Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Yadda Za Mu Sami ’Yanci na Gaske

Yadda Za Mu Sami ’Yanci na Gaske

“Idan Ɗan ya ’yantar da ku za ku sami ’yanci na gaske.”​—YOH. 8:36.

WAƘOƘI: 54, 36

1, 2. (a) Me ya nuna cewa mutane da yawa suna so su sami ’yanci? (b) Mene ne hakan yake jawowa?

A YAU, mutane a faɗin duniya suna yawan magana game da samun ’yanci da kuma daidaituwar al’umma. Mutane a ƙasashe da yawa suna so su sami ’yanci daga cin zarafi da nuna bambanci da kuma talauci. Wasu kuma suna son ’yancin yin magana da zaɓi da kuma zama a inda suke so. Babu shakka, mutane a ko’ina suna so su sami ’yanci.

2 Amma biyan waɗannan bukatun ba shi da sauƙi. Saboda haka, mutane suna yawan yin zanga-zanga da juyin mulki. Shin hakan na biyan bukatunsu? A’a. Maimakon haka, yana jawo matsaloli da kuma kashe-kashe. Hakan na nuna cewa abin da Sarki Sulemanu ya faɗa a cikin Littafi Mai Tsarki gaskiya ne. Ya ce: “Waɗansu sukan sami mulki, waɗansu kuwa su sha wuya a ƙarƙashinsu.”​—M. Wa. 8:​9, Littafi Mai Tsarki.

3. Me ya kamata mu yi don mu sami farin ciki da kuma gamsuwa?

3 Jehobah ya hure Yaƙub ya faɗi abin da zai sa mu sami ’yanci na gaske da kuma gamsuwa. Ya ce: “Mutumin da ya  mai da hankalinsa wajen bincike cikakkiyar koyarwar nan wadda ita ce mai kawo ’yanci, za a sa masa albarka cikin dukan abin da yake yi.” (Yaƙ. 1:25) Jehobah wanda shi ne ya tanadar da wannan cikakkiyar koyarwar ya san abin da ya fi dacewa da mutane don su yi farin ciki kuma su samu gamsuwa. Ya ba Adamu da Hauwa’u dukan abubuwan da suke bukata, har da ’yanci don su yi farin ciki.

LOKACIN DA ’YAN ADAM SUKE DA ’YANCI NA GASKE

4. Wane irin ’yanci ne Adamu da Hauwa’u suke da shi? (Ka duba hoton da ke shafi na 3.)

4 Idan mun karanta littafin Farawa, za mu ga cewa Adamu da Hauwa’u suna da irin ’yancin da mutane da yawa suke mafarkin samu a yau. Suna da duk abubuwan da suke bukata, ba sa jin tsoron kome kuma babu wanda ke nuna musu bambanci. A lokacin, ba sa rashin lafiya da mutuwa, suna da aiki da kuma abinci. (Far. 1:​27-29; 2:​8, 9, 15) Amma hakan yana nufin cewa Adamu da Hauwa’u suna da ’yancin yin duk abin da suka ga dama? Bari mu ga amsar.

5. Mene ne samun ’yanci ba ya nufi? Ka bayyana.

5 Mutane da yawa a yau suna ganin cewa samun ’yanci na gaske yana nufin samun zarafin yin duk abin da suka ga dama, ko da wane irin sakamako yin hakan zai kawo. Littafin nan The World Book Encyclopedia ya ce ’yanci yana nufi “zarafin yin zaɓi da kuma yin abin da muka zaɓa.” Amma ya ƙara da cewa: ‘A fannin shari’a, mutane suna da ’yanci idan hukuma ba ta kafa dokokin da suka danne hakkinsu ba.’ Hakan yana nufin cewa wajibi ne a hana mutane yin wasu abubuwa don kowa ya sami ’yanci. Amma ga wata tambaya: Wane ne ya isa ya gaya mana abin da ya dace da wanda bai dace ba?

6. (a) Me ya sa Jehobah ne kaɗai yake da ’yancin yin abin da ya ga dama? (b) Wane irin ’yanci ne ’yan Adam za su iya samu, kuma me ya sa?

