Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Kun Sami ‘Yanci Saboda Alherinsa

Kun Sami ‘Yanci Saboda Alherinsa

“Zunubi ba zai mallake ku ba, tun da yake ba shari’a ke iko da ku ba, alherin Allah ne.”​—ROM. 6:​14, Littafi Mai Tsarki.

WAƘOƘI: 261

1, 2. Me ya sa littafin Romawa 5:12 yake da muhimmanci ga Shaidun Jehobah?

A CE kana son ka rubuta nassosin da Shaidun Jehobah suka sani sosai kuma suka cika amfani da su. Shin za ka tuna da Romawa 5:12? Wurin ya ce: “Kamar yadda zunubi ya shigo cikin duniya ta wurin mutum ɗaya, mutuwa kuwa ta wurin zunubi; har fa mutuwa ta bi kan dukan mutane, da yake duka sun yi zunubi.” Babu shakka, kana amfani da wannan nassin sosai, ko ba haka ba?

2 An yi amfani da wannan ayar sau da yawa a littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? A lokacin da kake amfani da wannan littafin wajen yin nazari da yaranka ko wasu, kana iya karanta Romawa 5:12 sa’ad da kake tattauna nufin Allah game da duniya da fansa da kuma yanayin matattu a babi na 3 da 5, da kuma 6. Amma ka taɓa tunanin yadda Romawa 5:12 ta shafi dangantakarka da Allah da halinka da kuma abin da kake begensa?

3. Mene ne ya kamata mu sani game da yanayinmu?

3 Babu shakka, dukanmu mun san cewa mu masu zunubi ne. Muna kuskure kowace rana. Duk da haka, muna da  tabbaci cewa Allah yana sane da yanayinmu. Ya san mu turɓaya ne kuma zai nuna mana jin ƙai. (Zab. 103:​13, 14) A addu’ar misali, Yesu ya ce: “Ka gafarta mana zunubanmu.” (Luk. 11:​2-4) Saboda haka, bai kamata mu bar zunuban da Allah ya gafarta mana su riƙa damunmu ba. Don haka, yana da kyau mu bincika yadda Allah yake gafarta mana zunubanmu.

YA GAFARTA MANA SABODA ALHERINSA

4, 5. (a) Wane bayani mai muhimmanci ne muka samu a Romawa 5:12? (b) Mene ne ‘alherin’ Allah da aka ambata a Romawa 3:⁠24?

4 Bulus ya yi bayani mai muhimmanci sosai kafin ya faɗi abin da ke Romawa 5:12 da kuma bayan hakan, musamman ma abin da ya faɗa a sura ta 6. Wannan bayanin zai taimaka mana mu fahimci yadda Jehobah yake gafarta mana zunubanmu. Wasu ayoyi a sura 3 sun ce: “Dukan mutane sun yi zunubi . . . , bisa ga alherinsa an barata a yalwace ta wurin fansa da ke cikin Yesu Kristi.” (Rom. 3:​23, 24) Mene ne manzo Bulus yake nufi sa’ad da ya ambaci ‘alherin’ Allah? Wani bincike ya nuna cewa ya yi amfani da wata kalmar Helenanci da take nufin “alfarma da aka nuna wa wani ba tare da ya biya ba.” Kuma bai cancanci a yi masa wannan alfarma ba.

5 Wani masani mai suna John Parkhurst ya ce: “Wannan kalmar Helenanci da aka yi amfani da ita tana nufin abin da Allah da Yesu suka yi don su ceci mutane daga zunubi da mutuwa.” Kuma abin da aka fassara a juyin New World Translation ke nan kuma hakan ya dace. Amma ta yaya Allah ya nuna wannan alherin? Kuma ta yaya ya shafi begen da muke da shi da kuma dangantakarmu da Allah? Bari mu bincika.

6. Su wa za su amfana daga alherin Allah?

6 Adamu ne “mutum ɗaya” da ya sa zunubi da mutuwa suka “shigo cikin duniya.” Don haka, “laifin” mutum ɗaya ne ya sa ‘mutuwa ta mallake’ mu. Bulus ya ƙara da cewa mun sami “yalwar alheri” ta wurin “ɗayan, Yesu Kristi.” (Rom. 5:​12, 15, 17) Kuma wannan alherin zai amfani dukan mutane. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ta wurin biyayyar ɗayan [Yesu] masu-yawa za su barata.” Babu shakka, alherin Allah zai sa mutane su sami “rai na har abada ta wurin Yesu Kristi.”​—⁠Rom. 5:​19, 21.

