Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ku Riƙa Yin Aiki da Jehobah Kowace Rana

Ku Riƙa Yin Aiki da Jehobah Kowace Rana

“Mu abokan aiki na Allah ne.”​—1 KOR. 3:9.

WAƘOƘI: 64, 111

1. A waɗanne hanyoyi ne za mu iya yin aiki da Jehobah?

MAHALICCINMU ya ga cewa kamiltattun mutane za su goyi bayansa wajen sa ya cim ma nufe-nufensa. Duk da cewa mu ajizai ne a yau, mutane masu aminci za su iya yin aiki da Jehobah a kowace rana. Alal misali, yin wa’azin Mulkin Allah da kuma almajirantar da mutane ya sa mun zama “abokan aiki na Allah.” (1 Kor. 3:​5-9) Muna da gata na musamman domin muna goyon bayan Allah Maɗaukakin Sarki wajen yin aikin da ke da muhimmanci a gare shi. Duk da haka, ba yin wa’azi da kuma almajirantar da mutane ne kaɗai hanyoyin da muke aiki da Jehobah ba. A wannan talifin, za mu tattauna wasu hanyoyi da za mu iya yin hakan. Za mu ga yadda za mu taimaka wa iyalinmu da ’yan’uwanmu Kiristoci da kuma baƙi. Kuma za mu ga yadda za mu taimaka a aikin gine-gine da kuma faɗaɗa hidimarmu.​—Kol. 3:23.

2. Me ya sa bai dace mu gwada ayyukan da muke yi a hidimar Jehobah da na wasu ba?

2 Yayin da muke yin nazarin wannan talifin, kada ka gwada aikin da kake yi a hidimar Jehobah da na wasu. Ka tuna cewa dukanmu mun bambanta a shekaru da lafiyar jiki da yanayi da  kuma iyawa. Manzo Bulus ya ce: “Bari kowa ya gwada aikinsa ya gani. Idan ya yi kyau, sa’an nan zai iya taƙama da abin da ya yi da kansa, ba sai ya gwada kansa da wani ba.”​—Gal. 6:4.

KU TAIMAKA WA IYALINKU DA ’YAN’UWA A IKILISIYA

3. Me ya sa muka ce duk mutumin da ke kula da iyalinsa yana goyon bayan Allah?

3 Jehobah yana so bayinsa su riƙa kula da iyalinsu. Alal misali, wasu suna aiki tuƙuru don su tanadar da bukatun iyalinsu. Wasu mata suna zama a gida don su kula da jariransu. Wasu yara kuma da suka yi girma suna kula da iyayensu marasa lafiya. Waɗannan ayyukan suna da muhimmanci. Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Duk wanda ba ya kula da danginsa, musamman iyalin gidansa, ya yi mūsun bangaskiyarsa ke nan, ya kuma fi wanda yake marar ba da gaskiya muni.’ (1 Tim. 5:8) Babu shakka, idan kana yin waɗannan ayyukan, ba za ka sami isasshen lokacin yin hidimar Jehobah yadda kake so ba. Amma ka kwantar da hankalinka! Jehobah yana farin ciki sa’ad da ka tanadar da bukatun iyalinka.​—1 Kor. 10:31.

4. Ta yaya iyaye za su iya saka al’amuran Mulkin Allah farko, kuma wane sakamako ne za su samu?

4 Idan iyaye Kiristoci suka taimaka wa yaransu su kafa maƙasudai a hidimar Jehobah, suna goyon bayan Jehobah. Iyaye da yawa da suka yi hakan sun ga cewa yaransu sun yanke shawarar ƙaura zuwa wuri mai nisa don yin hidimar majagaba. Wasu suna wa’azi a ƙasashen waje ko kuma suna hidima a inda ake bukatar masu shela. Wasu kuma suna yin hidima a Bethel. Da yake suna da nisa da gida, ba za su riƙa ganin juna yadda suke so ba. Amma iyaye masu halin sadaukarwa suna ƙarfafa yaransu su ci gaba da hidimarsu. Me ya sa? Suna farin ciki da gamsuwa domin yaransu suna saka al’amura na Mulkin Allah farko a rayuwarsu. (3 Yoh. 4) Wasu cikin iyayen nan suna ji kamar Hannatu, sa’ad da ta ce ta “miƙa” ɗanta Sama’ila ga Jehobah. Iyaye sun san cewa yin hakan goyon bayan Jehobah ne kuma suna so hakan ya ci gaba.​—1 Sam. 1:28.

