HASUMIYAR TSARO—NA NAZARI Disamba 2016

Wannan fitowar tana dauke da talifofin nazari da za a yi daga ranar 30 ga Janairu zuwa 26 ga Fabrairu, 2017.

TARIHI

“Na Zama Dukan Abu ga Dukan Mutane”

Ayyukan da Denton Hopkinson ya yi sun taimaka masa ya ga yadda Jehobah yake kaunar dukan mutane.

Kun Sami ‘Yanci Saboda Alherinsa

Za ka sami albarka sosai ta wajen yin nazarin yadda Jehobah ya ‘yantar da kai daga zunubi.

Kwallafa Rai ga Al’amuran Ruhu Zai Sa a Sami Rai da Kuma Salama

Littafin Romawa sura 8 ya ba da shawarar da za ta iya taimaka maka ka sami albarkar Jehobah da zai yi wa dukan ‘yan Adam.

Ka Tuna?

Ka karanta Hasumiyar tsaro na kwanan bayan nan kuwa? Ka ga ko za ka iya amsa wasu tambayoyin Littafi Mai Tsarki.

Ku Gaya wa Jehobah Damuwarku

A wasu lokatai bayin Allah suna alhini. Matakai hudu za su taimaka maka ka amfana daga ‘salama ta Allah.’

Jehobah Yana Sāka wa Wadanda Suke Bidarsa

Ta yaya begen samun albarka daga wurin Jehobah yake amfanarmu? Ta yaya ya sāka wa bayinsa a dā kuma ta yaya yake yi hakan a yau?

Mai Hikima Yana Kame Kansa

Ba shi da sauki ka kame kanka sa’ad da wani ya hasala maka, duk da haka, Littafi Mai Tsarki ya karfafa Kiristoci su rika kame kansu. Mene ne za ka iya yi don ka kasance da irin wannan hali mai kyau?

Fihirisar Hasumiyar Tsaro ta 2016

Jerin talifofi da aka wallafa a Hasumiyar Tsaro na nazari da kuma na wa’azi.