Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 TALIFIN NAZARI NA 3

Allahnka Jehobah Yana Daraja Ka!

Allahnka Jehobah Yana Daraja Ka!

“Ya tuna da mu cikin ƙasƙancinmu.”​—ZAB. 136:23.

WAƘA TA 33 Mu Miƙa Dukan Damuwarmu ga Jehobah

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1-2. Waɗanne yanayoyi ne bayin Jehobah da yawa suke fuskanta, kuma yaya hakan zai iya shafan su?

KA YI la’akari da misalan nan uku: Likitoci sun yi wa wani ɗan’uwa matashi gwaji, kuma sun gano cewa yana da ciwo mai tsanani. Akwai wani ɗan’uwa da ya wuce shekara 50 kuma an sallame shi daga aiki. Bayan haka, ya kasa samun wani aiki duk da ƙoƙarinsa. Wata ʼyar’uwa tsohuwa ba ta iya yin ayyuka da yawa a hidimar Jehobah yadda ta saba ba.

2 Idan kana fuskantar ɗaya daga cikin waɗannan yanayoyin, za ka iya ji kamar ba ka da daraja. Irin yanayin nan zai iya sa ka baƙin ciki, ya sa ka rena kanka kuma ya hana ka yin cuɗanya da mutane.

3. Ta yaya Shaiɗan da bayinsa suke ɗaukan rayukan mutane?

3 Yanayin duniyar nan ya nuna yadda Shaiɗan yake ɗaukan rayukanmu. A kowane lokaci, Shaiɗan yana sa mutane su ji kamar ba su da amfani. Domin Shaiɗan mugu ne, ya yaudari Hauwa’u ta taka dokar Allah ko da yake ya san cewa za ta mutu. Shaiɗan ya daɗe yana iko a kan sashen kasuwanci da siyasa da kuma addini na wannan zamanin. Shi ya sa ba abin mamaki ba ne cewa mutane da yawa da suke kasuwanci da siyasa da malaman addinai ba sa daraja rayukan mutane kuma ba su damu da yadda suke ji ba.

4. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

4 Akasin haka, Jehobah yana so mu san cewa muna da  daraja a gare shi kuma yana taimaka mana sa’ad da muke cikin mawuyacin yanayi. (Zab. 136:23; Rom. 12:3) A wannan talifin, za mu tattauna yadda Jehobah yake taimaka mana a waɗannan yanayoyin: (1) Sa’ad da muke fama da rashin lafiya, (2) sa’ad da muke fama da rashin kuɗi, da kuma (3) sa’ad da tsufa ya sa mu ji kamar ba za mu iya yin hidima ga Jehobah ba. Bari mu fara tattauna dalilin da ya sa muke da tabbaci cewa Jehobah yana daraja kowannenmu.

JEHOBAH YANA DARAJA MU

5. Me ya sa ka tabbata cewa mutane suna da daraja ga Jehobah?

5 Muna da daraja sosai duk da cewa da turɓaya aka yi mu. (Far. 2:7) Ku yi la’akari da dalilan nan da suka nuna cewa muna da daraja. Jehobah ya halicce mu mu yi koyi da halayensa. (Far. 1:27) Ta hakan, ya sa mutane su fi sauran halittunsa a duniya daraja. Me ya sa? Domin ya ce mu kula da duniya da kuma dabbobi.​—Zab. 8:​4-8.

6. Wane abu ne kuma ya sa muka san cewa Jehobah yana daraja ʼyan Adam ajizai?

6 Jehobah ya ci gaba da daraja mutane har bayan da Adamu ya yi zunubi. Ya daraja mu sosai shi ya sa ya aiko da Ɗansa da yake ƙauna, wato Yesu don ya fanshe mu daga zunubi. (1 Yoh. 4:​9, 10) Da yake Yesu ya fanshe mu, Jehobah zai tayar da mutanen da suka mutu sanadiyyar zunubin Adamu, wato “masu adalci da marasa adalci.” (A. M. 24:15) Kalmar Allah ta nuna cewa muna da daraja a gabansa ko da mu talakawa ne ko tsofaffi ko kuma muna fama da rashin lafiya.​—A. M. 10:​34, 35.