5. A waɗanne hanyoyi ne za ka iya taimaka wa ’yan’uwa a ikilisiyarku? (Ka duba hoton da ke shafi na 23.)

5 Idan ba ka da wani abu na musamman da ke ɗaukan lokacinka a cikin iyalinku, ka duba ko za ka iya taimaka wa ’yan’uwan da ke rashin lafiya ko waɗanda suka tsufa ko suke da wani bukata. Ka bincika cikin ikilisiyarku ko za ka ga mutanen da suke bukatar taimako. Za ka iya taimaka wa wata ’yar’uwa kula da iyayenta tsofaffi idan tana bukatar lokacin yin wasu abubuwa. Za ka kuma iya kai su taro ko yin cefane ko saye-saye ko kuma ziyartar wani marar lafiya. Idan ka yi hakan, kana aiki da Jehobah don ya amsa addu’ar wani ko wata.​—Karanta 1 Korintiyawa 10:24.

KU RIƘA YI WA BAƘI ALHERI

6. A wace hanya ce za mu iya marabtar baƙi?

6 An san abokan aikin Allah da marabtar baƙi. (Ibran. 13:2) Kalmar Allah tana ɗauke da misalai da yawa da za su koya mana marabtar baƙi. (Far. 18:​1-5) Zai dace mu riƙa neman zarafin taimaka wa mutane a kai a kai ko da su “’yan’uwanmu” Kiristoci ne ko a’a.​—Gal. 6:10.

7. Me ya sa zai dace ka marabci masu hidima ta cikakken lokaci da suka ziyarce ku?

7 Za ku iya yin aiki da Allah ta wajen marabtar wani mai hidima ta cikakken lokaci da ya zo ziyara? (Karanta 3 Yohanna 5, 8.) Idan kun yi haka, za ku “ƙarfafa juna.” (Rom. 1:​11, 12) Ku yi la’akari da  labarin wani mai suna Olaf. Ya tuna abin da ya taɓa faruwa a ikilisiyarsu shekaru da yawa da suka shige. A lokacin, wani mai kula mai ziyara marar aure ya kawo ziyara ikilisiyarsu. Amma babu wani a ikilisiyar da ya iya ba shi masauki. Sai Olaf ya nemi izini daga wurin iyayensa da ba Shaidu ba don mai kula da da’irar ya sauka a gidansu. Sun yarda amma sun ce Olaf zai riƙa kwana a kan kujera. Olaf ya yi farin ciki sosai don wannan shawarar da ya yanke. Ya ce: “Na ji daɗi a wannan makon sosai! Ni da mai kula da da’irar muna tashi da sassafe don mu yi taɗi yayin da muke cin abinci. Ƙarfafar da ya yi mini ta motsa ni in soma hidima ta cikakken lokaci.” A yanzu, Olaf ya yi sama da shekaru 40 yana wa’azi a ƙasashe dabam-dabam.

8. Me ya sa ya kamata mu riƙa yin kirki ko da mutane ba su karɓe mu da hannu biyu ba? Ka ba da misali.

8 Za mu iya nuna cewa muna ƙaunar baƙi a hanyoyi da yawa, ko da a farko ba su nuna godiya ba. Ka yi la’akari da wannan misalin. Akwai ranar da wata ’yar ƙasar Sifen ta lura cewa ɗalibarta mai suna Yesica ’yar ƙasar Ecuador tana kuka sa’ad da suke nazari. Sai ta tambaye ta dalilin da ya sa take kuka. Yesica ta gaya mata cewa kafin su ƙaura zuwa Sifen, ta talauce sosai. Ta ce akwai ranar da ba ta da abincin da za ta ba ’yarta ƙarama, sai ruwa kawai. Ta lallashi ’yarta don ta yi barci yayin da take addu’a Allah ya taimaka mata. Jim kaɗan bayan haka, sai wasu Shaidun Jehobah guda biyu suka zo gidanta. Hakan ya sa ta fushi sosai har ta yayyaga mujallar da ’yar’uwar ta ba ta. Sai Yesica ta tambaye su: “Wannan ne abincin da kuke so in ba ’yata?” Shaidun sun yi ƙoƙari su ba ta haƙuri, amma hakan ya ci tura. Daga baya, suka kawo mata kwando cike da abinci kuma suka ajiye a bakin ƙofarta. Hakan ya sosa zuciyar Yesica sosai kuma ta soma kuka domin ba ta lura cewa Allah ne ya amsa addu’arta ba. Amma, Yesica ta ƙuduri niyyar bauta wa Jehobah. Babu shakka, karimcin da suka nuna mata ya kawo sakamako mai kyau!​—M. Wa. 11:​1, 6.

