Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 TALIFIN NAZARI NA 6

Ka Rike Amincinka!

Ka Rike Amincinka!

“Har in mutu, ba zan daina tsare mutuncina ba.”​—AYU. 27:5.

WAƘA TA 34 Mu Riƙe Amincinmu ga Jehobah

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Ta yaya Shaidun Jehobah da aka ambata a wannan sakin layi suka riƙe aminci ga Jehobah?

KA YI tunani a kan waɗannan yanayi uku da za su iya shafan Shaidun Jehobah. (1) Wata rana, wata yarinya Mashaidiya ta je makaranta kuma malamarsu ta ce dukan yaran ajin su yi wani bikin da bai dace ba. Yariyar ta san cewa yin wannan bikin ba zai faranta wa Allah rai ba. Saboda haka, ta ƙi saka hannu a bikin. (2) Wani matashi yana wa’azi gida-gida kuma ya san cewa gidan wani abokin makarantarsu da ya taɓa yi wa Shaidun Jehobah ba’a yana gaba. Duk da haka, matashin ya je gidan kuma ya ƙwanƙwasa ƙofar. (3) Wani mutum yana aiki tuƙuru don ya biya bukatun iyalinsa, sai wata rana shugaban aikinsa ya ce ya yi wani abu da ya taka doka. Ko da yake ya san cewa ƙin yin hakan zai iya sa ya rasa aikinsa, ya bayyana wa shugabansa cewa wajibi ne ya riƙa faɗin gaskiya kuma ya bi doka domin abin da Allah yake so ke nan.​—Rom. 13:​1-4; Ibran. 13:18.

2. Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna, kuma me ya sa?

2 Wane hali ne waɗannan Shaidu uku suke da shi? Suna da halaye da yawa, kamar ƙarfin hali da kuma faɗin gaskiya. Amma aminci ne ya yi fice a cikin sauran halayensu. Kowannensu ya kasance da aminci ga Jehobah kuma sun ƙi su taka ƙa’idodin Allah. Waɗannan Shaidun sun ɗauki wannan matakin don suna da aminci. Jehobah zai yi alfahari da kowannensu don amincinsu. Hakazalika, ya kamata mu sa Jehobah yin alfahari da mu. Saboda haka, bari mu tattauna waɗannan tambayoyin: Mene ne aminci? Me ya sa muke bukatar mu riƙe aminci? Ta yaya za mu ƙuduri niyyar mu ci gaba da riƙe aminci a yau?

 MENE NE AMINCI YAKE NUFI?

3. (a) Ta yaya bayin Allah suke nuna aminci? (b) Waɗanne misalai ne za su taimaka mana mu fahimci abin da aminci yake nufi?

3 Ta yaya bayin Allah suke nuna aminci? Suna yin hakan ta wurin ƙaunar Jehobah da dukan zuciyarsu, kuma hakan yana sa su yi abin da yake faranta masa rai. Ka yi la’akari da yadda ake amfani da kalmar nan a cikin Littafi Mai Tsarki. Kalmar nan aminci tana nufin cikakkiya ko marar aibi ko kuma abin da aka ba da gabaki ɗaya. Alal misali, Isra’ilawa sun miƙa hadayun dabobbi ga Jehobah kuma a Dokar, an ce ya kamata dabbar ta kasance cikakkiya ko lafiyayya. (L. Fir. 22:​21, 22) Ba a karɓan dabbar da ta gurgunce ko ta makance ko kuma ba ta da kunne ɗaya. Kuma ba a yin hadaya da dabba mai rashin lafiya. Jehobah yana bukatar dabbar ta zama cikakkiya ko lafiyayya ko kuma marar aibi. (Mal. 1:​6-9) Hakan ya sa mun fahimci abin da ya sa Jehobah yake son mu miƙa cikakkiyar hadaya. Idan muna so mu sayi wani abu, wataƙila ’ya’yan itatuwa ko littafi ko kuma wani kayan aiki, mukan sayi mai kyau ba mai huji ba ko kuma wanda ya rasa wasu sassa ba. Muna son abu cikakke ko lafiyayye ko kuma marar aibi. Hakazalika, Jehobah yana so mu riƙa ƙaunar sa da dukan zuciyarmu ko kuma mu riƙe amincinmu a gare shi. Wajibi ne hadayarmu ta zama cikakkiya ko marar aibi.

