Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 TALIFIN NAZARI NA 16

Ka Yi Koyi da Jehobah a Sha’aninka da ’Yan’uwa

Ka Yi Koyi da Jehobah a Sha’aninka da ’Yan’uwa

“Kada ku yi shari’a bisa ga yadda abubuwa suke a ganin ido, amma ku yi shari’a bisa ga abin da yake daidai.”​—YOH. 7:24.

WAƘA TA 101 Mu Riƙa Hidima da Haɗin Kai

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Wane abin ban ƙarfafa ne Littafi Mai Tsarki ya ce game da Jehobah?

ZA KA so mutane su shari’anta ka domin launin fatarka ko yadda fuskarka take ko kuma domin siffar jikinka? Ba za ka so ba. Abin ban ƙarfafa ne sanin cewa Jehobah ba ya shari’anta mu bisa abin da mutane suke gani! Alal misali, sa’ad da Sama’ila ya ga ’ya’yan Jesse, ya fi mai da hankali ga siffarsu. Jehobah ya gaya wa Sama’ila cewa ɗaya cikin ’ya’yan Jesse zai zama sarki a Isra’ila. Amma wane ne a cikinsu? Sa’ad da Sama’ila ya ga Eliab ɗan fari na Jesse, sai ya ce, “Wannan da yake tsaye a gaban Yahweh lallai shi ne sarkin da Yahweh ya keɓe!” Eliab yana da siffa kamar sarki. “Amma Yahweh ya ce masa, ‘Kada ka dubi tsayinsa ko kyansa, don na ƙi shi.’ ” Wane darasi ne muka koya? Jehobah ya ƙara da cewa: “Mutum yakan duba yadda mutum yake daga waje, amma Yahweh yakan dubi zuciya ne.”​—1 Sam. 16:​1, 6, 7.

2. Kamar yadda aka nuna a Yohanna 7:​24, me ya sa bai kamata mu shari’anta mutum ta siffarsa ba? Ka ba da misali.

2 Da yake mu ajizai ne, mukan yi saurin shari’anta mutane don siffarsu. (Karanta Yohanna 7:24.) Amma ba ma sanin mutum da kyau ta siffarsa. Alal misali, ko likita da ya ƙware sosai ba zai san abin da ke damun majiyyaci ba ta wurin kallon sa kawai. Yana bukatar ya saurari majiyyacin sosai don ya san irin jinyar da ya taɓa yi da yadda yake ji game da yanayinsa ko kuma yadda yake ji a jikinsa. Likitan zai iya ce a ɗauki hoton cikin jikin majiyyacin don a san abin da ke damunsa. In ba haka ba, likitan zai ba majiyyacin maganin da bai dace ba. Hakazalika, ba za mu iya sanin ’yan’uwanmu sosai ba ta wajen kallon siffarsu. Wajibi ne mu fahimci halayensu. Hakika ba za mu iya sanin  abin da ke cikin zuciyar mutane yadda Jehobah yake yi. Amma, za mu iya yin iya ƙoƙarinmu don mu yi koyi da shi. Ta yaya?

3. Ta yaya labaran mutane da ke wannan talifin zai taimaka mana mu yi koyi da Jehobah?

3 Ta yaya Jehobah yake sha’ani da bayinsa? Yana saurarar su. Yana yin la’akari da yanayinsu da abubuwan da suka fuskanta a rayuwa kuma yana jin tausayin su. Za mu tattauna yadda Jehobah ya yi sha’ani da Yunana da Iliya da Hajaratu da kuma Lutu. Hakan zai taimaka mana mu ga yadda za mu iya yin koyi da Jehobah sa’ad da muke sha’ani da ’yan’uwanmu.

