Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 TALIFIN NAZARI NA 1

Ku Je Ku Sa Mutane Su Zama Almajiraina

Ku Je Ku Sa Mutane Su Zama Almajiraina

JIGON SHEKARA TA 2020: Ku je ku sa mutane su zama almajiraina, kuna yi musu baftisma.​—MAT. 28:19.

WAƘA TA 79 Mu Koya Musu Su Kasance da Aminci

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1-2. Mene ne wani mala’ika ya gaya wa wasu mata a kabarin Yesu, kuma wane umurni ne Yesu ya ba su?

A SAFIYAR ranar 16 ga Nisan a shekara ta 33, wasu mata masu ƙaunar Allah da suke makoki sun je makabarta. An binne Yesu a wurin kwanaki biyu da suka shige. Sa’ad da suka isa kabarin don su zuba wa gawar Yesu turare da māi, sun yi mamaki da suka tarar cewa babu gawa a kabarin! Wani mala’ika ya gaya wa almajiran cewa an ta da Yesu daga mutuwa, ya ƙara cewa: “Ga shi kuma zai riga ku zuwa Galili, a can ne za ku gan shi.”​—Mat. 28:​1-7; Luk. 23:56; 24:10.

2 Bayan matan sun bar kabarin, Yesu ya same su a hanya kuma ya ba su wannan umurnin, ya ce: “Ku je ku faɗa wa ’yan’uwana su tafi Galili, a can ne za su gan ni.” (Mat. 28:10) Abu na farko da Yesu ya yi bayan an ta da shi daga mutuwa, shi ne yin taro da almajiransa. A wannan taron, ya ba su wasu umurnai masu muhimmanci!

SU WAYE NE AKA BA UMURNIN?

Sa’ad da Yesu ya haɗu da manzanninsa da kuma wasu a Galili bayan ya tashi daga matattu, ya ce su je su sa mutane su zama ‘almajiransa’ (Ka duba sakin layi na 3-4)

3-4. Ta yaya muka san cewa ba manzannin Yesu kaɗai aka ba umurnin da ke Matiyu 28:​19, 20 ba? (Ka duba hoton da ke bangon gaba.)

3 Karanta Matiyu 28:​16-20. A taron da Yesu ya yi da almajiransa, ya gaya musu aiki mai muhimmanci da za su yi a ƙarni na farko, wato aikin da muke yi a yau. Yesu ya ce: ‘Ku je ku faɗa wa dukan al’ummai . . . ku kuma koya musu su yi biyayya da dukan abubuwan da na umarce ku.’

4 Ba manzanninsa 11 masu aminci kaɗai ba ne Yesu yake so su riƙa yin wa’azi ba amma yana so dukan almajiransa su riƙa yin hakan. Ta yaya muka sani? A lokacin da Yesu ya ba da wannan umurnin, ba manzanninsa ne kaɗai ke kan dutsen  Galili ba. Ta yaya muka san hakan? Ka tuna cewa mala’ikan ya gaya wa matan cewa: ‘Za ku gan shi [a Galili].’ Don haka, zai yiwu cewa mata masu aminci ma sun halarci taron da Yesu ya yi da manzanninsa. Ƙari ga haka, manzo Bulus ya ce Yesu “ya bayyana ga ’yan’uwa fiye da ɗari biyar a lokaci guda.” (1 Kor. 15:6) A ina ne hakan ya faru?

5. Mene ne muka koya daga 1 Korintiyawa 15:6?

5 Da akwai dalilai da yawa da suka nuna cewa Bulus yana magana ne game da taron da aka yi a Galili wanda aka ambata a littafin Matiyu sura 28. Waɗanne dalilai ke nan? Na farko, yawancin mabiyan Yesu ’yan Galili ne. Don haka, yana da sauƙi su yi taron a dutsen Galili maimakon a gidan wani a Urushalima. Na biyu, Yesu ya riga ya haɗu da manzanninsa 11 a wani gida a Urushalima bayan ya tashi daga mutuwa. Da a ce Yesu yana so ya ba manzanninsa kaɗai umurni su yi wa’azi, da ya yi hakan sa’ad da ya haɗu da su a Urushalima. Maimakon haka, ya gaya wa su da matan da kuma wasu cewa su je su same shi a Galili.​—Luk. 24:​33, 36.