4. (a) Me ya sa ajizai za su iya riƙe aminci? (b) Mene ne Zabura 103:​12-14 ya ce Jehobah yake bukata a gare mu?

4 Ya kamata ne mu yi tunani cewa wajibi ne mu zama kamiltattu kafin mu riƙe aminci? Muna iya ganin cewa muna yin kuskure da yawa. Amma, ka yi la’akari da dalilai biyu da ya sa ba ma bukatar mu riƙa jin tsoro. Na farko, Jehobah ba ya mai da hankali ga kurakuranmu. Kalmarsa ta ce: “Ya Ubangiji, idan kana lissafa laifofi, wa zai tsaya?” (Zab. 130:3) Jehobah ya san cewa mu ajizai ne kuma mu masu zunubi ne, saboda haka yakan gafarta mana zunubanmu. (Zab. 86:5) Na biyu, Jehobah ya san kasawarmu, kuma ba ya sa mu yi abin da ya fi ƙarfinmu. (Karanta Zabura 103:​12-14.) Saboda haka, ta yaya za mu zama cikakku ko marar aibi a gaban Jehobah?

5. Me ya sa bayin Jehobah suke bukatar nuna ƙauna domin su kasance da aminci?

5 Abin da zai taimaka wa bayin Jehobah su riƙe aminci shi ne nuna ƙauna. Wajibi ne mu riƙa ƙaunar Allah da bauta masa da aminci da dukan zuciyarmu. Mu masu aminci ne idan muna ƙaunar Allah sosai har a lokacin da muke fuskantar gwaji. (1 Tar. 28:9; Mat. 22:37) Ka sake yin la’akari da Shaidu uku da aka ambata ɗazu. Me ya sa suka kasance da aminci? Shin yarinyar ba ta son shaƙatawa ne a makaranta ko kuma matashin yana son a riƙa masa ba’a ne? Mutumin nan kuma fa, yana so ya rasa aikinsa ne? A’a. Maimakon haka, sun san cewa Jehobah ya kafa ƙa’idodi masu kyau, kuma sun mai da hankali ga yin abin da yake faranta masa rai. Domin suna ƙaunar sa, sukan sa shi farko a duk shawarwarin da suke yi. Ta hakan suna nuna cewa su masu aminci ne.

ABIN DA YA SA MUKE BUKATAR MU RIƘE AMINCI

6. (a) Me ya sa kake bukatar ka kasance da aminci? (b) Ta yaya Adamu da Hauwa’u suka kasa kasancewa da aminci?

6 Me ya sa kowannenmu yake bukatar ya kasance da aminci? Muna bukatar hakan domin Shaiɗan ya zargi Jehobah, kuma ya zarge mu. Wannan mala’ika da ya yi  tawaye ya mai da kansa Shaiɗan ko “Mai tsayayya,” a lambun Adnin. Ya ɓata sunan Jehobah ta wajen cewa Allah mugu ne mai son kai, da kuma Sarkin da ba ya faɗin gaskiya. Abin baƙin ciki, Adamu da Hauwa’u sun goyi bayan Shaiɗan kuma suka yi wa Jehobah tawaye. (Far. 3:​1-6) Yin rayuwa a lambun Adnin ta ba su zarafin ƙaunar Jehobah sosai. Amma, ba su ƙaunace shi da dukan zuciyarsu ba a lokacin da Shaiɗan ya zargi Jehobah. Hakan ya sa aka yi wata tambaya: ’Yan Adam za su kasance da aminci ga Jehobah don suna ƙaunar sa kuwa? Wato, ’yan Adam za su iya kasancewa da aminci ne? Abin da Ayuba ya fuskanta ne ya sa aka yi wannan tambayar.