7. Wane ƙarin dalilai ne bayin Allah suke da shi na gaskata cewa Jehobah yana daraja su?

7 Muna da ƙarin dalilai na gaskata cewa Jehobah yana daraja mu. Ya sa mu kusace shi kuma ya lura da yadda muka ɗauki gaskiyar da muka koya. (Yoh. 6:44) Yayin da muka soma ƙulla abota da Jehobah, sai ya kusace mu. (Yaƙ. 4:8) Jehobah yana kuma mai da hankali sosai wajen ilimantar da mu kuma hakan ya nuna cewa yana daraja mu. A yanzu, ya san mu sosai kuma ya san abin da za mu iya zama a nan gaba. Ƙari ga haka, yana mana horo domin yana ƙaunar mu. (K. Mag. 3:​11, 12) Hakan ya nuna cewa Jehobah yana daraja mu!

8. Ta yaya Zabura 18:​27-29 za su iya shafan yadda muke ɗaukan ƙalubalen da muke fuskanta?

8 Wasu mutane sun ɗauki Sarki Dauda a matsayin mutumin banza, amma ya san cewa Jehobah yana ƙaunar sa kuma yana goyon bayansa. Kasancewa da wannan ra’ayin ya taimaka wa Dauda sosai. (2 Sam. 16:​5-7) Idan muna baƙin ciki ko fama da yanayi mai wuya, Jehobah zai iya taimaka mana mu kasance da ra’ayin da ya dace kuma mu magance matsalolin. (Karanta Zabura 18:​27-29.) Idan Jehobah yana goyon bayanmu, babu abin da zai iya hana mu bauta masa da farin ciki. (Rom. 8:31) Yanzu, bari mu tattauna yanayoyi uku da za mu bukaci mu tuna cewa Jehobah yana ƙaunar mu kuma yana daraja mu.

SA’AD DA MUKE RASHIN LAFIYA

Karanta Kalmar Jehobah zai taimaka mana mu magance baƙin cikin da muke yi don rashin lafiya (Ka duba sakin layi na 9-12)

9. Ta yaya rashin lafiya zai iya shafan yadda muke ɗaukan kanmu?

9 Rashin lafiya zai iya shafar mu sosai kuma ya sa mu ji kamar ba mu da amfani. Muna iya jin kunya sa’ad da mutane  suka lura cewa muna da matsala ko kuma muna bukatar taimako. Ko da mutane ba su lura cewa muna rashin lafiya ba, muna iya jin kunya domin mun kāsa sosai. Jehobah yana taimaka mana sa’ad da muke cikin irin yanayin nan. Ta yaya yake yin hakan?

10. Kamar yadda Karin Magana 12:25 ta nuna, me zai iya taimaka mana sa’ad da muke fama da rashin lafiya?

10 Kalma mai ban ‘ƙarfafa’ za ta iya sa mu farin ciki. (Karanta Karin Magana 12:25.) Jehobah ya yi furuci da yawa masu daɗi a cikin Littafi Mai Tsarki da suke tuna mana cewa yana daraja mu ko da muna rashin lafiya. (Zab. 31:19; 41:3) Idan muka karanta Kalmar Allah sau da sau, Jehobah zai taimaka mana mu magance baƙin cikin da muke fama da shi sanadiyyar rashin lafiya.

11. Ta yaya Jehobah ya taimaka wa wani ɗan’uwa?

11 Ku yi la’akari da labarin Jorge. A lokacin da Jorge yake matashi, ya kamu da wani ciwo mai tsanani kuma hakan ya sa shi baƙin ciki sosai. Jorge ya ce: “Saboda rashin lafiyata, mutane suna yawan kallo na kuma ban shirya fuskantar irin matsalar ba. Yayin da rashin lafiyar ta daɗa yin tsanani, na yi tunani a kan yadda rayuwata za ta canja. Na yi baƙin ciki matuƙa kuma na roƙi Jehobah ya taimaka mini.” Ta yaya Jehobah ya taimaka masa? Ya ce: “Da yake ina yawan tunani a kan rashin lafiyata, an ƙarfafa ni in riƙa karanta wasu gajerun ayoyi a Zabura da suka nuna cewa Jehobah yana kula da mu. Ina sake karanta ayoyin kowace rana, kuma sun ƙarfafa ni. Bayan ɗan lokaci, sai mutane suka lura cewa na soma farin ciki. Sun ma ce farin cikin da nake yi ya ƙarfafa  su. Na ga cewa Jehobah ya amsa addu’o’ina! Ya taimaka mini in canja yadda nake ɗaukan kaina. Na soma mai da hankali a kan abin da Kalmar Allah ta ce game da yadda Jehobah yake ɗauka na duk da rashin lafiyar da nake yi.”

