Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 TARIHI

Na Kudurta Cewa Ba Zan Karaya Ba

Na Kudurta Cewa Ba Zan Karaya Ba

MATASA da yawa a Bethel suna kirana “baba” ko “kaka” ko kuma “kawu.” Kuma ina son yadda suke kirana don shekarata 89 ne. Ƙari ga haka, ina ganin cewa waɗannan sunayen albarka ne da Jehobah ya yi mini don yadda na yi hidima ta cikakken lokaci shekaru 72. Kuma don abubuwan da na shaida a hidimata ga Allah, ina tabbatar wa waɗannan matasa da dukan zuciyata cewa, ‘Za ku karɓi ladan aikinku idan ba ku karaya ba.’​—2 Tar. 15:7.

IYAYENA DA ’YAN’UWANA

Iyayena sun ƙaura daga Yukiren zuwa Kanada kuma suka zauna a garin Rossburn a lardin Manitoba. Mahaifiyata ta haifi maza 8 da mata 8, kuma babu tagwaye a cikinsu. Ni ne ɗa na 14. Mahaifina yana son Littafi Mai Tsarki sosai kuma yakan karanta mana a kowace safiya ranar Lahadi. Duk da haka, yana ganin cewa limamai sun mai da addini wurin neman kuɗi kuma yakan ce, “Akwai wanda ya biya Yesu don wa’azinsa da kuma koyarwarsa?”

Daga baya, ’yan’uwana guda takwas, wato maza huɗu da mata huɗu sun soma bauta wa Jehobah. Yayata Rose ta yi hidimar majagaba har lokacin da ta mutu. Kafin ta mutu takan ƙarfafa mutane su karanta Kalmar Allah, kuma ta ce, “Ina so in gan ku a sabuwar duniya.” A dā, yayana Ted yakan yi wa’azi game da wutar Jahannama. A kowace safiya ranar Lahadi, yakan yi wa’azi a rediyo yana gaya wa masu sauraron sa cewa za a ƙona masu zunubi a wutar Jahannama har abada. Amma daga baya, ya zama mai bauta wa Jehobah da ƙwazo.

YADDA NA SOMA HIDIMA TA CIKAKKEN LOKACI

Wata rana a watan Yuni 1944 da na dawo gida daga makaranta, na ga wata ƙasida mai jigo The Coming World Regeneration * a kan teburi. Sai na karanta shafi na farko da na biyu, har na karance ƙasidar. Sa’ad da na karance ƙasidar, na tsai da shawara nan da nan cewa zan bauta wa Jehobah yadda Yesu ya yi.

Ta yaya aka ajiye ƙasidar a kan teburinmu? Yayana Steve ya ce mutane biyu da suke “sayar” da littattafai sun zo gidanmu. Ya ce: “Na sayi  wannan don yana da araha.” Mutanen sun dawo ranar Lahadi a mako na gaba. Sun gaya mana cewa su Shaidun Jehobah ne kuma suna amfani da Littafi Mai Tsarki don su amsa tambayoyin mutane. Hakan ya sa mu farin ciki domin iyayenmu sun koya mana mu riƙa daraja Kalmar Allah. Ƙari ga haka, mutanen sun gaya mana cewa Shaidu za su yi taron gunduma a birnin Winnipeg, wurin da yayata Elsie take da zama. Sai na tsai da shawara cewa zan je taron.

Na tuƙa keke zuwa Winnipeg da ke da nisan mil 200, amma na tsaya a garin Kelwood wurin da Shaidu biyu da suka ziyarce mu suke da zama. Da nake wurin, na halarci taro kuma na ga yadda ake gudanar da taron ikilisiya. Ban da haka, na koya cewa ya kamata kowa, maza da mata da yara su yi wa’azi gida-gida yadda Yesu ya yi.

A birnin Winnipeg, na haɗu da yayana Jack wanda ya halarci taron daga arewacin lardin Ontario. A rana ta farko na taron, wani ɗan’uwa ya yi sanarwa cewa za a yi baftisma. Sai ni da Jack muka tsai da shawarar yin baftisma a wannan taron kuma muka ƙuduri niyya cewa za mu soma hidimar majagaba nan da nan. Jack ya zama majagaba bayan taron, amma ban zama majagaba ba da yake shekarata 16 ne kuma zan koma makaranta. Duk da haka, na soma hidimar majagaba na kullum bayan shekara ɗaya.