7. Me ya sa fansar da Allah ya tanadar mana alheri ne?

7 Ba wajibi ba ne Jehobah ya aiko da ɗansa duniya don ya fanshe mu. Ƙari ga haka, mu ajizai ba mu cancanci wannan fansa da Allah da Yesu suka tanadar don gafarar zunubanmu ba. Don haka, tanadin fansa da kuma zarafin yin rayuwa a duniya har abada alheri ne da Allah ya nuna mana. Shi ya sa ya kamata mu ɗauki fansar da muhimmanci kuma mu riƙa yin rayuwa da ta jitu da ƙa’idodin Allah.

TA YAYA ZA MU NUNA GODIYA SABODA ALHERIN ALLAH?

8. Wane irin ra’ayi ne ya kamata mu guje wa?

8 Da yake mu ‘ya’yan Adamu ne, mun gāji zunubi. Duk da haka, ba zai dace mu riƙa tunanin cewa: ‘Ai bai kamata in damu ko na yi zunubi ba don Jehobah zai gafarta mini.’ Abin baƙin ciki, wasu Kiristoci sun kasance da wannan ra’ayin a ƙarni na farko. (Karanta Yahuda 4.) Ya kamata mu ma  mu yi hankali don kada mu soma irin wannan tunanin.

9, 10. Ta yaya aka ‘yantar da Bulus da wasu daga zunubi da mutuwa?

9 Manzo Bulus ya ce wajibi ne mu guji ra’ayin nan cewa: ‘Allah zai gane. Ba zai riƙa damuwa da zunubaina ba.’ Me ya sa? Domin Bulus ya ce Kiristoci sun “mutu ga zunubi.” (Karanta Romawa 6:​1, 2.) Ta yaya za a ce Kiristocin da suke raye a duniya sun “mutu ga zunubi”?

10 Bulus da kuma wasu a zamaninsa sun amfana daga fansar da Allah ya tanadar. Shi ya sa Jehobah ya gafarta musu zunubansu, ya shafe su da ruhu mai tsarki kuma ya kira su ‘ya’yansa. Don haka, suna da begen yin rayuwa a sama. Idan suka kasance da aminci, za su yi sarauta tare da Yesu a sama. Wannan ne ya sa Bulus ya ce sun “mutu ga zunubi” ko da yake har ila suna nan duniya suna yi wa Allah ibada. Ƙari ga haka, ya ba da misalin Yesu da ya mutu kuma aka tayar da shi a matsayin ruhu zuwa sama. Saboda haka, mutuwa ba ta sarauta a kan Yesu. Haka ma yake da Kiristoci shafaffu waɗanda suka zama ‘matattu ga zunubi amma rayayyu ga Allah cikin Kristi Yesu.’ (Rom. 6:​9, 11) Sun daina halaye marasa kyau kuma suka gyara rayuwarsu. Wannan canjin da suka yi yana kamar sun mutu ga zunubi ne.

11. Ta yaya mu da ke da begen rayuwa a Aljanna a duniya muka “mutu ga zunubi”?

11 Mu kuma fa? Kafin mu zama Kiristoci, mun yi ta zunubi ba tare da sanin yadda Allah yake ji game da zunubanmu ba. Mun zama kamar “bayi ga ƙazanta da mugunta” ko kuma “bayin zunubi.” (Rom. 6:​19, 20) Bayan haka, sai muka koyi gaskiyar Littafi Mai Tsarki muka gyara halayenmu kuma muka yi alkawarin bauta wa Allah, muka yi baftisma. Tun daga lokacin, muradinmu ne mu riƙa biyayya da “zuciya ɗaya,” muna bin umurni da ƙa’idodin Allah. Don haka, an ‘yantar da mu daga zunubi’ kuma mun “zama bayin adalci.” (Rom. 6:​17, 18) Saboda haka, za a iya ce waɗanda suke da begen rayuwa a duniya ma sun “mutu ga zunubi.”

