa tsai da shawara. Kana iya cewa ai wannan abu ne mai sauƙi don bauta wa Jehobah yana da amfani. A gaskiya, babu wani mutum mai tunani da zai so ya bauta wa Ba’al, allan ƙarya. Duk da haka, hankalin Isra’ilawa ya rabu biyu. Shi ya sa Iliya ya ba su shawara cewa bauta wa Jehobah ta fi muhimmanci.

7 Me ya sa ya yi wa Isra’ilawa wuya su yanke shawarar da ta dace? Da farko, sun daina kasancewa da bangaskiya kuma sun ƙi su saurare Allah. Ba su da hikima kuma ba su dogara ga Jehobah ba. Da a ce sun san Allah sosai, da sun tsai da shawarwarin da suka dace. (Zab. 25:12) Ƙari ga haka, sun bi ra’ayin wasu kuma sun bar su su riƙa tsai da musu shawara. Mutanen da suke ƙasar da ba sa bauta wa Jehobah sun rinjayi Isra’ilawan don su bi  ra’ayinsu na bauta wa wasu alloli. Jehobah ya riga ya ja kunnen Isra’ilawa kuma ya gaya musu cewa hakan zai iya faruwa.Fit. 23:2.

YA DACE NE MUTANE SU TSAI DA MANA SHAWARA?

8. Wane darasi mai muhimmanci ne muka koya game da tsai da shawara?

8 Mun koyi darasi daga misalin da aka ambata ɗazu. Mu muke bukatar mu tsai da wa kanmu shawarwarin da suka dace bisa ga abin da muka koya daga Nassi. Littafin Galatiyawa 6:5 ta ce: “Kowane mutum za ya ɗauki kayan kansa.” Bai kamata mu bar wasu su riƙa tsai da mana shawarwari ba. Maimakon haka, ya kamata mu da kanmu mu san abin da Allah yake so kuma mu yi ƙoƙari mu yi shi.

9. Me ya sa bai dace mu bar wasu su riƙa yanke mana shawara ba?

9 Me zai iya sa mu bar wasu su yanke mana shawara? Matsi daga tsaranmu zai iya sa mu yanke shawarar da ba ta dace ba. (Mis. 1:10, 15) Duk da haka, ko da yaya mutane suka matsa mana, mun san cewa ya kamata mu riƙa bin abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa. Idan kuma muka bar wasu su riƙa tsai da mana shawara, muna bin su ke nan kuma hakan zai iya kawo mugun sakamako.

10. Wane gargaɗi ne manzo Bulus ya yi wa Galatiyawa?

10 Manzo Bulus ya ja kunnen Galatiyawa cewa bai kamata su bar wasu su riƙa tsai da musu shawarwari ba. (Karanta Galatiyawa 4:17.) Wasu a ikilisiyar sun so su riƙa yanke wa mutane shawarwari don su janye su daga manzannin. Me ya sa? Domin suna son su yi suna. Hakan ya sa sun wuce gona da iri kuma ba su yarda su bar Kiristocin su yi amfani da ‘yancinsu na tsai da shawarwari ba, kuma hakan bai dace ba.

11. Ta yaya za mu taimaka wa wasu sa’ad da suke tsai da shawara?

11 Bulus ya kafa misali mai kyau don ya bar ‘yan’uwa su riƙa tsai da wa kansu shawarwari. (Karanta 2 Korintiyawa 1:24.) A yau ma, ya kamata dattawa su bi wannan misalin sa’ad da suke ba da shawara a kan wasu batutuwa da ya kamata  ’yan’ uwa su tsai da wa kansu. Suna murna su gaya wa ‘yan’uwa abubuwan da suka koya daga Littafi Mai Tsarki. Duk da haka, dattawa suna barin ‘yan’uwa su riƙa yanke shawara da kansu. Hakan ya dace don ‘yan’uwa ne za su fuskanci sakamakon shawarar da suka tsai da wa kansu. Wane darasi ne muka koya? Za mu iya taimaka wa ‘yan’uwanmu ta wurin taimaka musu su fahimci ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. Amma su suke da hakkin tsai da shawara da kansu. Idan suka tsai da shawarwari masu kyau, za su amfana. Saboda haka, bai kamata mu kasance da ra’ayin cewa muna da ikon yanke ma wasu shawara ba.