NA KOYI DARUSSA DA YAWA

Na soma hidimar majagaba tare da Stan Nicolson a garin Souris da ke lardin Manitoba. Ba da daɗewa ba, na koyi cewa mutum yakan fuskanci wasu ƙalubale a hidimar majagaba. Mun ci gaba da wa’azi ko da yake kuɗinmu ya kusan ƙarewa. Wata rana da muka koma gida bayan mun yi wa’azi, muna jin yunwa sosai amma ba mu da ko sisi. Mun yi mamaki sosai da muka tarar da babban buhu cike da kayan abinci a bakin ƙofarmu! Har yau, ba mu san wanda ya ajiye buhun ba. Da yammar nan, mun ci mun ƙoshi. Jehobah ya albarkace mu don ba mu karaya ba! Ƙari ga haka a wannan watan, na yi jiki sosai yadda ban taɓa yi ba.

Bayan ’yan watanni, sai aka tura mu hidima a garin Gilbert Plains da ke da nisan mil 150 daga arewacin Souris. A lokacin, kowace ikilisiya tana da babbar taswira a kan dakalin magana da ke nuna rahotannin wa’azi na ’yan’uwa a kowace wata. Akwai watan da ’yan’uwa ba su yi wa’azi sosai ba, sai na yi jawabi cewa ya kamata ’yan’uwa su ƙara ƙwazo a hidima. Bayan taron, wata ’yar’uwa tsohuwa majagaba da mijinta ba ya bauta wa Jehobah ta zo wurina tana kuka. Ta ce: “Na yi ƙoƙari amma ban iya yin fiye da abin da na yi ba.” Sai ni ma na soma kuka kuma na roƙe ta ta yi haƙuri.

Kamar yadda na yi, ’yan’uwa matasa masu kuzari sukan yi kuskure kuma su yi da-na-sani daga baya. Amma na koyi cewa, maimakon in bar kuskurena ya sa in karaya, ya fi in koyi darasi daga kuskurena. Za a albarkace ni don hidimar da na yi da aminci.

MATSALOLIN DA MUKA FUSKANTA A QUEBEC

Na yi farin ciki sosai sa’ad da na halarci aji na 14 na Makarantar Gilead ina ɗan shekara 21, kuma na sauke karatu a watan Fabrairu 1950! An tura mutane wajen 25 a ajinmu zuwa lardin Quebec a Kanada da ake Faransanci kuma a wurin ana tsananta wa Shaidu sosai. An tura ni hidima a garin Val-d’Or kuma ana haƙa zinariya a wurin. Wata rana, muka je wa’azi a ƙauyen Val-Senneville. Limamin da ke wurin ya ce zai kawo mana hari idan ba mu bar ƙauyen nan da nan ba. Sai na kai ƙarar limamin kotu, kuma aka ci masa tara. *

Mun fuskanci irin waɗannan matsaloli da yawa a lardin Quebec. Cocin Katolika ne mutane da yawa suke zuwa fiye da shekara 300. Limamansu da abokansu ’yan siyasa sun tsananta wa Shaidun Jehobah sosai. Ba shi da sauƙi a wannan lokacin don ba mu da yawa, amma ba mu  karaya ba. Mutanen Quebec masu zuciyar kirki sun saurari saƙonmu. Na yi farin cikin yin nazari da mutane da yawa a cikinsu. Akwai wani a cikinsu da dukan mutane goma a iyalinsa suka soma bauta wa Jehobah. Yadda suka kasance da gaba gaɗi ya sa wasu suka daina zuwa Cocin Katolika. Mun ci gaba da wa’azi kuma daga baya aka daina tsananta mana!

AN KOYAR DA ’YAN’UWA A YARENSU

A shekara ta 1956, aka tura ni hidima a ƙasar Haiti. Yawancin sababbi masu wa’azi a ƙasar waje ba su iya Farasanci ba, duk da haka, mutane sun saurare su. Wani ɗan’uwa mai suna Stanley Boggus ya ce, “Mun yi mamaki yadda mutanen suka yi iya ƙoƙarinsu don su taimaka mana mu yi Farasanci.” Da farko, ba ni da matsala don na koyi Farasanci a Quebec. Amma ba da daɗewa ba, muka ga cewa yaren Creole na Haiti ne yawancin ’yan’uwan suke yi. Saboda haka, idan za mu yi nasara, wajibi ne mu koyi yarensu. Mun yi hakan kuma Jehobah ya albarkace mu.