KU TAIMAKA A AYYUKAN ƘUNGIYAR JEHOBAH

9, 10. (a) A wane lokaci ne aka bukaci bayin Allah su ba da kai a zamanin dā? (b) Waɗanne ayyuka ne ’yan’uwa maza a cikin ikilisiya suke yi a yau?

9 A zamanin dā, Isra’ilawa suna da zarafofi da yawa na ba da kansu a hidimar Jehobah. (Fit. 36:2; 1 Tar. 29:5; Neh. 11:2) A yau ma, kuna da zarafofi da yawa na yin amfani da lokacinku da wadatarku da kuma iliminku don taimaka wa ’yan’uwanku. Idan kun yi haka, za ku yi farin ciki sosai kuma za ku sami albarka.

10 Kalmar Allah ta ƙarfafa maza a cikin ikilisiya cewa su yi aiki da Jehobah ta wajen zama bayi masu hidima da kuma dattawa. (1 Tim. 3:​1, 8, 9; 1 Bit. 5:​2, 3) Mutanen da suka yi hakan suna so su taimaka wa wasu a ibadarsu da kuma a wasu hanyoyi. (A. M. 6:​1-4) Shin dattawa sun taɓa ce ka zama ɗan atenda ko ka kula da littattafai ko yankin da kuke wa’azi ko kuma yin gyare-gyare a majami’arku da dai sauransu? ’Yan’uwan da ke yin waɗannan ayyukan za su gaya muku cewa wannan aikin yana da daɗi sosai.

Idan mun ba da kai don yin hidima a ƙungiyar Jehobah, za mu sami zarafin yin abokai (Ka duba sakin layi na 11)

11. Ta yaya wata ’yar’uwa ta amfana daga ƙawayen da ta samu sa’ad da suke gina Majami’un Mulki?

11 ’Yan’uwan da suka ba da kai don su yi aikin gine-gine suna yawan yin sababbin abokai. Ku yi la’akari da misalin wata ’yar’uwa mai suna Margie wadda ta yi aikin gine-gine na Majami’ar Mulki har  tsawon shekara 18. Margie tana yawan koya wa ’yan’uwa mata matasa aiki. Ta ce lokacin da ake gina Majami’ar Mulki zarafi ne na ƙarfafa juna. (Rom. 1:12) A duk lokacin da take fuskantar mawuyacin yanayi a rayuwarta, waɗannan ƙawayenta suna ƙarfafa ta. Ka taɓa ba da kai don yin irin wannan aikin kuwa? Za ka iya ba da kai ko da ka iya aikin gini ko a’a.

12. A wace hanya ce za ka iya taimaka a lokacin da bala’i ya auku?

12 Za mu kuma iya yin aiki da Jehobah idan mun taimaka wa ’yan’uwanmu sa’ad da bala’i ya addabe su. Alal misali, za mu iya ba da gudummawar kuɗi. (Yoh. 13:​34, 35; A. M. 11:​27-30) Wani abu kuma da za mu iya yi shi ne taimaka wajen share da kuma gyara gidajensu. Wata ’yar ƙasar Folan mai suna Gabriela, ta yi farin ciki sa’ad da ’yan’uwa a wata ikilisiya suka taimaka mata bayan da aka yi ambaliyar ruwa a garinsu. Gabriela ta ce: “Ba na so in ambata abubuwan da na rasa domin kayan duniya ne. Amma ina so in gaya muku albarkar da na samu. Abin da ya faru ya koya mini cewa muna da gata babba na zama Shaidun Jehobah kuma hakan na sa mu farin ciki matuƙa.” Mutane da yawa da aka taimaka musu bayan bala’i ya addabe su suna ji kamar wannan ’yar’uwar. Kuma mutanen da suke aiki da Jehobah don su taimaka wa ’yan’uwansu suna samun gamsuwa sosai.​—Karanta Ayyukan Manzanni 20:35; 2 Korintiyawa 9:​6, 7.

13. Ta yaya ba da kai don taimaka wa wasu zai iya ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah? Ka ba da misali.