MU RIƘA SAURARAWA DA KYAU

4. Me ya sa za mu iya zato cewa Yunana ba shi da aminci?

4 Da yake ba mu fahimci yanayin Yunana sosai ba, muna iya ɗauka cewa ba shi da aminci. Jehobah ya umurce shi ya sanar da hukuncinsa a kan mutanen Nineba. Maimakon Yunana ya bi umurnin da aka ba shi, sai ya shiga jirgin ruwa da ke zuwa wani wuri dabam kuma “ya gudu daga gaban Yahweh.” (Yona 1:​1-3) Da a ce kai ne, za ka ba Yunana wata damar yin biyayya ga Jehobah? Wataƙila ba za ka yi hakan ba. Amma Jehobah ya ga ya dace ya sake ba Yunana wani zarafi.​—Yona 3:​1, 2.

5. Mene ne ka koya game da Yunana daga kalaminsa da ke Yona 2:​1, 2, 9?

5 Addu’ar da Yunana ya yi ta nuna abin da ke cikin zuciyarsa. (Karanta Yona 2:​1, 2, 9.) Babu shakka, Yunana ya yi addu’a ga Jehobah sau da yawa. Amma addu’ar da ya yi sa’ad da yake cikin kifi ta taimaka mana mu san halayensa masu kyau. Furucinsa ya nuna cewa shi mai sauƙin kai ne, mai nuna godiya kuma yana shirye ya yi biyayya ga Jehobah. Shi ya sa Jehobah bai mai da hankali ga kuskuren Yunana ba. Maimakon haka, ya amsa addu’arsa kuma ya ci gaba da zama annabi!

Idan mun san yadda mutum yake ji, hakan zai sa mu riƙa mutunta shi (Ka duba sakin layi na 6) *

6. Me ya sa ya dace mu riƙa saurarawa sosai?

6 Idan muna so mu riƙa saurarawa sosai, muna bukatar mu kasance da sauƙin kai da haƙuri. Hakan ya dace don dalilai uku. Na farko, zai hana mu kasancewa da ra’ayin da bai dace ba game da mutane. Na biyu, zai sa mu san yadda ’yan’uwanmu suke ji da kuma muradinsu, kuma hakan zai taimaka mana mu riƙa jin tausayin su. Na uku, idan muka bar  ɗan’uwanmu ya faɗi ra’ayinsa, hakan zai taimaka masa ya fahimci yadda yake ji. A wasu lokuta, mutum ba ya sanin yadda yake ji sai ya gaya wa mutane. (K. Mag. 20:5) Wani dattijo a Asiya ya ce: “Akwai lokacin da na yi magana kafin in fahimci ainihin batun. Na gaya ma wata ’yar’uwa cewa ya kamata ta kyautata kalaminta a taro. Amma daga baya sai na ji cewa karatu yana yi mata wuya kuma yin kalami ba ya mata sauƙi.” Yana da muhimmanci cewa kowane dattijo ya “ji” ainihin abin da ya faru kafin ya ba da shawara!​—K. Mag. 18:13.

7. Mene ne ka koya daga yadda Jehobah ya bi da Iliya?

7 Yana yi ma wasu ’yan’uwanmu wuya su faɗa yadda suke ji domin abin da ya taɓa faruwa da su ko kuma al’adarsu. Ta yaya za mu sa ya yi musu sauƙi su gaya mana yadda suke ji? Ka tuna da yadda Jehobah ya bi da Iliya sa’ad da ya gudu don Jezebel tana so ta kashe shi. Iliya ya yi kwanaki kafin ya gaya wa Jehobah yadda yake ji. Jehobah kuma ya saurare shi sosai. Sai ya ƙarfafa Iliya kuma ya ba shi aiki mai muhimmanci da zai yi. (1 Sar. 19:​1-18) Yana iya ɗaukan lokaci kafin ’yan’uwanmu su saki jiki su gaya mana yadda suke ji, sai sun yi hakan ne za mu fahimci ainihin yadda suke ji. Idan mun yi koyi da Jehobah ta wajen kasancewa da haƙuri, za su amince da mu daga baya. Sa’an nan idan sun shirya su gaya mana yadda suke ji, ya kamata mu saurare su sosai.