Don a taimaka wa ’yan’uwan, Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu ta ba da izini a fassara Hasumiyar Tsaro da wasu littattafai zuwa harshen Creole na Haiti. Hakan ya sa waɗanda suke halartan taro a ƙasar suka ƙaru. A shekara ta 1950, da akwai masu shela 99 a Haiti, amma sun ƙaru zuwa fiye da 800 a shekara ta 1960! An tura ni hidima a Bethel a lokacin, kuma a shekara ta 1961 na sami gatar gudanar da Makarantar Hidima ta Mulki. Mun koyar da dattawa da majagaba na musamman guda 40. Ƙari ga haka, a taron gunduma da aka yi a watan Janairu 1962, mun ƙarfafa ’yan’uwa maza su ƙara ƙwazo a hidimarsu, kuma aka naɗa wasu majagaba na musamman. Hakan ya dace don ba da daɗewa ba, za a tsananta musu sosai.

A ranar 23 ga Janairu, 1962, bayan da muka gama taron, aka kama ni da Ɗan’uwa Andrew D’Amico a ofishinmu, kuma aka ƙwace dukan mujallun Awake! na 8 ga Janairu 1962 da aka fassara a Farasanci. A cikin mujallar, an yi ƙaulin jaridun Farasanci da aka ce mutanen Haiti suna  tsafi. Wasu ba su so furucin nan ba kuma suka ce a ofishinmu ne aka rubuta talifin. Bayan ’yan kwanaki, sai aka kori masu wa’azi a ƙasar waje daga ƙasar. * Amma, ’yan’uwa da aka koyar da su sun ci gaba da gudanar da aikin. A yau, ina farin ciki don yadda suka jimre da kuma yadda suka ƙara kasancewa da bangaskiya. A yanzu suna da fassarar New World Translation of the Holy Scriptures a harshen Creole na Haiti. A dā, ba su taɓa tsammanin cewa hakan zai yiwu ba.

GINE-GINE A JAMHURIYAR AFIRKA TA TSAKIYA

Bayan na yi hidima a Haiti, sai aka tura ni Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Na yi hidimar mai kula da da’ira da kuma mai kula da ofishinmu a wurin.

A wannan lokacin, Majami’un Mulki da yawa ba su da kyau. Na koyi yadda ake neman ciyawa a cikin jeji kuma ina yin jinka da ita. Mutane da suke wucewa suna mamakin ganin yadda nake yin wannan aikin. Hakan ya ƙarfafa ’yan’uwa su riƙa yin gine-gine da kuma gyara Majami’unsu. Limamai sukan yi mana dariya domin cocinsu yana da rufin kwano amma Majami’unmu ba haka suke ba. Duk da haka, ba mu karaya ba kuma muka ci gaba da amfani da jinkar ciyawa a Majami’unmu. Mutanen sun daina yi mana dariya sa’ad da aka yi wata guguwa a birnin Bangui. Guguwar ta ɗauke rufin kwano na cocinsu kuma ya faɗi a kan titi, amma babu abin da ya sami jinkar ciyawa da ke Majami’unmu. Don a riƙa gudanar da ayyuka na Mulki da kyau, mun gina sabon ofishi da kuma masaukin masu wa’azi a ƙasar waje cikin wata biyar kawai. *

NA AURI WATA MAI ƘWAZO SOSAI

Ranar aurenmu

A shekara ta 1976, aka saka wa aikinmu takunkumi a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, kuma aka tura ni birnin N’Djamena da ke ƙasar Chadi. A wurin ne na haɗu da wata majagaba na musamman mai ƙwazo sosai. Sunanta Happy ne kuma ita ’yar ƙasar Kamaru ce. Sai muka yi aure a ranar 1 ga Afrilu, 1978. An soma yaƙi a ƙasar a wannan watan, sai muka gudu zuwa kudancin ƙasar. Sa’ad da aka gama yaƙin, sai muka dawo amma mun ga cewa rukunin ’yan tawaye sun mai da gidanmu hedkwatarsu. Ƙari ga haka, an ɗauke littattafanmu da rigar auren matata da kuma kyaututtukan da aka ba mu a ranar aure. Duk da haka, ba mu karaya ba, don muna tare da juna kuma muna da ƙarin aikin da za mu yi a nan gaba.

Bayan shekara biyu, sai aka ɗage takunkumin da aka saka wa aikinmu a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Sai muka koma ƙasar kuma muka yi hidimar mai kula mai ziyara. Gidanmu wata babbar motar ɗaukan kaya ce mai gado da ake naɗewa da duro da za a iya zuba ruwa galan 53, da kuma firiji da murhu masu amfani da gas. Yin tafiye-tafiye a lokacin yana da wuya sosai. Akwai wata tafiya da muka yi da ’yan sanda suka tsayar da mu har aƙalla sau 117.

