Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 TALIFIN NAZARI NA 8

Me Ya Sa Nuna Godiya Yake da Muhimmanci?

Me Ya Sa Nuna Godiya Yake da Muhimmanci?

Ku “kasance masu godiya.”​—KOL. 3:15.

WAƘA TA 46 Muna Godiya, Ya Jehobah

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Ta yaya wani Basamaren da Yesu ya warkar ya nuna godiya?

AKWAI wasu mazaje goma da suke cikin mawuyacin yanayi. Suna da ciwon kuturta kuma ba su da bege cewa za su sami sauƙi. Amma wata rana, sai suka hango Yesu Babban Malami daga nesa. Sun taɓa ji cewa Yesu yana warkar da dukan cututtuka kuma suna da tabbaci cewa zai iya warkar da su. Saboda haka, sai suka ɗaga murya suka ce: “Ya Yesu Mai girma! Ka ji tausayinmu!” A sakamakon haka, Yesu ya warkar da su. Babu shakka, sun yi farin ciki don yadda Yesu ya tausaya musu. Amma ɗaya daga cikinsu ya dawo wurin Yesu don ya gode * masa. Mutumin Basamare ne kuma abin da Yesu ya yi masa ya motsa shi ya “yi wa Allah godiya.”​—Luk. 17:​12-19.

2-3. (a) Me zai iya hana mu nuna godiya? (b) Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

2 Muna so mu yi koyi da halin wannan Basamaren ta wajen nuna godiya don alherin da aka yi mana. Amma a wasu lokuta, muna iya manta mu yi godiya don alherin da aka yi mana.

3 A wannan talifin, za mu tattauna muhimmancin nuna godiya ta furucinmu da ayyukanmu. Za mu koyi darasi daga misalan wasu da aka ambata a Littafi Mai Tsarki da suka nuna godiya da kuma waɗanda ba su yi hakan ba.  Bayan haka, za mu tattauna wasu hanyoyin da za mu iya nuna godiya.

ME YA SA YA DACE MU RIƘA NUNA GODIYA?

4-5. Me ya sa ya dace mu riƙa nuna godiya?

4 Jehobah ya kafa mana misali a nuna godiya. Hanya ɗaya da yake yin hakan ita ce ta wajen sāka wa mutanen da ke faranta masa rai. (2 Sam. 22:21; Zab. 13:6; Mat. 10:​40, 41) Kuma Nassosi sun ƙarfafa mu mu ‘ɗauki misali daga wurin Allah a cikin zamanmu.’ (Afis. 5:1) Saboda haka, dalili na musamman na nuna godiya shi ne domin muna so mu bi misalin Jehobah.

5 Ku yi la’akari da wani dalili kuma na nuna godiya ga mutane. Muna farin ciki idan muka san cewa mutane suna godiya don abin da muka yi. Saboda haka, muna sa mutane farin ciki idan muka nuna godiya don abin da suka yi mana. Mutumin da muka nuna masa godiya ya san cewa yadda ya taimaka mana ko kuma kyautar da ya ba mu ta biya bukatunmu. Kuma hakan zai sa abokantakar mu da shi ya yi ƙarfi.

6. Wace alaƙa ce ke tsakanin nuna godiya da kuma adon zinariya da aka a yi a kan azurfa?

6 Nuna godiya yana da muhimmanci sosai. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Maganar da ta fito daidai take, kamar adon zinariyar da aka yi a kan azurfa.” (K. Mag. 25:11) Babu shakka, adon zinariyar da aka yi a kan azurfa yana da kyau sosai da kuma tamani! Yaya za ka ji idan aka ba ka irin wannan kyautar? Babu shakka, za ka yi farin ciki. Hakazalika, nuna godiya don abin da aka yi maka yana da tamani sosai. Ƙari ga haka, adon zinariya a kan azurfa ba ya saurin lalacewa. Saboda haka, mutumin da ka nuna masa  godiya zai ci gaba da tunawa da furucinka muddar ransa.

SUN NUNA GODIYA

7. Ta yaya Dauda, kamar yadda Zabura 27:4 ta nuna da kuma wasu marubutan zabura suka nuna godiya?

7 Bayin Allah da yawa a dā sun nuna godiya. Ɗaya cikinsu shi ne Dauda. (Karanta Zabura 27:4.) Ya ɗauki bauta wa Allah da muhimmanci sosai kuma ya nuna hakan ta abubuwan da ya yi. Ya ba da gudummawa da dama sa’ad da ake shirin gina haikali. ’Ya’yan Asaf sun nuna godiya ta wajen rubuta waƙoƙin yabo. A wata waƙar da suka rera, sun yabi Allah kuma suka furta cewa ayyukansa na da “ban mamaki.” (Zab. 75:1) Hakika, Dauda da ’ya’yan Asaf suna so su nuna wa Jehobah cewa suna godiya don dukan abubuwan da ya yi musu. Ka san hanyoyin da za ka iya yin koyi da waɗannan marubutan zabura kuwa?