MU SAN ’YAN’UWANMU SOSAI

8. Kamar yadda aka nuna a Farawa 16:​7-13, ta yaya Jehobah ya taimaka wa Hajaratu?

8 Hajaratu baiwar Saratu ta yi wawanci bayan ta zama matar Ibrahim. Hajaratu ta yi juna biyu kuma ta soma raina Saratu don ba ta da yara. Yanayin ya yi muni sosai har Saratu ta kori Hajaratu. (Far. 16:​4-6) Domin mu ajizai ne, muna iya ganin cewa Hajaratu mai fahariya ce, saboda haka abin da Saratu ta yi mata ya dace. Amma ba haka Jehobah ya ɗauki batun ba. Jehobah ya tura mala’ikansa ya je ya same ta. Sa’ad da mala’ikan ya same ta, sai ya taimake ta ta canja halinta kuma ya albarkace ta. Hajaratu ta fahimci cewa Jehobah yana kallon ta kuma ya san yanayinta. Hakan ya burge Hajaratu kuma ta ce Jehobah “Allah ne mai gani.”​—Karanta Farawa 16:​7-13.

9. Me ya sa Allah ya yi la’akari da Hajaratu?

9 Mene ne Jehobah ya lura game da Hajaratu? Jehobah ya san yanayin Hajaratu sosai da abin da ta fuskanta a dā. (K. Mag. 15:3) Hajaratu ’yar Masar ce da ke zama da Ibraniyawa. Wataƙila a wasu lokuta tana ji kamar ita baƙuwa ce. Mai yiwuwa ta yi kewar iyalinta da kuma ƙasarsu. Ba ita ce kaɗai matar Ibrahim ba. Akwai lokacin da wasu maza masu aminci suke auran mata da yawa. Amma hakan ba ainihin nufin Jehobah ba ne. (Mat. 19:​4-6) Shi ya sa hakan ya jawo matsaloli sosai kamar kishi da kuma ƙiyayya a iyali. Ko da yake Jehobah ya san cewa abin da Hajaratu ta yi bai dace ba, ya yi la’akari da ita sosai kuma ya nuna mata alheri.

Ka san ’yan’uwanka sosai (Ka duba sakin layi na 10-12) *

10. Me zai taimaka mana mu san ’yan’uwanmu sosai?

10 Za mu iya yin koyi da Jehobah ta wajen yin ƙoƙari mu fahimci juna. Zai dace mu san ’yan’uwanmu sosai. Ka tattauna da su kafin a soma taro da kuma bayan hakan. Ka riƙa fita wa’azi da su kuma idan zai yiwu ka gayyace su gidanka don ku ci  abinci tare. Idan ka yi hakan, za ka yi mamaki cewa ’yar’uwa da kake zato cewa ba ta da fara’a, tana jin kunya ne. Kuma ɗan’uwa da kake zato yana son abin duniya yana da karimci. Ƙari ga haka, iyalin da ke yawan makara zuwa taro suna fuskantar tsanantawa. (Ayu. 6:29) Hakika, bai kamata mu zama masu shishigi a “al’amuran” mutane ba. (1 Tim. 5:13) Amma, ya dace mu koyi wani abu game da ’yan’uwanmu da abubuwan da suka fuskanta a rayuwa. Hakan zai taimaka mana mu fahimce su sosai.

11. Me ya sa ya dace dattawa su san ’yan’uwansu sosai?

11 Ya dace dattawa musamman su san ’yan’uwansu sosai. Ka yi la’akari da misalin wani ɗan’uwa mai suna Artur wanda ya yi hidimar mai kula da da’ira. Shi da wani dattijo sun ziyarci wata ’yar’uwa da take jin kunya. Artur ya ce: “Ta gaya mana cewa mijinta ya rasu bayan ’yan shekaru da suka yi aure. Ta koya wa yaranta mata biyu su ƙaunaci Jehobah duk da matsaloli da ta fuskanta a rayuwa. Yanzu ba ta gani sosai kuma hakan yana sa ta baƙin ciki. Duk da haka, tana ƙaunar Jehobah sosai kuma tana da bangaskiya. Mun lura cewa za mu iya koyan darasi mai kyau daga wannan ’yar’uwar.” (Filib. 2:3) Wannan mai kula da da’ira yana yin koyi da Jehobah. Jehobah ya san bayinsa da kuma matsalolin da suke fuskanta. (Fit. 3:7) Dattawan da suka san ’yan’uwansu da kyau za su iya taimaka musu.

