Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Masu Karimci Suna Farin Ciki

Masu Karimci Suna Farin Ciki

“Ya fi albarka a bayar da a karɓa.”​—A. M. 20:35.

WAƘOƘI: 76, 110

1. Mene ne ya nuna cewa Jehobah Allah ne mai karimci?

JEHOBAH ne kaɗai yake wanzuwa kafin ya halicci sama da duniya. Amma duk da haka, bai mai da hankali ga kansa kawai ba. A maimakon haka, ya ba halittunsa na ruhu da kuma ’yan Adam rai kyauta. “Allah mai albarka” ko kuma farin ciki yana ba da kyauta mai tamani. (1 Tim. 1:11; Yaƙ. 1:17) Yana so mu riƙa farin ciki, shi ya sa ya koya mana mu riƙa yin karimci.​—Rom. 1:20.

2, 3. (a) Me ya sa ba da kyauta yake sa mu farin ciki? (b) Me za mu tattauna a wannan talifin?

2 Allah ya halicci mutum a kamanninsa. (Far. 1:27) Hakan yana nufin cewa an halicce mu domin mu kasance da irin halayen Allah. Idan muna so mu riƙa farin ciki da kuma samun gamsuwa, dole ne mu bi misalin Jehobah. Muna bukatar mu nuna mun damu da mutane kuma mu zama masu karimci. (Filib. 2:​3, 4; Yaƙ. 1:5) Me ya sa yin haka yake da muhimmanci? Domin Jehobah ya halicce mu mu riƙa yin hakan. Duk da cewa mu ajizai ne, za mu iya bin misalin Jehobah ta wajen zama masu karimci.

 3 Littafi Mai Tsarki ya koya mana yadda za mu zama masu karimci. Bari mu tattauna wasu darussa daga Littafin Mai Tsarki game da wannan batun. Za mu ga yadda ba da kyauta zai sa mu sami tagomashin Allah da kuma yadda zai taimaka mana mu yi aikin da Allah ya ba mu. Ƙari ga haka, za mu tattauna yadda yin karimci zai sa mu farin ciki da kuma dalilin da ya sa muke bukatar mu ci gaba da zama masu karimci.

YADDA ZA MU SAMI TAGOMASHIN ALLAH

4, 5. Wane irin misalin karimci ne Jehobah da Yesu suka kafa mana?

4 Jehobah yana so mutane su riƙa bin misalinsa, shi ya sa yake farin ciki idan muna yin karimci. (Afis. 5:1) Yadda Jehobah Allah ya halicce mu da kuma abubuwa masu kyau da ya halitta a duniya, sun nuna cewa Allah yana so dukan ’yan Adam su riƙa farin ciki. (Zab. 104:24; 139:​13-16) Idan muka yi iya ƙoƙarinmu don mu sa mutane farin ciki, hakan yana daraja Allah.

5 Kiristoci na gaske suna bin misalin Kristi. Yesu ya kafa mana misali mai kyau a yadda za mu riƙa nuna karimci. Yesu da kansa ya ce: “Ɗan mutum bai zo domin a bauta masa ba, sai dai domin ya yi bauta, ya kuma ba da ransa domin ceton mutane da yawa.” (Mat. 20:28) Don haka, manzo Bulus ma ya ƙarfafa Kiristoci ya ce: “Ku kasance da hali irin na Almasihu Yesu, . . . ya mai da kansa kamar ba kome ba, ya ɗauki matsayin bawa cikin sifar ɗan Adam.” (Filib. 2:​5-7) Dukanmu muna bukatar mu tambayi kanmu, ‘Zan iya bin misalin Yesu fiye da yadda nake yi a dā kuwa?’​—Karanta 1 Bitrus 2:21.