Wane darasi ne wasiƙar Bulus ga Romawa ya koya mana game da nuna godiya? (Ka duba sakin layi na 8-9) *

8-9. Ta yaya manzo Bulus ya ƙarfafa ’yan’uwansa, kuma wane sakamako ne hakan ya kawo?

8 Manzo Bulus yana daraja ’yan’uwansa kuma ya nuna hakan ta yadda yake musu magana. Bulus yakan gode wa Allah don waɗannan ’yan’uwa a duk lokacin da yake addu’a ga Allah. Kuma yana gaya musu cewa suna da daraja a gare shi a lokacin da yake rubuta musu wasiƙa. A littafin Romawa sura 16 ayoyi 1 zuwa 15, Bulus ya ambata sunayen ’yan’uwa maza da mata 27. Ya tuna cewa Akila da Biriskilla sun yi hassada da “ransu” dominsa, kuma ya ce Fibi ta taimaka wa shi da kuma “mutane da yawa.” Ya yaba ma waɗannan ’yan’uwa maza da mata masu ƙwazo sosai.​—Rom. 16:​1-15.

9 Manzo Bulus ya kammala wasiƙarsa ga Romawa ta wajen ambata halaye masu kyau na ’yan’uwan, duk da cewa yana sane da kurakurensu. Ka yi tunanin yadda ’yan’uwan suka ji sa’ad da aka ambata sunayensu a wasiƙar da aka karanta wa ikilisiyar! Babu shakka, hakan ya ƙarfafa abotarsu da Bulus. Kana yawan nuna godiya don alherin da ’yan’uwa a ikilisiyarku suka yi maka?

10. Wane darasi ne za mu iya koya daga yadda Yesu ya nuna godiya ga mabiyansa?

10 A cikin saƙonnin da Yesu ya aika wa wasu ikilisiyoyin da ke Asiya Ƙarama, ya nuna godiya don ayyukan da mabiyansa suke yi. Alal misali, ya soma saƙon da ya aika wa ikilisiyar Tiyatira da kalmomin nan: ‘Na san ayyukanki, da ƙaunarki da amincinki. Na san hidimarki da jimrewarki. Na sani cewa ayyukanki na yanzu sun fi na farkon.’ (R. Yar. 2:19) Yesu bai yaba musu don ci gabar da suka samu kawai ba, amma ya yaba musu don halayen da suka motsa su su yi hakan. Ko da yake Yesu ya yi wa wasu cikinsu gargaɗi, duk da haka, ya soma maganarsa da ƙarfafawa. (R. Yar. 2:​25-28) Yesu ne shugaban dukan ikilisiyoyi kuma yana da iko sosai. Ba ya bukatar ya gode mana don aikin da muka yi masa, duk da haka, yana tabbatar da cewa ya yaba mana. Babu shakka, wannan misali mai kyau ne sosai ga dattawa!

BA SU NUNA GODIYA BA

11. Kamar yadda littafin Ibraniyawa 12:16 ya nuna, ta yaya Isuwa ya ɗauki abubuwa na ibada?

11 Abin baƙin ciki ne cewa wasu mutanen da aka ambata a Littafi Mai Tsarki ba su nuna godiya ba. Alal misali, Isuwa bai daraja abubuwa na ibada ba duk da cewa iyayensa bayin Jehobah ne. (Karanta Ibraniyawa 12:16.) Wane abu ne Isuwa ya yi da ya nuna wannan hali marar  kyau? Ya sayar wa ƙanensa Yakubu gādonsa saboda jar miya. (Far. 25:​30-34) Daga baya, Isuwa ya yi da-na-sani sosai don zaɓin da ya yi. Dā ma can bai daraja gādonsa ba. Saboda haka, ba shi da hujjar yin gunaguni sa’ad da bai sami albarka ba.

12-13. Ta yaya Isra’ilawa suka nuna rashin godiya, kuma wane sakamako ne hakan ya jawo?