12. Ta yaya ’yar’uwa Yip Yee ta amfana ta wajen sanin wata ’yar’uwa a ikilisiyarsu sosai?

12 Idan ka yi ƙoƙari ka san ɗan’uwan da jininku ba ya haɗuwa, za ka riƙa mutunta shi. Alal misali, wata ’yar’uwa mai suna Yip Yee da take zama a Asiya ta ce: “Wata ’yar’uwa a ikilisiyarmu tana ɗaga murya sosai sa’ad da take magana. Sai na soma ji cewa ba ta da tarbiyya. Amma, sa’ad da muka fita wa’azi tare, ta gaya mini cewa a dā tana taya iyayenta sayar da kifi a kasuwa. Kuma takan ɗaga murya don ta kira kwastomomi.” Yip Yee ta daɗa cewa: “Na koyi cewa don na fahimci ’yan’uwana, ina bukatar in san su sosai.” Muna bukatar mu ƙoƙarta mu san ’yan’uwanmu sosai. Idan muka bi shawarar Littafi Mai Tsarki cewa mu ƙaunaci dukan ’yan’uwanmu, muna yin koyi da Jehobah, wanda yake ƙaunar “dukan mutane.”​—1 Tim. 2:​3, 4; 2 Kor. 6:​11-13.

 KA NUNA TAUSAYI

13. Kamar yadda Farawa 19:​15, 16 suka nuna, mene ne mala’iku suka yi sa’ad da Lutu ya ci gaba da jan jiki, kuma me ya sa?

13 Lutu ya yi jinkirin bin umurnin Jehobah a lokaci mai muhimmanci. Mala’iku biyu sun ziyarci Lutu kuma suka ce shi da iyalinsa su fita daga birnin Saduma. Sun ce: “Za mu halaka wurin nan.” (Far. 19:​12, 13) Amma har washegari, Lutu da iyalinsa ba su fita daga birnin ba. Sai mala’ikun suka sake yi wa Lutu gargaɗi. Amma Lutu “ya yi ta jan jiki.” Muna iya gani cewa Lutu bai ɗauki umurnin Jehobah da muhimmanci ba. Amma Jehobah ya ci gaba da taimaka masa. Mala’ikun sun riƙe hannun Lutu da iyalinsa kuma suka fitar da su daga birnin. Me ya sa? Domin “Yahweh ya yi masa jinƙai.”​—Karanta Farawa 19:​15, 16.

14. Me ya sa Jehobah ya ji tausayin Lutu?

14 Jehobah ya ji tausayin Lutu don dalilai da yawa. Wataƙila Lutu yana jin tsoron mutanen da ke wajen birnin, shi ya sa bai yi saurin barin gidansa ba. Ban da haka, akwai wasu haɗarurruka. Mai yiwuwa Lutu ya ji cewa sarakuna biyu sun faɗi cikin ramukan mān kwalta da ke kusa da wani kwari. (Far. 14:​8-12) A matsayin Lutu na mahaifi da magidanci wataƙila ya damu da iyalinsa. Ƙari ga haka, Lutu mai arziki ne sosai, mai yiwuwa yana da gida mai kyau a Saduma. (Far. 13:​5, 6) Hakika, bai kamata waɗannan abubuwan su sa Lutu jinkirin yin biyayya ga Jehobah ba. Jehobah bai mai da hankali ga kuskuren Lutu ba, amma ya ɗauke shi a matsayin “mutum mai adalci.”​—2 Bit. 2:​7, 8.