12. Wace shawara ce kowannenmu yake bukatar ya tsai da wa kansa?

12 Yanzu ka yi tunani a kan kalaman Bulus cewa: “Kada zunubi fa ya yi mulki cikin jikinku mai-mutuwa, da za ku biye wa sha’awoyinsa.” (Rom. 6:12) Za mu iya barin “zunubi ya yi mulki” a kanmu idan muka yi duk wani abin da zuciyarmu take so. Da yake muna da ikon tsai da shawarar barin zunubi ya yi mulki a kanmu ko kuma mu sa ya daina yin hakan, Me ya kamata mu yi? Za ka iya tambayar kanka: ‘Ina barin zuciyata a wasu lokuta ta rinjaye ni in riƙa yin abin da bai dace ba? Ko kuma na daina yin zunubi kuma ina rayuwa daidai da ƙa’idodin Allah?’ Hakan ya dangana ga yadda muka ɗauki alherin da Allah ya nuna mana ta wurin gafarta mana zunubanmu.

ZA KA IYA YIN NASARA

13. Wane misali ne ya nuna mana cewa zai yiwu mu daina yin zunubi?

13 Bayin Jehobah sun daina halayen banza da suke yi a dā kafin su san shi, sun ƙaunace shi kuma suka soma bauta masa. Suna ganin abubuwan da suka yi a dā kamar “abin kunya” ne kuma waɗannan abubuwan suna iya kai ga mutuwa. (Rom. 6:21) Amma sun gyara halayensu. Haka ne yanayin waɗanda manzo Bulus ya rubuta musu  wasiƙa a Koranti yake. Wasunsu masu bautar gumaka ne da mazinata da ‘yan daudu da ɓarayi da masu shaye-shaye da dai sauransu. Duk da haka, “aka wanke” su kuma aka “tsarkake” su. (1 Kor. 6:​9-11) Haka yanayin wasu yake a ikilisiyar da ke Roma. Shi ya sa Bulus ya gaya musu cewa: “Kada ku ba da gaɓaɓuwa naku ga aika zunubi da kuma aika rashin adalci; amma ku miƙa kanku ga Allah, wato, masu rai daga cikin matattu, gaɓaɓuwa naku kuma alatun adalci zuwa ga Allah.” (Rom. 6:13) Bulus ya tabbata cewa irin waɗannan mutanen za su iya kasancewa da dangantaka mai kyau da Allah kuma su amfana daga alherinsa.

14, 15. Me ya kamata mu tambayi kanmu game da yin biyayya da “zuciya ɗaya”?

14 Haka yake a yau, a dā wasu a cikinmu kamar ‘yan’uwa a ikilisiyar Koranti suke. Amma sun daina halayen banza kuma suka gyara rayuwarsu sai “aka wanke” su. Kai fa, yaya dangantakarka da Allah take? Yanzu da Allah ya nuna maka alheri kuma aka gafarta maka zunubinka, shin ka kuɗiri aniya ka daina yin “zunubi” kuma ka riƙa yin adalci?

15 Don mu iya yin haka, wajibi ne mu guji zunubai masu tsanani da wasu a Koranti suka yi. Yana da muhimmanci sosai mu yi hakan idan har mun amince da alherin Allah kuma ba ma barin “zunubi ya yi mulki” a kanmu. Ƙari da haka, muna bukatar mu kuɗiri aniya mu riƙa biyayya da “zuciya ɗaya,” ta wurin yin iya ƙoƙarinmu don mu guji yin zunubai da wasu suke ganin ba shi da tsanani.​—⁠Rom. 6:​14, 17.

16. Ta yaya muka san cewa zama Kirista ba kawai daina yin zunubai masu tsanani ba?

16 Ka yi tunani game da manzo Bulus. Mun tabbata cewa bai yi waɗannan abubuwan da aka ambata a 1 Korintiyawa 6:​9-11 ba. Duk da haka, ya ce shi ma mai zunubi ne. Ya rubuta cewa: “Ni kuwa mai halin mutuntaka ne, bautar zunubi kawai nake yi. Ban ma fahimci abin da nake yi ba. Don ba abin da nake niyya shi nake aikatawa ba, abin da nake ƙi, shi nake yi.” (Rom. 7:​14, 15, LMT) Hakan ya nuna cewa akwai wasu abubuwan da Bulus yake yi da yake gani zunubai ne kuma yana ƙoƙarin ya kawar da su, ko ba haka ba? (Karanta Romawa 7:​21-23.) Bari mu ma mu bi misalinsa sa’ad da muke ƙoƙarin yin biyayya da “zuciya ɗaya.”