6. Wane darasi ne Yesu ya koya mana da kwatancin Basamariye? (Ka duba hoton da ke shafi na 18.)

6 Za mu sami tagomashin Jehobah idan muka bi misalin da shi da Yesu suka kafa mana. Ta yaya? Ta wajen nuna cewa mun damu da mutane da kuma yin iya ƙoƙarinmu don mu taimaka musu. A kwatanci Basamariye da Yesu ya yi, ya nuna sarai cewa hakan yana da muhimmanci. A kwatancin, Yesu ya koya wa mabiyansa cewa suna bukatar su riƙa taimaka wa mutane ko da garinsu ba ɗaya ba ne. (Karanta Luka 10:​29-37.) Ka tuna dalilin da ya sa Yesu ya ba da kwatancin? Domin wani Bayahude ya tambaye shi cewa: “Shin, wane ne maƙwabcina?” Amsar da Yesu ya ba da ya nuna cewa muna bukata mu riƙa yin karimci kamar wannan Basamariye idan muna so mu sami tagomashin Allah.

7. Ta yaya muke nuna cewa yadda Jehobah yake yin abubuwa ne ya fi kyau?

7 Wani abu kuma da ya sa Kiristoci suke bukatar su riƙa nuna karimci shi ne abin da ya faru a lambun Adnin. A lambun, Shaiɗan ya yi da’awar cewa Adamu da Hauwa’u za su fi yin farin ciki idan suka taka dokar Allah kuma suka fi mai da hankali ga bukatun kansu. Hauwa’u ta nuna sonkai domin tana so ta zama kamar Allah. Adamu kuma ya nuna sonkai domin ya so ya sa matarsa Hauwa’u farin ciki maimakon Allah. (Far. 3:​4-6) Babu shakka, muna ganin sakamakon rashin biyayya da suka yi. Nuna sonkai ba ya kawo farin ciki, sai dai baƙin ciki. Amma idan muna yin karimci, hakan zai nuna cewa yadda Jehobah yake yin abubuwa ne ya fi kyau.

 KU YI AIKIN DA ALLAH YA BA BAYINSA

8. Me ya sa Adamu da Hauwa’u suke bukatar su yi tunani a kan yaran da za su haifa?

8 Duk da cewa Adamu da Hauwa’u ne kaɗai a lambun Adnin, suna bukatar su yi tunanin yadda abin da za su yi zai shafi wasu. Jehobah ya albarkaci Adamu da Hauwa’u kuma ya ce musu su haifi yara su cika duniya kuma su mayar da ita aljanna. (Far. 1:28) Kamar yadda Mahalicci ya nuna ya damu da halittunsa, Adamu da Hauwa’u ma suna bukatar su nuna sun damu da yaran da za su haifa. Jehobah ya so Adamu da Hauwa’u da yaransu su yi aiki don su mayar da duniya gabaki ɗaya aljanna. Wannan aiki ne babba!

9. Ta yaya mutane za su yi farin ciki yayin da suke aiki don mayar da duniya aljanna?

9 Da kamiltattun mutane sun yi aiki tare da Jehobah don su mai da duniya aljanna kuma su cika nufin Allah ga duniya. Ta yin hakan ne za su shiga cikin hutunsa. (Ibran. 4:11) Babu shakka, da aikin ya sa mutane farin ciki da kuma samun gamsuwa! Ƙari ga haka, Jehobah zai albarkace su domin ba su nuna sonkai ba, amma sun nuna cewa sun damuwa da wasu fiye da kansu.

10, 11. Me zai taimaka mana mu cim ma aikinmu na yin wa’azi da kuma almajirtarwa?

10 A yau, Jehobah ya ba mutanensa aikin yin wa’azi da kuma koyar da mutane. Idan muna so mu yi waɗannan ayyukan, muna bukatar mu nuna mun damu da mutane sosai. Abin da zai sa mu jimre yayin da muke yin wannan aikin shi ne ƙauna ga Allah da kuma maƙwabtanmu.

11 A ƙarni na farko, Bulus ya ce shi da kuma wasu Kiristoci “abokan aiki na Allah ne,” domin suna yin wa’azi da kuma koyar da mutane gaskiyar da ke Kalmar Allah. (1 Kor. 3:​6, 9) A yau, muna iya zama “abokan aiki na Allah” idan muna yin amfani da lokacinmu da wadatarmu don yin wa’azi. Babu shakka, wannan gata ce babba!