12 Da akwai abubuwa da dama da suka faru wa Isra’ilawa da ya kamata ya riƙa sa su nuna godiya. Jehobah ya cece su daga zaman bauta a ƙasar Masar bayan ya kawo Annoba Goma a kan Masarawa. Bayan haka, ya halaka rundunar Masarawa a Jar Teku don kada su kashe Isra’ilawa. Hakan ya sa Isra’ilawa murna sosai har suka soma rera waƙar yabo ga Jehobah. Amma sun ci gaba da yin godiya kuwa?

13 Sa’ad da Isra’ilawa suka soma shan wahala, sun manta dukan alherin da Jehobah ya yi musu. Sai suka soma tawaye. (Zab. 106:7) Littafi Mai Tsarki ya ce “dukan jama’ar Isra’ila suka yi wa Musa da Haruna gunaguni,” amma Jehobah ne ainihi suka wa gunagunin. (Fit. 16:​2, 8) Rashin godiyar da mutanen suka nuna ya sa Jehobah baƙin ciki sosai. Bayan haka, ya faɗa cewa dukan tsarar za su mutu a cikin jeji. Ya ce Yoshuwa da Kaleb ne kawai za su tsira. (L. Ƙid. 14:​22-24; 26:65) Bari mu ga yadda za mu guji bin waɗannan misalai marasa kyau kuma mu yi koyi da misalai masu kyau.

YADDA ZA MU RIƘA NUNA GODIYA A YAU

14-15. (a) Ta yaya ma’aurata za su nuna cewa suna daraja juna? (b) Ta yaya iyaye za su koya wa yaransu su riƙa nuna godiya?

14 A cikin iyali. Kowa a cikin iyali yana amfana idan kowannensu yana nuna godiya. Idan ma’aurata suna nuna godiya ga juna, hakan zai sa su kusaci juna sosai. Zai kuma kasance musu da sauƙi su riƙa gafarta wa juna. Mijin da ke daraja matarsa yana lura da ayyukanta masu kyau da kuma furucinta masu daɗi. Ƙari ga haka, “yakan yabe ta.” (K. Mag. 31:​10, 28) Kuma macen kirki tana gaya wa mijinta halayensa masu kyau da take so.

15 Iyaye, ta yaya za ku koya wa yaranku su riƙa nuna godiya? Ku tuna cewa yaranku suna yin koyi da furucinku da ayyukanku. Saboda haka, ku kafa misali mai kyau ta wajen ce musu kun gode a lokacin da suka taya ku yin wani abu.  Ƙari ga haka, ku koya musu su riƙa yin godiya a duk lokacin da aka yi musu alheri. Ku taimaka wa yaranku su fahimci cewa nuna godiya abu ne da ke fitowa daga zuciya kuma furta hakan yana da muhimmanci sosai. Alal misali, wata mai suna Clary ta ce: “Sa’ad da mahaifiyata take ’yar shekara 32, an kai babanmu kurkuku kuma ita ce kaɗai ta kula da mu uku har muka girma. A lokacin da ni ma na kai ’yar shekara 32, na yi tunani a kan yadda ya kasance wa mahaifiyata da wuya ta kula da mu a lokacin. Saboda haka, na gode mata sosai don dukan sadaukarwar da ta yi domin ta rene mu. A kwana-kwanan nan, ta gaya mini cewa furucina ya taimaka mata sosai, ta ce tana yawan tunani a kan furucin kuma yana sa ta farin ciki.”

Ku koya wa yaranku su riƙa nuna godiya (Ka duba sakin layi na 15) *

16. Ka faɗi misalin da ya nuna cewa nuna godiya yana ƙarfafa mutane sosai.

16 A cikin ikilisiya. Nuna godiya ga ’yan’uwanmu yana ƙarfafa su. Alal misali, akwai wani dattijo ɗan shekara 28 mai suna Jorge da ya yi ciwo mai tsanani. Ciwon bai bari ya je taro ba har tsawon wata ɗaya. Bayan ya sami sauƙi, bai iya yin jawabi ba. Jorge ya ce: “Na yi baƙin ciki sosai domin ban iya yin kome a cikin ikilisiya ba. Amma wata rana bayan an tashi taro, wani ɗan’uwa ya ce min: ‘Ina so in gode maka sosai don yadda ka kafa wa iyalina misali mai kyau. Ba ka san yadda muka daɗe muna jin daɗin jawabanka ba.’ Hakan ya sosa zuciyata sosai har na fara kuka. Furucinsa ne ainihin abin da nake so in ji.”