6. Ta yaya Matiyu 28:20 ta nuna cewa umurnin Yesu game da almajirtarwa ya shafe mu, kuma ta yaya ake bin wannan umurnin a yau?

6 Ka yi la’akari da dalili na uku mai muhimmanci. Ba Kiristoci a zamaninsa ne kaɗai Yesu ya ba umurnin ba. Ta yaya muka san hakan? Domin Yesu ya kammala umurnin da ya ba mabiyansa da wannan furuci: ‘Ina tare da ku kullum har ƙarshen zamani.’ (Mat. 28:20) Kamar yadda Yesu ya faɗa, mutane da yawa a yau suna zama mabiyansa. A kowace shekara, kusan mutane 300,000 ne suke yin baftisma a matsayin Shaidun Jehobah. Hakika wannan abin farin ciki ne!

7. Mene ne za mu tattauna, kuma me ya sa?

7 Mutane da yawa da suke yin nazarin Littafi Mai Tsarki suna samun ci gaba kuma su yi baftisma. Amma wasu da muke yin nazari da su suna yin jinkirin zama mabiyan Yesu. Suna jin daɗin nazarin da suke yi, amma ba sa samun ci gaba da zai sa a yi musu baftisma. Idan kana nazari da mutane, muna da tabbaci cewa kana so ka taimaka wa ɗalibinka ya riƙa yin amfani da abubuwan da yake koya, kuma ya zama mabiyin Yesu. A wannan talifin, za mu tattauna yadda za mu iya ratsa zuciyar ɗalibinmu da kuma yadda za mu iya taimaka masa ya samu ci gaba. Me ya sa muke bukatar mu tattauna wannan batun? Domin a wasu lokuta, muna bukatar mu tsai da shawara ko zai dace mu ci gaba da nazarin ko kuma a’a.

KA ƘOƘARTA KA RATSA ZUCIYA

8. Me ya sa zai iya yi mana wuya mu ratsa zuciyar ɗalibinmu?

8 Jehobah yana so mutane su bauta masa domin suna ƙaunar sa. Saboda haka, maƙasudinmu shi ne mu taimaka wa ɗalibanmu su fahimci cewa Jehobah ya damu da su kuma yana ƙaunar su sosai. Muna so mu taimaka musu su ɗauki Jehobah a matsayin “baban marayu, kuma mai lura da matan da mazansu suka mutu.” (Zab. 68:5) Yayin da ɗalibanka suka fahimci cewa Jehobah yana ƙaunar su, hakan zai motsa su kuma su ma za su soma ƙaunar sa. Yana yi ma wasu ɗalibai wuya su ɗauki Jehobah a matsayin Uba mai ƙauna domin mahaifinsu bai nuna musu ƙauna ba. (2 Tim. 3:​1, 3) Sa’ad da kuke nazari, ka riƙa nanata halaye masu kyau da Jehobah yake da su. Ka taimaka wa ɗalibinka ya fahimci cewa Allahnmu mai ƙauna yana so  ya sami rai na har abada, kuma yana shirye ya taimaka masa ya cim ma hakan. Mene ne kuma za mu iya yi?

9-10. Waɗanne littattafai ne ya kamata mu yi amfani da su don yin nazari, kuma me ya sa?

9 Ka yi amfani da waɗannan littattafan “Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?” da kuma “Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah.” An shirya waɗannan littattafan ne musamman don su taimaka mana mu ratsa zuciyar ɗalibanmu. Alal misali, babi na ɗaya a littafin nan Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki? ya amsa waɗannan tambayoyin: Allah ya damu da mu kuwa ko shi marar tausayi ne? Yaya Allah yake ji idan ya ga mutane suna shan wahala? Zai yiwu ka zama aminin Jehobah? Littafin nan Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah kuma fa? Wannan littafin zai taimaka wa ɗalibin ya fahimci yadda yin amfani da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki zai inganta rayuwarsa kuma ya sa ya kusaci Jehobah. Ko da ka yi nazarin littattafan nan da ɗalibanka, kana bukatar ka yi shiri  sosai don ka taimaka wa ɗalibinka daidai da bukatunsa.