Taimaka wa mutane su koyi gaskiya zai sa ka farin ciki (Ka duba sakin layi na 12)

12, 13. Wace albarka ce yin wa’azi yake kawowa?

12 Idan muka yi amfani da lokacinmu da kuma ƙarfinmu don yin wa’azi da kuma koyar da mutane, za mu yi farin ciki sosai. Abin da ’yan’uwa da suka sami gatan yin nazarin da wasu suka ce ke nan. Babu shakka, muna farin ciki sosai sa’ad da muka ga yadda ɗalibanmu suke murna idan suka koyi ainihin abin da Littafi Mai Tsarki ya koyar. Yesu ya yi farin ciki sosai sa’ad da mabiyansa 70 da ya tura wa’azi suka “dawo da murna” don yadda mutane suka saurare su.​—Luk. 10:​17-21.

13 ’Yan’uwa a faɗin duniya suna farin  ciki sosai yayin da suka ga yadda Littafi Mai Tsarki yake gyara rayuwar mutane. Ka yi la’akari da labarin wata ’yar’uwa matashiya mai suna Anna da ta ƙaura zuwa wani yanki da ake bukatar masu shela a Gabashin Turai. * Ta ce: “Mutane da yawa suna son yin nazarin Littafi Mai Tsarki a nan kuma hakan yana burge ni sosai. Hidimar da nake yi a nan tana sa ni matuƙar farin ciki. Idan na je gida, ba ni da lokacin mai da hankali ga matsalolina. Abin da nake tunani a kai shi ne matsalolin da mutanen da nake nazari da su suke fuskanta. Ina ƙoƙari don in san yadda zan ƙarfafa su da kuma taimaka musu. Yin hakan ya tabbatar mini da cewa ‘ya fi albarka a bayar da a karɓa.’ ”​—A. M. 20:35.

Idan muka je wa’azi a dukan gidajen da ke yankinmu, muna ba mutanen damar yin zaɓi (Ka duba sakin layi na 14)

14. Ta yaya za ka yi farin ciki a wa’azi ko da mutane ba sa saurarar ka?

14 Za mu sami gamsuwa sosai idan muka ba mutane damar zaɓa ko za su ji wa’azi ko a’a. A yau, Jehobah yana so mu yi abin da ya gaya wa annabi Ezekiyel. Ya ce: “Za ka faɗa musu maganata, ko su ji, ko su ƙi.” (Ezek. 2:7; Isha. 43:10) Ko da mutane sun ƙi saurarar mu, Jehobah yana ɗaukan ƙoƙarin da muke yi da muhimmanci sosai. (Karanta Ibraniyawa 6:10.) Wani ɗan’uwa ya kafa misali mai kyau a wannan batun. Ya ce: “Mun shuka, mun yi ban ruwa, kuma muna addu’a cewa Jehobah ya sa mutanen su yi abin da suka ji.”​—1 Kor. 3:6.

YADDA ZA MU RIƘA YIN FARIN CIKI

15. Me mutane da yawa suke yi idan aka yi musu alheri, me ya kamata mu yi?

15 Yesu yana so mu riƙa yin karimci don mu yi farin ciki. Yawancin mutane suna so a nuna musu karimci. Yesu ya ce: “Ku bayar, ku ma za a ba ku mudu a cike, a cika har ya yi tudu yana zuba, har a juye muku sauran a hannun riga. Gama da mudun da kuke auna wa mutane da shi, da shi za a auna muku.” (Luk. 6:38) Hakika ba kowa ba ne yake nuna godiya don karimcinmu ba, amma idan sun nuna godiya, karimcinmu yana iya motsa su su zama masu  bayarwa. Don haka, ka riƙa yin karimci ko da mutane sun nuna godiya ko a’a. Ba ka san irin sakamakon da za ka samu don yin karimci ba.