6 Idan ya zo ga batun ’yanci, ya kamata mu tuna cewa Jehobah ne kaɗai yake da cikakken ’yancin yin duk abin da ya ga dama. Me ya sa? Domin shi ne Mahaliccin dukan abu da kuma Maɗaukakin Sarki. (1 Tim. 1:17; R. Yar. 4:11) Sarki Dauda ya yi amfani da furuci mai ban sha’awa sa’ad da yake kwatanta matsayin Jehobah. (Karanta 1 Tarihi 29:​11, 12.) Akasin haka, dukan halittu a sama da duniya ba su da cikakken ’yancin yin dukan abin da suka ga dama. Dole ne su san cewa Jehobah ne yake da ikon kafa doka a kan abin da ya dace da kuma abin da suke bukatar su yi. Abin da Jehobah ya yi da mutane ke nan tun lokacin da ya halicce su.

7. Waɗanne abubuwa ne muke yi da ke sa mu jin daɗin rayuwa?

7 Ko da yake Adamu da Hauwa’u suna da ’yanci sosai amma ’yancinsu na da iyaka. An halicce su da wasu abubuwan da ya wajaba su yi. Alal misali, sun san cewa idan suna so su ci gaba da rayuwa, dole ne su yi numfashi, su ci abinci, su yi barci da dai sauransu. Babu shakka, ba su ɗauka cewa yin waɗannan abubuwan sun danne musu ’yanci ba. Jehobah ya tabbatar da cewa ya sa su ji daɗin yin waɗannan abubuwan. (Zab. 104:​14, 15; M. Wa. 3:​12, 13) Dukanmu muna jin daɗin shaƙar iska mai daɗi da cin abinci mai ɗanɗano da  kuma yin barci. Yin abubuwan nan na da sauƙi sosai. Hakika, haka Adamu da Hauwa’u suka ji.

8. Wane umurni ne Allah ya ba Adamu da Hauwa’u, kuma me ya sa?

8 Jehobah ya umurci Adamu da Hauwa’u kai tsaye cewa su haifi ’ya’ya su cika duniya kuma su kula da ita. (Far. 1:28) Wannan umurnin ya hana su samun ’yanci ne? A’a! Jehobah ya ba da umurnin ne don ya sa mutane su cika nufinsa. Yana so su mayar da duniya gabaki ɗaya aljanna domin su da ’ya’yansu kamiltattu su zauna a cikinta har abada. (Isha. 45:18) A yau, ba laifi ba ne idan mutane sun zaɓi su yi aure, ko ba sa so su yi aure ko kuma sun yi aure amma ba sa son haihuwa. Mutane suna yin aure da haifan yara duk da ƙalubalen da yin hakan ke jawowa. (1 Kor. 7:​36-38) Me ya sa? Domin suna jin daɗin yin waɗannan abubuwan. (Zab. 127:3) Da a ce Adamu da Hauwa’u ba su karya dokar Allah ba, da sun ji daɗin aurensu da iyalinsu har abada.

YADDA ’YAN ADAM SUKA RASA ’YANCI NA GASKE

9. Me ya sa dokar da ke Farawa 2:17 ta dace?

9 Jehobah ya ba Adamu da Hauwa’u wata doka kuma ya gaya musu sakamakon karya dokar. Ya ce: “Daga itace mai kawo sanin nagarta da mugunta ba za ka ci ba, gama a ranar da ka ci daga itacen nan lallai za ka mutu.” (Far. 2:17) Suna bukatar dokar kuwa? Ta dace da su kuwa? Dokar ta hana Adamu da Hauwa’u samun ’yanci ne? A’a. Mutane da yawa da suke binciken Littafi Mai Tsarki sun ce dokar ta dace sosai. Alal misali, ɗaya cikinsu ya ce: “Dokar Allah da ke [Farawa 2:​16, 17] ta nuna cewa Allah ne kaɗai ya san abin da ya dace . . . da mutane kuma Allah ne kaɗai ya san abin da bai dace . . . da su ba. Idan mutane suna so su ji daɗin ‘abu mai kyau,’ dole ne su dogara ga Allah kuma su yi masa biyayya. Idan sun yi rashin biyayya, su ne za su yanke wa kansu shawara a kan abu mai kyau . . . da marar kyau.” Babu shakka, wannan abu ne da zai yi wa mutane wuya sosai.