10 Amma idan ɗalibin yana so ku tattauna wani batu da ba ya cikin littattafan da muke amfani da su don nazari kuma fa? Wataƙila kana iya ƙarfafa shi ya karanta littafin da ya yi magana game da batun domin ku sami damar ci gaba da yin nazarin da littafin da kuke amfani da shi.

Ka soma nazarin da addu’a (Ka duba sakin layi na 11)

11. A wane lokaci ne zai dace mu soma addu’a da ɗalibinmu, kuma ta yaya za mu iya taimaka masa ya fahimci amfanin yin hakan?

11 Ku soma nazarin da addu’a. Zai fi dacewa mu soma nazari da addu’a da zarar mun sami zarafi. Muna bukatar mu taimaka wa ɗalibinmu ya fahimci cewa ruhu mai tsarki ne kaɗai zai iya taimaka mana mu fahimci Kalmar Allah. Wasu ’yan’uwa suna ta da batun yin addu’a ta wajen karanta Yaƙub 1:​5, da ya ce: “In waninku yana bukatar hikima, sai ya roƙi Allah.” Bayan haka sai su yi wa ɗalibin tambaya cewa, “Ta yaya za mu roƙi Allah ya ba mu hikima?” Ɗalibin zai faɗa cewa za mu yi hakan ne ta addu’a.

12. Ta yaya za ka yi amfani da Zabura 139:​2-4 don ka taimaka wa ɗalibinka ya inganta yadda yake yin addu’a?

12 Ka koya wa ɗalibinka yadda zai riƙa yin addu’a. Ka tabbatar masa cewa Jehobah yana so ya saurari addu’arsa. Ka bayyana masa cewa, sa’ad da muke addu’a, muna iya gaya wa Jehobah dukan abin da ke damunmu da ba za mu iya gaya wa kowa ba. Saboda Jehobah ya san dukan abin da ke zuciyarmu. (Karanta Zabura 139:​2-4.) Ƙari ga haka, za mu iya ƙarfafa ɗalibanmu su roƙi Jehobah ya taimaka musu su daina yin tunanin da bai dace ba da kuma ayyukan banza. Alal misali, wataƙila ɗalibin yana jin daɗin wani biki da bai kamata Kiristoci su saka hannu ba. Ya san cewa bai kamata ya yi wannan bikin ba, amma yana jin daɗin yin wasu abubuwa a bikin. Kana iya ƙarfafa shi ya gaya wa Jehobah abin da ke damunsa kuma ya roƙe shi ya taimaka masa ya riƙa son yin abin da ke faranta wa Allah rai.​—Zab. 97:10.

Ka gayyaci ɗalibinka zuwa taro (Ka duba sakin layi na 13)

13. (a) Me ya sa muke bukatar mu gayyaci ɗalibanmu zuwa taro ba tare da ɓata lokaci ba? (b) Ta yaya za mu taimaka wa ɗalibinmu ya saki jiki a Majami’ar Mulki?

13 Ka yi saurin gayyatar ɗalibinka ya halarci taro. Abubuwan da ɗalibinka zai ji da kuma gani a taron zai ratsa zuciyarsa kuma ya taimaka masa ya soma samun ci gaba. Ka nuna masa bidiyon nan Me Ake Yi a Majami’ar Mulki? kuma ka gayyace shi taro. Idan zai yiwu ka biya masa kuɗin mota. Zai dace masu shela dabam-dabam su riƙa bin ka yin nazari da ɗalibin. Idan kana yin hakan, ɗalibinka zai saɓa da ’yan’uwa a ikilisiya kuma hakan zai taimaka masa ya saki jiki sa’ad da ya halarci taro.