16. Su waye ne ya kamata mu yi wa karimci, kuma me ya sa?

16 Mutane masu karimci ba sa yin ba-ni-in-ba-ka. Yesu Kristi ya ce: “In za ka kira mutane biki, ka kira talakawa, da guragu, da shanyayyu da makafi. Ta haka za ka sami albarka, domin waɗannan dai ba za su iya biyanka ba.” (Luk. 14:​13, 14) Ban da haka, wani marubucin zabura ya ce: “Mai bayarwa hannu sake mai albarka” ne. Wani kuma ya ce: “Mai albarka ne wanda yake kula da marasa ƙarfi.” (K. Mag. 22:9; Zab. 41:1) Hakika, ya kamata mu riƙa bayarwa domin muna farin cikin taimaka wa mutane.

17. Wane irin bayarwa ne zai sa ka farin ciki?

17 Sa’ad da Bulus ya yi ƙaulin furucin Yesu cewa “ya fi albarka a bayar da a karɓa,” ba bayar da kyauta kaɗai yake magana a kai ba. Amma yana nufin ƙarfafa mutane da ba su shawara daga Littafi Mai Tsarki da kuma taimaka musu. (A. M. 20:​31-35) Ta ayyukan Bulus da kuma furucinsa, ya nuna cewa yana da muhimmanci mu yi amfani da lokacinmu da ƙarfinmu da ƙaunarmu don taimaka wa mutane.

18. Mene ne masana da yawa suka ce game da yin karimci?

18 Masu ilimin zaman jama’a sun lura cewa yin karimci yana sa mutane farin ciki. Wani talifin da suka buga ya ce, “Mutane suna farin ciki sosai a duk lokacin da suka yi karimci.” Sun ƙara da cewa, “Idan muka taimaka wa mutane, za mu ga cewa rayuwarmu tana ƙara kasancewa da ma’ana.” Don haka, wasu masana suna ƙarfafa mutane su riƙa ba da kai don taimaka wa mutane. Yin hakan zai taimaka musu su kasance da ƙoshin lafiya da kuma farin ciki. Hakan ba abin mamaki ba ne a gare mu, domin Jehobah Mahaliccinmu ya riga ya faɗi hakan a Kalmarsa.​—2 Tim. 3:​16, 17.

MU CI GABA DA NUNA KARIMCI

19, 20. Me ya sa kake son ka zama mai karimci?

19 Yin karimci yana iya kasancewa da wuya da yake muna rayuwa tare da mutanen da suke son kansu fiye da wasu. Amma Yesu ya bayyana cewa dokoki biyu da suka fi muhimmanci su ne, mu yi ƙaunar Jehobah da dukan zuciyarmu da dukan ranmu da dukan hankalinmu, kuma mu ƙaunaci maƙwabtanmu kamar kanmu. (Mar. 12:​28-31) Kamar yadda muka gani a wannan talifin, waɗanda ke ƙaunar Jehobah za su riƙa bin misalinsa. Jehobah da Yesu masu karimci ne. Idan muka yi iya ƙoƙarinmu don mu riƙa yin karimci ga Jehobah da kuma ’yan’uwanmu, za mu daraja Allah, kuma za mu amfane kanmu da kuma wasu.

20 Babu shakka, kana iya ƙoƙarinka don ka taimaka wa mutane musamman ma ’yan’uwa Kiristoci. (Gal. 6:10) Idan ka ci gaba da yin hakan, mutane za su nuna maka godiya kuma su ƙaunace ka, ban da haka ma, za ka yi farin ciki. Littafin Karin Magana 11:25 ya ce: “Mai bayarwa hannu sake zai ƙara yalwata, mai taimaka wa waɗansu, shi kansa zai sami taimako.” Hakika da akwai hanyoyi da yawa na yin karimci da alheri da ba da kyauta a rayuwarmu ta Kirista da kuma hidimarmu ga Jehobah. A talifi na gaba, za mu tattauna waɗannan hanyoyin.

^ sakin layi na 13 An canja wasu sunaye.