Dattawa masu kirki suna taimaka ma wasu su yanke shawara da kansu (Ka duba sakin layi na 11)

KADA KA TSAI DA SHAWARA SA’AD DA KAKE FUSHI KO BAƘIN CIKI

12, 13. Me ya sa bai dace mu tsai da shawara ba sa’ad da muke fushi ko kuma sanyin gwiwa ba?

12 Wani ra’ayi da mutane suke da shi a yau shi ne, ka yi abin da zuciyarka ta gaya maka. Amma yin hakan bai yi daidai da abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa ba. Littafi Mai Tsarki ya ja kunnenmu cewa bai kamata mu bi zuciyarmu ba sa’ad da muke yanke shawara. (Mis. 28:26) Ban da haka ma, labaran Littafi Mai Tsarki sun nuna haɗarin da yake tattare da bin zuciyarmu. Matsalar ita ce, da yake mu ajizai ne, ‘zuciyarmu ta fi komi rikici, cuta gareta ƙwarai irin ta fidda zuciya.’ (Irm. 3:17; 13:10; 17:9; 1 Sar. 11:9) To, me zai iya faruwa idan muka bi zuciyarmu sa’ad da muke tsai da shawarwari?

13 Zuciyarmu tana da muhimmanci don an umurce mu mu ƙaunaci Jehobah da dukan zuciyarmu kuma mu ƙaunaci maƙwabcinmu kamar kanmu. (Mat. 22:37-39) Amma ya kamata mu mai da hankali domin kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya faɗa a sakin layi na baya, bai kamata mu bar zuciyarmu ta ja-gorance mu ba sa’ad da muke so mu tsai da wata shawara. Alal misali, me zai iya faruwa idan muka tsai da shawara sa’ad da muke fushi? Babu shakka, duk wanda ya taɓa yin hakan a dā, ya san cewa bai yi nasara ba. (Mis. 14:17; 29:22) Ban da haka ma, kuna ganin zai yiwu mu yanke shawara mai kyau sa’ad da muka yi sanyin gwiwa? (Lit. Lis. 32:6-12; Mis. 24:10) Ya kamata mu tuna cewa Kalmar Allah tana ɗauke da “shari’ar Allah,” da za ta taimaka mana mu riƙa yanke shawara mai kyau. (Rom. 7:25) Hakika, bai kamata mu riƙa tsai da shawara mai muhimmanci a lokacin da muke fushi ko sanyin gwiwa ba.

LOKACIN DA YA DACE KA CANJA SHAWARWARINKA

14. Ta yaya muka sani cewa ya dace mutum ya canja wata shawara da ya riga ya yanke?

14 Muna bukatar mu riƙa yanke shawarwari masu kyau. Amma hakan ba ya nufin cewa ba za mu iya canja wata shawarar da muka yanke ba. A wasu lokuta bayan mun yi tunani sosai, za mu iya canja wata shawarar da muka riga muka yanke. Ka yi la’akari da yadda Jehobah ya bi da mutanen Nineba a zamanin Yunana. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Allah kuwa ya ga ayyukansu, da suka juya ga barin mugun tafarkinsu; Allah kuwa ya tuba ga barin masifar da ya ce za ya yi masu; ba ya kuwa aikata ba.” (Yun. 3:10) Bayan da Jehobah ya ga cewa mutanen Nineba sun canja halinsu kuma sun tuba, ya canja shawarar da ya yanke kuma ya ce ba zai halaka su ba. A yin hakan Allah ya nuna cewa shi mai sauƙin kai ne kuma mai jin tausayi. Saboda haka, ko da Jehobah yana fushi, yana iya yanke shawarwari masu kyau ba kamar mu ‘yan Adam ba.