KA TAIMAKA WA ƊALIBIN YA SAMI CI GABA

14. Mene ne zai iya motsa ɗalibinmu ya soma samun ci gaba?

14 Maƙasudinmu shi ne mu taimaka wa ɗalibanmu su ƙarfafa dangantakarsu da Jehobah. (Afis. 4:13) Wataƙila sa’ad da wasu ɗalibai suka yarda a yi nazari da su, suna so ne su amfani kansu. Amma yayin da suke daɗa ƙaunar Jehobah, za su soma tunanin yadda za su taimaka wa mutane har ma da ʼyan’uwa a ikilisiya. (Mat. 22:​37-39) Idan ka sami zarafi, kada ka manta ka ambata gatan da muke da shi na goyan bayan Mulkin Allah ta wajen ba da gudummawa.

Ka koya wa ɗalibinka abin da zai yi sa’ad da ya fuskanci matsaloli (Ka duba sakin layi na 15)

15. Ta yaya za mu taimaki ɗalibinmu ya yi abin da ya dace sa’ad da ya fuskanci matsala?

 15 Ka koya wa ɗalibanka abin da za su yi sa’ad da suke fuskantar matsaloli. Alal misali, a ce ɗalibinka mai shela da bai yi baftisma ba ne, kuma ya gaya maka cewa wani a ikilisiya ya ɓata masa rai. Maimakon ka goyi bayan shi, ka bayyana masa abin da Littafi Mai Tsarki ya ce ya kamata ya yi. Yana iya gafarta wa mutumin kuma ya mance da batun, ko kuma ya je wajen mutumin don su sasanta. (Ka gwada Matiyu 18:15.) Ka taimaka wa ɗalibinka ya shirya abin da zai ce. Ka koya masa yadda zai yi amfani da manhajar JW Library® da Littafin Bincike Don Shaidun Jehobah da kuma jw.org®. Hakan zai taimaka masa ya san hanyoyin da zai iya magance waɗannan matsalolin. Idan ka koya masa yadda zai riƙa sasanta matsaloli da ’yan’uwa kafin ya yi baftisma, hakan zai taimaka masa ya riƙa zaman lafiya da ’yan’uwa bayan ya yi baftisma.

16. Me ya sa yake da kyau ka gayyaci wasu masu shela su bi ka yin nazari da ɗalibinka?

16 Ka gayyaci ’yan’uwa a ikilisiya da kuma mai kula da da’ira sa’ad da ya ziyarce ku don su bi ka yin nazari da ɗalibinka. Me ya sa? Ban da dalilan da aka ambata ɗazu, wasu masu shela suna iya taimaka wa ɗalibinka a hanyar da ba za ka iya ba. Alal misali, wataƙila ɗalibin yana fama ya daina shan sigari. Ka gayyaci wani Mashaidi da ya taɓa fuskantar irin matsalar nan don ya bi ka yin nazari da shi. Wannan Mashaidi yana iya ba ɗalibinka shawarwarin da yake bukata. Idan kana jin tsoron yin nazari domin ɗan’uwa da ya ƙware yana tare da kai, kana iya ce masa ya yi nazari da ɗalibinka a wannan lokaci. Idan ka gayyaci wasu su bi ka yin nazari, ɗalibin zai amfana sosai. Ka tuna cewa maƙasudinka shi ne ka taimaka masa ya sami ci gaba.

IN DAINA NAZARIN NE?

17-18. Mene ne kake bukatar ka yi la’akari da shi kafin ka daina yin nazari da ɗalibinka?

17 Idan ɗalibinka ba ya yin canje-canje a rayuwarsa, za ka bukaci ka tambayi kanka, ‘In daina yin nazari da shi ne?’ Kafin ka yanke wannan shawarar, ka yi tunanin yanayin da ɗalibin yake ciki. Wasu mutane suna saurin samun ci gaba fiye da wasu. Ka tambayi kanka: ‘Shin ɗalibina yana samun ci gaba da ya kamata kuwa?’ ‘Yana yin “biyayya” ko kuma amfani da abubuwan da yake koya kuwa?’ (Mat. 28:20) Yana iya ɗaukan tsawon lokaci kafin ɗalibi ya soma samun ci gaba, amma yana bukatar ya yi canje-canje a rayuwarsa.