Ana yawan yin matsananciyar zafi a ƙasar kuma a wasu lokuta, yana da wuya a sami isasshen ruwan yin baftisma a manyan taro. Saboda haka, ’yan’uwa sukan haƙa rami kusa da kogi kuma su riƙa ɗiban ruwa kaɗan-kaɗan har su sami isashen ruwan yin baftisma. Kuma sau da yawa ana yin baftismar a cikin duro.

HIDIMA A WASU ƘASASHEN AFIRKA

An tura mu zuwa Nijeriya a shekara ta 1980. Mun yi shekara biyu da rabi a wurin, kuma mun taimaka musu yin shirye-shirye don sabon ofishin da suke so su gina. ’Yan’uwan sun sayi gidan bene mai hawa biyu da ake ajiye kayayyaki a ciki. Za a kwance gidan kuma a kafa shi a filin da muka saya. Wata rana da safe, na hau saman gidan don in taimaka da aikin. Da rana, sai na soma sauka yadda na hau, amma an riga an kwance wasu wurare, sai na faɗo daga sama. Mun yi zato cewa na ji rauni sosai, amma bayan da aka yi wasu gwaje-gwaje, sai likitan ya gaya wa matata cewa: “Kada ki damu, ya ɗan ji rauni ne  a mahaɗin kashinsa kuma zai samu sauƙi bayan mako ɗaya ko fiye da haka.”

Za mu taron da’ira a cikin “motar haya”

Mun ƙaura zuwa ƙasar Kwaddebuwa a shekara ta 1986, kuma muka yi hidimar mai kula mai ziyara. Ƙari ga haka, mukan yi wannan hidimar a Burkina Faso da ke kusa da ƙasar. Ban taɓa zato cewa a nan gaba, za mu yi hidima shekaru da yawa a Burkina Faso ba.

Babbar mota ce gidanmu sa’ad da muke hidimar mai kula mai ziyara

Na bar Kanada a shekara ta 1956, amma a shekara ta 2003 bayan shekara 47, sai na koma hidima a Bethel da ke Kanada tare da matata. Mu ’yan ƙasar Kanada ne, amma mun fi son Afirka.

Ina nazarin Littafi Mai Tsarki da wani a Burkina Faso

Mun koma Afirka a shekara ta 2007, sa’ad da nake ɗan shekara 79! An tura mu Burkina Faso kuma na zama memban Kwamitin na Ƙasar. Daga baya aka canja ofishin zuwa ofishin fassara kuma ofishinmu da ke ƙasar Benin ne ke kula da aikin da ake yi a Burkina Faso. An tura mu hidima a Bethel da ke Benin a watan Agusta na 2013.

Ni da matata sa’ad da muke hidima a ofishinmu da ke Benin

Har ila ina son yin wa’azi sosai duk da cewa na tsufa. A shekaru uku da suka shige, na taimaka wa mutane biyu su yi baftisma, wato Gédéon da Frégis. Na yi hakan da taimakon dattawa da kuma matata. Yanzu waɗannan ’yan’uwa suna bauta wa Jehobah da aminci.

A yanzu, ni da matata muna ofishinmu da ke Afirka ta Kudu, kuma ’yan’uwan suna kula da ni sosai. Afirka ta Kudu ce ƙasar Afirka ta bakwai da muka yi hidima a ciki. A watan Oktoba 2017, mun sami albarka ta musamman. Mun halarci bikin keɓe hedkwatarmu a Warwick da ke New York. Ba za mu taɓa manta wannan bikin ba!

An faɗi a shafi na 255 na 1994 Yearbook of Jehovah’s Witnesses cewa: “Muna ƙarfafa duk waɗanda suka yi shekaru da yawa suna hidima: ‘Ku yi ƙarfin zuciya, kada ku fid da rai, gama za ku karɓi ladan aikinku.’​—2 Tar. 15:7.” Ni da matata mun ƙuduri niyyar bin wannan umurnin kuma muna ƙarfafa ’yan’uwa su yi hakan.

^ sakin layi na 9 Shaidun Jehobah ne suka wallafa ta a 1944. Amma an daina buga ta.

^ sakin layi na 18 Ka duba talifin nan “Quebec Priest Convicted for Attack on Jehovah’s Witnesses” da ke Awake! na 8 ga Nuwamba, 1953, shafuffuka na 3-5.

^ sakin layi na 23 An faɗi abin da ya faru dalla-dalla a littafin nan 1994 Yearbook of Jehovah’s Witnesses, shafuffuka na 148-150.

^ sakin layi na 26 Ka duba talifin nan “Building on a Solid Foundation” da ke Awake!, na 8 ga Mayu, 1966, shafi na 27.