15. Me zai iya sa mu canja wata shawarar da muka yanke?

 15 A wasu lokuta zai dace mu sake tunani sosai a kan wasu shawarwarin da muka yanke wataƙila don yanayinmu ya canja. Alal misali, Jehobah ya canja wasu shawarwarin da ya yanke. (1 Sar. 21:20, 21, 27-29; 2 Sar. 20:1-5) Wani sabon bayani zai iya sa mu canja wata shawarar da muka riga muka yanke. An yi wa Sarki Dauda ƙarya game da jikan Saul mai suna Mephibosheth. Amma sa’ad da Dauda ya sami cikakken bayani, sai ya canja shawarar da ya yanke. (2 Sam. 16:3, 4; 19:24-29) A wasu lokuta zai dace mu ma mu yi hakan.

16. (a) Waɗanne irin bayanai ne za su taimaka mana sa’ad da muke tsai da shawarwari masu kyau? (b) Me ya sa ya kamata mu canja wasu shawarwari da muka riga muka yanke, kuma ta yaya za mu yi hakan?

16 Littafi Mai Tsarki ya ce kada mu yi hanzarin yanke shawarwari masu muhimmanci. (Mis. 21:5) Za mu yi nasara idan muka yi tunani ko bincike sosai kafin mu yanke wata shawara. (1 Tas. 5:21) Kafin magidanta su tsai da shawara, suna bukatar su bincika Nassosi da littattafanmu su kuma ji ra’ayin iyalinsu. Ka tuna cewa Allah ya gaya wa Ibrahim ya saurari matarsa. (Far. 21:9-12) Dattawa ma ya kamata su yi bincike sosai. Kuma idan suna da sauƙin kai da kuma tawali’u, ba za su ji kunya su yi amfani da wani sabon bayani mai muhimmanci da suka samu da zai iya sa su canja wata shawarar da suka riga suka yanke ba. Suna bukata su canja ra’ayinsu da shawarwarinsu idan da bukata, kuma mu ma muna bukatar mu bi misalinsu. Hakan zai sa a kasance da salama da kuma haɗin kai a cikin ikilisiya.A. M. 6:1-4.

KA YI ABIN DA KA TSAI DA SHAWARAR YI

17. Me zai taimaka mana mu yi nasara sa’ad da muke yanke shawarwari?

17 Wasu shawarwari da muke yankewa sun fi wasu muhimmanci. Muna bukatar mu yi tunani da addu’a kafin mu yanke masu muhimmancin. Wasu Kiristoci suna bukatar su tsai da shawarar ko za su yi aure da kuma wanda za su aura. Wata shawara mai muhimmanci ita ce lokacin da ya kamata mu soma hidima ta cikakken lokaci. A irin wannan yanayin, ya dace mu tabbata cewa Jehobah zai yi mana ja-gora mai kyau. (Mis. 1:5) Saboda haka, yana da muhimmanci mu dogara ga Littafi Mai Tsarki da yake a ciki ne za mu samu shawarar da ta dace. Ban da haka ma, yin addu’a ga Jehobah zai taimaka mana sosai. Ƙari ga haka, Jehobah zai sa mu kasance da halaye da muke bukata don mu iya tsai da shawarwarin da suka yi daidai da nufinsa. Kafin ka yanke shawara mai muhimmanci, zai dace ka riƙa yin waɗannan tambayoyin: ‘Wannan shawarar za ta nuna cewa ina ƙaunar Jehobah? Shin za ta sa iyalina ta yi farin ciki kuma mu yi zaman lafiya? Kuma shawarar za ta nuna cewa ina da haƙuri da kirki?’

18. Me ya sa Jehobah yake so mu yanke shawarwarinmu da kanmu?

18 Jehobah ba ya sa mu dole mu ƙaunace shi ko kuma mu bauta masa. Hakan zaɓinmu ne. Da yake ya ba mu ‘yanci, yana barin mu mu zaɓi ko za mu bauta masa. (Josh. 24:15; M. Wa. 5:4) Amma yana son mu yanke shawara bisa ga ƙa’idodinsa. Idan muka gaskata umurnin Jehobah kuma muka bi ƙa’idodinsa, hakan zai sa mu iya yanke shawarwari masu kyau kuma mu nuna cewa za a iya amincewa da mu.Yaƙ. 1:5-8; 4:8.