18 Me za mu yi idan mun ɗau shekaru muna yin nazari da wani amma ba ya ɗaukan nazarin da muhimmanci? Ka yi  la’akari da misalin nan: Ɗalibinka ya kammala nazarin littafin nan Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki? kuma wataƙila ya soma nazarin Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah amma bai taɓa halartan taron ikilisiya ko taron Tuna da Mutuwar Yesu ba! Ƙari ga haka, yakan ƙi yin nazari ba tare da wata ƙwaƙƙwarar dalili ba. A irin wannan yanayin, zai dace ka gaya masa gaskiya. *

19. Mene ne za ka iya gaya wa ɗalibinka da ba ya ɗaukan nazarinku da muhimmanci, kuma me kake bukatar ka yi tunani a kai?

19 Kana iya tambayar sa, ‘Me kake ganin zai iya sa ya yi maka wuya ka zama Mashaidin Jehobah?’ Wataƙila ɗalibin yana iya cewa, ‘Ina son yin nazarin Littafi Mai Tsarki, amma ba zan taɓa zama Mashaidin Jehobah ba!’ Idan ɗalibinka yana da wannan ra’ayin bayan kun ɗau tsawon lokaci kuna nazari, shin zai dace ka ci gaba da nazarin? Ko kuma wataƙila ɗalibinka ya gaya maka dalilin da ya sa ba ya samun ci gaba. Alal misali, ƙila yana ganin cewa ba zai iya yin wa’azi gida-gida ba. Idan ka fahimci abin da ke damun sa, hakan zai sa ka iya taimaka masa.

Kada ka yi nazari da mutumin da ba ya samun ci gaba (Ka duba sakin layi na 20)

20. Ta yaya Ayyukan Manzanni 13:48 zai taimaka mana mu san ko ya dace mu ci gaba da nazari ko a’a?

20 Abin takaici, wasu ɗalibai suna kamar Isra’ilawa a zamanin Ezekiyel. Jehobah ya gaya wa Ezekiyel game da su cewa: “Ga shi, a gare su ka zama kamar mai waƙar ƙauna ne, mai rera waƙa da murya mai daɗi da gwanin kiɗi kawai. Suna jin abin da kake faɗi, amma abin bai taɓa zuciyarsu ba.” (Ezek. 33:32) Yana iya yi mana wuya mu gaya wa ɗalibinmu cewa za mu daina yin nazari da shi. Amma lokacin da Allah ya ƙayyade wa zamanin nan ya “kusan ƙārewa.” (1 Kor. 7:29) Maimakon mu ɓata lokaci muna yin nazari da mutumin da ba ya samun ci gaba, muna bukatar mu nemi mutanen da ‘suke a shirye su saurari gaskiyar da ke ba da rai na har abada.’​—A. M. 13:​48NW.

Wataƙila da akwai mutane a yankinku da suke addu’a don samun taimako (Ka duba sakin layi na 20)

21. Mene ne jigon shekara ta 2020, kuma me ya sa ya dace?

21 Jigonmu na shekara ta 2020 zai taimaka mana mu inganta yadda muke almajirtarwa. Wannan jigon ya ƙunshi wasu daga cikin furucin da Yesu ya yi a kan dutsen Galili, ya ce: ‘Ku je ku faɗa wa dukan al’ummai . . . , ku sa su zama almajiraina, kuna yi musu baftisma.’​Mat. 28:19.

Bari mu ƙuduri niyyar inganta yadda muke almajirtarwa da kuma taimaka wa ɗalibanmu su yi baftisma (Ka duba sakin layi na 21)

WAƘA TA 70 Ku Nemi Masu Zuciyar Kirki

^ sakin layi na 5 Jigonmu na shekara ta 2020 zai ƙarfafa mu mu taimaka wa mutane su zama almajiran Yesu. Wannan umurnin ya shafi dukan bayin Jehobah. Ta yaya za mu ratsa zuciyar ɗalibanmu don su zama almajiran Yesu? Wannan talifin zai taimaka mana mu ga yadda za mu iya taimaka wa ɗalibanmu su kusaci Jehobah. Ƙari ga haka, za mu tattauna yadda za mu san ko ya dace mu ci gaba da yin nazari da ɗalibinmu ko a’a.