7. Ta yaya Jehobah da Shaiɗan suka ɗauki amincin Ayuba kamar yadda littafin Ayuba 1:​8-11 ya nuna?

7 Ayuba ya yi rayuwa a zamanin da Isra’ilawa suke Masar, kuma babu mai aminci a lokacin kamar shi. Amma kamar mu, shi ajizi ne kuma ya yi kurakurai da yawa. Duk da haka, Jehobah ya ƙaunaci Ayuba sosai domin amincinsa. Kamar dai Shaiɗan ya riga ya gaya wa Jehobah cewa ’yan Adam ba za su kasance da aminci ba. Shi ya sa Jehobah ya gaya wa Shaiɗan cewa Ayuba mai aminci ne kuma amincinsa ya nuna cewa Shaiɗan maƙaryaci ne! Shaiɗan ya ce Jehobah ya ƙyale shi ya jarraba Ayuba. Jehobah ya amince da abokinsa Ayuba kuma Ya bar Shaiɗan ya jarraba shi.​—Karanta Ayuba 1:​8-11.

8. Ta yaya Shaiɗan ya kai wa Ayuba farmaki?

8 Shaiɗan mazalunci ne da kuma mai kisan kai. Ya halaka dukiyar Ayuba, ya kashe bayinsa kuma ya ɓata sunansa. Ya kashe dukan yaran Ayuba guda goma. Ƙari ga haka, ya sa Ayuba rashin lafiya sosai ta  wajen harbin sa da marurai daga kansa har ƙafafunsa. Waɗannan abubuwa sun sa matar Ayuba baƙin ciki da kuma makoki har ta gaya wa mijinta ya zagi Allah kuma ya mutu. Ayuba ya gwammaci mutuwa amma ya riƙe aminci. Sai Shaiɗan ya yi amfani da wata dabara. Ya yi amfani da abokan Ayuba guda uku. Mutanen sun kawo ma Ayuba ziyara amma sun yi kwanaki ba su ce masa kome ba. Maimakon haka, sun zarge shi kuma sun tsauta masa. Sun ce Allah ne ya jawo dukan matsalolin da yake fuskanta kuma Allah bai damu ba ko ya riƙe aminci. Ban da haka, sun ce Ayuba mugu ne kuma abubuwan da yake fuskanta ya dace da shi!​—Ayu. 1:​13-22; 2:​7-11; 15:​4, 5; 22:​3-6; 25:​4-6.

9. Duk da jarrabawar da Ayuba ya fuskanta, mene ne ya ƙi yi?

9 Yaya Ayuba ya bi da dukan waɗannan matsaloli? Shi ajizi ne, ya yi fushi, ya tsauta wa abokansa kuma ya yi magana a garaje. Ƙari ga haka, ya fi ɗaukaka kansa don amincinsa fiye da yadda ya ɗaukaka Allah. (Ayu. 6:3; 13:​4, 5; 32:2; 34:5) Amma, Ayuba ya ƙi ya daina bauta wa Jehobah ko a lokacin da yanayinsa ya yi muni sosai. Ya ƙi ya gaskata da ƙaryace-ƙaryacen abokansa. Ya ce: “Allah ya sawwaƙa in yarda kuna da gaskiya, har in mutu, ba zan daina tsare mutuncina ba.” (Ayu. 27:5) Wannan furuci ya nuna cewa Ayuba ya ƙuduri niyyar riƙe amincinsa ko da mene ne ya faru. Ayuba ya kasance da aminci sosai, mu ma za mu iya yin hakan.

10. Ta yaya batun da Shaiɗan ya ta da game da Ayuba ya shafe ka?

10 Ta yaya batun da Shaiɗan ya ta da game da Ayuba ya shafe mu? Yana da’awa cewa, ba ka ƙaunar Jehobah, wai za ka daina bauta wa Jehobah kuma ba za ka riƙe aminci ba! (Ayu. 2:​4, 5; R. Yar. 12:10) Yaya hakan ya sa ka ji? Ya ɓata maka rai, ko ba haka ba? Amma ka yi tunanin wannan, Jehobah ya amince da kai sosai har ya ba ka wannan zarafi mai ban al’ajabi. Jehobah yana barin Shaiɗan ya jarraba amincinka, amma Allah yana da tabbaci cewa za ka riƙe aminci kuma ka nuna cewa Shaiɗan maƙaryaci ne. Kuma Jehobah ya yi alkawari cewa zai taimaka maka ka yi hakan. (Ibran. 13:6) Hakika, samun amincewar Jehobah gata ne babba. Hakan ya nuna cewa kasancewa da aminci yana da muhimmanci sosai. Yana taimaka maka ka ƙaryata Shaiɗan, ka ɗaukaka sunan Jehobah kuma ka goyi bayan sarautarsa. Mene ne za mu yi don mu riƙe aminci?