Idan muka saurari mutane da kyau, za mu riƙa jin tausayin su (Ka duba sakin layi na 15-16) *

15. Maimakon mu riƙa sūkar mutane, me ya kamata mu yi?

15 Maimakon ka riƙa shari’anta mutum, ka yi ƙoƙari ka fahimci yadda yake ji. Wata ’yar’uwa mai suna Veronica a Turai ta yi ƙoƙari ta yi hakan. Ta ce: “A kowane lokaci, wata ’yar’uwa tana yawan baƙin ciki. Ta ci gaba da ware kanta. A wasu lokuta, ina jin tsoron yi mata magana.  Amma sai na yi tunani cewa ‘idan ina yanayinta, zan bukaci abokiya.’ Sai na tsai da shawara in tambaye ta yadda take ji. Kuma ta soma gaya min dukan matsalolinta! Yanzu na fi fahimtar ta sosai.”

16. Me ya sa ya kamata mu roƙi Jehobah ya taimaka mana mu riƙa jin tausayin mutane?

16 Jehobah ne kaɗai ya fi fahimtar mu. (K. Mag. 15:11) Saboda haka, ka roƙe shi ya taimaka maka ka riƙa ɗaukan mutane yadda yake yi kuma ka san yadda za ka riƙa jin tausayinsu. Addu’a ta taimaka wa wata ’yar’uwa mai suna Anzhela ta riƙa jin tausayin mutane. Yana da wuya a yi cuɗanya da wata ’yar’uwa a ikilisiyar da Anzhela take. Ta ce: “Da zai yi sauƙi in soma sūkar ’yar’uwar kuma in guje ta. Amma na roƙi Jehobah ya taimaka mini in ji tausayin wannan ’yar’uwar.” Jehobah ya amsa addu’ar Anzhela ne? Ta ƙara da cewa: “Sai muka fita wa’azi tare kuma muka yi magana na dogon lokaci. Sai na saurare ta sosai. Yanzu ina ƙaunarta, kuma na ƙuduri niyya in taimaka mata.”

17. Me ya kamata mu ƙuduri niyyar yi?

17 Ba zai dace ka zaɓi ’yan’uwa da za ka riƙa jin tausayin su ba, duk da cewa wasu cikinsu suna fama da matsalolin da suka jawo wa kansu. Yunana da Iliya da Hajaratu da kuma Lutu sun fuskanci matsaloli, kuma sau da yawa, su suka jawo wa kansu matsalolin. Hakika, dukanmu mukan jawo wa kanmu matsaloli a wasu lokuta. Saboda haka, ya dace da Jehobah ya gaya mana mu riƙa jin tausayin juna. (1 Bit. 3:8) Idan muka yi biyayya ga Jehobah, za mu daɗa sa ’yan’uwa a dukan duniya su kasance da haɗin kai. Saboda haka, sa’ad da muke cuɗanya da juna, bari mu yi iya ƙoƙarinmu mu riƙa yin koyi da Jehobah ta wajen nuna tausayi.

WAƘA TA 87 Ku Zo Mu Sami Ƙarfafa!

^ sakin layi na 5 Da yake mu ajizai ne, mukan yi saurin shari’anta mutane da kuma muradinsu. Amma Jehobah “yakan dubi zuciya.” (1 Sam. 16:7) A wannan talifin, za a tattauna yadda Jehobah ya taimaka wa Yunana da Iliya da Hajaratu da kuma Lutu. Kuma hakan zai taimaka mana mu yi koyi da Jehobah a yadda muke sha’ani da ’yan’uwa.

^ sakin layi na 52 BAYANI A KAN HOTO: Wani ɗan’uwa tsoho ya damu don wani matashi ya zo taro a makare, amma daga baya ya ji cewa ɗan’uwan ya yi hatsari ne.

^ sakin layi na 54 BAYANI A KAN HOTO: Da farko, wani mai kula da rukunin wa’azi yana ganin cewa wata ’yar’uwa ba ta da fara’a, amma ya fahimci cewa tana jin kunya kuma ba ta sakewa da mutanen da ba ta sani ba sosai.

^ sakin layi na 56 BAYANI A KAN HOTO: Sa’ad da wata ’yar’uwa ta san wata sosai, ta ga cewa ʼyar’uwar tana da fara’a fiye da yadda take zato a lokacin da suka haɗu a Majami’ar Mulki.