13 Wata ’yar’uwa mai suna Stephanie da wasu masu shela sun yi aiki tare da Allah ta wajen taimaka wa wasu Shaidu da suka yi gudun hijira zuwa Amirka. Sun taimaka wajen nema musu masauki da kuma gyara masaukin. Waɗannan Shaidun sun gudo ne daga ƙasarsu sanadiyyar yaƙi da ake yi. Stephanie ta ce: “Ƙauna irin ta ’yan’uwa da muka nuna musu ta sa su farin ciki sosai kuma hakan ya sosa zuciyarmu. Iyalan nan sun yi tsammani cewa mun taimaka musu. Amma a gaskiya,  su ne suka taimaka mana.” Ta ƙara da cewa: “Ƙaunar waɗannan ’yan’uwan da haɗin kansu da bangaskiyarsu da kuma yadda suke dogara ga Jehobah sun sa mu daɗa ƙaunar Jehobah. Hakan ya motsa mu mu daraja tanadodin da ƙungiyar Jehobah take mana.”

KU FAƊAƊA HIDIMARKU

14, 15. (a) Wane hali mai kyau ne annabi Ishaya yake da shi? (b) Ta yaya masu shela a yau za su iya yin koyi da Ishaya?

14 Za ku so ku ƙara yawan aikin da kuke yi wa Jehobah? Za ku so ku ƙaura zuwa inda ake bukatar masu shela sosai a ƙungiyarsa? Gaskiya ne cewa ba lallai sai mun ƙaura zuwa wani wuri mai nisa ba kafin mu zama masu karimci ba. Amma yanayin wasu ’yan’uwa zai iya ƙyale su su ƙaura zuwa wani wuri mai nisa. Yin hakan zai sa su zama kamar annabi Ishaya. Sa’ad da Jehobah ya yi tambaya cewa: “Wane ne zan aika? Wa zai tafi a madadinmu?” Ishaya ya amsa cewa: “Ga ni nan, ka aike ni!” (Isha. 6:8) Kana da niyyar taimaka a ƙungiyar Jehobah kuma yanayinka zai ƙyale ka ka yi hakan? A waɗanne hanyoyi ne za ka iya taimaka?

15 Yesu ya yi wannan furucin game da yin wa’azi da kuma almajirtarwa. Ya ce: “Girbin yana da yawa, amma masu aikin kaɗan ne. Saboda haka ku roƙi Ubangijin girbin ya aiko da masu aiki su yi masa girbi.” (Mat. 9:​37, 38) Za ka iya yin hidimar majagaba a yankin da ake da bukata sosai? Ko kuwa za ka iya ƙarfafa wani ya yi hakan? Wasu ’yan’uwa sun ga cewa hanya mafi kyau na nuna ƙauna ga Allah da kuma maƙwabta ita ce ta wajen yin hidima a yankunan da ake bukatar masu shela sosai. Shin da akwai wasu hanyoyin da za ka iya taimaka? Yin hakan zai sa ka farin ciki sosai.

16, 17. Wane zarafi ne kake da shi na faɗaɗa hidimarka ga Jehobah?

16 Za ka so ka yi hidima a Bethel ko kuma ka taimaka a gine-ginen da ake yi a ƙungiyar Jehobah? Wannan hidimar za ta iya zama na ɗan lokaci ko kuma wadda za ka riƙa yi a wasu ranaku a kowane mako. A kowane lokaci, ƙungiyar Jehobah tana bukatar mutanen da suke da niyyar yin hidima a kowane wurin da aka ce su yi. Ƙari ga haka, ana bukatar waɗanda suke da niyyar yin kowane aikin da aka ba su ko da sun ƙware a wani aiki dabam. Jehobah yana daraja dukan waɗanda suke da niyyar yin sadaukarwa don su yi hidima a inda akwai bukata.​—Zab. 110:3.

17 Za ka so a daɗa koyar da kai don ka ƙware a hidimarka ga Jehobah? Idan haka ne, za ka iya cika fom na halartar Makarantar Masu Yaɗa Bisharar Mulki. A wannan makarantar, ana koyar da ’yan’uwa maza da mata da suka manyanta kuma suke da niyyar yin hidima ta cikakken lokaci a ƙungiyar Jehobah. Waɗanda suka cika wannan fom suna bukatar su kasance a shirye cewa za su yi hidima a duk inda aka tura su bayan sun sauke karatu. Za ka so ka yi hidima ga Jehobah a wannan hanyar kuwa?​—1 Kor. 9:23.

18. Ta yaya za ka amfana daga yin aiki da Jehobah kowace rana?

18 Da yake mu bayin Jehobah ne, muna yin karimci da alheri da kuma ƙauna ga mutane. Muna kuma kula da mutane a kowace rana. Yin hakan na sa mu murna da kwanciyar rai da kuma farin ciki. (Gal. 5:​22, 23) Ko da yaya yanayinka yake, za ka iya yin murna idan kana yin karimci kamar Jehobah kuma ka zama abokin aikinsa mai daraja sosai.​—K. Mag. 3:​9, 10.