17. Me ya sa muke bukatar mu kasance masu faɗan gaskiya?

17 Alal misali, bari mu tattauna batun kasancewa mai faɗan gaskiya. Ya kamata Kiristoci su riƙa faɗan gaskiya. (Karanta Misalai 14:5; Afisawa 4:25.) Shaiɗan “uban ƙarya” ne. Hananiya da matarsa sun mutu saboda yin ƙarya. Da yake ba ma so mu yi koyi da irin waɗannan mutanen, muna guje wa yin ƙarya. (Yoh. 8:44; A. M. 5:​1-11) Shin wannan dalilin ne kaɗai ya sa muke guje wa yin ƙarya? A’a. Idan muna faɗin gaskiya, hakan yana nuna cewa muna godiya don alherin da Allah ya nuna mana.

18, 19. Me yake nufi mutum ya kasance mai faɗan gaskiya?

18 Mutum yana iya zama wanda ba ya faɗan gaskiya ko da bai yi ƙarya kai tsaye ba. Jehobah ya gaya wa Isra’ilawa na dā: “Sai ku zama masu-tsarki: gama ni Ubangiji Allahnku mai-tsarki ne.” Bayan haka, sai ya ba su misalan kasancewa da tsarki. Ya ce: ‘Ba za ku yi sata ba: ba kuwa za ku yi  aikin ha’inci ba, ba kuwa za ku yi ma junanku ƙarya ba.’ (Lev. 19:​2, 11) Saboda haka, mutumin da ba ya ƙarya kai tsaye zai iya yin ha’inci ko kuma ya yaudari mutane.

Shin mun kuɗiri aniyar guje wa yin ƙarya da yaudara? (Ka duba sakin layi na 19)

19 Alal misali, wani zai iya gaya wa shugabansa ko abokan aikinsa cewa ba zai iya zuwa aiki washegari ba don yana son ya je asibiti ko wurin da ake sayar da magani da sassafe. Amma ba wai yana ciwo ba ne, mai yiwuwa yana son ya je ya yi wani abu dabam ne a wurin. Ba rashin lafiya ba ne ya sa bai je aiki ba, amma yana son ya yi wata tafiya ne da iyalinsa don shaƙatawa. Ko da yake ya je asibiti ko kuma wurin da ake sayar da magani, za ka ce ya faɗi ainihin dalilin da ya sa bai je aiki ba ne? Hakan babu shakka yaudara ce ko wayo, ko ba haka ba? Wataƙila ya yi hakan ne don ya sami hujjar yin tafiya. Ko da yake bai yi ƙarya kai tsaye ba, amma umurnin da Allah ya bayar shi ne: ‘Ba kuwa za ku yi aikin hainci ba,’ wato yaudarar mutane. Har ila littafin Romawa 6:19 ya ce: “Ku ba da gaɓaɓuwanku bayi ga adalci zuwa tsarkakewa.”

20, 21. Mene ne alherin Allah zai sa mu yi?

20 Nuna godiya ga alherin Allah ya ƙunshi fiye da guje wa zina da shaye-shaye da wasu zunubai da wasu a ikilisiyar Koranti suka yi a dā. Amincewa da alherin Allah zai sa mu guji fasikanci har da nishaɗin da zai sa mu yi tunaninsa. Kasancewa bayin adalci ko masu adalci ya kamata ya sa mu daina yawan shan giya. Don haka, muna bukatar mu yi ƙoƙari sosai don mu guji irin waɗannan halayen. Idan muka yi hakan, za mu yi nasara.

21 Ya kamata mu ƙuduri aniyar guje wa dukan zunubai, ko da yake yin hakan zai iya yi mana wuya don mu ajizai ne. Ya kamata mu yi ƙoƙari kamar yadda Bulus ya yi. Ya ce: “Kada zunubi fa ya yi mulki cikin jikinku mai-mutuwa, da za ku biye wa sha’awoyinsa.” (Rom. 6:12; 7:​18-20) Amma idan muka yi ƙoƙari wajen guje wa kowane irin zunubi, hakan zai nuna cewa muna godiya ga alherin Allah.

22. Wane lada ne waɗanda suka nuna godiya ga alherin Allah za su samu?

22 Ta wurin alherin Allah an gafarta mana zunubanmu kuma Allah zai ci gaba da yin hakan. Don haka, bari mu yi ƙoƙari mu shawo kan abubuwan da muke yi da muke gani ba zunubi ba ne. Bulus ya ambata ladan da za mu samu. Ya ce: “Amma yanzu ‘yantattu daga zunubi, har kun zama bayi ga Allah, kuna da amfaninku zuwa tsarkakewa, matuƙa kuma rai na har abada.”​—Rom. 6:22.