YADDA ZA MU RIƘE AMINCI A YAU

11. Mene ne za mu iya koya daga Ayuba?

11 Shaiɗan yana daɗa tsananta wa bayin Allah a wannan “kwanakin ƙarshe.” (2 Tim. 3:1) Ta yaya za mu riƙe aminci a duk lokacin da muka samu kanmu a irin wannan yanayin? Za mu koyi darasi sosai daga Ayuba. Ayuba mutum ne mai aminci kafin Shaiɗan ya soma tsananta masa. Ka yi la’akari da darussa uku da za mu koya daga Ayuba da za su taimaka mana mu riƙe aminci.

A waɗanne hanyoyi ne za mu ƙarfafa kanmu don mu riƙe amincinmu? (Ka duba sakin layi na 12) *

12. (a) Kamar yadda littafin Ayuba 26:​7, 8, 14 ya nuna, ta yaya Ayuba ya koyi girmama Jehobah da kuma daraja shi? (b) Me zai taimaka mana mu riƙa girmama Jehobah?

12 Ayuba ya ƙarfafa ƙaunarsa ga Jehobah ta wajen girmama shi. Ayuba yakan keɓe lokaci sosai yana tunani game da abubuwan da Jehobah ya yi. (Karanta Ayuba 26:​7, 8, 14.) Ya yi mamaki sosai sa’ad da yake tunani game da duniya da sararin sama da gajimare da kuma  tsawa. Duk da haka, ya fahimci cewa bai san abubuwa da yawa game da halittun Jehobah ba. Ƙari ga haka, yana daraja furucin Jehobah, shi ya sa ya ce: “Zuciyata na ɓoye maganar bakinsa.” (Ayu. 23:12) Ayuba yana girmama Jehobah sosai kuma hakan ya sa shi ya riƙa daraja shi. Yana ƙaunar Allah kuma ya so ya faranta masa rai. Saboda haka ya ƙuduri niyyar riƙe aminci ga Jehobah kuma muna bukatar mu yi koyi da shi. Mun san game da halittun Allah fiye da mutanen da ke zamanin Ayuba. Muna da Littafi Mai Tsarki da zai taimaka mana mu san Jehobah sosai. Dukan abubuwan da muka koya zai sa mu riƙa daraja Jehobah. Hakan zai sa mu riƙa ƙaunar Jehobah da yi masa biyayya. Ƙari ga haka, za mu ƙuduri niyyar riƙe aminci.​—Ayu. 28:28.

Muna ƙarfafa kanmu mu riƙe amincinmu ta wajen ƙin kallon hotunan batsa (Ka duba sakin layi na 13) *

13-14. Ta yaya littafin Ayuba 31:1 ya nuna cewa Ayuba mai biyayya ne? (b) Ta yaya za mu bi misalin Ayuba?

13 Yin biyayya ga Jehobah a kowane lokaci ya taimaka wa Ayuba ya riƙe amincinsa. Ayuba ya san cewa idan yana so ya riƙe aminci wajibi ne ya riƙa yi wa Jehobah biyayya. Muna ƙarfafa amincinmu ga Jehobah idan muna yi masa biyayya a kowane lokaci. Ayuba ya yi iya ƙoƙarinsa don ya riƙa yi wa Allah biyayya kullum. Alal misali, ya mai da hankali a yadda yake sha’ani da mata. (Karanta Ayuba 31:1.) Tun da yake yana da aure, ya san bai dace ba ya riƙa yin kwarkwasa da mace da ba matarsa ba. A yau, muna zama da mutane da ke yawan jarraba mu da abubuwan lalata. Kamar Ayuba, za mu riƙa yin cuɗanya da bai dace da wanda ba miji ko matarmu ba? Ya dace ne mu riƙa kallon hotunan batsa? (Mat. 5:28) Idan muna kame kanmu a kowace rana, za mu ƙarfafa kanmu mu riƙe aminci.

