Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DAGA TARIHINMU

Jawabi ga Jama’a Ya Sa Bishara Ta Yadu a Ireland

Jawabi ga Jama’a Ya Sa Bishara Ta Yadu a Ireland

YAYIN DA jirgin ya kusan kai gaɓar tekun da ke Belfast, fasinjoji ƙalila da ke tsaye sun hango wani tudun mai cike da ciyayi da itatuwa. Hakan ya faru ne a watan Mayu, 1910. Wannan ne ƙaro na biyar da Ɗan’uwa Charles T. Russell ya je ƙasar Ireland. Sai Ɗan’uwa Russell ya ga manyan jirage guda biyu da ake ƙerawa, wato Titanic da kuma Olympic. * Ɗaliban Littafi Mai Tsarki da yawa sun tsaya a gaban masana’ar jirgin suna jiran shi.

A wajen shekara 20 kafin wannan lokacin, Ɗan’uwa Russell ya soma tafiye-tafiye zuwa wasu ƙasashe don ya yaɗa bishara. Wurin da ya fara zuwa shi ne Ireland a watan Yuli na 1891. Da suke cikin jirgi a Chicago, ya hangi faɗuwar rana a garin Queenstown da ake kira Cobh yanzu. Babu shakka, ya tuna yadda iyayensa suke kwatanta garinsu. Yayin da Ɗan’uwa Russell da abokan tafiyarsa suke wucewa ta ƙananan garuruwa da ƙauyuka masu kyau, sun lura cewa birnin ya “isa girbi.”

Sau bakwai ne Ɗan’uwa Russell ya ziyarci ƙasar Ireland. Ziyararsa ta farko ce ta sa mutane da yawa suka saurare shi sa’ad da ya sake ziyartar su. Da ya sake yin hakan a ƙaro na biyu a watan Mayu, 1903, an sanar da jawabi ga jama’a da za a yi a birnin Belfast da Dublin a jaridu. Russell ya ce “mutane sun saurari” jawabin da ya yi game da bangaskiyar Ibrahim da kuma albarkar da ʼyan Adam za su samu a nan gaba.

Da Ɗan’uwa Russell ya je ƙasashen Turai a ƙaro na uku, ya sake zuwa Ireland domin mutanen suna son gaskiya. ’Yan’uwa biyar ne suka marabce shi sa’ad da ya sauko daga jirgin ruwa a birnin Belfast a wata safiya na watan Afrilu, 1908. “Mutane wajen 300 masu ilimi sosai” ne suka saurari jawabin da yammar. Jigon shi ne “The Overthrow of Satan’s Empire” (Yi wa Shaiɗan Juyin Mulki). Russell ya yi amfani da Nassosi wajen amsa tambayoyin da wani ɗan sūka ya yi. Akwai wani ɗan sūka kuma a Dublin mai taurin kai sosai mai suna O’Connor. Shi ne sakataren ƙungiyar YMCA kuma ya nemi ya sa wajen mutane 1,000 su ƙi sauraron Ɗaliban Littafi Mai Tsarki. Amma me mutanen suka yi?

Bari mu kwatanta abin da wataƙila ya faru a wannan taron. Wani mutum da ke son ya san game da Jehobah ya zo jin jawabin da aka sanar a jaridar The Irish Times. Da kyar ya sami wurin zama a wajen taron don mutane sun cika maƙil. Mutumin ya saurara sosai sa’ad da wani mai furfura da ke sanye da doguwar baƙar riga yake yin jawabi. Mai jawabin yakan yi ta yawo a dakalin kuma yana alama da hannunsa. Ƙari ga haka, yana bayyana Nassosi ɗaya bayan ɗaya kuma wannan mutumin da ya halarci taron yana fahimta sosai. Ko da yake mai jawabin ba ya amfani da makarufo, masu  sauraro suna jin muryarsa sosai kuma sun saurara har awa ɗaya da rabi. O’Connor da abokansa sun so su ƙaryata mai jawabin a sashen tambayoyi da kuma amsoshi. Amma, ya amsa tambayoyinsu da Littafi Mai Tsarki kuma masu sauraron sun tafa masa sosai. Sa’ad da yanayin ya lafa, sai mutumin ya je wurin ’yan’uwan don ya sami ƙarin bayani. Waɗanda suka shaida abin da ya faru sun ce ta hakan ne mutane da yawa suka koyi gaskiya.

A ƙaro na huɗu da Ɗan’uwa Russell ya je tsibirin Mauretania daga birnin New York a watan Mayu na 1909, ya je da Ɗan’uwa Huntsinger. Russell ya je da ɗan’uwan don ya iya amfani da tafireta. Sa’ad da suke cikin jirgi, Russell yana gaya masa abin da zai rubuta, sai ɗan’uwan ya buga talifofin Hasumiyar Tsaron a tafireta. Mutane 450 ne suka saurari jawabin da Ɗan’uwa Russell ya yi a Belfast, kuma wajen mutane 100 sun tsaya don babu wurin zama.

Ɗan’uwa C. T. Russell a cikin jirgin Lusitania

Haka ma suka yi a ƙaro na biyar kamar yadda aka ambata a farkon talifin nan. Bayan an gama jawabin a birnin Dublin, Ɗan’uwa Russell ya amsa tambayoyin da wani shahararren limami da O’Connor ya kawo ya yi. Amsoshin ya sa mutanen farin ciki sosai. Washegari, sai suka shiga jirgi zuwa birnin Liverpool. Bayan haka, suka shiga jirgin ruwan da ake kiran Lusitania zuwa birnin New York. *

An sanar da jawabi a jaridar The Irish Times, a ranar 20 ga Mayu, 1910

An kuma yi jawaban da aka sanar a jaridu sa’ad da Russell ya je ziyararsa ta shida da bakwai a 1911. A watan Afrilu, Ɗaliban Littafi Mai Tsarki a Belfast sun kula da mutane 2,000 da suka saurari jawabin nan mai jigo “Hereafter” (Rayuwa Bayan Mutuwa). Sai O’Connor ya sake zuwa Dublin tare da wani limami da ya ta yi wa Russell tambayoyi. Amma Russell ya amsa tambayoyin kuma masu sauraro sun yi tafi sosai. A watan Oktoba da Nuwamba, mutane da yawa daga garurruka biyu sun halarci taron. O’Connor da maza 100 sun sake zuwa taron da aka yi a Dublin don su ta da ƙura, amma masu sauraron su goyi bayan mai jawabin.

Ko da yake Ɗan’uwa Russell ne yake yawan yin jawabi a lokacin, amma ya san cewa Jehobah zai iya yin amfani da kowane mutum wajen cim ma nufinsa. Jawabai ga jama’a sun taimaka wajen koyar da gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Wane sakamako ne aka samu? Mutane a ko’ina sun ji bisharar Mulki kuma an kafa sababbin ikilisiyoyi da yawa a Ireland.​—Daga tarihinmu a Biritaniya.

^ sakin layi na 3 Jirgin Titanic ya nitse wajen shekara biyu da ƙera shi.

^ sakin layi na 9 An halaka jirgin Lusitania a kusa da gaɓar tekun da ke kudancin Ireland a watan Mayu, 1915.