12. Idan muna fama da rashin lafiya, me za mu iya yi don Jehobah ya taimaka mana?

12 Idan kana fama da rashin lafiya, ka kasance da tabbaci cewa Jehobah ya san abin da kake fuskanta. Ka roƙe shi ya taimake ka ka kasance da ra’ayi mai kyau game da yanayinka. Bayan haka, ka bincika kalmomi masu daɗi da Jehobah ya sa a rubuta a Kalmarsa domin kai. Ka mai da hankali a kan ayoyin da ke nuna yadda Jehobah yake daraja bayinsa. Yayin da kake yin haka, za ka ga cewa Jehobah yana yin alheri ga dukan masu bauta masa da aminci.​—Zab. 84:11.

SA’AD DA MUKE FAMA DA RASHIN KUƊI

Tuna cewa Jehobah ya ce zai tanadar da bukatunmu zai taimaka mana sa’ad da ba mu da aiki (Ka duba sakin layi na 13-15)

13. Ta yaya magidanci zai ji idan ya rasa aikinsa?

13 Babu shakka, dukan magidanta suna so su biya bukatun iyalinsu. Amma wani ɗan’uwa zai iya rasa aikinsa duk da cewa bai yi wani laifi ba. Bayan haka, zai iya neman wani aiki amma ya kasa samu. Hakan zai iya sa shi matuƙar baƙin ciki. Ta yaya mai da hankali a kan alkawuran Jehobah zai iya taimaka masa?

14. Me ya sa Jehobah yake cika alkawuransa?

14 Jehobah yana cika alkawuransa a koyaushe. (Yosh. 21:45; 23:14) Yana yin hakan don dalilai da yawa. Na farko, hakan zai iya shafan sunansa mai tsarki. Jehobah ya riga ya ce zai kula da bayinsa masu aminci kuma ya zama masa tilas ya yi hakan. (Zab. 31:​1-3) Bugu da ƙari, Jehobah ya san cewa ranmu zai ɓace idan bai kula da mu ba, wato iyalinsa. Ya yi mana  alkawari cewa zai tanadar da bukatunmu na zahiri kuma zai taimaka mana mu riƙa bauta masa. Babu wani abu da ya isa ya hana shi cika alkawarinsa!​—Mat. 6:​30-33; 24:45.

15. (a) Wane ƙalubale ne Kiristoci suka fuskanta a ƙarni na farko? (b) Wane tabbaci ne Zabura 37:​18, 19 suka sa mu kasance da shi?

15 Idan mun tuna dalilan da suka sa yake cika alkawuransa, za mu iya tabbata cewa zai taimaka mana sa’ad da muke fama da rashin kuɗi. Ka yi la’akari da misalin Kiristoci a ƙarni na farko. A lokacin da aka soma tsananta wa Kiristoci a Urushalima, dukansu sun warwatse “sai dai manzannin ne kawai suka rage.” (A. M. 8:1) Ka yi tunani a kan abin da hakan ya jawo. Da yake sun rasa gidajensu da sana’o’insu, babu shakka, sun talauce sosai! Duk da haka, Jehobah bai yasar da su ba kuma ba su daina farin ciki ba. (A. M. 8:4; Ibran. 13:​5, 6; Yaƙ. 1:​2, 3) Jehobah ya taimaka wa waɗannan Kiristoci masu aminci, kuma mu ma zai taimaka mana.​—Karanta Zabura 37:​18, 19.