Zaɓin da Adamu da Hauwa’u suka yi ya jawo mummunan sakamako! (Ka duba sakin layi na 9-12)

10. Me ya sa ’yancin yin zaɓi da kuma ’yancin zaɓan abu mai kyau da marar kyau suka bambanta?

10 Sa’ad da mutane da yawa a yau suka karanta dokar da Jehobah ya ba Adamu da Hauwa’u, suna tunani cewa Allah ya hana su yin abin da suka ga dama. Amma ba su san cewa akwai bambanci tsakanin kasancewa da ’yancin yin zaɓi da kuma samun ’yancin sanin abu mai kyau da marar kyau ba. Adamu da Hauwa’u suna da ’yancin zaɓar yin biyayya ga Allah ko a’a. Amma Jehobah ne kaɗai yake da ikon faɗin abu mai kyau da marar kyau. “Itace mai kawo sanin nagarta da mugunta” da ke lambun Adnin ya tabbatar da hakan. (Far. 2:9) Ya kamata mu san cewa ba a kowane lokaci muke sanin sakamakon zaɓin da muka yi ba. Ƙari ga haka, ba za mu iya sanin ko sakamakon zai zama mai kyau ko marar kyau ba. Shi ya sa muke yawan ganin mutane sun yi zaɓi da kyakkyawar niyya, amma sai ya jawo wahala da rikici ko tashin hankali. (K. Mag. 14:12) Babu shakka, ’yan Adam suna da kasawa. Jehobah ya ba Adamu da Hauwa’u dokar don ya koya musu cewa idan suna so su sami ’yanci na gaske, wajibi ne su yi masa biyayya. Wane zaɓi ne suka yi?

11, 12. Me ya sa zaɓin da Adamu da Hauwa’u suka yi ya kawo mummunan sakamako? Ka ba da misali.

 11 Abin baƙin ciki shi ne cewa Adamu da Hauwa’u sun yi rashin biyayya. Hauwa’u ta amince da alkawarin da Shaiɗan ya yi cewa: “Idanunku za su buɗe. Za ku kuwa zama kamar Allah, masu sanin nagarta da mugunta.” (Far. 3:5) Shin bayan Adamu da Hauwa’u sun karyar dokar Allah, sun sami ’yancin da suke nema? A’a. Bayan haka, sun lura cewa karya dokar ta jawo musu mummunan sakamako. (Far. 3:​16-19) Me ya sa? Domin Jehobah bai ba mutane ’yancin zaɓan abu mai kyau da marar kyau ba.​—Karanta Karin Magana 20:24 da Irmiya 10:23.

12 Alal misali, idan matuƙin jirgin sama yana so ya kai inda za shi, wajibi ne ya bi hanyar da aka amince ya bi. Matuƙin jirgin sama yana yin amfani da na’urorin da aka tanadar a jirgin wajen sadawa da mutumin da ke kula da jigilar jirgin a ƙasa. Matuƙin zai yi hatsari idan bai bi umurnin mai kula da jirgin ba, amma ya bi hanyar da ya ga dama. Hakazalika, Adamu da Hauwa’u sun so su yi abin da suka ga dama. Sun ƙi bin umurnin da Allah ya ba su. Wane sakamako suka samu? Sun sami mummunan sakamako, wato sun jawo wa kansu da ’ya’yansu zunubi da kuma mutuwa. (Rom. 5:12) Adamu da Hauwa’u ba su sami ’yancin da suke nema ba. Maimakon haka, sun rasa ’yanci na gaske da Jehobah ya ba su.

YADDA ZA MU SAMI ’YANCI NA GASKE

13, 14. Ta yaya za mu sami ’yanci na gaske?