17. Kamar yadda littafin Kolosiyawa 3:15 ya nuna, ta yaya za mu nuna godiya ga Jehobah don karimcinsa?

17 Ga Allahnmu mai karimci. Jehobah ya yi mana tanadodi masu yawa da suke ƙarfafa dangantakarmu da shi. Alal misali, muna samun koyarwa masu kyau a taro da mujallunmu da kuma dandalinmu. Ka taɓa karanta wani talifi ko ka kalli shirin JW kuma ka yi tunani cewa, ‘Ainihin abin da nake bukata ke nan.’ Ta yaya za mu nuna godiya ga Jehobah? (Karanta Kolosiyawa 3:15.) Hanya ɗaya ita ce ta wajen gode masa a cikin addu’a a kai a kai don waɗannan kyaututtuka.​—Yaƙ. 1:17.

Taimakawa wajen tsabtace Majami’ar Mulki hanya ce mai kyau ta nuna godiya (Ka duba sakin layi na 18)

18. Ta yaya za mu nuna cewa muna daraja majami’unmu?

18 Muna kuma nuna godiya ga Jehobah  sa’ad da muka tsabtace da kuma gyara wuraren ibadarmu. Muna taimaka wajen share Majami’un Mulki da yin gyare-gyare, kuma wasu suna mai da hankali sosai wajen kula da na’urorin da ake amfani da su a taro. Idan muna kula da Majami’unmu sosai, za su daɗe kuma ba za su riƙa saurin lalacewa ba. Ta hakan, za a sami kuɗaɗen gina da kuma gyara wasu Majami’un Mulki a faɗin duniya.

19. Wane darasi ne ka koya daga wani mai kula mai ziyara da matarsa?

19 Ga mutanen da suke aiki tuƙuru dominmu. Idan muna gode wa mutane, hakan zai iya canja ra’ayinsu game da ƙalubalen da suke fuskanta. Ka yi la’akari da labarin wani mai kula mai ziyara da matarsa. Akwai wata rana da suka dawo daga wa’azi a gajiye. A lokacin, ana sanyi sosai kuma matarsa ta yi barci sanye da rigar sanyinta. Washegari da safe, sai ta gaya wa maigidanta cewa ba za ta iya ci gaba da hidimar ba. Bayan ’yan sa’o’i, sai suka sami wasiƙa daga ofishinmu kuma matarsa ce aka aika wa wasiƙar. A cikin wasiƙar, an yaba mata don hidimar da take yi da kuma jimirinta. An ambata a wasiƙar yadda yake da wuya mutum ya riƙa kwana a gidaje dabam-dabam kowane mako. Maigidan ya ce: “Wasiƙar ta sosa zuciyarta sosai har ba ta sake cewa za ta daina hidimar ba. Ta ma ƙarfafa ni sau da yawa sa’ad da na ce ina so in daina hidimar.” Waɗannan ma’auratan sun ci gaba da yin wannan hidimar har kusan shekara 40.

20. Me ya kamata mu riƙa yi a kowace rana?

20 Zai dace mu riƙa nuna godiya kowace rana ta furucinmu da ayyukanmu. Wataƙila furucinmu ko ayyukanmu ne zai taimaka wa wani ɗan’uwa ya ci gaba da jimrewa a wannan duniyar da yawancin mutane ba sa nuna godiya. Kuma zai sa mu ƙulla dangantakar da za ta jure har abada. Mafi muhimmanci ma, za mu nuna cewa muna yin koyi da Ubanmu Jehobah, Mai alheri da kuma godiya.

WAƘA TA 20 Ka Ba da Ɗanka Mai Daraja

^ sakin layi na 5 Wane darasi ne za mu iya koya daga wurin Jehobah da Yesu da kuma wani kuturu Basamare game da nuna godiya? Za mu tattauna waɗannan misalan da kuma wasu a wannan talifin. Za mu kuma tattauna muhimmancin nuna godiya da hanyoyin da za mu iya yin hakan.

^ sakin layi na 1 MA’ANAR WASU KALMOMI: Nuna godiya yana nufin sanin darajar wani abu ko kuma wani mutum. Kalmar tana iya nufin yin matuƙar farin ciki.

^ sakin layi na 55 BAYANI A KAN HOTUNA: Ana karanta wa ikilisiyar da ke Roma wasiƙar Bulus; Akila da Biriskilla da Fibi da kuma wasu suna farin ciki don an ambata sunayensu.

^ sakin layi na 57 BAYANI A KAN HOTUNA: Wata mahaifiya tana taimaka wa ’yarta ta nuna godiya ga wata ’yar’uwa tsohuwa don misalinta mai kyau.