SA’AD DA KAKE FAMA DA TSUFA

Mai da hankali a kan abin da za mu iya yi ko da mun tsufa zai tabbatar mana da cewa Jehobah yana daraja mu da kuma hidimarmu (Ka duba sakin layi na 16-18)

16. Mene ne zai iya sa mu ji kamar Jehobah ba ya daraja ibadarmu?

16 Yayin da muke tsufa, za mu iya soma lura cewa ƙarfinmu ya ragu kuma abin da muke yi a hidimar Jehobah ya ragu. Wataƙila Sarki Dauda ma ya ji haka sa’ad da yake tsufa. (Zab. 71:9) Ta yaya Jehobah zai iya taimaka mana?

17. Wane darasi ne za mu iya koya daga labarin Jheri?

17 Ku yi la’akari da labarin wata ʼyar’uwa mai suna Jheri. An kira ta da wasu ʼyan’uwa zuwa Majami’ar Mulki don a koya musu yadda ake kula da wuraren ibadarmu.  Amma ba ta so zuwa ba. Ta ce: “Ni gwauruwa ce, na tsufa kuma ba ni da wani iyawa don yin aikin nan. A gaskiya, ba ni da wani amfani.” A dare na ƙarshe kafin su je ajin, ta yi addu’a sosai ga Jehobah. Sa’ad da ta isa Majami’ar washegari, ta ci gaba da yin shakka ko ya dace da ta je wurin. A lokacin da aka soma koyar da su, ɗaya cikin ʼyan’uwan ya gaya musu cewa baiwa mafi muhimmanci da suke bukata don yin aikin shi ne su yarda Jehobah ya koyar da su. Sai ta ce wa kanta: “ ‘Ina da wannan baiwar!’ Bayan haka, na soma zub da hawaye domin na ga cewa Jehobah ya amsa addu’ata. Jehobah yana gaya min cewa ina da abu mai daraja da zan iya ba shi kuma yana a shirye ya koyar da ni!” Jheri ta daɗa da cewa: “A ranar, na shiga Majami’ar cike da tsoro da sanyin gwiwa. Amma na fito cike da farin ciki da kuma ƙarfafa.”

18. Ta yaya Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Jehobah yana daraja ibadarmu yayin da muke tsufa?

18 Yayin da muke tsufa, ya kamata mu kasance da tabbaci cewa Jehobah zai ci gaba da yin amfani da mu. (Zab. 92:​12-15) Yesu ya koya mana cewa kome iyawarmu ko ƙarfinmu, Jehobah yana daraja kowane abu da muke yi a hidimarsa. (Luk. 21:​2-4) Saboda haka, ku mai da hankali a kan abin da za ku iya yi. Alal misali, za ku iya yin addu’a a madadin ʼyan’uwanku, ku yi wa’azi kuma ku ƙarfafa ʼyan’uwa su riƙe aminci. Jehobah yana ɗaukan ku a matsayin abokan aikinsa, ba domin abubuwan da kuke yi a hidimarsa ba, amma domin kuna a shirye ku yi masa biyayya.​—1 Kor. 3:​5-9.

19. Wane tabbaci ne Romawa 8:​38, 39 suka ba mu?

19 Muna murna sosai cewa muna bauta wa Jehobah, wanda shi Allah ne da ke daraja bayinsa. Ya halicce mu mu riƙa yin nufinsa kuma bauta ta gaskiya ce take sa mu samun gamsuwa. (R. Yar. 4:11) Ko da yake mutane a duniyar nan za su iya sa mu ji kamar ba mu da amfani, amma Jehobah yana daraja mu. (Ibran. 11:​16, 38) Idan muna baƙin ciki saboda rashin lafiya, ko rashin kuɗi ko kuma tsufa, ya kamata mu riƙa tuna cewa babu abin da zai iya raba mu da ƙaunar da Ubanmu na sama yake mana.​—Karanta Romawa 8:​38, 39.

^ sakin layi na 5 Ka taɓa fuskantar yanayin da ya sa ka ji kamar ba ka da daraja? Wannan talifin zai sa ka san cewa Jehobah yana daraja ka sosai. Zai sa ka ci gaba da daraja kanka ko da wacce irin matsala ce kake fuskanta a rayuwa.

WAƘA TA 30 Jehobah Ubana, Allahna da Abokina