13 Wasu mutane suna ganin cewa samun ’yancin yin duk abin da suka ga dama zai fi dacewa. Hakan gaskiya ne kuwa? Ko da yake idan muna da ’yanci, za mu amfana. Amma ka yi tunanin yadda rayuwa za ta kasance da a ce ’yan Adam ba su da dokokin da suke bi? Littafin nan The World Book Encyclopedia ya ce kowace al’umma tana da dokoki masu wuya domin suna kāre mutane kuma ba sa barin su su yi abin da suka ga dama. Hakan ba abu mai sauƙi ba ne. Shi ya sa akwai lauyoyi da  alƙalai da yawa da suke bayyana dokokin kuma suke nuna yadda za a aiwatar da su.

14 Yesu ya bayyana yadda za mu iya samun ’yanci na gaske. Ya ce: “In dai kun ci gaba da riƙe koyarwata, ku almajiraina ne na gaske. Sa’an nan za ku san gaskiya, gaskiyar kuwa za ta ba ku ’yanci.” (Yoh. 8:​31, 32) Yesu ya ce yin abubuwa biyu za su sa mu sami ’yanci na gaske. Na ɗaya, riƙe koyarwarsa. Na biyu kuma zama almajiransa. Yin hakan zai sa mu sami ’yanci na gaske. Amma za mu sami ’yanci daga me? Yesu ya ci gaba da cewa: “Duk mai yin zunubi bawan zunubi ne. . . . Idan Ɗan ya ’yantar da ku za ku sami ’yanci na gaske.”​—Yoh. 8:​34, 36.

15. Me ya sa ’yancin da Yesu ya ambata ne zai sa mu sami “’yanci na gaske”?

15 Babu shakka, ’yancin da Yesu ya yi wa almajiransa alkawari, ya fi wanda mutane da yawa suke nema a yau. Sa’ad da Yesu ya ce: “Idan Ɗan ya ’yantar da ku za ku sami ’yanci na gaske,” yana magana ne game da ’yanci daga zunubi. Zunubi yana sa mu yi abin da muka san cewa bai dace ba ko kuma yana hana mu yin abin da za mu iya yi. Hakan ya sa mun zama bayi ga zunubi. A sakamako, muna fuskantar ɓacin rai da wahala da kuma mutuwa. (Rom. 6:23) Manzo Bulus ya yi baƙin ciki sosai don shi bawa ne ga zunubi. (Karanta Romawa 7:​21-25.) Sai lokacin da Allah ya cire zunubi gabaki ɗaya ne za mu sami irin ’yancin da Adamu da Hauwa’u suke da shi a dā, wato ’yanci na gaske.

16. Me zai taimaka mana mu sami ’yanci na gaske?

16 Furucin nan da Yesu ya yi cewa “in dai kun ci gaba da riƙe koyarwata,” yana nufin cewa idan muna so mu sami ’yanci, dole ne mu bi wasu dokoki. Waɗanne dokoki ke nan? Da yake mun yi alkawarin bauta wa Allah, mun sadaukar da kanmu kuma mun yarda mu bi dokokin da Yesu ya kafa wa almajiransa. (Mat. 16:24) Yesu ya yi alkawari cewa hadayar da ya yi a madadinmu, za ta sa mu sami ’yanci na gaske a nan gaba.

17. (a) Me ya kamata mu yi don mu riƙa farin ciki sosai kuma mu sami gamsuwa? (b) Me za mu tattauna a talifi na gaba?

17 Me ya kamata mu yi idan muna so mu riƙa farin ciki sosai kuma mu sami gamsuwa? Wajibi ne mu bi koyarwar Yesu da yake mu mabiyansa ne. Yin hakan zai sa mu sami ’yanci daga zunubi da kuma mutuwa a nan gaba. (Karanta Romawa 8:​1, 2, 20, 21.) A talifi na gaba, za mu ga yadda za mu yi amfani da ’yancin da muke da shi a hanyar da ta dace. Hakan zai sa mu ɗaukaka Jehobah, Allahn da ke ba da ’yanci na gaske har abada.