Muna ƙarfafa kanmu mu riƙe amincinmu ta wajen kasancewa da ra’ayin da ya dace game da abin duniya (Ka duba sakin layi na 14) *

14 Ayuba ya kuma yi wa Jehobah biyayya a yadda yake ɗaukan abin duniya. Ya fahimci cewa idan ya dogara ga dukiyarsa, zai yi zunubi mai tsanani kuma ya  kamata a hukunta shi. (Ayu. 31:​24, 25, 28) A yau, muna zama a duniyar da mutane suke yawan son abin duniya. Za mu ƙuduri niyyar riƙe aminci idan muka bi ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da suka ce mu kasance da ra’ayin da ya dace game da kuɗi da kuma dukiya.​—K. Mag. 30:​8, 9; Mat. 6:​19-21.

Muna ƙarfafa kanmu mu riƙe amincinmu ta wajen yin tunanin begen mu na nan gaba (Ka duba sakin layi na 15) *

15. (a) Begen wace albarka ce ya taimaka wa Ayuba ya riƙe amincinsa? (b) Me ya sa yin tunanin yadda Jehobah zai albarkace mu a nan gaba zai taimaka mana?

15 Ayuba ya riƙe aminci ta wajen sa rai cewa Allah zai albarkace shi. Ya gaskata cewa Allah yana farin ciki don yana riƙe da aminci. (Ayu. 31:6) Duk da jarrabawar da Ayuba ya fuskanta, yana da tabbaci cewa Allah zai albarkace shi. Jehobah ya yi farin ciki cewa Ayuba ya riƙe aminci kuma ya albarkace shi sosai duk da cewa shi ajizi ne! (Ayu. 42:​12-17; Yaƙ. 5:11) Ƙari ga haka, za a albarkaci Ayuba sosai a nan gaba. Kana da tabbaci cewa Jehobah zai albarkace ka don amincinka? Allahnmu bai canja ba. (Mal. 3:6) Idan muka tuna cewa Allah yana son mu kasance da aminci, hakan zai taimaka mana mu riƙa tunanin irin rayuwa da za mu yi a nan gaba.​—1 Tas. 5:​8, 9.

16. Me ya kamata mu ƙudiri niyyar yi?

16 Saboda haka, ka kuɗiri niyyar riƙe amincinka! A wasu lokuta za ka ga kamar duk mutane da ke kusa da kai ba sa riƙe aminci, amma ba za ka taɓa kaɗaita ba. Za ka kasance cikin miliyoyin mutane masu aminci a faɗin duniya. Ƙari ga haka, za ka kasance cikin maza da mata masu bangaskiya a dā da suka riƙe amincinsu, har a lokacin da ake barazana cewa za a kashe su. (Ibran. 11:​36-38; 12:1) Bari dukanmu mu kuɗiri niyyar riƙe amincinmu kamar Ayuba da ya ce: “Ba zan daina tsare mutuncina ba.” Kuma bari amincinmu ya sa a ɗaukaka Jehobah har abada!

WAƘA TA 124 Mu Kasance da Aminci

^ sakin layi na 5 Mene ne aminci yake nufi? Me ya sa Jehobah yake so bayinsa su kasance da wannan halin? Me ya sa yake da muhimmanci kowannenmu ya riƙe aminci? Wannan talifin zai taimaka mana mu sami amsoshin waɗannan tambayoyin. Ƙari ga haka, zai taimaka mana mu ci gaba da riƙe aminci a kowace rana, don yin hakan zai sa mu sami albarka sosai.

^ sakin layi na 49 BAYANI A KAN HOTUNA: Ayuba sa’ad da bai tsufa ba yana koya ma wasu cikin yaransa game da abubuwan da Jehobah ya halitta.

^ sakin layi na 51 BAYANI A KAN HOTUNA: Wani ɗan’uwa ya ƙi bin abokan aikinsa kallon batsa.

^ sakin layi na 53 BAYANI A KAN HOTUNA: Wani ɗan’uwa a ƙi sayan babban talabijin mai tsada don ba ya bukatar sa kuma ba shi da kuɗin saya.

^ sakin layi na 55 BAYANI A KAN HOTUNA: Wani ɗan’uwa yana keɓe lokaci don ya yi bimbini a kan begen yin rayuwa a cikin Aljanna.